DAUƊAR GORA!

Magana... (Zarar bunu)

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®AS-2023.







         *♡DAUƊAR GORA¸.•💥*

           (Cɪᴋɪ ᴋᴀ sʜᴀ ᴛᴀ)  







Nᴀ

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

••••••••••


*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..*




              16 




#Magana... (Zarar bunu) 



           Aikinta ta ci gaba da yi tana ƴan tunane² game da rayuwarsu,yayin da yanayin zaman da suke yake sake dukan zuciyarta,tabbas ta san Yayan nata ba sonta yake ba,kawai dai ya yi mata alfarma ne ya yarda zai zauna da ita,ba a matsayin macen da zuciyarsa ta aminta ya bawa dukkanin ragamar rayuwarsa ba,sai dai a matsayin matar da iyayensu suka zaɓar masa,har ga Allah bata so rayuwarta ta kasance a haka ba,ta yi burin ace ta yi zurfi a karatu,sannan idan za tayi aure,ya kasance ta auri namijin da ya fahimceta kuma yake sonta saboda Allah not for granted,bata san yaushe hawaye suke saukowa fuskarta ba,haka nan bata san yaushe ya shigo gidan ba,sai dai taji an rungumeta ta baya,a ɗan firgice ta dawo hayyacinta ta fara ƙoƙarin juya,even though ƙamshin scent's ɗinsa yasa ta fahimci shi ne,kasancewar idan ba shi ba babu wani mutum da yake da access na shigowa haka kai tsaye,tana sauke ajiyar zuciya ta ɗan dakata da yanka albasan da take tana kallon wanda ta gyara,yanda yaji jikinta yai sanyi lokaci ɗaya yasa shi sakinta tare da juyo da ita dukanta,kallonta ya tsaya yi a bit scared ganin hawaye a fuskarta har wasu suna ɗiɗɗiga jikinta,duk da ba wai kuka take me sauti ba,sai dai hakan yasa shi fahimtar akwai wani abu dake damunta wanda take ɓoyewa ba ta so ya sani,saurin matsowa daf da ita yayi yana faɗin "Ƙanwata! Me yake faruwa? Kukan me kike?" Saurin juya masa baya tayi tana kai bayan hannunta ta share fuskarta,da sauri ta ɗauki wuƙar ta ci gaba da yanka albasar da take,duk da albasar tana da zafi a ido,sai dai ba iya zafin nata ne yasa ta kuka ba,kawai abun yazo mata a kan gaɓa ne tana jin yin kukan,wannan shi ne kaɗai hanyar da take samu ta rage nauyin zuciyarta,ita ba me surutu bace kamar Tayyibah,shi yasa ma wasu abubuwan dake damunta ba ta iya buɗe baki ta sanar mata,akan haka har complaint Tayyibar take mata tana cewa bata yarda da ita kamar ita data bata aminci ba,duk sanda ta faɗi haka sai Aya taji babu daɗi sam,amma ya za tayi? Ita kou a gidama bata cewa komai duk yanda abu yakai ga damunta,saboda Ummiinta tana yawan kwaɓarta tare da sanar mata cewa ciki ba an yi shi ne domin ci ba kawai har da adana sirri,dan haka ba kowane sirrinka kake ɗauka ka fitar da shi ba,wannan dalilin yasa ta koyi haɗiye damuwarta,sake rungumeta yai ta baya ya ɗaura fuskarsa a saman wuyanta,cikin wani irin yanayi me kashe jiki yace "Ƙanwata! Please ki sanar min me yake faruwa,me yasa ki kuka?" Numfashi ta ɗan huro daga bakinta,baza ta iya sanar masa komai ba,kuma ta san yanzu idan ya fahimci wani abu zai iya sata gaba da tambayoyi,dole tayi ƙoƙarin saita kanta,tana gyara yanayin fuskarta tace "babu komai.. Ni ba kuka nake ba,albasar ne da zafi,shi ne yasa ni kuka" yace "are u sure babu komai?" Ta gyaɗa masa kai a hankali,sai kuma zuciyarta take tambayarta "me ya dawo yi gida yanzu,shi da sai can yamma?" Yana sauke ajiyar zuciya yace "thought na yi maki wani abu ne da ba kya so,kou wani abu na damunki" ba tare da ta yi magana ba ta girgiza masa kai kawai,so take ta ci gaba da aikinta dan tana so ta gama da wuri,sai dai rungumeta da yayi yasa ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi,ita duk waɗannan abubuwan da yake mata ba sonsu take ba saboda ta san kwanan zancen,kissing ɗin wuyanta yayi kaɗan yana cewa "me za ki yi da albasar da kike yankawa?" Muryarta na seizing tace "Mmmm.. Zan yi.." Kasa ci gaba da magana tayi jiyo hannunsa a cikin rigarta yana shafa mata tummy,gaba ɗaya nema yake ya birkita mata ƙwaƙwalwa,ita duk wannan abubuwan da yake yi ba wai tana son hakan bane har ranta,domin ta san ƙarshen zancen dole sai ta sha wahala a gurinsa,sai dan ta karanta kuma ta sani cewa wannan abubuwan da suke faruwa tsakanin su shi ne auren,shi yasa baza ta iya hana shi ba,jikinta ne ya fara rawa saboda irin abubuwan da yake mata da suke ƙara dagula mata lissafin ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwarta,underneath tana addu'ah da zai barta tai aikinta duk da sauƙi,amma ta tabbatar yau me karɓanta a hannunsa sai Allah,romancing ɗinta ya fara a haukace kafin ya ɗauketa