Page:6
by @maidambu41
SANIN GAIBU...!!
_Sai Allah_
ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023
*Mai_Dambu*
Page:06
Bayan fitar Kabiru daukar wayarta tayi ta shiga niman layin mahaifinta. Bugu biyu yayi ya dauka, "Baffa!" "Na'am Noor!" "Yanzu aka zo min da wani al'amarin da ya shafi mutuwar Mansurah" "Alhamdulillahi, ki saurare ni maza kar ki yi kasa a gwiwa waɗanda suka aikata haka sun san me suke yi ba jahilai ba ne, don haka kowacce kankantar hujja boye ta zasu yi." Mikewa tayi ta fita tare da budar kasa, bata yi wasa da wannan damar ba, kai tsaye ɗakinta ta nufa domin nan dakin hutawar ne, alkyabar ta dauka ta nufi heeram, bangaren Sultan Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari. Duk inda ta gifta zubewa bayi suke tare da mika mata gaisuwa, yadda zaka fahimci tana da mugun matsayi a cikin Masarautar. Bangaren Sultan yafi kusan kowani bangare girma da tsaro, domin bayan fadawa akwai sojoji da civil defense, akwai mopol, bata yarda ta bi kofar baya da yake cikin gidan ba, so take tayi amfani da damar ta, wanda ita kadai tabarwa kanta sanin shi, yadda ta sauya ba zaka tab'a cewa akwai abin da yake damunta ba. Yadda ta sake tana amsa gaisuwar, "A hanyar isa farfajiyar heeram suka yi kicibis da Hajiya Turai, ita ce matar Sultan ta uku. " Kallon juna suka yi kowacce da abun da ranta yake kitsima mata, musamman ita Hajiya Turai da take tare da bayi da kuyanginta suna take mata baya. Duk da kallon farincikin da takewa Sultanah Badi'atul Noor, sai dai har yau tana mamakin girman halinta. Zubewa bayin Hajiya Turai suka yi suna "Barka da warhaka Giwar mata, Barka da maraici magajiyar Sulu gambari." Cikin wani irin yanayi na nuna ita din ce suke gaisarwa ta juyar da kanta izuwa gare su ta ce. "Allah ya albarkaci rayuwar ku, Turai da fatan kina lafiya" "ke baki da damuwa ne? Kin san bana kaunarki amma kika matsa min dole sai kin shiga damuwa ta, ko kunya baki ji ba, kin dibo jiki zaki tafi wurin Sultan da yace baya kaunar ganinki a bangaren shi." Wani irin blush tayi tana kara daidaita nutsuwar ta. Matsawa tayi sosai suna fuskantar juna ta ce. "Ko shi Abdulrahman bai da ikon korata idan na shiga idan kin Musa muje ki gani" ta fasa ƙasa ƙasa yadda bayin da suke bayan Hajiya Turai ba zasu ji abin da yake fada ba. Sannan ta gyara alkyabar ta, tayi gaba abinta tana murmushin karfin hali. Gidan sarauta sai ka iya takun ka, sai ka iya adana fushin ka, sai ka iya makirci sai ka iya kissa da kisisina. Bude mata kofar suka yi Hajiya Turai ta bi bayanta da idanu, an dadde ana ruwa kasa yana shanyewa, tun kawo ta gidan kusan shekaru goma sha biyar har yau bata taɓa ganin macen da ta iya wanka da ado ban mamaki kamar Sultanah ba, kuma har kwanan gobe babu wacce take irin wankar ta, karya ne babu abin da zuciyarta ya gaya mata kenan, shi yasa ta tsane ta mugun tsaya, tsabar iyayi irin na Badi'atul Noor bata yawo da bayinta ko daya. Wai a haka ma don Sultanah Babba tana tsaye kenan amma baki daya Sultan Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari bai da nutsuwa matukar abin da ya shafi Sultanah karama ce, kwafa tayi ta nufi hanyar cikin gidan ta kofar baya, leshen jikinta ruwan makuba ne, amma matar nan dan tsiya ta haɗa mishi golden alkyabar wanda ya dace da ingancin shigar jikinta, ga wani fitinannen kanshi me sanyin dadi da yake tashi a jikinta, "Mtseeeeeew tsohuwar banza ta tsufa amma kullum zuciyarta na yara ne" kwafa ta kuma yi, bayinta suka kalli juna, suna kunshe dariyar su.
