DAUĆŠAR GORA!

EDD

by @realsmasher

đź’ đź’ đź’ đź’ đź’ 

©®AS-2023.







         *♡DAUĆŠAR GORA¸.•💥*

           (CÉŞá´‹ÉŞ á´‹á´€ sĘśá´€ ᴛᴀ)  







Ná´€

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).đź’•

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

••••••••••


*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..*




              20 




#EDD! 



             Kallon Ummii kawai take zuciyarta na mata Ć™aiĆ™ayi,Allah ya sani har ranta take jin ba ta son tafiyar nata,sai dai ba ta da bakin cewa komai,kasancewar jirgin dare Ummii za ta bi,Iyami kuma za ta kwana nan gidan Aya,sai washe gari sannan ta kama hanyar komawa gida,yinin ranar haka nan Aya taita hidima da su har yamma suna ta hira da Tayyibah akan tafiyar ta Ummii,kou da Amado ya dawo daga aiki ya tarar da su a gidan,bai nuna damuwa ba tunda sun saba zuwa,ya tsaya tare da gaishe da su Iyami respectfully kafin ya wuce É—akinshi,Aya ta tashi tabishi tai masa sannu da zuwa ya amsa,kasancewar yau ya É—an so yin dare yasa a hankali tace "a kawo abincin yanzu kou sai ka dawo daga masjeed?" Yana É—an yamutsa sumar kanshi mara yawa yace "no! Zan yi sallah first sai na ci" tace "okay!" Tare da gyaÉ—a kanta,har ta juya za ta fita ta dawo tana cewa "ohh! Na manta ban sanar maka zuwansu Ummii ba" ya gyaÉ—a kansa yana rage kayan jikinshi yace "no worries! Ai na gansu mun gaisa yanzu kafin na shigo" tace "ehh! Hakane,amma Iyami za ta kwana nan ne tare da mu,gobe in sha Allah tace za ta wuce" juyowa yayi yana kallonta a gajiye yace "and then?" Tace "a'a babu komai,dama na manta ne bamu yi maganar tafiyar Ummii ba" wani irin kallo yai mata yace "wani gurin za taje?" Aya tace "ehh! Yau da dare jirginsu zai É—aga" yace "as in? Zuwa ina?" Jikinta a sanyaye tace "za ta koma Saudiyya ne" kallonta ya dunga yi har na tsawon minti uku,kafin yace "Saudiyya?" Ta gyaÉ—a mashi kai tana ta Ć™oĆ™arin mayar da hawayen da suke son saukowa fuskarta,kasa cewa komai Amado yayi,kawai sai ya wuce ya nufi bathroom,a hankali Aya ta É—ago kanta tare da sa hannu ta share hawaye sannan ta juya ta fita É—akin. Har Amado yai wanka ya fito ya shirya cikin Ć™ananan kaya ya fita masallaci sallar ishaa maganar da Aya tayi bai bar yi masa yawo a cikin kai da zuciya ba,sam bai ga dalili kou amfanin ace Ummii za ta koma Saudiyya da zama ba,tou amma shi meye nashi? Tunda har mahaifiyarta ta amince mata,ina ruwansa da saka kanshi cikin matsalar da bai shafeshi ba? Tou amma kuma ai ya ga kamar Aya ba ta son tafiyar nata,wani zuciyar yace "dan ba ta so kou ta nuna maka haka,mene ne ribar ka idan ka shiga tunda ba fasawa za tayi ba?" TaÉ“e baki yayi tare da shigewa masjeed,bayan an idar da sallah ya taso tare da nufo gida,sai dai wannan karon bai tarar da su a parlour ba,kai tsaye shima ya wuce É—akinsa cikin halin kou in kula da wancan maganar,yana shiga ya samu guri gefen katifarsa yai zamansa yana wani tunanin daban akan matsalar gidansu,Aya da taji shigowarsa ta fito bedroom inda suke tare da su Iyami bayan sun idar da sallah,kitchen ta isa ta haÉ—a masa abinci sannan ta É—auko tana tafiya a