yai waje,wani bedroom ɗin da ba wanda suka saba kwana ciki ba ya shiga da ita,ya ƙarasa lafiyayyan gadon dake ɗakin ya kwantar da ita,juyar da kanta tayi gefe ɗaya,bata yarda ta kalleshi ba ta lumshe idanunta tana sakin siririn ajiyar zuciya,fuskarta ya kai hannu ya juyo da shi tare da haɗe bakinsa da nata,numfashinsa yana sauya yanayin fita tare da ɗaukewa ya dawo ya rabata da komai na jikinta,sannan ya shiga sarrafa gangar jikinta,yau ma kamar ranar farko ta sha wahala,sai dai bai kai wancan ba ita kanta ta bambance,ta yi kuka ta kira Ummii da Iyami kamar ranta zai fita,haka shima tun tana kiranshi har ta koma roƙo da turje² har sai da muryarta ya dashe,sanda yai bidirinsa ya juyata son ransa,bai ɗauki dogon lokaci ba yana gama biyawa kanshi buƙata ya sauka tare da wucewa bathroom yana blushing,a gurguje yai wanka ya fito ya mayar da kayanshi,fuskarsa tana fitar da annuri ya ƙaraso gurin da take tare da sunkuyowa kaɗan yace "Aya wake-up ki gyara jikinki,zan koma office ne ina sauri" ajiyar zuciya tayi tare da gyaɗa masa kai,yai mata kiss a forehead ɗinta sannan yace "bye.. Ki kula da kanki" daga haka ya fice yana jinsa kamar zai yi tsuntsu ya tashi sama. Aya na jin sanda ya fita ta buɗe lumsassun swollen idanunta da sukai jaa,ajiyar zuciya ta dunga saukewa tana kallon ɗakin da take ciki,kou kaɗan babu abunda ya burgeta cikin duk abubuwan da yai na gyaran gidan,domin duk ba ta wannan take ba,farin ciki kawai take buƙata a rayuwarta,kuma bata ga alamun za ta sameshi ba,hawayen da suka gangaro mata tasa hannu ta share sannan a hankali ta yunƙura ta tashi zaune,sai da ta ɗan huta kafin ta gyara zanin jikinta ta miƙe da ƙyar walking slowly ta nufi bathroom,ruwa masu zafi sosai ta tara ta shiga,tana cizar lips tana komai ta daure ta gasa jikinta,sai da tayi haka kusan sau 5 kafin taji dama²,tayi wankan tsarki ta ɗauro towel ta fito,kaya ta fita ta canja sannan ta kama aikin da bata samu ta yi ba tun safe,sai dai gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikinta,rashin mataimaki yasa ta jajircewa take ƙoƙarin yin aikin,kasancewar jikinta babu ƙwari sosai yasa tana yi tana hutawa,a haka ta gama lokacin ana kiran sallar zhuhur,ta miƙe da ƙyar ta shiga cikin tsohon bedroom ɗinsu tai sallah,tana idarwa a nan inda take ta kwanta,babu jimawa wani irin bacci ya ɗauketa. Tun around 11am Tayyibah ta sauko saboda ta duba jikin Ayan da kuma taimaka mata da aikin gidan,tsaye take gaban entrance ɗinsu tana knocking,ta wuce 15 minutes tsaye a gurin,ganin Aya bata zo ta buɗe ba yasa ta juyawa ta koma,sai dai tana cikin zullumin kou wani abu ya faru da ita ta kasa fitowa,data koma apartment ɗinsu kasa shiga ciki tayi ta tsaya gaban railer tana kallon ƙasa gabanta na ɗan faɗuwa,ba ta fatan ace wani abu ne ya samu Aya,wannan tunanin yasa gaba ɗaya ta zama so upset saboda rashin sanin takamaiman abunda ke faruwa,bata san wa za ta sanarwa ba kou dan ma a shiga a duba lafiyarta,tunani iri² da tsoro babu wanda bai zo ya cika mata zuciya ba,almost 30-40 minutes taji alamun buɗe ƙofa,da sauri ta kalli ƙasan zuciyarta na sake cika da fargaba,Oga Ahmad da ta gani ya fito yana ɗan sauri zai bar gidan,yasa ta ware idanunta da mamaki,kenan yana gidan bai fita ba kou kuma dawowa yayi daga baya? Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke tana ɗan gasping,duka tsoronta yana biyo iskar bakinta yana fita,har Amado ya fice daga gidan bata iya yi masa magana kou ta tambaye shi taji lafiyar Aya ba,saboda wani irin kunyarsa da kuma kunyar kanta da ya cikata,Allah ya so ma batai masa magana ba da abun sai yai yawa,juyawa tayi da sauri ta shige cikin parlonta,sai dai har lokacin wani gefe na zuciyarta dake da rauni ya kasa nutsuwa,tana son sanin yanda Ayan take,bata sani ba kou da wani abu da za ta nema,amma kuma sai zuciyarta ya bata kada tayi tunanin haka,duk abunda Ayan za ta nema a gurinta,ai bayan wanda za ta nema ne daga gurin mijinta kuma ɗan uwanta,tunda babu abunda bata sanar mata ba na daga alaƙar dake tsakanin su biyun. A hankali rayuwar ta fara sauyawa ga dukaninsu,a ɓangaren Amado shi kam yanzu bai da wata damuwa,domin a duk lokacin da yake buƙatar kasancewa da Aya,ya san yanda zai yi ya sha kanta ta bashi haɗin kai,da zaran buƙatarsa ta biya kuma shi kenan bai da sauran damuwa. While a gefen Aya kuma tunda suka fara rayuwa ƙarƙashin inuwar aure,gida guda sannan shimfiɗa ɗaya,kaɗaici tare da ƙuncin da bata san dalilinsa ba,suka zo suka