Da sallama ta shiga babban falon shi, yana zaune a kasa, Sultanah Babba tana saman kujeran, Hajiya Bariyyah tana zaune a kasa, tayi kasa da kan ta. Gefe guda Hajiya Mariyah tana gefen shi, Amaryan shi. Sai Hajiya Suhailah, gabanta ne ya fadi Hajiya Suhailah Matar wan Sultan ne Sultan Abdulsamad Dan Aliyu sulu gambari, gefe guda Alhaji Marwan ne mahaifin Ummul Mansurah. Ji take kamar zuciyarta zata fashe,.asalima kamar ta juya amma kuma ma hakan zai iya janyo cece ku ce, wani malalacin murmushi Sultanah Babba tayi tana cewa. "Uwar dan gata,." "Hmmm, Sultanate masu abu da abin su kura da kallabin kitse, Allah ya kawo mu zamanin da ake yaki da gaskiya" "Aikuwa an zunguro inda ba za a iya ba." Wani munafikin murmushi Sultanah karama tayi, tana me jiman wuri ta zauna a saman kujeran, kamar yadda Sultanate ta zauna wato Sultanah Babba ita suke kira Sultanate. Kallon Badi'atul Noor Alhaji Marwan yayi. Yana mata alamu da ƙasa, domin shi kan Sultan ya kasa kome sai bin su yake da idanu, musamman yadda suke yab'a mata magana kuma murmushi take har tana washe baki, ba zaka tab'a cewa maganar su yana mata zafi ba, kallon Sultan Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari tayi cikin murmushi ta ce mishi." Allah ya huci zuciyar jan gwarzo ina bukatar ganawa da kai." A duk lokacin da ta ambace shi da jan gwarzo wallahi ji yake kamar ta dauke shi ta cilla shi wata nahiyar da babu kowa sai shi, kan shi sai yaji yayi rantalel, karkace kai tayi cikin iya kirsa ta fara wurga mishi kirari. "Wannan shine Sultan Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari,
Jan wuya
Zakin talakawa
Dodon azzalumai
Lange Lange me kamar bazai je ba
Nan gani nan bari dumamen mayya
Kududdufin barkono iyakacin mace gwiwa
Kaga Abba na Abubakar da Umar, Uban Rumaisah da Zakiyyah, Baban Aliyu Abu turab me takama da Hasbuballahu.
Rankwatakwale ba shiga jirgin ba inda kan zai zauna
Barka da Rana Mijina" jin shi yayi duk wani fushi da b'acin ran da suke tsakanin su ya kare, wato Ubangiji ya baka macen da zata kashe ka da takaici ta kuma rayaka da annashuwa arzikn ne. Kallon Mahaifiyar shi yayi da sauran jama'ar falon, ya mike yana faɗin "bari na gana da ita." Babu wanda ya ce mishi cikanka domin matukar Badi'atul Noor tana wuri wallahi babu wanda ya isa da shi. Yana gaba ta juya cikin murmushi ta ce musu. "Ba fada damu bane kwana mita." Daga haka ta wuce falon shi na musamman. Tana shiga ta same shi zaune yana wani haɗe rai, zubewa tayi a gaban shi, ta zuba hannunta akan gwiwar ta. "tun ranar da abin ya faru har yau baka ce min kome ba, ko da minti goma baka bani domin na gaya maka yadda muka yi da Baba karami ba " ta fada tana me isa gaban shi, "akan me zan baki damar magana? Bayan nasan duk abin da zaki fada wanke danki zaki yi? Idan maganar Babana ne ya kawo ki muje can na yanke hukunci." "Sultan ina son na gaya maka ɗazun na samu wasu bayanai ne na mutanen da suka yi kisan." Kallonta yayi sosai kafin ya ce mata. "Domin kare Kanki da danki shi ne zaki daurawa wasu sharri?" "Don Allah ka yarda da ni wallah......" Ƙarar tamburar masarautar suka ji sai da gabanta ya fadi, zubur ta mike jikinta yana rawa kamar zata tashi sama ta fita daga cikin falon yana biye da ita, sarkin gida ne ya shigo da mugun gudu ya zube a gabanta. "Sultanah an kashe Kabirun Gajiyah" luuuuu ta tafi zata zube cikin zafin nama Sultan ya riko kafad'ar ta, ta koma jikin shi, damuwa ta mata yawa tashin hankali yana niman kassara ta, janye daga jikin shi, ta nufi kofar da sassarfa ta nufi bangaren ta. Koda ta isa ga gawar Kabiru kwance cikin jini, window dakin Abu turab an balle shi, da alamu watsawa window ruwan battery aka yi, zubewa tayi a gaban gawar Yaron tayi, abin da kakar take gudu kenan. Juyawa tayi cikin