hankali ta nufi É—akinsa tare da yin knocking,yana jinta amma kou tari bai yi niyyar yi wanda zaisa ta fahimci kou yana wani uzurin ne shi yasa bai amsa ta ba,da yake ta saba da wasu cikin halayensa dan kanta ta buÉ—e a hankali tare da yin sallama ta shiga,bai É—ago ba har ta isa gabansa ta ajiye tray É—in sannan ta miĆ™e tana sakin numfashi me kama da haki tace "kana son wani abu kuma?" Ya É—ago idanunsa ya kalleta,ba tare da ya ce komai ba ya kalli warmers É—in abincin,kamar bazai buÉ—e baki yai magana ba,cike da izza yace "ina son tea" gyaÉ—a mashi kai tayi sannan ta juya ta fita,ruwan tea É—in ta É—aura mashi tasa kayan Ć™amshi sannan ta haÉ—awa su Iyami abinci ta fito ta nufi É—akinta,tana yin sallama Iyami ta tashi ta tareta tana cewa "sannu Shalele.. Allah ya raba ku lafiya,kina ta Ć™oĆ™ari da mu tunda muka zo" sanyayyan murmushi tayi kafin tace "Iyami bari na kai masa tea na dawo,ku fara cin abincin kada ku jirani" Iyami tace "tou ki samu ki ci abincin mana tukun" Aya tai mata murmushi cike da son É“oye damuwarta tace "zan ci Iyami,bari na kai masa na dawo" Iyami ta gyaÉ—a mata kai a hankali tace "tou shi kenan" juyawa Aya tayi ta fita,Ummii ta bita da kallo cike da so da tausayinta,sai ta tuno lokacin da take É—auke da cikinta kamar haka,mahaifinta sam bai bari tai hidima da shi kamar yanda Ć´arta ke fafutuka da nata mijin,tun yamma take ta zarya tsakanin kitchen da parlour,haka kou yanzu ma tunda tai sallah take ta hidima da su da kuma mijinta,ita lokacinta duk abunda za tayi Bukar ke tayata,haka za aita tsaiguminta ana mata habaici ta shanye shi,shi kuma ana ce masa mijin tace,sai yai murmushi yace "ni mijin kafin tace ne,baza ku gane adadin soyayyar da nake ma Maryama ba,kou dan baku yi dace da miji kamar nata bane shi yasa kuke adawa? Ni É—an zamani ne,kuma na san soyayya,duk abunda nake mata ina yi ne saboda sunnah,ina koyi da Annabin rahama (S.A.W),kuma kuce da mazajenku suje su koyo yanda ake soyayya" da irin maganganun nan yake kashe bakinsu,sai kaji shiru baza'a samu wanda zai sake cewa komai ba,ajiyar zuciya Ummii ta sauke tare da jinjina Ć™oĆ™arin Aya da dauriyarta. Aya na fitowa kitchen ta sake nufa,nan ra tarar ruwan yai zafi sosai yana neman tafasa,tsayawa tayi gefe har ya juya,kamar baza ta sauke ba ta barshi yaita tafasa,sanin ya fi son a haÉ—a masa tea yana sha yana Ć™ona baki,idan ma yasha yaji bai masa yanda yake so ba,zai iya cewa ta koma kou ya ajiye mata abunta yace tasan yanda za tayi da shi,sai can kafin tasa karamin rariya na tatar shayi ta tace,sannan ta haÉ—a ta É—auko ta nufi É—akinsa,tana shigowa ta sameshi kishingiÉ—e yana operating wayarshi,tai sallama tare da Ć™arasawa ta ajiye masa tea É—in a cikin mug,tashi yayi yana kallon yanda ruwan ke tiriri ya kai hannu ya fara taÉ“a jikin mug É—in kafin ya É—auka,ita kuma Aya ta samu guri nan saman carpet ta zauna jiran ya gama ta kwashe kayan kamar yanda ta saba dare da safiya,ruwan tea É—in na Ć™ona masa baki ya dunga sha a haka har ya kammala sannan tayi serving É—insa abinci,babu mai magana cikinsu ya kama cin abincinsa,sanda ya gama ta tattara komai