rufe mata zuciya,idan kaga yanda Amado yake janta a jiki yanzu za kayi matuƙar mamaki,sai dai tun tana ɗari² da shi har ta sauko a yanzu kuma ta fahimceshi,a lokuta da yawa ma sukan zauna suyi hira tare da wasa da dariya,duk da ba wai tana iya zagewa tai magana bane kou ta hau bashi labarai kamar yanda yake mata,idan abun dariya ya faɗa za kaga ta saki jiki tai dariya,sai dai a can ƙasan zuciyarta akwai abubuwa da yawa da suke damunta game da rayuwar aurensu,kuma abun ya shafesu ne su duka biyu,tun daga daren farkonsu har yau da suka ɗauki hanyar wata guda,a duk sanda zai nemeta a shimfiɗa bata taɓa nuna masa a'a ba kou ta kawo masa uzuri,sai dai abunda ke cizon zuciyarta shi ne zafin da take ji,sam ta kasa sabawa da yanayin,kuma kou da suke magana da Tayyibah take mata complaint tun farko²n auren nasu akan haka,ta ce mata tayi haƙuri za ta saba nan da ɗan wani lokaci,itace har da zagewa tana mata lecture tare sa bata logics na abubuwan da za ta dage tana masa,da kuma shawarwarin abunda za ta nema da zasu sa ta daina jin ciwo,sai dai har yau al'amarin bai canza zani ba,ita kuma ta kasa saduda har gobe bare ta iya yi masa wani abu,hasalima baza ta iya cewa ta san daɗin sex ba,kamar yanda har yau ta kasa gwada jarumta,ta kuma kasa daina kuka,kaɗaici kuwa na Iyami da Ummiinta kullum da shi take kwana ta tashi,ta yi karar ta yi kawaicin amma shiru kake ji,tou ta ina ma za ta fito tai masa maganarsu bayan kou shima rabonsa da yace mata zai je gida,tun da suka taho bai ƙara zuwa ba kou maganar ƴan gidansu,yawan tunani da damuwar da take shiga yasa sam ta kasa gaba,kullum sai ƙara ramrewa take tana lalacewa kamar kuɗin guzuri,sai dai a ɗan zaman da suka yi da Tayyibah yasa ta fara gogewa ta wasu guraren,kasancewar ba wai dama can asali tana cikin duhun jajilci bane,da za'a ce bata san komai ba kou yanda za ta tafiyar da rayuwarta,cikin haka ta fara rashin lafiya a tsaitsaye,tun suna ɗaukan abun wasa har sanda al'amarin ya ta'azzara,jikin kuma ya mugun rikice,zazzafan zazzaɓi ya rafketa ta kwanta sadidan,ga rashin cin abinci,duk yanda taso abu da zarar an kawo mata shi gabanta za taji ba ta so,wani zubin har da su amai,idan akai mata maganar hospital sai kuka koma kaga ciwon ya tafi,sai an kwana biyu ta sake kwanciya,cikin ɗan lokaci ramarta ta sake fitowa,haskenta yai wani irin fau yana ɗaukan idanuwa,da ka kalleta za ka fara zargin lallai akwai wani abu,a haka har suka kama hanyar watanni 3 da aure. Zaune take parlour saman kujera tasa TV a gaba da kallo,knocking ƙofarsu aka yi jikinta a sanyaye tana daga inda take tace "yes come in" Tayyibah ce ta shigo da sallama,hannunta ɗauke da plate a rufe ta ƙaraso,Aya dake kallonta tana murmusawa tace "ba kya gajiya da hidima Sister" Tayyibah dake zaunawa kusa da ita tace "kema dai banda abunki idan ban maki ba wa zan yiwa? Ni dai fatana wannan ciwace²n da kike,Allah yasa Oga ne yai mana ajiya" sakin baki Aya tayi tana kallonta tace "kin ji ki da wata magana dan Allah" Tayyibah tace "ai gaskiya na faɗa,ke dan Allah baki taɓa kawo haka a ranki ba?" Aya ta girgiza mata kai tace "ba na tunanin haka,ni na fi zargin stressing kaina da nake ne kullum da rashin samun wadataccen hutu da bacci" Tayyibah tai mata wani kallo kafin tace "uhmn! Ma ji ma gani.. Amma kin san Allah kou da ban san komai akan harkar lafiya ba,na tabbatar kina ɗauke da ciki,duba da yanayin ciwonki" kallon Tayyibah ta tsaya yi mamakin kalamanta sun cika mata zuciya,tambayar kanta ta fara "shin da gaske ciki ne da ni?" Wata zuciyar tace "a'a Aya kawai dai tana hasashen haka ne,ki ɗauka wannan kawai ciwo ne ya sameki daga Allah,ki manta da maganarta" ajiyar zuciya ta sauke kaɗan,tana sake zurfafa tunaninta wajen son sanin gaskiya,gabanta ne yai mugun faɗuwa tuno rabonta da ganin al'adarta,zuciyarta tana bugawa da ƙarfi ta ɗago ta kalli Tayyibah dake cewa "Madam ki bar damun kanki da tunani fa,kou ki yarda kou ƙi idan har za kuje hospital za'a tabbatar maki maganata.." Wani irin tsinkakken yawu Aya ta haɗiye,a hankali tace "Sister me yake sawa mace ta gane tana da ciki? Wane alama ce ta farko?" Tayi tambayar saboda ta tabbatar da zarginta,sam ƙwaƙwalwarta ta ɗauke,lokaci ɗaya komai yai hooking up,gyara zama Tayyibah tayi kamar gaske tace "ni dai na san ana cewa rashin ganin period yana cikin alamun farko da ake gane mace ta samu juna biyu,sannan sai yawan laulayi kuma,kai ta ciwo a rasa gane me yake damunka" Aya ta gyaɗa mata kai