DAUƊAR GORA!

Disappeared

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®AS-2023.







         *♡DAUƊAR GORA¸.•💥*

           (Cɪᴋɪ ᴋᴀ sʜᴀ ᴛᴀ)  







Nᴀ

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

••••••••••


*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..*




              05 




#Disappeared!



         Kou da Lawan ya ɗaga kansa yabi hanyar da Bukar yabi da kallo,tuni har ya ɓacewa ganinsa,ya girgiza kansa cikin takaici da sanyin jiki kafin yaja ƙafarsa ya shige gida,ba ya tunanin kai takardar yau saboda hidimar da ake a gidan,zai bari har a ɗan natsa tukuna. Bayan Bukar ya koma gida,har ɗaki yaje ya samu Iya,nan ya sanar mata ya bayar da takardar akai,Iya tai wani ajiyar zuciya tare da shewa tana faɗin "kaii amma wannan Yaro Allah yai maka albarka,saboda gudun zuciyata ka aikata abunda nake so.. Yau dai Allah ya rabamu da alaƙaƙai,wannan ƴa ai baƙar kadara ce,zama da ita sai dole.. Tou yanzu abunda zan gaya maka shi ne,ina son ka kwantar da hankalinka,in sha Allahu zan nemar maka aure gidan mutunci inda ya dace.." Saurin ɗago kansa Bukar yayi ya kalleta,yana ta ƙoƙarin mayar da hawayen da suke idonsa,dan kar ta gani ya zama magana,ya tashi tare da yi mata sallama ya tafi,daga nan bai koma ɗakinsa ba ya fice ya bar gidan,domin damuwa tai masa mugun yawan da yake jin kuka ne maganinsa,hakan kuma bazai faru ba sai idan yana shi kaɗai,sai yasa gaba ɗaya ya nisanci cikin mutane,yai tafiyarsa can bayan gari inda gonarsa take,nan ya nemi guri ya zauna yana tunanin gobensu su duka uku,haka ya yini bai ba ci ba sha,sallah kawai ke tada shi daga inda yake zaune. A gefen Maryama kuwa kasancewar yau ne suna,duk da ba taron suna za'ayi ba,gidansu ma daga Uwani sai Iyami da wasu few maƙota suke ta aikin suyar naman suna da abincin da za'a kaiwa Bukar da abokansa,sai dai kou da aka gama aka raba,ba'a nufi gidansu Bukar ba kai tsaye,aka nemo yara suka kai gidansu Lawan,tare da naman da aka ware na miji da na danginsa,yinin ranar kasancewar Bukar bai zo ba kuma basu haɗu ba,haka Lawan ɗinma yaita yawon nemansa,duk inda yasan zai sameshi yaje amma babu shi babu dalilinsa,sai can dare da yake dawowa suka gamu a hanya,sam ba ya cikin walwala,Lawan ɗin yace "abokina ina ka shiga yau? Na yita yawon nemanka amma sam ban ganka ba,tun yamma aka kawo abinci daga gidansu Maryama,har da naman gidanku" Bukar da yinin ranar bazai iya cewa ga abunda ya tsinana ba,banda kuka da tunani wanda har sai da ya haddasawa kansa ciwon kai mai tsanani,ya ɗan girgiza kai a hankali yace "da Allah ka barshi,ni dama ka san kun cinye da iyalinka,ni yanzu me zan yi da abinci?" Lawan cikin yanayin tausayawa yace "Bukar dan Allah ka sawa ranka haƙuri kuma kaita addu'ah,in Allah ya nufa idan Maryama tana da sauran zama da kai sai kaga ta dawo" ajiyar zuciya kawai Bukar yayi ba tare da ya sake cewa komai ba yai masa sallama zai tafi,Lawan yai saurin riƙo hannunsa yace "ai kuwa sai ka tsaya na ɗauko maka kayanka,amana ce aka kawo min taya zan cinye bayan nasan ba nawa bane?" Da ƙyar Bukar ya tsaya bayan ya sha magiya,Lawan ya shiga ciki da sauri ya ɗauko komai kamar yanda aka kawo,kallon Lawan ya dunga yi kafin yace "kaga ka ɗauki abincin da kashin naman mutanen gidanmu ka shiga da shi ku ci a gida,ka san idan na tafi da shi ma wata fitar zai haddasa" haka kuwa Lawan ya koma da naman saboda babu yanda zai yi,saboda ya fahimci damuwar abokin nasa,shi kuma yai masa sallama ya tafi. Wasa² har tsayin kwana uku aka ɗauka,Iya tana ta jira taga anzo ɗiban kayan Maryama,amma shiru kake ji wai Malam ya ci shirwa,hakan yasa ta sake kiranshi ta hura masa wuta,har tana tambayarsa kou dai ita ya rainawa hankali? Yace mata "a'a Iya ina ga dai wanda na bawa takardar ne bai kai ba,amma zan tuntuɓeshi naji" buɗar bakin Iya sai cewa tayi "tou kou dai za ka rubuta wani ka bani ni nasa akai masu,saboda suzo su kwashe kayan da wuri,kaga maganar aurenka ba wani ɗaukan lokaci za ayi ba,za'a gama komai a kawo maka matarka" shi dai bai ce mata komai ba bayan da yace "zan masa magana idan na fita,idan ma bai kai bane zansa yaje ya kai yau" tace "tou shi kenan Allah ya jisshemu alkhairi,Allah kuma yayi maka albarka" daga haka yai ficewarsa daga ɗakin cikin wani irin yanayin damuwa mai wuyar fassara,daga gida gurin da yasan zai samu Lawan ya nufa,cikin rashin walwala suka gaisa,suna zaune sun yi shiru,Bukar cikin muryar dake bayyanar da karyewar zuciya yace "shin ka kai takardar nan kuwa?" Lawan dake kallon abokin nasa cike da tausayi ya girgiza masa kai yana cewa "na ɗan jinkirta ne saboda a ranar daka kawo min takardar suna cikin hidima,zuwana da kai saƙon zai iya haddasa abubuwa da yawa.. Amma in sha Allahu zan bada akai yau,domin ni kaina ina jin nauyin ace,ni zan kai irin wannan mummunan labarin,bazan so na zama wanda daga gareni Maryama za ta fuskanci tashin hankali ba,hakan zaisa kullum ta ganni ta dunga tunawa da abunda ya faru" gyaɗa masa kai Bukar yayi tare da ɗauke ƙwallar data taru gefen idonsa,bai jima ba ya tashi yaiwa Lawan sallama ya tafi,Lawan ya bi shi da kallo cike da tausayi. Da yamma can gabannin almuru Yaro yayi sallama cikin gidan,Iyami dake tattare sauran kaya a tsakar gida ta amsa,Yaron ya nufo inda take yace "ina yini?" Iyami tace "lafiya lau" takardar dake hannunsa ya miƙa mata yace "wai gashi inji wani a waje yace a bawa Maryama" Iyami ta karɓa tana faɗin "tou za'a bata" Yaron ya juya ya fita,Iyami dai sai kallon takardar take gabanta na faɗuwa,bata san dalili ba haka nan zuciyarta ta shiga tsinkewa,juyawa tayi ta nufi ƙofar ɗaki tana shiga take faɗin "Maryama kin tashi kin goya yarinyar nan,kou kuwa har yanzu kina nan kin barta a kwance? Kin san fa na faɗa maki,kwanciya dai² wannan lokacin bai da kyau,haka iyayenmu suke faɗa mana,shi yasa hatta marasa lafiya da zaran almuru ya fara yi ake tayar da su.." Tsaye ta ganta ta gama goya Aya,sai tayi murmushi tace "ashe kin tashi.. Tou ga shi Yaro ya shigo yace a baki" kallon takardar da Iyami take bata tayi,ba tare da ta yi magana ba ta karɓa gabanta na tsananta faɗuwa,tun ana gobe suna da Bukar suka zo har yau bata sake sa shi a ido ba,tana cikin damuwa sosai tun ranar,saboda yai mata alƙawarin idan suka koma gurin Liman,duk yanda suka yi da shi akan maganar samun Iya zai sanar mata,tou kuma gashi har kwana huɗu yau babu shi babu labarinsa,kou Lawan ma bata gani ba bare ta tambayeshi kou abokin nasa yai tafiya ne,tace masa amma tafiya babu sallama? Takardar dake hannunta ta shiga warwarewa tana sakin ajiyar zuciya,a hankali ta fara bin rubutun ajamin da idanuwa tana karanta Hausar larabcin a zuciya "ni Abubakar Abubakar Gida 10,na saki mata ta Maryama saki ɗaya,ba tare da wani dalili kou laifi ba,idan ta samu miji za ta iya yin aure.." Saurin rufe bakinta tayi zuciyarta ta wani irin buga da ƙarfi,take jikinta da ƙafafunta suka fara rawa,tai saurin dafa gadon Iyami,cikin ƙaramin sauti dake tafe da kuka ta furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allahumma ajurniiy fiiy musatiiy wa'aklufniiy khairan minha.." Tana faɗan haka wasu irin sanyayyun hawaye suka zubo daga idanunta,a hankali ta ɗaga kanta sama tana kallon rufin ɗakin dake nan na azara,cikin wata muryar data karya ta sake furta "ƙadarallaahu wamaa shaa'afa'ala.." Ta faɗa tare da gyaɗa kanta tana sakin murmushi mai ciwo,a hankali taja jiki ta zauna saman gadon,tana ta kallon takardar dake hannunta,fuskarta ɗauke da murmushi mai ciwo,yayin da hawaye suke saukowa suna ɗiɗɗiga akai,a haka Iyami data ɗauro alwala ta shigo ta sameta tana kuka mara sauti,fuskarta kuma da murmushi sosai,irin wanda zaisa ka rantse bata san wane irin saƙo ne akan takardar ba,kou kuma dai ace ƙwaƙwalwarta ta taɓu,da kallon mamaki Iyami ta bita kafin tai tambayar "Maryama! Lafiya kike kuka da murmushi? Me ya faru? Me aka yi maki?" Ɗago kai tayi tana kallon Iyami ta furta "Iyami ya sake ni.." Tana faɗan haka ta fashe da kuka,sosai maganar ya girgiza Iyami,cikin sanyi da tausayin ƴarta ta furta "haka Allah ya ƙaddara maki Maryama,ki ɗauka haka sai ya sameki,kou da dama tsohuwar nan bata ci alwashin sai Bukar ya sakeki ba,na san wata rana dole ne sai haka ya faru dama.. Kiyi haƙuri ki ɗauki dangana,in sha Allahu Ubangiji zai canja maki da wanda yafi Bukar zama alkhairi a rayuwarki,kada kiyi baƙinci da abunda ya faru,kisa a ranki haka Allah ya kaddara,duk wanda ya yarda da Allah kuma yake karɓar duk ƙaddarar data sameshi,da sannu Ubangiji zai masa canjin alkhairi.. Ke dai ki kasance me karɓar duk wani hukuncin da Ubangiji ya ƙaddara a rayuwarki.. Bar kuka haka nan kin ji,Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi" gyaɗa mata kai Maryama tayi jikinta a mugun sanyaye,Iyami ta kai hannu fuskarta ta shiga share mata hawaye tana cewa "duk abunda ya sameki akasin wanda zai faranta maki,kice innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" gyaɗawa Iyami kai tai ta yi,tana sake faɗan hakan a ranta,nasiha sosai Iyami ta dunga mata,har sai da ta samu ta dawo dai²,tana shirin sake mata magana kuma Aya dake bayanta ta fara nata kukan,al'amarin da ya sake ruɗa Maryama ta rasa me zata yi mata,sai da Iyami tace "saukota ki bata nono" da sauri ta kwantota daga bayanta tana jijjigata,amma sam taƙi yin shiru,kou nonon data sa mata a baki taƙi karɓa,hakan yasa ta sake rikicewa,kawai ta fashe da sabon kukan itama tana faɗin "Iyami ta ƙi karɓa,ni ban san me take so ba kuma" tausayin uwa da ƴar ne ya kama Iyami dake shirin tada sallah,dole ta tsaya tazo ta karɓi Aya,ita kanta duk abunda take tsammanin idan ta yiwa Aya za tai shiru,ta yi mata amma kamar sake turata ake yi,kuka take da dukkannin muryarta,al'amarin da ya tada masu hankali kenan su duka,ga muryarta har wani irin ɗaukewa take ta dawo,addu'ah Iyami ta fara mata tana tofa mata,har sai da akai sallah duhu ya fara shiga,sannan aka samu tayi shiru bayan taiwa Maryama faɗan ta daina kuka haka nan,wata ƙila ma kukan nata ne yasa Aya birkice masu,sanda tai shiru Iyami ta miƙa mata ita tace "kiyi bismillah ki gwada bata muga idan za ta karɓa" gyaɗawa Iyami kai ta sake yi ta karɓeta,kamar yanda Iyami tace tayi hakan tayi,sai ga shi ta karɓa tana wani irin fidda ajiyar zuciya,Iyami tayi hamdala tare da girgiza kai cikin tausayinsu ta tafi ta kabbarta sallarta,ajiyar zuciya suka dunga saukewa tare,Maryama ta zubawa ƴarta idanuwa sai kallonta take,tausayin rayuwar da za ta taso ciki yana sake damun zuciyarta,bayan ta gama sha ta ɗagata tasa a kafaɗarta tana shafa bayanta,sai da tayi gyatsa sannan ta sauketa ta kwantar da ita ganin ta yi bacci,sai dai har lokacin bata bar sauke ajiyar zuciya ba,sosai hankalin Maryama ya ɗan kwanta itama ta samu ta kwanta kusa da ita tana ta addu'ar duk da yazo bakinta. Washe gari da rana tana ɗaki Iyami ta fita gidan Uwani,can ta sanar mata abunda ya faru,ai kuwa kamar Uwani za ta aro baki saboda faɗan abunda Iya tayi,Iyami tayi murmushi mai ciwo tace da Uwani "kayyade Uwani idan har halinta ne ai akwai Allah.. Saboda haka ni bazan biye mata ba mu zama ɗaya,yanzuma zanje nayi tunanin yanda za'aje ɗebo kayan,kafin tasa a walaƙantar mana da kaya" Uwani ta gyaɗa kai tace "muje mu ɗebo kayan yau,domin barinsu ma baida amfani,tunda ba kirki gareta ba,tsaf za ta aiko aje a ɗebo kayan" Iyami tai ajiyar zuciya ta amsa mata,daga can suka tafi gidan tare,a hanya Iyami sai roƙon Uwani take tana haɗata da girman Allah kou me zai faru kada ta tanka,Uwani ta amsa mata da "shi kenan tunda kin haɗa ni da Allah na bari muje" ita dai Maryama tana can gida suna bacci ita da ƴarta sam bata san me ake ba,sai dai ta farka ta samu har Iyami sun gama kwaso kayan,nan cikin tsohon ɗakinta na da suka saka kayan aka rufe. Tun daga ranar babu wanda ya sake sa Bukar a idanunsa tsakanin Maryama da Iyami,a gefen Maryama kuwa kullum tana cikin damuwa,idan Iyami taga tana tunani haka za taita mata nasiha,har sai ta ga ta dawo dai²,cikin haka kwanaki suka fara tafiya,yayin da a ɓangaren gidansu Bukar Iya keta shirin auren da ita kaɗai ke kiɗanta kuma take rawarta,matar ma bai san kalarta ba duk da Iya tace yaje ya ganta,kullum sai dai yace mata tou,amma da ya fita zai manta zancen,dan sosai yake cikin damuwa,ga kunya da tunanin yanda zai yi idan Maryama taji labarin auren,kun san kuma ƙauye basa saka ranar aure da nisa,duka sati biyu aka tsayar,tuni ankai kuɗin aure da lefe,sanda ya rage kwana uku bikin sannan labarin yajewa Maryama,sosai ta shiga damuwa duk da bata ji har ranta shima yana farin ciki ba,amma kuma mahaifiyarsa ce tayi masa zaɓin dan haka baida ikon bijirewa,itama ba ta fatan yaƙi yiwa Iya biyayya,domin basu san me haƙurinsu zai janyo masu ba,da irin nasarar da za su samu a gaba. 2 days tsakani ranar ana gobe ɗaurin aure,da yamma wata budurwa tai sallama gidan,Iyami ta amsa masu suka shigo tare da ƙawayenta biyu,a tsaye suka gaisar da Iyami dake aikin girkin dare,tana ta kallonsu da rashin sani tace "sannunku da zuwa" suka ce "sannu tsohuwa" Iyami tana ta daurewa ganin tsageranci suke ji,tace "gurin wa kuka zo bayin Allah?" Ɗaya daga cikinsu tace "nan ne gidansu Maryama?" Iyami tayi ɗan murmushi tace "ehh nan ne" ɗayar dake da fuskar marasa kunya tace "gidan tsohuwar matar Bukar fa muke tambaya" turus Iyami ta tsaya tana kallonsu,sai yanzu ta fahimci irin kallon da yarinyar take mata,da sauri Iyami ta bar aikin da take ta taho tana kallonsu tace "nan ne.. Ya akayi?" Yarinyar tace "gurinta muka zo" kamar Iyami za tace su shiga tana ɗaki sai tai tunanin kada su cutar mata ƴa,tana ɗaure fuskarta tace "ba ta nan,idan wani abu ya kawoku tou za ku iya faɗa sai a gaya mata" fitsararriyar cikinsu tace "chingam ɗin biki muka kawo mata dama" Iyami tace "tou za'a ajiye mata" yarinyar ta bata chingam ƙwaya biyu irin na biki,sannan ta kalli mutum biyun dake ta taunar chingam tace masu "mu tafi tunda ba ta nan" juyawa sukai zasu tafi ɗayar take cewa "Allah ya so ta bamu sameta ba,da ta raina kanta yau" Iyami da taji maganar tace "akwai saƙon da kuka manta baku faɗa bane hala?" Sai ɗaya daga cikinsu tace "a'a babu komai" suna fita Uwani ta shigo gidan,nan ta samu Iyami na faɗawa Maryama data fito daga ɗaki tana tambayar su waye suka zo nemanta bayani,ai Uwani daga jin zancen batai magana ba ta juya har da ɗan gudunta,can ta hangosu sun miƙi hanya,ta ɗaga murya tace "ku yaran nan.. Kaiii ƴan matan matan nan" ai kuwa suka juyo tare da tsayawa suna faɗin "mu?" Tace "ehh kuzo nan" kamar baza su dawo ba ɗayar tace "muje muji me za tace" suka dawo suna kallonta,Uwani tace "wa kuke nema?" Fitsararriyar cikinsu tace "Maryama!" Uwani tace "ai kuwa yanzun nan ta dawo tana ciki" shewa tayi tace "kuzo muje" ɗaya daga ciki mai shiru² tace "don Allah Zulai kizo mu tafi,ni banga amfanin zuwan nan namu ba wallahi" Uwani dai bata ce masu komai ba ta nufi cikin gidan tana yin ƙwafa,da addu'ar Allah yasa su dawo taci ƙaniyarsu,Zulai dake fiffiƙala tace "wallahi sai naje na faɗa mata maganar da nazo saboda shi" bata sauraresu ba ta nufi cikin gidan,su kuwa suka tsaya waje suna faɗin "idan da rabon shan duka,ai bari ba magani take ba.. Allah ya haɗa ki da daidai ke" Zulai tana shigowa cikin gidan,Uwani data laɓe bayanta riƙe da bulalarta tai caraf ta kamota tana faɗin "fitsararriya tsagera ke ce kika dawo kenan.. Tou kuwa za kici ƙaniyarki" tana magana ta shiga tsula mata igiyar da aka ɗauro rago da shi,Iyami faɗi take "a'a Uwani dan Allah barta kada ki dakar masu ƴa" Uwani kuwa zane Zulai take tana ihu,ita kuma tana faɗin "barni da shrgiya tsagera na dai²ta mata zama,har dan an saki wata za'a aureta shi ne za ta zo kawo mana wargi" da ƙyar Iyami ta ƙwaceta a hannun Uwani tana faɗin "ke wuce ki fita,kuma kada na sake ganin ƙafarki a nan gidan da sunan kin zo ganin Maryama" Uwani tana kawo mata duka ta kwasa a guje tai waje,cikin ɗaga murya tace "wallahi ban yafe ba,dukkanku baƙin ciki kuke dan zan auri mijin sakakkiyar ƴarku.. Woooooo" Uwani tai wuff ta fito tana faɗin "kyaci buhun ubanki shegiya fitsararra,in dai Bukar ne ai gaki nan gashi nan,ayi auren dai mu gani,amma ki sani kou shiga gidan kikai tou baza ki taɓa mallakar zuciyarsa ba,domin Maryama kaɗai yake so.. Ayi dai mu gani" daga haka tai masu tsawa tana faɗin "kun ɓace daga nan kou sai nasa yara sun maku atile" biyun da suka rakota ne suka fara bawa Uwani haƙuri,ai kuwa Zulai ta hayayyaƙo masu,Uwani tace "ku wuce ku bar ƙofar gidan nan,kou da wasa na sake ganinku zansa ai maku shegen duka" babu shiri su dai sukai gaba suka bar Zulai,itama ɗin duk rashin kunyar ta ta sai gata ta bisu,Uwani tai wani dariya tana faɗin "da kin tsaya ai mara kunyar ƙarya" sai da taga sun yi nisa sannan ta dawo cikin gidan ta fara yiwa Iyami faɗan ai ba'a masu ta daɗi,kamasu ya kamata tayi tai masu shegen duka,taga uban da zaizo jin ba'asi,Iyami ta girgiza kai tana dariyar ƙarfin halin Uwani,har sai da Uwanin taji haushi ta fita,daga can kuwa ta tafi ta samu Lawan tace ya sanar da Bukar,lallai ya jawa yarinyar da zai aura kunne,idan ta sake zuwa gidansu Maryama taiwa mutane rashin kunya,wallahi za tasa a targaɗa ƴa,shima Lawan ɗin sai haƙuri yake ta bata tare da alƙawarin zai isar da saƙonta,sannan ta tafi sai mita take akan rashin kunyar yarinyar. At that same night suka haɗu da Bukar da babu wani shirin da yake akan auren,yana sanar masa saƙon Uwani ya taɓe baki,ya miƙa masa ledar Viva da kaya a ciki,yace "ka kaiwa Maryama dan Allah,sannan kace tayi haƙuri tayi min addu'ah,Allah ya ƙaddara saduwarmu.." Kallon rashin fahimta ya dunga bin Bukar da shi,amma sai Bukar ɗin yayi masa murmushi irin wanda ya jima baiba yace "kada ka damu ba wani abu nake nufi ba,kawai dai na san ba lallai Iya ta sauko bane,ita kuma na san dole za ta sake yin aure tunda har na saketa,sannan ka ga iyayenta ai baza su tsaya jiran gawon shanu ba.." Daga haka yai masa sallama shima me cike da jirwaye ya tafi yana masa murmushin da ya kasa ganewa,jikinsa kuma ya yi sanyi sosai. Washe gari tun safe ake ta shirin ɗaurin aure,kasancewar Jumu'ah daga an sauko masallaci za'a ɗaura,amma tun safen har akai kiran sallah babu Bukar babu alamunsa,sai shigowa ake kiransa daga waje,Iya data cakare ana bikin ɗa tana cewa ba ya gida a nemeshi a waje,sai dai har aka idar da sallah aka zo ɗaurin aure,akaita kiran ango amma kowa sai raba ido yake yana neman ta inda zai ganoshi,da dai aka fuskanci baya nan haka nan aka aika gida aka sanar da Iya,ita kuma tace kawai a ɗaura tunda babu wanda yasan ina ya shiga,duk ma inda yaje zai dawo ya tarar da matar,ai kuwa aka ɗaura aure babu ango,ana gamawa a ranar da dare aka kawo amarya aka sata ɗakin Maryama daya sha gyara,ƴan kai amarya suka juya abunsu suka bar amarya tana jiran ango. Wasa² tun ana abu da wasa har dai ya zama na gaske,domin har ta gaji tai bacci bai shigo ba,kuma haka kou washe gari ma aka sake tashi babu shi sam a garin,sai lokacin sannan hankalin Iya ya fara tashi,nan ta baza Yayyu da ƙannensa suka shiga yawon nemansa,kwararo² suna tambayar wanda ya ganshi,sai dai mutane sun shaida masu tun ana gobe ɗaurin auren da suka gamu rabonsu da shi,a nan kuma gari ya sake ɗauka Bukar ya ɓace...



       #Wayyooo Allah mugunta fitsarin faƙo.. Iya ina tayaki murna,kin yiwa kanki aure fa,domin Bukar dai tuni ya fece ya barki da matar,na san labarin amaren da suke guduwa idan basa son miji,amma yau na farko na ji namijin da ya gudu saboda bai son auren,tou jama'a me kuka ce? 😂😆



*MAZAN FAMA GLOBAL COMMUNICATION..*


     ```Muna farin cikin sanar da ƴan uwa tare da masoya cewa,wannan Company namu yana siyar da data akan farashi me sauƙi na networks da muke da su a Nigeria kamar haka:```


*MTN*

 

500MB—₦150 

1G—₦300 

2G—₦550 

3G—₦850 

5G—1,450 

10G—₦2,750. 


FOR DATA BALANCE 

DIAL:*460*260# or *461*4#


 *AIRTEL*


500MB—₦150 

1G—₦300 2G—₦550 

5G—₦1,4000 

6G—1,650. 


DATA BALANCE *140#


 *GLO* 


1.35G—₦550 

2.9G—₦1,050 

5.8G—₦1,500 

7.7G—2,050.


DATA BALANCE *127*0#


*9MOBILE*


2G—₦1,200 

3G—₦1,650 

4G—1,950 

6G—₦2,600 

7G—₦2,900. 


DATA BALANCE *228# 


contacts:***



Account №:6074981401 

Account name:Aliyu Muhammad Usman

Bank name:9 Payment Service Bank. 



#Follow

#Vote

#Comment

#Share

#Asli Smasher.