ta É—auka,za ta fita yace "idan kin gama abunda kike kizo ina son ganinki" gyaÉ—a mashi kai tayi tare da juyawa ta fita,sai da ta fara kai kayan kitchen sannan ta koma É—akinta,tana shigowa Iyami ta fara yi mata sannu,tai murmushi ta Ć™arasa tare da zama tana sauke ajiyar zuciya,sai sannan ta É—ebi abinci ta fara ci,dan already su Iyami su har sunci tunda ta ce kada su jirata,so they thought can gurinsa za ta ci,sai suka ga saÉ“anin haka,sai dai babu wanda ya tambayeta tsakanin Iyami da Ummii suka zub mata idanu kawai,tana gamawa ta kwashe kayan ta fita da su,sanin ba É—an tayin aiki gareta ba yasa take dabara tayi wanke² tun dare,da safe kuma sai dai taji da shirya breakfast da gyaran gida,ba ita ta baro kitchen ba sai da ta wanke komai ta mayar da shi muhallinsa,tana gamawa ta dawo É—akinta ta shiga tai wanka,sanda ta fito sai da ta gama komai har sallar shafa'i da wutr kafin tace masu za taje yana kiranta,Ummii tai mata murmushi tace "tou ni dai sai muyi sallama dake tun yanzu kou?" Aya ta girgiza mata kai tace "a'a Ummii ai zan dawo,kuma ina son zuwa nai maki rakiya airport" Ummii tai mata murmushi tace "tou shi kenan,sai ki sanar masa idan kin je,in ya barki sai muje É—in kwa dawo daga baya" gyaÉ—a mata kai tayi sannan ta juya ta fita,knocking Ć™ofar É—akin ta fara yi then ta tura ta shiga da Ć´ar siririyar muryarta tai masa sallama ya amsa,ta yi zaton wani abu yasa shi kiranta,da ta shigo ta É—an tsaya tare da cewa "ga ni kace nazo idan na gama" bai É—ago ba haka nan fuskarshi babu fara'a kou kaÉ—an yace "samu guri ki zauna" kamar yanda ya buĆ™ata ta zauna a hankali,tana wasa da yatsun hannunta tai shiru tana jiran yai magana,bai bi ta kanta ba sai da ya gama abunda yake a wayarshi kafin ya ajiye tare da miĆ™ewa yaje ya kashe bulbs É—in É—akin,duhun da ta gani ya mamaye ko ina,da sauri ta É—ago kanta tana kalle²,kamar wacce bata saba da yanayin ba,haka nan tsoro ya cikata ta dunga Ć™yafta idanunta har sanda ya iso gurinta,a hankali ya kai hannu ya cire hijab É—in dake jikinta,ita kam tana ganin ikon Allah,dan batai zaton wannan al'amarin yanzu ba,kou dan su Iyami da Ummiinta da suke gidan,har ya gama budurinshi ya koma gefe ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya bai ce komai ba,ta laluba a hankali tare da janyo rigarta kafin ta sauka tare da wucewa bathroom ta gyara jikinta,tana wanka tana sauke ajiyar zuciya tare da kallon cikinta dake motsawa lokaci²,har ta gama ta fito ta tsaya tare da tsane gashin kanta sannan ta É—auki hijab É—inta za ta fita,sai sannan ya É—ago kansa a hankali yace "ina za kije?" Juyowa tayi tace "zan koma gurinsu ne" yana mayar da kanshi saman pillow yace "kada ki sake ki bar É—akin nan" ba ta da zaÉ“i bayan tabi umarninsa,jikinta a sanyaye ta dawo tare da komawa ta kwanta tayi shiru tana tunani har bayan wani lokaci,É—an juyowa tayi tana kallon gurin da yake kwance,cikin sanyin lafazi tace "Mmmm! Yaya!" Da sauri ya buÉ—e ido sosai yana kallonta,sai tai shiru kuma ta rasa me za tace,da wani murya yace "ina jinki" cikin wani trembling voice tace "dan Allah ina son zuwa raka Ummii" kai