DAUƊAR GORA!

Dicision maker

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®AS-2023.







         *♡DAUƊAR GORA¸.•💥*

           (Cɪᴋɪ ᴋᴀ sʜᴀ ᴛᴀ)  







Nᴀ

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

••••••••••


*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..*




              13 




#Decision-maker



           Murmushi me taɓa zuciya Iyami ta saki tana ɗagota daga jikinta tace "a'ahhhaaa! Haba Aya mene ne na kuka kuma? Baki yi farin ciki bane kou kuwa mu koma ba kya son ganinmu?" Girgiza kanta tayi cikin damuwa tace "na yi kewarku Iyami,ina Ummiina? Ita bata biyoku ba?" Tayi maganar tana share hawaye tare da leƙen bayansu taga kou tare suke,Uwani dake tsaye ɗauke da kaya a kanta ta janye Aya daga kan hanya tace "ja'ira! Ni ba ni hanya na wuce,nan da an kwana biyu kika saba duka mantawa za kiyi da mu" tsofaffin da suke tare su 3 sukai dariya,suna bin Uwani cikin ɗakin suna ajiye kayayyakin hannunsu,hannun Iyami ta kamo fuskarta kamar za ta sake fashewa da wani kukan tace "Iyami me yasa Ummii bata zo ba?" Iyami tana sauke numfashi tace "haba Aya,taya Ummiinki za ta biyomu gidanki? Daga kawoki jiya,nima ban yi niyyar zuwa ba,Uwani ce tasa ni dole sai na zo naga jikinki,sannan mu gyara maki ɗakin idan akwai abunda baiba" dame fuskarta tayi idanunta suna ciccikowa da ƙwalla tace "shi kenan Ummii baza ta zo ta ganni ba kuma?" Iyami tace "a'a za ta zo amma sai an kwana biyu tukun,idan kin daina damuwa kin zauna ɗakin ki" juyawa tayi cikin ɗakin Iyami ta biyota,sanda suka zauna sannan ta gaisar da tsofaffin da Uwani dake tai mata tsiya,ita dai kallon Iyami kawai take,Iyamin ce ma tayi ƙarfin halin tsayar da hankalinta akan Aya ɗin da take ganin alamun kamar yanzu ta tashi daga bacci,tace "Aya ba dai baki yi wanka ba har yanzu?" Gyaɗa mata kai tayi a saluɓe tace "Iyami ai yanzu na tashi daga bacci" Iyami ta waro idanunta tana kallonta tace "kuma da kika tashi baza ki nemi ruwa ki wanke idonki ba sai ki nemi guri ki zauna,a haka mijin zai dawo ya tarar dake kina fama da tsamin jiki? Ke fa amarya ce yanzu,sai kin dage da tsafta,kuma abunda baki yi sanda kina gida ba shi ne kike yi yanzu Aya?" Turo baki tayi a shagwaɓe tace "tou ni Iyami ina ruwana da shi?" Ɗaure fuska Iyami tayi tace "tashi ki fita kije kiyo wanka,kafin nasa yanzu aje gida a faɗawa Ummiinki" da sauri Aya tace "za ta zo idan ban yi wanka ba?" Iyami tai mata wani kallo tare da girgiza kanta,kawai sai tayi mata banza ta miƙe,sauke mayafinta tayi ta ajiye sannan ta shiga aikin da ya kawosu,haka Uwani ma da sauran tsofaffin. Aya kuwa ganin duk sun bawa banza ajiyarta yasa ta tashi ta cire kayanta,ruwa ta ɗiba nan cikin babban abun aje ruwanta sannan ta tafi banɗaki tayi wanka,kafin ta fito sun gama gyara ɗakin sun yi mata shara an saka turaren wuta,nan da nan ɗakin ya ɗauki ƙamshin gidan amarya,sanda ta fito babu kowa tsakar gidan kamar ba gidan Mata 10 ba,dake cika da hayaniya kullum kowa na sana'ar da yafi ƙwarewa akai,da ɗan saurinta ta wuce ta nufi ɗakinta tana tafiya tana waiwayen wanda zai fito kou ya shigo gidan. Bata jima da