tace "nima na san ana cewa haka" kallon tuhuma Tayyibah tai mata tace "so kin gano wani abu kenan?" Aya ta gyaɗa mata kai tace "Mmmm!" Tayyibah tace "me kika gano?" Aya tace "tunda muka zo nan ban sake yi ba.." Tayyibah ta ɗan fiddo idanuwanta fuskarta da alamun farin ciki sosai akai tace "da gaske kike?" Ta gyaɗa mata kai da sauri tace "ehh! Tun kafin bikinmu da nayi a can garinmu ni dai ban kuma yi ba har yau" ɗaga hannuwa sama Tayyibah tayi da muryar excitement tace "Alhamdulillah! Wallahi Sister Aya ina ga zarginmu ne yake neman zama gaskiya,amma baza mu tabbatar ba yanzu har sai munje hospital tukuna.. Ina ga ki sanar da Oga Ahmad,kou da bai da lokacin zuwa ya kaiki,sai muje tare na rakaki" Aya ta gyaɗa mata kai a hankali tace "tou! Zan tambayeshi idan ya dawo yau" Tayyibah tace "Allah yasa muji alkhairi.. Ubangiji ya tabbatar mana da hasashenmu.. Dama mu biyu muke rayuwa sai mazajenmu,idan muka fara tara ƴaƴa kinga mun samu ƙarin wanda za su ɗebe mana kewa" Aya dai gaba ɗaya ta ɗauke wuta,wani irin tsoro take ciki haka kawai,ba wai dan ba ta fatan ace cikin gareta ba,itama ai mutum ce kuma haifarta akayi,saboda haka za tayi farin ciki idan aka ce ta haifi ƴaƴanta,kou da mutuwa tayi ta san ta bar masu yi mata addu'ah,sai dai haka nan jikinta yake mata babu daɗi,tana jin kamar wani abu zai sameta ba da jimawa ba,hira Tayyibah taita mata ganin kamar ba ta cikin mutuwarta tare da janyo plate ɗin data shigo da shi tana cewa "kinga muna ta hira baki ga abunda na kawo maki ba kou za ki iya ci" buɗe mata plate ɗin tayi,kwaɗon zogale ne ciki an zuba ƙuli² sosai an yanka masa kayan haɗi,Aya na gani yawunta ya fara tsinkewa,da sauri ta gyara zamanta tana cewa "kaii Allah ya biyaki Sister,wallahi har yawuna ya fara tsinkewa" Tayyibah tai dariya tare da miƙa mata tace "tou ga shi in dai za ki iya ci,kuma zai zauna bazai dawo ba" Aya tana gyaɗa kanta tace "Allah yasa ya zauna ɗin" Tayyibah tace "ameen.." Miƙewa tayi ta nufi kitchen da sauri ta wanko hannunta,tana dawowa ta zauna ta ɗauki plate ɗin ta ɗaura kan cinyarta tare da yin bismillah ta fara ci,lumshe idanunta tayi tana taunawa,tace "Mmmm! Wow anjad.. Gaskiya ya yi daɗi sosai,amma fa kada kice ban maki bismillah ba" dariya Tayyibah taita mata tana cewa "ni wallahi ban damu ba kici ke dai,fatana Allah ya taimakemu ya zauna" kasa mata magana Aya tayi sai kwatance da hannu,Tayyibah kuwa ta sata gaba da dariyar farin ciki. Knocking akai tare da danna bell,Tayyibah ta miƙe tana cewa "let me check" Aya ta gyaɗa mata kai alamun tou,Tayyibah na buɗe ƙofar taga Amado tsaye bakin ƙofar sai wasu mata biyu da bata sani ba,dukanninsu manya ne amma ɗayar babba ce sosai,sannu da zuwa tai masu kafin ta basu hanya,suka shigo tare da matan da taga suna kama sai dai dukansu babu fara a cikinsu bare tayi tunanin suna da alaƙa,shigowasu Amado da maganarsa da taji yasa Aya juyowa,sai tai ido biyu da Ummii da Iyami suna mata murmushi,fiddo idanuwanta tayi da muryar excitement ta ƙwalla kiran "Iyami!" Da sauri ta taso fuskarta ta kasa ɓoye how happy she's da ganinsu,kallo ɗaya sukai mata duk sukai turus suka tsaya,yanda ta ƙanjame sai idanuwa da karan hancinta daya sake fitowa sai kuma hasken da tai kamar wanda ba ta da isasshen jini a jiki yasa Iyami faɗin "Shalele! Ba ki da lafiya ne?" Murmushi tayi tace "sannunku da zuwa.." Ummiinta ta ajiye kayan da suke hannunta sannan tana ƙarasawa ta zauna tace "yawwa Aya ya gidan?" Murmushinta ta sake faɗaɗawa tace "lafiya lau Ummii.. Ina yini,kun zo lafiya?" Ummii tace "lafiya lau alhmdllh.. Mun sameku lafiya?" Aya tace "lafiya lau Ummii.. Na yi kewarku sosai" murmushin ƙarfin hali Ummiin tayi,Tayyibah data dawo ta wuce kitchen kawo masu ruwa tana murmushi tace "sannunku da zuwa Ummii" Ummii tana kallonta da rashin sani tace "yawwa.. Mun sameku lafiya?" Tayyibah tace "lafiya lau.." Ta juya tare da gaisar da Iyami dake ta sauraron jin abunda Aya za tace mata,kira Amado da ya shige ɗakinsa tun shigowarsu ya ƙwalomata,ta amsa cikin jin nauyin Ummiinta da Iyami kafin ta miƙe tana kame²,ɗauke kai dukansu suka yi daga Ummiin har Iyami,ta wuce sum² ta isa ɗakin tare da buɗe ƙofa ta shiga da sallama,ya amsa daga inda yake yana kallonta fuskarsa a ɗan sake da fara'a sosai yace "come and sit,magana za muyi" ƙarasawa tayi gaban gadon da yake zaune ta zauna gefenshi,ya juyowa ya fuskanceta yace "shawara nake so muyi" ta gyaɗa kanta a hankali tace "tou na mene ne?" Yace "me