tsaye muryarshi babu alamun wasa yace "zuwa ina?" A hankali tace "airport!" Wani irin kallo ya dunga yiwa inuwarta kafin ya miĆ™e,ba tare da yace komai ba yai wucewarshi bathroom,sanda yayo wankan tsarki ya dawo,ya canja kayansa zuwa na bacci yai kwanciyarsa tare da juya mata baya ya kulle idanunsa,Aya da batai zuciya ba cikin sanyin jiki ta sake cewa "dan Allah.." Bai juyo ba yace "ki yi bacci" kamar za tayi kuka tace "ai idan na kwanta lokacin tafiyarta yai bazan sani ba" da wani kakkausar murya kamar suna faÉ—a kou kuma dama yana jin haushinta yace "and so fucking what? Malama kin dameni da maganar tafiyar nan,ta tafi mana sai me? Ni mene ne nawa a ciki,zan hanata yin abunda zuciyarta ke so ne?" Wani irin kuka taji yana neman Ć™wace mata ta daure muryarta na rawa alamun kukan yana daf da zuwa tace "amma bamu yi sallama ba ai" so pissed off yace "will u please shut ur mouth up? Nace baza kije ba,kou akwai wanda ya isa sawa na barki?" Da sauri ta rufe bakinta hawaye suna É“allewa idanunta ta fashe da wani irin kuka me cin rai,yaja tsaki ba tare da ya juyo ba yace "ki mutu!" Sosai taci kukanta ita É—aya,duk tayi shiru tana tuna maganganunsa sai taji hawaye sun sake É“allewa idanunta,tsayin lokaci ta É—auka kafin wahalallen bacci ya sace ta,duk yanda taso kada tai bacci saboda tayi sallama da Ummiinta,amma ina ciwon da kanta yaita yi saboda kuka da kuma gajiyar da ya tara mata,banda na aikin da taita faman yi,nan suka taru suka danneta,sam ta kasa hana kanta faruwar hakan. Around 1am Ummii suka fito parlour ita da Iyami,Ć™asa² Iyami take cewa "Aya kam ina jin ta yi bacci can gurin mijinta,gashi kuma baku yi sallama ba har lokacin tafiyar naki ya yi" Ummii tai É—an murmushi tana kallon hanyar É—akin Amado tace "babu komai Iyami,ina ga gajiya tasa ta yin bacci" Iyami tace "ai fa ta yi fama kam ta sha aikace²,Allah dai ya basu zaman lafiya" Ummii tace "ameen.. Iyami bari na wuce,idan ta tashi da safe kya sanar mata na tafi,tayi min addu'ah na sauka lafiya" Iyami ta gyaÉ—a mata kai a hankali tace "tou! Kou dai aiwa shi Ahmadin magana ne ya taso ta?" Ummii tai saurin girgiza mata kai tace "a'a Iyami gara ki barta,yanzu idan ta fito kin san halin rigimarta,gara ace sai bayan na tafi sannan ta samu labarin,na san kukan da za tayi bazai kai wanda idan ace a gabanta zan tafi ba" Iyami ta sake gyaÉ—a kanta tace "tou shi kenan.. Allah ya tsare Maryama,ubangiji ya kaiku lafiya,dan Allah ki kula kin ji,ki kama mutuncin kanki.." Ummii tace "in sha Allah Iyami,na gode sosai Allah ya saka da alkhairi.. Yanda zan barku lafiya,Allah yasa na dawo na sameku lafiya.." Rungume Ummii Iyami tayi tana goge Ć´an Ć™wallar data taru gefen idanunta tace "dan Allah ki dunga bugo waya kina jin halin da muke ciki ni da Ć´arki" Ummii tace "in sha Allah Iyami" horn É—in da suka jiyo,yasa ta saurin É—aukan jakarta ta rataya sannan ta É—auki ta kayanta tana cewa "Iyami me motar ya iso" Iyami tace "tou muje na rakaki bakin Ć™ofa na dawo" tare suka fito da Iyami ta rakota har bakin get inda me motar da zai kai Ummii airport yake tsaye yana jiranta da yin horn,yana ganin