shiga ɗaki ba,Yaro yayi sallama ƙofar ɗakin,Uwani ta amsa tare da cewa "shigo ɗan nan" ya ɗaga labulen ya shiga yana rarraba idanuwa hannunsa riƙe da ledoji masu yellow da baƙi,hango Aya dake zaune bakin gado tana shafa mai ya ƙarasa inda take yana gaisheta tare da su Iyami,ita dai gaba ɗaya ta ƙame a gurin tana kallonsa tana jira taji dame yazo,dan ta tabbatar aikoshi akayi,sai dai bata san waye kou kuma wa akace ya kawowa ba,miƙa mata ledojin yayi yana cewa "wai gashi inji Yaya Amado yace a kawo" mutuwar zaune tayi tana kallonsa ƙwayoyin idanunta suna motsawa cikin wani irin shock ta kasa motsa kowace gaɓa ta jikinta,Iyami da suka haɗa ido da Uwani tayi ɗan murmushi irin nasu na manya ta ɗauke kanta,ganin Aya ta ƙi karɓan aiken,Uwani ta taso tana faɗin "kawo mu gani ɗan nan kaji,Allah ya maka albarka.." Ta karɓa tare da sallamarsa,ya juya ya fita yana waigen ɗakin da kuma Aya,yana fitowa Amado dake tsaye ƙofar gida yana jiransa ya kalleshi,Yaron yayi dariya yace "na kai" Amado ya gyaɗa masa kai yace "wa ka bawa?" Yaron yace "ba ita ta karɓa ba" Amado ya ɗan kalleshi,sai kuma ya basar dan yana ganin sanda su Iyami suka shiga gidan,dalilin da yasa ya tsaya nan waje kenan bai shiga ba,sai kuma Innarsa da ba ya son su haɗu sam,ya san tun jiya tana nan tana jiransa,numfashi ya sauke domin ya san akwai sauran ƙalubale a gaba,yana ɗan bubbuga shoulder ɗin Yaron yace "okay! Thank u" ya zaro Naira 50 ya bashi yace "shi kenan jeka na gode" Yaron ya ɗaga 50 ɗin yana dariyar farin ciki,yace "an gode Allah ya saka da alkhairi ya barku tare da Aya.." Cak Amado da har yayi gaba ya tsaya tare da lumshe idanunsa,haka kawai yaji wani irin sanyi ya tsirga zuciyarsa wanda bazai iya tantance asalin mene ne shi ba,samun kansa yayi da ɗan sakin murmushi kafin ya wuce yai gaba yana shafa sumar kansa mara yawa,Yaron ya biyoshi da gudu yana cewa "Yaya Amado dan Allah na dunga zuwa kana aikena da yi maku aikace²?" Ahmadi yai ɗan murmushi tare da ɗaga masa kai,daga nan yai gaba abunsa ya bar Yaron yana ta murna. Cefanen kayan girki ne a leda ɗaya,ɗayan kuma kayan miya da ƙunshin naman kasuwa ɗanye,Uwani dake duba kayan ta ɗago ta kalli Iyami tana faɗin "tou yanzu ya za'ayi da wannan Iyami? A gyara mata su a dafa sai ta ajiye?" Iyami ta ɗan kalli Aya dake ɓata rai,ba tare da tai magana ba ta gyaɗa mata kai,miƙewa Uwani tayi ta nufi inda aka ajiye kayan kitchen ɗinta ta nemo abunda take buƙata sannan ta dawo ta shiga gyara kayan miyar tana ƴan waƙe²n tsokana wa Aya,ita kam tana gama shiryawa cikin riga da skirt ɗinta na atamfar sheraton me kyau Iyami ta nuna mata abinci da suka zo da shi,zaunawa tayi ta ɗibi yanda zai mata,miyar da Iyami tayi mata a safiyar ta buɗe,ta ganshi cikin babban langa ga naman kaji da aka soya mata shima daban a cikin fanteka ƙarama,abincinta ta nutsu taci sai da ta ƙoshi sannan ta sha ruwa tai hamdala ta miƙe ƙafafuwanta,kanta ta kwantar saman gadon tana lullumshe idanunta,Iyami ta kalleta tana cewa "tou tunda uwar hanjinki ta ɗauka ai sai ki tashi kuma kije ki gaisar da kakarki da surukuwarki kou?" Saurin girgiza kai tayi