kike ganin ya kamata za'a siyoma su Iyami?" Ta ɗan girgiza kanta tace "ban gane me kake son cewa ba" yace "okay! I mean wani abu da za su so,and na ga kamar baki yi girki bane shi ne nake tambayarki" murmushi ta saki tana girgiza kanta tace "yanzu zan shiga nayi masu,ba sai an siyo wani abu daga waje ba" yace "za ki iya yi ɗin?" Ta gyaɗa masa kai tace "Mmmm!" Yace "okay! Shi kenan,bari naje zan dawo ba da jimawa ba" tace "tou a dawo lafiya.." Ya amsa yana ɗaukan wayarshi tare da miƙewa zai fita,itama ta miƙe ta bi bayanshi suka fito tare,yana ɗan nuna jin kunya yaiwa su Iyami da suke hira da Tayyibah sallama ya fita,Aya da su duka sukai mashi fatan dawowa lafiya har ya fita. Fasa zaunawa tayi ta ɗauki plate ɗinta da bata gama cinye kwaɗon zogalen ba,ta nufi hanyar kitchen tana cewa "Iyami bari na ɗaura maku abinci,ban san za ku zo ba da kafin kuzo na yi" da sauri Iyami tace "dawo kiyi zamanki ki huta Shalele.." Aya ta juyo tana kallonsu kamar za tayi kuka tace "Iyami baza kuci abincin ba?" Iyami tace "kafin mu fito sai da muka ci abinci,zo kiyi zamanki ki huta,ke da baki da lafiya ta ina za musa ki wahala?" Aya tace "Iyami ai ba wahala bane,kuma na warke ma" Iyami tace "tou ke da bake kaɗai ba,idan ba kya samun hutu ai sai kisa abunda ke cikinki ya zube" kallon kallo akai tsakanin Aya da Tayyibah da kuma Iyami,Tayyibah tana dariya tace "Iyami ciki ne da ita kou?" Iyami tace "shi ne mana ga ta nan duk ta ɗashe tai fari fau" Tayyibah tace "alhmdllh! Kinga maganar da na gama maki kenan kika ce ba haka ba" dawowa Aya tayi ta zauna tana cin zogalenta a shagwaɓe tace "ni ba ni da komai" Iyami tai mata wani kallo tace "idan kina musu ai shi ciki ɗan duma ne,da kansa zai bayyana kansa idan lokaci yayi" cikin son kawar da maganar da suke Aya tace "Iyami amma a nan za ku kwana kou?" Ummiinta tai saurin tarar numfashinta tace "a'a yau za mu koma,mun shigo sari ne muka biyo ganinku" rau² idanunta sukai tace "tou Ummii ku kwana mana gobe sai ku tafi" Ummii tace "ai ba a garin gaɓa² muke ba da za mu kwana gidanki" a shagwaɓe ta juya ta kalli Iyami tace "Iyami ai ke za ki zauna kou?" Murmushi Iyami tayi tana girgiza mata kai tace "a'a Shalele tafiya za muyi,wata rana dai idan Allah ya nufa ɗin idan muka zo zan kwana" tashi Tayyibah tayi tana cewa "Sis bari naje na dawo" Aya ta gyaɗa mata kai tace "tou shi kenan,yau kin bani abu na ci bai dawo min ba,Allah har murna nake nima,Allah ya biyaki da gida a aljannah" Tayyibah tace "ameen.. Haka ake so ai,bari naje nai sauri sai an jima zan dawo" Aya tace "alright ina nan ina jiranki" sallama taiwa su Iyami sannan ta fita. Tana tafiya Iyami tace "Shalele ita wannan a ina kika samota?" Aya tace "a samanmu suke ita da mijinta" Iyami tace "Allah sarki ba dai fara'a da kirki ba kuwa" Aya tana murmushi ta kwantar da kanta jikin Iyami tace "Tayyibah! Ai Iyami baki ga komai ba daga cikin halayenta,tunda muka zo garin nan wallahi ko yaushe muna tare,idan ban je ba za ta zo,kuma ta ma fini zuwa,tun tana fushi tace itama za ta dena zuwa har ta gaji ta watsar.. Tunda na fara rashin lafiya ita take zuwa ta taimaka min da aikace²,babu abunda zan ce mata sai godiya" Iyami tana gyaɗa kanta tace "Allah sarki,ai kuwa kin samu abokiyar zama ta ƙwarai,Allah ya biyata ladan wannan ɗawainiya dake da take" Ummii da Aya suka amsa da "ameen." Hira suka ci gaba da yi tun bayan fitar Tayyibah,Iyami take cewa "shiru² kuma Shalele tunda kuka taho,muna can sai zuba ido muke muga kou za ku zo" Aya tai ajiyar zuciya tace "nima tunda muka zo nake son ganinku amma kuma sai na kasa tambayarsa,saboda rashin lafiyar da naita yi,tou shima ɗin kuma ba zama yake ba,sannan bai ma je garin ba nake ga,yau nake maganar zan faɗa masa kou zai barni naje,sai kuka min bazata kuka zo" Iyami tace "ai kuwa muna zuwa garin sosai muma,sai dai bamu taɓa maganar zuwa dubaku ba,kada ace muna sintiri gidanki.." Aya tace "Iyami waye zai ce kuna zuwa? Mu da nan kowa rayuwarsa yake yi babu ruwan kowa da wani" Iyami tace "ai na ga alamun haka,tunda muka shigo naga manyan gidaje nake ta mamaki" murmushi Aya tayi tace "ai kuwa Iyami daga ni sai Tayyibah muke rayuwa bamu san kowa ba a nan,da ita kaɗai ce sai da muka zo,mijinta ma ya saba idan ya dawo yaga ba ta nan ya san tana nan,shi yasa ba ya damuwa" Iyami dai ta sake sai hiransu suke Aya tana bata labarin Tayyibah,Ummiinta kam sai dai tayi murmushi kawai,maganarta ba ya wuce jefi² har aka fara kiran asr,suka