fitowarta ya sauko motar tare da karÉ“ar kayanta yasa a booth,Ummii kuma ta buÉ—e gaba ta shiga,bayan ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima ya tada motar,Iyami na tsaye get É—in gidan su Ummii kuma suna shirin tafiya sai ga Tayyibah da Usman sun fito,da É—an gudunta Tayyibah ta isa gaban motar tana faÉ—in "Ummii! Allah ya tsare ya sauke ku lafiya" murmushin Ć™arfin hali Ummii tayi idanunta akan get É—in gidan zuciyarta na mata babu daÉ—i saboda rashin ganin Aya ba tare da sunyi sallama ba,ta amsa mata tana cewa "kuyi haĆ™uri mun tasheku daga bacci" Tayyibah tace "laaa! Ummii babu komai wallahi,ai gashi har na fito mun yi sallama" sai ta miĆ™awa Ummii wani roba me É—an girma tace "Ummii ga shi babu yawa,Allah ya sauke ku lafiya" kallon robar dake cikin leda Ummii tayi kafin ta É—ago kanta ta kalli Tayyibah tace "na gode sosai Tayyibah,Allah yayi albarka,ya kawo babban rabo" Tayyibah tai dariya sannan ta É—an koma baya tana É—agawa Ummii hannu,Usman yai mata addu'ar sauka lafiya tare da bata Ć´an kuÉ—i yace ta sha ruwa a hanya,ita kuma tana tai masu godiya har me motar yaja suka tafi,sanda suka dena gano motarsu kafin su koma ciki,Usman ya rufe get tare da yiwa Iyami sai da safe,Tayyibah ta kalli yanda jikin Iyami yai sanyi lokaci É—aya,kafin a hankali ta juya tabi windows É—insu Aya da kallo kamar yanda taga Iyami na kallon gurin,kou da ba'a faÉ—a mata ba zuciyarta ta sanar mata Iyami bata ji daÉ—i ba,haka nan itama sai take tuhumar kanta dalilin rashin ganin Aya da Oga Ahmad,kou dai ace basu raka Ummii airport ba a matsayinta na surukarshi,amma ai ya kamata ace sun fito kou iya bakin get ma suga tafiyarta,wannan tunanin sai yasa ta saka alamar zargi cikin abunda ya faru,da Ć™yar ta iya yiwa Iyami sai da safe kafin tabi bayan Usman zuwa É“angarensu,Iyami ma haka nan taja jikinta ta koma ciki ta rufe ta isa É—akin Aya,sai dai tuda ta dawo ta kasa bacci saboda tunanin dalilin rashin fitowar Aya da Amado,tabbas ta san ba nauyin bacci ne da Aya ba kou da can,sai dai in akwai abunda yake faruwa ne kawai,tunani iri² haka yaita zuwa zuciyarta sai dai ba ta son ta yanke hukunci,dole yasa ta kawar da tunanin ta shiga banÉ—aki tai alwala tazo tayi nafila daga nan ta koma saman gadon ta kwanta har bacci ya É—auketa. Kiran assalatu ya tayar da Aya,ta miĆ™e a É—an hanzarce kamar kuma wanda ke jin tsoron rasa wani abu,cikin É—an sauri ta sauke Ć™afarta Ć™asa kafin ta tashi ta fita É—akin tana faÉ—in "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Yana jin sanda ta rufe Ć™ofar É—akin ya miĆ™e zaune yana jan siririn tsaki,komai da ya faru tun daga fitowar su Ummii,maganar da suka yi da Iyami,har zuwa fitarsu daga gidan,da horn É—in da me taxi da yazo É—aukar Ummii yayi ta yi,fitowar su Tayyibah da maganganunsu duk yana ji,kuma har sauka yayi daga saman katifar yaje ya tsaya bakin window yana kallonsu,duk akan idanunsa da kunnensa komai ya faru,sai dai tun lokacin da yaji maganar tafiyar,haka nan ya dunga jin zuciyarshi tana zafi,kuma yake jin haushin Ummii akan tafiyar da za tayi,though bai ga dalilin kanshi na jin haushin