tana buɗe idanunta da suka fara tara hawaye,a shagwaɓe tace "Iyami wace ce surukuwa kuma?" Iyami ta saki baki tana kallonta cike da mamaki kafin tace "Uwar mijinki nake nufi kije ki gaisar,kou baki san ana haka bane?" Ɓata rai tayi tana kautar da kanta tace "ni bazan je ba" ɗaure fuska Iyami tayi cikin faɗa ta buɗe mata wuta,ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba,Aya da dama ke jiran ƙiris ta fashe kuka,sai da tsofaffin suka sa baki gurin bawa Iyami haƙuri sannan ta share fuskarta ta tashi ta ɗauki vail ɗinta ta yafa ta fita ɗakin,Iyami ta bita da kallo tana girgiza kanta da sauke ajiyar zuciya,maganar Liman na sake yi mata yawo cikin kai,tabbas ba ta son auren nan,amma kuma a matsayinta na Babba baza ta tsananta ƙiyayya ba,za ta bi komai a sannu har zuwa taga abunda Allah ya hukunta a kan auren. Aya kam ba'a son ranta ta fito ba,sai dan tana gudun faɗan Iyami da fushinta,ɗakin Iya ta fara nufa lokacin tana zaune tana kaɗinta tai sallama ta shigo,ƙamshin turarenta da ƴar siririyar muryarta suka sa Iya ɗagowa tana kallonta,mitsi² tayi da ido tana cewa "waye wannan kuma?" Turo bakinta tayi a shagwaɓe tace "Iya nice" Iya bata bar kallonta ba tace "ke wa? Ai ban ganeki ba" rau² idanunta suka yi,Aya dake tsaye tace "Aya ce" Iya tace "auuu! Tou sannu shigo" durƙusawa tayi a ƙasa daga ɗan nesa tace "ina kwana?" Iya tace "lafiya.. Kin tashi lafiya?" Jikin Aya a sanyaye tace "lafiya lau" Iya tace "tou sannu.." Tashi Aya tayi tana cewa "sai an jima" Iya ta ɗaga kai ta bita da kallo,har ta kusan fita tace "auuu! Nace ina shi mijin naki yayi? An ce ya dawo gari kuma ban ganshi ba" tsaiwa Aya tayi tana kame²,Iya ta ɗaga kai ta kalleta,lokaci ɗaya tace "idan ya shigo kice ina nemansa,wallahi tun safe ban karya kumallo ba har yanzu,shi nake ta zaman jira bai shigo ba" Aya ta gyaɗa kanta a hankali tace "tou!" Sannan ta fita,daga can ƙin zuwa ɗakin Inna Larai tayi saboda ta san me zai faru,ɗakinta ta nufa tana shiga tai sallama,direct ta nufi gurin abincin da Iyami tayo mata,kwano ta samu ta ɗiba ta rufe,Iyami na kallon duk abunda take sai dai bata tambayeta ba har ta fita,ɗakin Iya ta nufa tai sallama kafin ta shiga,Iya ta ɗago ta kalleta,ganinta da kwano a hannu yasa ta tsaya da kaɗin da take,Aya ta ƙarasa gabanta tace "Iya gashi babu yawa" tana ajiyewa ta tashi za ta fita,Iya ta miƙa hannu ta buɗe silver ɗin tana faɗin "me na samu ne?" Naman data gani yasa ta washe baki tana faɗin "a'a kaii tubarkalla,ashe jikan nawa har yayi cefane" ita dai Aya tuni ta fice daga ɗakin,dai² lokacin Inna Larai tana kulle ɗakinta za ta fita,ta gefen idonta Aya ta kalleta,har kamar baza tayi magana ba sai kuma taga rashin dacewar hakan,kou dai baza ta amsa ba a matsayin mahaifiyar Yaya Amado ya ci ta gaisheta,fasa wucewa tayi ta nufi ƙofar ɗakin nata da take tsaye tana kokawar rufewa,gaba ɗaya ganin Aya da tayi yasa ta birkicewa,gani take kamar idan tayi sake Amado zai iya watsa mata ƙasa a ido a kan yarinyar nan,ita ba komai yake ba ta tsoro ba game da Aya irin kyaunta,kaf ƴaƴan gidan da jikoki babu wanda ya kama ƙafarta,dama² Amado shi za