tashi domin gabatar da sallah,Aya ta kaisu bedroom ɗinta suka yi,bayan ta idar ta fito ta barsu a ciki ta nufi kitchen domin sama masu abunda za su ci kafin su tafi,tunda sun dage tafiyar za suyi a yau,sai ga Tayyibah ta yi knocking,ta tafi tare da buɗewa tana murmushi,Tayyibah dake ɗauke da basket da warmers a ciki ta shigo tana cewa "maman biyu sannu da gida" kallonta Aya ta tsaya tana yi cike da mamaki tace "ba dai wahala kika sa kanki ba Sister?" Tayyibah tai mata wani kallo tace "wahala? Ke kika sanshi.. Dan na yima su Ummii girki shi ne ya zama wahala? Allah za mu samu matsala dake akan maganar nan" Aya tai ɗan murmushin yaƙe tace "yi haƙuri tou na daina muje ciki" kallon parlon Tayyibah tayi ta juyo ta kalli Aya tana cewa "ba dai sun tafi ba?" Aya ta girgiza mata kai tace "a'a suna sallah ne,nima fitowata kenan zan shiga kitchen nai girki naji knocking" Tayyibah tace "ohh! Na ɗauka har sun wuce ne,baki ji yanda naji ba,nace amma baki sanar min nazo muyi sallama ba" Aya tace "a'a suna ciki" zaunawa nan parlour sukai suna ta hira har su Iyami suka fito,Aya take cewa "Iyami ga abinci Sister Tayyibah ta kawo maku" Iyami tana kallon warmers ɗin masu kyau tace "har da wahala kuma ƴar nan?" Tayyibah tace "ba wahala bane Iyami,ai duk abunda nayi maku ban faɗi ba,matsayin iyaye kuke a gurina nima" Iyami tace "haka ne mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi.. Ya baku masu yi maku kuma" Tayyibah tace "ameen.." Zama suka yi Aya ta taso za ta zuba masu,Tayyibah ta rigata tana cewa "mu dai ki rufa mana asiri ki zauna,ke da ba isasshen lafiya ba yau sai son ki wahalar da kanki kike,salon gobe ki kwanta ki barmu da aiki.. Don't worry abeg je ki zauna,zan yi serving ɗinsu" abinci ne me rai da lafiya da haɗin salad,sai tamarind juice da tayi masu a wani madaidaicin cooler,ta shiga kitchen ta ɗauko plates ta zuba masu ta ajiye,Iyami da Ummii sai sannu suke mata suna mata godiya,nan suka zauna suka ci suka ƙoshi,Aya kam lemon tamarind ɗin taita sha abunta,tsami²n sosai yai mata daɗi a baki. Guraren 6pm su Iyami suka fara shirye-shiryen wucewa,gaba ɗaya Aya tai wani irin laushi,haka kawai taji ba ta son su tafi,amma ganin da gaske baza su zauna ba yasa ta haƙura,kayan da suka saro da suke ajiye parlon Iyami ta isa ta kwance ta fitar da tsaraban da suka yo mata,tana cewa "Shalele ga nan tsaraban da muka yi maku babu yawa" su Aya suna tai masu addu'ah,Iyami da Ummii suka ɗauki kayansu,Tayyibah ta karɓi wani suna shirin fita,Aya tace "Iyami baza ku jira har Yaya ya dawo kuyi sallama ba?" Iyami tace "a'a idan ya dawo dai kya sanar masa mun tafi,kada mu ɗaura masa nauyi" Aya tace "kai Iyami ke dai kawai kina son ku tafi ne" Iyami tai murmushi tace "tou Shalele so kike mu dawo gidanki mu tare?" Aya ta rausayar da kai cikin damuwa tace "Iyami tou amma za ku sake dawowa?" Iyami ganin damuwa a fuskarta tace "in sha Allahu za mu dunga zuwa muna dubaku akai² yanzu" Aya tace "tou! Allah ya kaiku lafiya,a gaida Baaba Uwani" Iyami tace "za taji in sha Allah.. A gaisar da shi Ahmadin,kice masa mun tafi" Aya tace "tou Iyami" tare suka fito ta rufe ƙofar da makulli,saboda zuwa raka su har wani irin farin ciki take ji ganin za ta fita yau,tunda suka zo bata taɓa zuwa ƙofar get ɗinsu ba,idan kaga ta fito tou sama za taje gurin Tayyibah,banda nan ba ta da gurin zuwa,suna fitowa get ɗinsu sai ga shi tare da Usman suna sauka Napep da ya kawosu,ganinsu yasa su Aya tare da su Iyami tsayawa,suna fitowa cikin tricycle ɗin Amado ya tsayar da me Napep ɗin,gaishesu Usman yayi suka amsa suna yi masu sannu da zuwa,Amado yana kallon Aya yace "ba dai har tafiya za suyi ba?" Ta gyaɗa masa kai a sanyaye,kamar za tayi kuka tace "ehh! Nace ma su jira har ka dawo suka ce a'a dare zai masu a hanya" Amado ya ɗan yi murmushi yace "Iyami baza ku kwana ba? Yamma ai ya yi sosai yanzu,kafin ku samu abun hawa dare zai iya yi" Ummii tai saurin tarar numfashinsa tana cewa "a'a Ahmadi gara mu wuce,wani lokaci ai za mu sake zuwa dubaku,tunda munga lafiya kuke alhmdllh" gyaɗa kansa Amado yayi yana cewa "shi kenan Aunty bari na shiga na fito" Ummii tace "tou Ahmadi Allah yasa baza ka jima ba" yai murmushi yace "yanzu zan fito in sha Allah" Usman da suka koma gefe da Tayyibah tana son yi masa bayanin su Ummii tace "Baby Ummiin Sister Aya ne da Grandma ɗinta suka zo" Usman yace "Allah sarki,tafiya za suyi ne?" Tace "ehh haka suka ce,sun ƙi yarda su kwana" Usman yace "Allah