ba,amma kuma sai zuciyarshi ta dunga saĆ™a masa kar ya bar Aya suyi sallama da mahaifiyarta,saboda wannan ne hanyar da kamar zai amfani da power É—inshi a matsayin mijinta ya Ć™untatawa Ummii. Aya na fitowa ta shiga É—akinta,sai ta tsaya turus tana kallon É—akin da Iyami dake Ć™oĆ™arin tada sallah,hawaye suna ciccikowa idanunta jikinta na sakewa cikin wani murya me rauni tace "Iyami ina Ummiina? Kada kice min ta tafi banyi sallama da ita ba?" Juyowa Iyami da bata riga ta tada sallah ba tayi tana gyaÉ—a mata kai tace "ta tafi tuni Aya.. Sai dai kiyi mata fatan sauka lafiya" wani irin kuka ne ya Ć™wace mata tace "amma Iyami me yasa baki tasheni ba?" Iyami ta taho tare da riĆ™o hannunta ta zaunar da ita gefen gado tace "kiyi haĆ™uri Aya,Ummiinki ita ta hana na buga maku Ć™ofa,naje dai na rakata bakin Ć™ofar gida,har su Tayyibah ma suka fito sukai mata sallama" kallon Iyami ta É—ago tana yi hawaye wasu na korar wasu a fuskarta tace "shi ya fito yai mata sallama ne?" Iyami ta girgiza mata kai a hankali tana jin kamar da sannunshi yayi haka,Aya ta dunga kallon Iyami ta kasa dena kuka,can ta gyaÉ—a kanta tare da miĆ™ewa ta nufi banÉ—aki,har tai alwala tazo ta tada sallah kuka take,zuciyarta na mata wani irin ciwo saboda baĆ™in ciki,sai dai kou da take yarinya amma ai ta san me take,kuma tana da hankalin da za ta gane fari da baĆ™i,tas ta fahimci inda ya dosa,bayan ta idar tai azkar É—inta,ta miĆ™e tana dafe cikinta ta haura saman gadonta tare da kwanciya tayi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa,Iyami ma data idar tazo ta É—an kwanta kaÉ—an tana bata haĆ™uri,sai ta lumshe idanunta taĆ™i cewa komai,ganin kamar ta yi bacci yasa Iyami yin shiru nan bacci ya É—auketa,har gari ya gama wayewa Aya bata iya komawa bacci ba,duk sanda ta tuno Ummiinta ta tafi basu yi sallama ba,sai hawaye sun gangaro idanunta. Can guraren 8am saura ya gama shirin tafiya aiki ya fito daga É—akinsa,sai dai abun da ya bashi mamaki shi ne,yanda yaji gidan shiru babu alamun motsinta,ya gama kallon parlon kafin ya wuce hanyar kitchen,yau kam kou Ć™ofar ma a rufe yake,ya buÉ—e tare da shiga ciki,duk da shigowarsa bai fi a Ć™irga ba,amma ya karanci komai yana zaune ne a muhallinsa,babu alamar an taÉ“a wani abu kou an É—aura,tas ya Ć™araci observation É—insa ya fito tare da rufewa,Ć™ofar É—akinta ya isa yai knocking a hankali,tana jinsa itama ta shareshi,saboda yanda ta sha alwashin komai zai faru sai ta nuna masa kuskurensa,tunda sukai aure dai² da sau É—aya bata taÉ“a É—aga kai tai masa kou da kallon banza ba duk tsayin zamansu,shi ne har kuma har zai samu damar taka ta,idan yana taĆ™amar haÉ—ashi akai da ita,ai itama ba ita tace tana sonsa ba,da zai dunga mata abubuwa kamar basu haÉ—a jini ba,ita fa sai yanzu ne ma da zama ya haÉ—a su guri É—aya ta fara gane halayenshi,da can lokacin da yake mata kirki ne take masa kallon mutumin arziki,ashe mugun halinsa a É“oye suke,ai kuwa ya yi da ita dan itama side É—inta É—aya ya sani na,shi ne gefen haĆ™urinta da kawaici,aita mata abu tana shanyewa,ba ta kou kallon mutane bare ta nuna masu ta san me suke nufi,bai ga