ace na biyunta da yake Babansa yayo,shima Baba Wada kuma da Baban Aya a cikin ƴaƴan Iya mahaifinsu suka ɗauko,kasancewar yafi Iya kyau nesa ba kusa,a da kafin a haifi Aya shi ne first a kaf ƴaƴan gidan,hakan yasa Inna Larai take taƙama da ɗanta yafi kowa,sai ga Maryama ta shigo ta haifi wanda ta disashe Amado,hakan yasa Aya ta zama tamkar wata rival ɗinsa,shi yasa ba ta ƙaunarta kamar yanda ba ta ƙaunar mahaifiyarta,idan akace gida akwai mutane da yawa,tou tabbas ne sai an samu munafuki da maƙiyi,yayin da za kaga wasu sun ware gefe sun haɗe kansu,za suyi mu'amala da wannan,basa yi da wancan,saboda hassada musamman idan ya fisu wani abu,imma ci gaba kou kuma dai bai iya kawo zancen wani kou tona asirin cikinsa ba,tou kuma Maryama ta fisu komai na rayuwa,tun ma ba kyaunta na fulani usul da kuma gatan da Hjy Mama kakarta ta gwada mata lokacin aurenta,wannan tasa sam basa jituwa da ita,ƙiri² suke nuna tsanarta suna yar mata habaici,sannan babu me shiga harkarta. Gaisheta Aya tayi da yasa ta juyowa tana mata wani kallo me cike da ƙiyayya,ba tare da ta amsa ba tai fuuu ta nufi ƙofar gida tana jan tsaki,Aya ta ɗaga kai ta bita da kallo har ta fita gidan,samun kanta tayi da jin babu daɗi,a hankali ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinta,tunda ta shigo Iyami ta kalleta ta karanci damuwa kan fuskarta,sai dai bata tambayeta ba,wucewa tayi ta kwanta tare da rufe idanunta,nan take bacci ya ɗauketa. Tass Uwani ta gyara komai ta bada kayan miya a markaɗo mata,kafin Yaron data aika ya dawo ta tafasa naman da spices masu kyau wanda Ummiinta ta siyo mata a can Kano ta soya,sannan ta ɗaura kayan miyan a wuta shima,har yamma su Iyami suka kai a gidan,Aya kam ganinsu sosai yasa ta sake tai bacci cikin nutsuwa,sai idan lokacin sallah ya yi Iyami ta tasheta tayi,sai da sukai sallar maghreeb sannan suka yi mata sallama za su tafi,nan da nan idanunta sukai rau² tana kallon Iyami tace "Iyami gobe ma za ku zo?" Cikin gatse Iyami tace "me zai hana? Ai tattaro kayanmu ma za muyi mu dawo nan da zama" dariya ta fara yi sai kuma ta tsaya tana kallon Iyami jiki a sanyaye,nasiha sosai Iyami suka ƙara yi mata sannan sukai sallama suka miƙe za su tafi,tsofaffin kam daga nan baza su dawo ba za su wuce Yobe gobe in Allah ya nufa sai kuma me tsawon rai zai sake dawowa,Iyami kam tuni ta kama hanyar fita tana cewa "Uwani ku sameni a waje ni na yi gaba" Aya ta bisu da kallo ƙwalla na taruwa idanunta,tunda suka bar gidan ta nemi guri ta zauna ta takure kanta haka nan ta kama kuka saboda kewa da kaɗaici. Kallon Iyami Ummii keyi tana sauraren labarin da take bata na Aya,Ummii tayi ɗan murmushi cike da kewar yarta dake damunta ta furta "Allah sarki Aya,Allah ya baku zaman lafiya.." Dawowarsu Iyami gida babu jimawa,Amado tare da amininsa Aminu suka zo yi masu ban gajiya da alkhairi a matsayin wanda suka bashi ƴarsu,ƴan turamen atamfofi ne masu kyau da turaruka,sai ɗan kuɗi ba masu yawa ba a ragewa baƙi kuɗin mota,duk da auren babu shiri,shi kansa kuma angon bai ma san ayi ba,sannan gidansu kou da wasa ba'ayi wani shagali ba,tun a ranar dai da ƴaƴa da jikoki suka haɗu a gida,hatta wanda suke gidajensu sai da suka taso ƴaƴansu suka zo,wanda suke wasu garuruwan ne kawai basu samu zuwa ba,duk da a lokacin da suka samu labarin ya ci ace an yi wani abu,amma kasancewar Uwar ango tayi uwa tai makarɓiya akan ba ta so,shi yasa babu wanda ya ɗaga maganar,haka akai bikin ɗanta na fari mafi soyuwa a gurinta lami,babu wanda ta gayyato a ta ɓangarenta,kamar ba aure ake a gidan ba haka akai aka gama kowa ya koma gidansa,kou Iya ma ƙawarta ɗaya Tasallah kawai ta gayyato tazo suka yini a gidan kuwa,bayan tafiyarsu Amado daga zuwa gaisar da su ne Iyami suka tado da labarin shirmen Aya na yau,Ummiinta na gefe tana saurarensu tana sauke ajiyar zuciya,ƙarƙari idan anyi addu'ar Allah ya basu zaman lafiya ta amsa a ƙasan ranta da "ameen.." Amma sam ta ƙi sa masu baki ciki kada aga rashin kunyarta,hiransu tsofaffin sukai ta yi suna faɗin kirkin Amado da hidimar da yayi a can gidan da kuma wannan,ita dai Ummiin Aya saurarensu kawai take har lokacin kwanciyar bacci yayi suka kwanta,sosai zuciyarta ta ɗan samu nutsuwa da jin Amado ne mijin ƴarta,bata san me yasa ba haka kawai take ji kamar an zare mata ƙin al'amarin,nauyin da zuciyarta tayi ya rage,kou dan Aya na yawan bada labarin yanda yake kyautata mata ne tun kafin aurensu? Oho ita dai bata sani ba. Amado kuwa tun fitarsa gidan bai waiwayo ba sai past 9,suka shigo kusan tare da Baba Wada,direct ɗakin Aya ya nufa yana satar kallon Baban ta gefen ido,shi kuma sai yai kamar bai ganshi ba ya nemi benchi ya zauna nan tsakar gida ganin ɗakin Inna Larai a kulle har wannan lokacin,ya kunna ƙaramar Radio ɗinsa ya ajiye yana jan casbaha ɗinsa yana tahlili ga Allah,da sallama Amado da ya san no way out ya shigo ɗakin,lokacin Aya bata jima da idar da sallar ishaa ba,ya wuce ya nemi kujera ya zauna,har lokacin nasihar su Iyami take ji tana mata yawo a cikin kai,tana runtse idanunta tace "sannu da dawowa" bai taɓa zaton za tayi magana ba,sanda ya kalleta kanta a ƙasa yace "thank u" ƙoƙarin tashi ta fara jikinta na ɗan rawa tana naɗe abun sallarta tace "Mmmm! Iya tana nemanka" juyowa yayi dukansa yana kallonta kafin yace "lafiya?" Tace "a'a haka tace min nace maka idan ka dawo" taɓe bakinsa yayi sannan ya miƙe yana faɗin "okay! Bari naje" yana fita ɗakin ta sauke wani irin ajiyar zuciya,Allah ya sani ita dai tsoro yake bata yanzu,musamman idan ya shigo mata ɗaki ya nemi guri ya zauna,abinci da ruwa da Iyami sukai mata magana ta dunga bashi idan ya dawo daga aiki kou wani waje ta ɗebo taje ta ajiye masa inda ya tashi,sannan ta miƙe ta koma kan gadonta ta ɗan kwanta tare da ɗaga kanta sama tana kallon rufin ɗakin,ba komai take tunani ba sai school,kou zai yarda ya barta ta ci gaba da zuwa oho? Tunda ita dai tana ganin duk wanda aka yiwa aure a garin,idan tana makaranta daina zuwa take,ita kuma ga shi ta ƙwallafa rai akan karatun,saboda haka ne ma take yawan faɗawa Ummiinta idan ta gama secondary school za ta tafi can health technology ta karanci health,amma yanzu kam ta tabbatar tana ƙila waƙala ne,musamman data san gidan babu wata mace da tayi karatun boko,share guntayen hawayen da suka sauko fuskarta tayi ta sauke ajiyar zuciya,tabbas itama yanzu ta san ta zo intaha a karatu,a matsayinta na ƴa mace wacce rayuwarta duka taƙaitatta ce,sannan tana ƙarewa ne a bauta,sam ba zata samu lokacin kanta ba tunda tayi aure,a yanzu nauyin mijinta ne kawai akanta sai na iyayensa,nan gaba kuma nauyin ƴaƴan da za ta haifa zai zo ya sake ɗauruwa kanta,shin ta ina ma za ta samu lokacin zuwa makarantar? "Babu" shi ne amsar da ta bawa kanta tana sake share hawaye tare da sakin murmushi me ciwo. Da sallama ya shiga ɗakin Iya bayan ya wuce Babanshi a zaune tsakar gida,he thought zai masa magana da ya fito,sai yaga bai ce masa komai ba,Iya dake zaune ɗakin ta kunna Radio itama tana sauraran shirin *IN DA RANKA* a Freedom radio ta amsa tare da ɗagowa ta kalleshi,tana ƙanƙantar da idanunta duk da hasken wutar NEPA ya haska shi sosai tace "Amado!" Kallonta yayi yana ƙarasawa ciki ya zauna bakin gadon ƙarfenta yace "ina yini?" Tace "lafiya lau.. Har ka dawo?" Yana ɗan gyara zamansa yace "ga ni ance kina nemana tun ɗazu" Iya tace "auuu! Tou kuma ai ya wuce,ba dai ka sa matarka tayi girki ta kawo min ba? Ai kuwa baka ga naman kazar data zubo min ba wallahi,ni tunda naci wannan abincin ma,ban sake sa komai cikin nan nawa ba har yanzu,sai ruwa kawai nake ta sha ina kwantar da maiƙo,kai dai Allah yai maka albarka ɗan nan,ya baku zaman lafiya" kallon Iya ya tsaya yi yana squeezing face ɗinsa,cikin yanayin dake bayyana gaskiyarsa yace "waye ya kawo maki abinci?" Tace "wannan yarinya mana da akai aurenku.. Wa take ma da suna?" Ya buɗe ido sosai yana kallonta cikin mamaki yace "Aya!?" Tace "iihhhh! Ita kuwa,amma nace haka ta iya girki dama? Ashe uwar bata sangartar da ita ba,ta koya mata abun arziki,nace ai kuwa Allah ya taimaketa dan duk kyaun nan nata da ya tashi a banza,girki ai shi ne mace.. Kai dai wallahi kai sa'ar mata,ba mu yi maka zaɓen tumun dare ba,mun maka zaɓi na gari wallahi,ai baza ka taɓa yin dana sani kou kuka da mu ba.." Kallon bakin Iya yai tayi,sai da ya bari ta kai aya sannan yace "ni bansa ta kawo maki abinci ba,ra'ayi tayi ta kawo maki.. Har kina min maganar naman kaza,sai dai idan Iyami da suka zo gurinta suka kawo,amma ni ban sai komai ba,ni da ban san da auren ba sai da na dawo jiya da dare,ta ina zan fita har na siyo kajin da kike magana?" Tsayawa Iya tayi tana kallonsa baki sake,tace "ɗan nan da gaske kake baka sai komai ba?" Bai amsa tambayarta ba yace "wannan shi ne kiran da kikai min?" Tace "iiihhh! Tou me zai sa na kiraka dama? Mutumi kullum sai dai ka shigo kai min gurum,baza kai magana ba sai dai ka mayar da ni gantalalliya,naita maka hira kana ji baza ka kulani ba.. Nan fa ta shigo ta gaisheni,ka ga can wajen,nan ta durƙusa cikin kunya da girmamawa ta gaisheni na amsa,da za ta tafi tai min sai an jima,har ta tashi nace mata na ji ance ka zo,idan kana nan ta turo min kai,tun safe babu shegen da ya kalleni a gidan nan yau saboda na san za ka zo,kuma dama na hana su bani ruɓaɓɓen abincinsu idan kana gari,na sanar mata ban karya kumallo ba ina ta jiran ka shigo tace min tou,na ɗauka data fita ta ganka ne ta sanar maka,kai kuma kasa ta kawo min wannan abinci da na ci.." Taɓe bakinsa yayi ya tashi zai fita yace "tou ni na ce maki ban aikota ba,ita tasa kanta ta kawo maki.. Daga zuwanta gashi nan ta fara kyautata maki,amma sai ta zo gaisheki sai ki kama tambayar sunanta,yarinyar da har yau bakya ganewa a cikin jikokinki,wannan abun da kuke mata a gidan nan ya yi yawa,idan an faɗa maku gaskiya kuma ku fara yiwa mutane faɗa kamar ba jikan gidan ba.." Yayi maganar yana ficewa daga ɗakin cikin nuna jin haushi,sakin baki Iya tayi ta bishi da kallo,har ranta take tambayar kanta da gaske ra'ayin Aya ne ta kawo mata abincin da taci? Kou kuma Amado ya faɗa mata haka ne saboda ya siyawa matarshi kima a gurinta? Taɓe bakinta tayi tana faɗin "kaiii wannan ɗa koi shaharu,ji yanda ya lafta min ƙarya da girmana da ƴaƴa har da ƴaƴan jikoki.." Mita Iya taita yi kamar Amado na ɗakin har lokacin,sanda ta gaji tai shiru tana kashingiɗa bacci yai gaba da ita. Sanda ya dawo yana shigowa ya tarar da Aya kwance ta juyawa ƙofa baya,ya yi tunanin bacci take sai bai mata magana ba,ya zauna saman kujerar da ya tashi yana kallon kwanonin data ajiye na abinci da ruwa,sake ɗaga kansa yayi ya kalleta,ganin babu alamun dake nuna masa idonta biyu kawai sai ya share shima,kamar bazai buɗe ya duba ba yana tuna yanda suka yi da Iya ya sauko ya buɗe,sosai mamakinta ya cika shi,bai taɓa tunanin wai a shekarun Aya za ta iya wannan sadaukarwar ba,rufewa yayi ya tashi ya nufi gurin jakar kayanshi ya ɗauki abunda yake so sannan ya wuce ya fita,ya jima kafin ya dawo ya kwanta yana danna sabuwar wayarshi da ya sake ƙiran BlackBerry bold touch 2. Da asubah kou data tashi bayan ta idar da raka'atanil fajr ta tashi ta shiga ɗaki tana faɗin "Aya! Baki fito ba har yanzu kina kwancen naki? Wace irin yarinya ce ke da kullum sai an yi fama dake idan kina nan?" Sai kuma tayi saurin rufe bakinta jikinta a sanyaye ta dunga kallon ɗakin,sam ta manta da cewa yanzu fa Aya ta barsu kenan,ta jima a tsaye tana tunani kafin ta juya ta fita,Iyami da taji komai ta bita da kallon tausayi,haka Ummii ta wuce ta kabbarta sallah,bayan ta idar ta fita tsakar gida ta kama aiki tunanin Aya fal ranta,Iyami ce ma tayi mata magana take cewa "da kin bari kin zo kin kwanta,idan gari ya gama haske sai na kama maki aikin muyi tare" tace "a'a Iyami ki barni nayi,kou na dawo na kwanta ma ba baccin zan yi ba" Iyami ta gyaɗa kanta tace "shi kenan.. Allah yayi maki albarka" Ummiin tace "ameen.." Tana ci gaba da aikinta. Yau ma tun asubah da ya fita bai sake shigowa ba,Aya da bata iya yin bacci ba yauma,ganin bai shigo ba ta kwanta tai bancinta sosai,kou da gari ya waye sanda ta tashi,bata manta da khuɗubar Iyami ba,ta ɗebi ruwa taje tai wanka ta dawo ta shirya,sannan ta ɗebi namanta duk da Iyami ta ce mata ba sawa za tayi a gaba ta cinye ba,sai idan za tayi girki ta dunga ɗiba tana sawa ciki,ta ɗan ci da yawa ta sha ruwa,har dare ita kaɗai ta yini,can bayan sallar ishaa tana zaune gurin da tayi sallah,dan sosai yau ita kanta ta gaji da kwanciyar da take,sai ga shi ya shigo da yake ya san babu kowa sai ita kaɗai,sallamar da yayi ta amsa ƙasa² tana sauke idanunta,ya ɗan kalleta kaɗan,ita kuma tai masa sannu da dawowa ba tare da ta kalleshi ba,ya amsa mata yana neman guri ya zauna,har ta yi shiru sai kuma ta tuna basu gaisa ba kamar jiya ya fita,ɗago manyan idanunta tace "ina yini?" Yana duba wani saƙon da aka turo masa daga can office ɗinsu ya amsa ba tare da ya kalleta ba,a hankali tana kallonsa ganin hankalinsa ba ya kanta tace "na kawo maka abinci?" Ɗago idanunsa yayi ya kalleta,suna haɗa ido tai saurin ɗauke nata tana kallon ƙasa,sliding wayar yayi ya ajiye gefensa,idanunsa akanta cikin tarin mamaki yace "me kika ci?" Tana wasa da hannunta a ɗan shagwaɓe tace "naman da Iyami ta kawo min" lumshe idanunsa yayi na ɗan lokaci,tunani da yawa ya sauko masa a rai,sam ya manta ya tafi Kano bai bar mata komai ba,saboda processing yanda za'ayi ya kai takardar neman hutun aure,yinin yau gaba ɗaya can suka yi shi tare da Aminu abokinsa dan shi ya rakashi,da sauri ya ware idanunsa yana kallonta yace "no! I'm ok" kasa ɗagowa ta kalleshi tayi ta ci gaba da zamanta a nan,shi kuma sai ya ɗauki wayarsa yaci gaba da operating,can ba'a jima ba suka jiyo muryar Baba Wada yana ƙwalo masa kira,ya amsa tare da tashi ya fita,a bakin ƙofar ɗakin ya ganshi tsaye,ya durƙusa ƙasa yana faɗin "Baba ga ni" Baba Wada yana kallonshi yace "ka sanar da gurin aikin naka ne?" Yace "ehhh na je na kai letter,amma sun ce lallai na koma goben" Baba Wada yace "baza su baka ɗan hutu ba?" Amado yace "Baba duk yanda zanyi na yi amma sun ce lallai² na koma,idan ba haka ba zan fuskanci hukunci" ajiyar zuciya Baba Wada ya sauke yana kallonshi sannan ya shiga yi masa nasiha akan amanar Aya da kuma hakkinta na marainiya,a matsayin matarsa yanzu idan ya zalunceta babu ruwan Allah da kasancewarsu dangi ɗaya,Ubangiji zai bi mata hakkinta kou da bata ce Allah ya isar mata ba,jikin Amado sosai yayi sanyi dan bai fahimci me Baban nashi zai ce ba,Baba Wada na gamawa ya kalleshi yace "kaje ka sanar mata ta shirya ƴan kayanta,idan Allah ya kaimu da safe za ka tafi,ka ɗauki matarka ku tafi tare,sabon aure kukai bai kamata ka barta a nan ba,duka yaushe ta tare da za'a ce ka yi tafiya ka barinta tana maka gadin gida? Allah ya baku zaman lafiya ya kare,idan kun samu lokaci kwa dunga ɓillowa a gaisa.."




*MAZAN FAMA GLOBAL COMMUNICATION..*


     ```Muna farin cikin sanar da ƴan uwa tare da masoya cewa,wannan Company namu yana siyar da data akan farashi me sauƙi na networks da muke da su a Nigeria kamar haka:```


*MTN*

 

500MB—₦150 

1G—₦300 

2G—₦550 

3G—₦850 

5G—1,450 

10G—₦2,750. 


FOR DATA BALANCE 

DIAL:*460*260# or *461*4#


 *AIRTEL*


500MB—₦150 

1G—₦300 2G—₦550 

5G—₦1,4000 

6G—1,650. 


DATA BALANCE *140#


 *GLO* 


1.35G—₦550 

2.9G—₦1,050 

5.8G—₦1,500 

7.7G—2,050.


DATA BALANCE *127*0#


*9MOBILE*


2G—₦1,200 

3G—₦1,650 

4G—1,950 

6G—₦2,600 

7G—₦2,900. 


DATA BALANCE *228# 


contacts:***



Account №:6074981401 

Account name:Aliyu Muhammad Usman

Bank name:9 Payment Service Bank. 



#Follow

#Vote

#Comment

#Share

#Asli Smasher.