sarki ai kin san Fulani,baza su zo gidan ƴarsu su zauna ba" Tayyibah tace "danma they're relative" yai murmushi yace "ai duk da haka,in da wani yaren ne bama sai ance masu ba zama za suyi,gaskiya suna da kirki" Tayyibah tace "danma sun fito za su tafi ne,amma kar kaga hiran da muka yi da su,suna da kirki sosai²" fitowar Amado yasa Usman da Tayyibah isowa gurinsu Iyami,a gurguje sukai sallama su Iyami kam tuni suna cikin tricycle,Amado ya ƙarasa ta gefen Iyami tare da miƙa mata kuɗin da ya fito da su da wata baƙar leda babba da ya ajiye sanda suka sauka tricycle ɗin,yana cewa "Iyami ga shi babu yawa,Allah ya tsare hanya" Iyami ta buɗe baki tace "haba Ahmadi har da wahala" yayi murmushi yace "Iyami babu wahala ai yiwa kai ne" Usman ma da bai san da zuwansu ba,2k ya zaro ya ƙara masu akai yana cewa "Iyami ayi haƙuri dan Allah babu yawa,kou ruwa kwa sha a hanya" Iyami tace "tou kaima Usman har da kai,mun zo baku sani ba mun saku wahala,mun gode Allah ya saka da alkhairi" Usman yai murmushi yace "babu komai Iyami,Allah ya tsare ya sauke ku lafiya" suka amsa suna sake yi masu sallama,Ummii tana ɗagama su Aya dake gefe hannu tace "tou mun tafi sai wani lokacin idan Allah ya sake kawomu" Tayyibah ta amsa tana masu fatan sauka lafiya,mai Napep ya tada za su wuce,sai ga hawaye ya fara saukowa shar fuskar Aya,Ummiinta na kallonta tace da me Napep "ɗan nan yi maza kaji muje" Amado ya sunkuyo yana son yai masa bayani yace "arghm! Ka san ta inda za ka bi ai kuyi saurin isa kou?" Me Napep ya ɗan yi jimm alamar tunani,Amado yace "ka ga yanzu idan kun fita daga nan zaku kai har ƙofar ɗan agundi,sai ka ɗauke hanya ku koma ta gandu,daga nan sai ka koma kan Zaria road,idan kun kai roundabout kafin AKTH sai ka bi ta Maiduguri road,kana kaisu can Mariri hotoro za su samu motar in sha Allah,idan kabi nan kamar zai fi sauƙi baza ku tsaya ba" Me Napep yace "haka ne Oga.." Iyami tace "tou Ahmadi mun gode Allah yayi albarka,mun barku lafiya.. Sai wani lokacin idan baku zo kafin nan ba" ya amsa da "ameen.. A gaida mutanen gidan,in sha Allah za mu zo,amma ba yanzu ba" suka amsa sannan me Napep yaja suka tafi,suna tsaye a gurin su dukansu sai da suka daina gano Napep ɗin,sannan suka koma ciki,Tayyibah na tsokanar Aya wai kou dai a kira su Ummii su dawo ne? Ita dai bata ce komai ba suka wuce,a compound Tayyibah tai masu sallama tabi bayan Usman da ya wuce ɓangarensu,while tana bawa Amado sallahun ya rarrashi Aya,yai murmushi har suka shige parlour suma,saurin janyota jikinsa yayi bayan ya rufe ƙofar yana mata wani irin kallo ƙasa²,ita kam har tsoro ma ya bata ta zazzaro idanuwanta tana yin fuskar kuka,a hankali yace "kukan me kike? Kou duk na shagwaɓar ganin Ummii ne da Iyami?" Gyaɗa masa kai tayi tace "tou ba kaƙi bari muje ba? Ni tunda muka zo kou waya da su ban yi ba,ai dole na damu" yana mata murmushi yace "ba laifi na bane kou da kika ga bamu je ba har yanzu,Baba ne yace muyi zamanmu mu huta ba sai mun je ba" saurin kallonshi tayi tace "saboda me?" Da muryar raɗa yace "cewa yayi kada muzo yanzu,sai an kwana biyu" Aya tace "tou kai me yasa baka je ba?" Yace "muna yin waya ai" taɓe baki tayi tace "okay!" Daga haka ta fara ƙoƙarin ƙwacewa ta tafi,yai saurin dawo da ita yana kallonta yace "saurin me kike ne?" Tace "fitsari nake ji ka sakeni,kuma lokacin sallah ya kusa ma" yace "and then?" Tace "a'a shi kenan" yace "alright! Amma na ga kamar yau kin samu lafiya,kou duk ganin Ummii ne?" Ta gyaɗa masa kai da sauri tace "ehh! Yawwa ɗazu ma muna magana da Sis Tayyibah" yace "okay! Akwai wani abu da ya kamata na sani ne?" Tace "Mmmm! Cewa tayi na sanar maka kou za ka bari muje hospital" yace "me za kuje yi hospital?" Tace "Mmmm.. Dama" sai kuma tayi shiru,hannunta yaja suka ƙarasa saman kujera yace "uhmn! Ci gaba ina ji" tace "babu komai.." Kallon tuhuma yai mata yace "kin taɓa ganin anje hospital babu dalili?" Tace "um'um! Dama ita da Iyami ne suka ce wai.." Sai ta sake yin shiru,zaunar da ita yai yana mata murmushi yace "suka ce me?" Ɓata rai tayi tace "wai ciki ne da ni.." Dariya sosai ya fashe da shi yana buɗa idanuwa yace "Wow! Really?" Ta watsa hannuwa tace "ما بعرف.." Sam ta manta ba da Ummiinta take magana ba,ya ɗan yi jimm yana kallonta fuskarsa da murmushi yace "tou yanzu ya za'ayi?" Ta sake cewa "ما بعرف.." Yana kallonta da kyau tare da gasping yace "uhmnn! Amma dai kin san ni ba balarabe bane,sannan kuma banje Saudi na yi zaman shahada ba.. Right?" 



     #Ehhh! Lallai Amado ka kyauta tabbas da wannan maganar,dama ai mun san baka je ka yi zaman shahada a Saudiyya ba,ba sai ka faɗa dan ka ɓata mana rai ba..🤔🤕



*MAZAN FAMA GLOBAL COMMUNICATION..*


     ```Muna farin cikin sanar da ƴan uwa tare da masoya cewa,wannan Company namu yana siyar da data akan farashi me sauƙi na networks da muke da su a Nigeria kamar haka:```


*MTN*

 

500MB—₦150 

1G—₦300 

2G—₦550 

3G—₦850 

5G—1,450 

10G—₦2,750. 


FOR DATA BALANCE 

DIAL:*460*260# or *461*4#


 *AIRTEL*


500MB—₦150 

1G—₦300 2G—₦550 

5G—₦1,4000 

6G—1,650. 


DATA BALANCE *140#


 *GLO* 


1.35G—₦550 

2.9G—₦1,050 

5.8G—₦1,500 

7.7G—2,050.


DATA BALANCE *127*0#


*9MOBILE*


2G—₦1,200 

3G—₦1,650 

4G—1,950 

6G—₦2,600 

7G—₦2,900. 


DATA BALANCE *228# 


contacts:***



Account №:6074981401 

Account name:Aliyu Muhammad Usman

Bank name:9 Payment Service Bank. 



#Follow

#Vote

#Comment

#Share

#Asli Smasher.