her other side ba idan tai fushi. Tana jinsa haka tai banza da shi,Iyami data farka ta kai hannu tana taÉ“ata da kiran sunanta "Shalele! Tashi maza kije mijinki na kira" sake kulle idanunta tayi tace "Iyami ba na jin daÉ—i ki barni dan Allah" Iyami tace "a'a tashi kije sai ki sanar masa,ai zai maki uzuri idan kuma za kuje asibiti nema tou" ba dan taso ba ta tashi,lokacin shi kuma yana sake knocking da kiranta "Aya please!" BuÉ—e Ć™ofar tai fuskarta É—aure tace "ga ni!" Ya dunga kallon yanda fuskarta yai ja idanunta a kumbure,lokaci É—aya kamar bai san me ya faru ba yace "breakfast fa?" Janyo Ć™ofar tayi tana wucewa parlour tace "ban yi ba" ya dunga kallonta kafin ya biyo bayanta,ya tsaya da wani irin fuska yace "kamar ya baki yi ba?" Tace "ehh! Ba na jin daÉ—i ne" tsaiwa yai ya kasa ce mata komai,ita kuma ta Ć™i kallonshi sam,gyaÉ—a kansa yai kafin a gajarce yace "okay!" Daga haka ya juya ba tare da ya sake ce mata komai ba,ya koma ya É—auko jakarshi ya fito,bai kalli inda take ba yace "na wuce office" ta sake É—auke kanta kamar bata ji ba tana dafe Ć™asan mararta dake É—an mata ciwo tana yatsina fuska,har ya kai bakin Ć™ofa Ć™ala bata ce masa ba,ya buÉ—e ya fita yana jin wani irin É“acin rai na cika masa zuciya,taÉ“e baki Aya tayi bayan ta tabbatar ya wuce kafin ta tashi da É—an sauri ta shiga kitchen,abunda za ta iya girkawa Iyami ta duba ta É—aura,har ga Allah kou da tace bata jin daÉ—i ba Ć™arya take ba saboda kukan da ta kwana yi kuma ta sake tashi da shi,amma ganin yanda ya nuna mata halin ko in kula nan ya Ć™ara tunzurota,tai Ć™wafa da faÉ—in "za ka san ka yi da me yi" da Ć™yar ta daure tai aikace²n da za ta iya,sannan ta nemi guri ta kwanta,kou abincin bata iya ci ba haka taita bin Iyami da kallo,Iyami kam tana gama yin breakfast ta fara shirin tafiya,10am ta kammala kayanta guri É—aya ta fito tana cewa "Tou! Shalele ni zan wuce" Aya ta buÉ—e idanunta da har sannan basu gama komawa dai² ba,da sanyayyan murya tace "Iyami ki bari sai anjima dan Allah" Iyami ta girgiza mata kai tace "a'a Shalele barni dai na tafi yanzun,kinga ni kaÉ—ai ce kuma zan koma na kama aikin gida nima,sai dai nace sai kun zo É—in" Aya dake jin kuka yana taho mata tace "shi kenan! Allah ya tsare hanya ya saukeki lafiya" Iyami ta amsa sannan ta É—auki buhun kayanta,a hankali Aya ta tashi ta É—auki hijab É—inta tace "bari na rakaki na dawo" Iyami bata hanata ba ta amsa mata,suna shirin fitowa sai ga Tayyibah da uban warmers É—inta ta yowa Iyami girki,tana fiddo idanuwanta take cewa "Iyami ba dai har tafiya za kiyi ba da safen nan?" Iyami tai mata murmushi tace "in sha Allahu yau sai kwanan gida,kuma yanzu ba da É“ata lokaci ba" Tayyibah tace "Iyami ai na yi zaton kin zo kenan fa sai Sister ta haihu" Iyami ta girgiza mata kai tace "a'ahh! Na dai yi magana da ita,idan mijinta ya barta ta dawo gida ta haihu" kallon Aya Tayyibah tayi lokaci É—aya ta matso tana cewa "Sis amma dai baki da lafiya?" Murmushin Ć™arfin hali ta yiwa Tayyibah ta gyaÉ—a mata kai a hankali tace "Mmmm!" Tayyibah tace "eyyahh! Sannu dear Allah ya Ć™ara lafiya" Iyami da Aya suka amsa,babu