matsanancin fushi da b'acin rai ta ce. "A tsare duk wani da me rai da yake numfashi a cikin gidan nan" "Babu wanda zaa tsare, da Abu turab ya kashe Mansurah cewa kika yi sharri ne bazai kashe ba, yanzu da kika saka a kashe dan mutane shi ne zaki fara borin kunya." A fusace ta juya tana kallon Sultanate da take maganar cikin fushi.Murmushi tayi sannan ta ce. "Ba laifi bane idan nayi hukunci a nan amma kuskure ne shiga cikin abin da yake mallakata. Sarkin dogarai! Maza a tsare kowa na ce" tunda aka fara al'amarin sai yau aka ga b'acin rai. "Wallahi babu wanda za a tsare" wani irin juyawa tayi tana kallon Sultanate, ja da baya tayi ita kanta a wannan gabbar kasa rike fushinta tayi, Sultanate zata yi magana Sultan ya ce mata. "Bangaren ta ne ko bata saka a tsare kowa ba, ni zan saka." "Au biye mata kayi abdurrahman kayi? Shi kenan Allah ya bada sa'a" ta futa daga cikin gidan, gawar Kabiru aka dauka aja fita da shi, ikon Allah ne kawai yake tafiyar da ita, amma tabbas yadda numfashin ta yake sama da kasa, zata iya faduwa domin baki daya karfin ta da kuzarinta ya kare, shigowa ɗakinta tayi, ta rufe dakin tare da shiga ban daki ta kunna ruwa, yana zuba a kanta. Bata son karaya amma tabbas abin da Baffa ya fada kenan? Da Gajiyah take cewa ta hako abin da ya wuce tow kuwa mutuwa zata yi.
Bin bayan mahaifiyar shi yayi, tunda ta shiga falonta ta zauna tana huci. "Har ni abdurrahman zan nunawa ban isa ba? Yaushe aka haifi Badi'atul Noor da zata saka doka ya goya mata baya? Ni da na haife shi bai saurare ni b sai ita, wato bani da daraja." Shigowa yayi ya zube akan gwiwar shi, tare da dan durkusawa. "Badi'atul Noor ta fini daraja kenan? Ta fini kenan tow ka je kai da ita na bar mata kai, Hakkin Mansurah kuma zan kai ku kotu a nima mata hakkinta" fada take yi inda take shiga ba nan take fita ba, fada take kamar zata rufe shi da duka, tana gamawa ta wuce ɗakinta har lokacin yana durkushe. Bai tashi ba. Duk ya rasa inda zai saka rayuwar shi..
**
Sokoto.
Yau lahadi, iro da kan shi ya zo har garin sokoto ya dauke ta, suna tafiya tana mita kome ta gani sai ya saya mata har suka Binji,shagon tela ya kaita ya amsa mata dinkin sabon uniform ɗinta. Kallon shi tayi ta daura kanta a kafad'ar shi tana jin ina ma da zata iya mishi bayani a ya maida ita Sokoto domin tunda ta je zero tension, babu tsana babu tsangwama. Har suka iso gida da magariba, da murnanta ta shiga cikin gidan tana jin kamar ta shekara bata ga innarta. "Assalamu alaikum, sannun ku da gida." "Yawwa iro ya can wurin ku?" Inna Larai ta amsa masa. "Alhamdulillahi ya muka same ku?" "Masha Allah, Bimbi an dawo kenan." Dake kunne me jin ta juya gyada mata kai tayi, ta shiga ware ledar ta mikawa Rabi da Harirah kayan su, sannan ta wuce dakin su. Inna Laminde tana sallah, ta koma gefe ta zauna. Ganin zaman ba zai kare ta ba, ta nufi waje tayi alola domin shima Iro masallaci ya tafi. Koda suka dawo tana kwance a saman cinyar Inna Laminde, bakinta dauke yake da magana da labarai amma ta rasa yadda zata bata su. Sai murmushi take, ita kuwa Innar ta dage sai mata hira take, dan ajiyar da tayi dauko wannan ajiye wancan har ya cika mata gaba da abinci. "Inna yanzu ita haka zata rayu babu me gane abin da take so?" "Allah almusawiru yana sane da ita, babu abin da zan iya sai abin da hali ya bamu" "Gaskiya akwai matsala wallahi ita zata iya ji da kunne daya amma ba zata iya mayarwa ba." "Ibrahim don ka rena ni, har ka dawo da wancan abar ba zaka gaya min ba" inji malam yana shigowa dakin, duk da taji shi, kara rufe idanu tayi tana rike zanin Innar ta. Shure kafar ta yayi ta mike zubur jikinta yana kerma......
ASHRAF, SANIN GAIBU,TSINTUWA is not free, Pay N400 ONE, TWO N800, THREE 1K to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza