FreeArewaPen original
DAUƊAR GORA!
- 1views
- 77chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Novelist Introvert Nigerian
Sample · Mafari!
💠💠💠💠💠©®AS-2023. *♡DAUƊAR GORA¸.•💥* (Cɪᴋɪ ᴋᴀ sʜᴀ ᴛᴀ) Nᴀ *HAWWA__B__KUMO.* (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕****:REAL-SMASHER.**AREWABOOKS:REALSMASHER.*••••••••••```Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.``` ```D̶I̶S̶C̶L̶A̶I̶M̶E̶R̶:Tʜɪs ɪs ᴀ ᴡᴏʀᴋ ᴏғ ғɪᴄᴛɪᴏɴ,ɴᴀᴍᴇs,ᴄʜᴀʀᴀᴄᴛᴇʀs,ʙᴜsɪɴᴇss,ᴇᴠᴇɴᴛs ᴀɴᴅ ɪɴᴄɪᴅᴇɴᴛs ᴀʀᴇ ᴛʜᴇ ᴘʀᴏᴅᴜᴄᴛs ᴏғ ᴛʜᴇ ᴀᴜᴛʜᴏʀ's ɪᴍᴀɢɪɴᴀᴛɪᴏɴ,ᴀɴʏ ʀᴇsᴇᴍʙʟᴀɴᴄᴇ ᴛᴏ ᴀᴄᴛᴜᴀʟ ᴘᴇʀsᴏɴs,ʟɪᴠɪɴɢ ᴏʀ ᴅᴇᴀᴅ,ᴏʀ ᴀᴄᴛᴜᴀʟ ᴇᴠᴇɴᴛs ɪs ᴘᴜʀᴇʟʏ ᴄᴏɪɴᴄɪᴅᴇɴᴛᴀʟ..```*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..* 01 #Mafari!*KACHAKO,TAKAI LGA*```KANO STATE.``` •••A hankali nishi da salatin da take yake fita,cikin tsananin gami da azabar ciwo wanda yasa ta fara sarewa da rayuwa,ita kaɗai ce a cikin ɗakin tana faman gwagwarmaya tsakanin rayuwa da mutuwa,sallamar da akayi cikin gidan dake cike da hayaniyar sauran mata abokan zamanta yasa tayi furucin "Yah ubangijin al'arshi maɗaukakiya ka taimake ni,ka kawo min maceci.. Bazan iya ba ni kaɗai,ni baiwace gajiyayya a gareka.. Kou da wannan ciwon shi ne ƙarshen rayuwata,yah Allah ina roƙonka ka raya abunda yake cikina,imma mace kou namiji ya Allah kai masa tsawon rai,ka yiwa rayuwarsa albarka,kasa ya yiwa addininka hidima,ka bashi ikon taimakon al'umma.. Yah Allah ka saukeni lafiya.." Katsewa maganarta tayi cikin zafin ciwo da tsananin azaba ta runtse idanunta tare da sakin gwauron numfashi,gadan² ciwo ya sake taso mata fiye da da,wanda yasa ta janyo jikinta ta sauko daga saman ƙaramin gadonta ta durƙusa ƙasa kan gwuiwoyinta,ta dafa hannayenta duka a kan gadon tana fizgar numfashinta dake barazanar ɗaukewa,ruwan naƙuda wanda jariri ke rayuwa a ciki ne suka fara biyo jikinta,duk da wannan shi ne haihuwarta na farko,amma ganin ruwa ga mace mai cikin da ya haura watanni 7 yasa ta fahimci haihuwarta na kusa,ɗaga labulen ɗakin akayi tare da sallama,jin muryar mutumin da a yanzu yafi kowa kusanci da ita dama rayuwarta,yasa tayi ƙoƙarin buɗe gajiyayyun idanunta da ciwo yasa su yin laushi tana kallonsa,shi ɗin ne kuwa ya shigo kamar yanda tai fata,shimw ganinta a durƙushe da kuma halin da take ciki,yasa shi saurin ƙarasowa a kiɗime yana faɗin *"MARYAMA!* Lafiya kike?" Tana kallonsa da idanunta da suke bayyana tsananin azabar da take ciki,a hankali tana daurewa tace "Malam dan Allah ka taimaka min ka aika a kirawo Ungozoma,ina jin haihuwar ne.." Saurin gyaɗa mata kai yayi jikinsa na mazari yana mata sannu sannan ya juya da gudu² ya fita. Da kallo matan gidan suk...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.