irin roĆ™on da Tayyibah bata yiwa Iyami akan ta zauna ba Iyami tace a'a,haka ta ajiye warmers É—in cikin parlon Aya suka fita rakata tare,kafin Iyami ta tafi haka tai ta jaddadawa Aya maganar zuwanta gida haihuwa,sannan tai masu sallama suna tsaye me tricycle yaja suka É—auki hanya. Tunda suka dawo Aya ta samu guri ta kwanta ta rasa me yake mata daÉ—i,da Ć™yar Tayyibah tasa ta cin abinci kafin ta kwanta,nan bacci ya É—auketa Tayyibah kuma ta zauna gadinta har yamma,kou sallah ranar sai haÉ—awa tayi,Tayyibah na tai mata sannu,tai mata murmushin Ć™arfin hali tace "thank u Sister.. Ba dan Allah ya haÉ—a ni dake ba da ban san yau ya zanyi ba" tana maganar zuciyarta a karye,hawaye suka fara biyo fuskarta,rikicewa Tayyibah tayi ta fara bata haĆ™uri tana tambayarta kou jikin ne suje asibiti,Aya ta girgiza mata kai tace "a'a lafiya ta Ć™alau,ba na jin ciwon komai yanzu.. Kawai dai ina jin zuciyata na zafi ne" Tayyibah tace "wani abu yana damunki kenan,amma kin san condition É—inki fa,kin fi kowa sanin ba'a son kina zama da damuwa,dan Allah ki sanar min me yake faruwa,domin tun dare na fahimci kamar akwai wani abu" murmushi me ciwo Aya tayi tana share hawayen da suka zubo mata,sannan ta shiga bawa Tayyibah labarin komai,Tayyibah ta dunga kallonta tana jin ranta na É“aci for no reason,dama ta fahimci haka tunda taga basu fito ba daga ira har shi kanshi Oga Ahmad É—in,tace "amma me yasa zai yi haka? Mahaifiyarki ce fa,kuma inda kara ai shima ta haifeshi tunda ta bashi Ć´arta ya aura,fisabilillah ya kamata ace har ta zo gidanki kuma ta tafi bai barki kuyi sallama ba,shi yasa mana naga Iyami ma ta dage tafiya za tayi,ashe abunda ya faru kenan" faÉ—a sosai Tayyibah taita yi kamar za ta aro baki kou kuma kamar ance mata ga Amado a gabanta,Aya tace "ai babu komai hankali ya koyamin nima.." Haka sukai ta tattaunawa kan maganar,Ć™arshe ma Tayyibah taji haushi kou jira ya dawo batai ba ta fita,dan ta rantse baza ta gaisheshi ba. Yau ma É—in bai dawo da wuri ba,dan sai can bayan ishaa sosai sannan ya shigo,Aya dake kwance ita kaÉ—ai shiru ta amsa underneath her breath sai dai bata É—ago kanta ta kalli inda yake ba,shima bai ce mata ba ya wuce É—akinsa,bayan ya gama uzurorinsa da yaga bata shigo ba,ya fito tare da buÉ—e É—akinta ya tsaya daga bakin Ć™ofar yana kallonta,sanda ya gaji dan kansa yace "na kasa fahimtar abunda kike nufi,idan wani abu akai maki ai sai ki fito fili ki faÉ—a,ba wai ki kama fushi mara dalili ba" idan ta É—ago ta kalleshi kou ta nuna da ita yake,tou Ć™ofar da yake kusa da ita ta tanka masa,ganin ba ta da niyyar kulashi ya daÉ—a sawa ya shaĆ™a,kawai sai ya fice ya bar mata daÉ—in,duk yanda wani gefe na zuciyarta yaso tanĆ™warata,fushin da take ciki da shi yasa ta rufe ido ta shareshi,a haka kwanaki suka ci gaba da wucewa,tsakaninsu babu me yiwa wani magana,kullum damuwarta tunda Ummii ta tafi bai wuce ta san yaya take ba,sai dai babu wanda ta sani da zai ara mata waya ta kirata,kou da ma ta samu É—in ita kanta ba ta da lambar Ummii É—in,shi kaÉ—ai ta sani da yake da waya,amma duk da yana matsayin mijinta,sam taji bazs ta iya cewa ya ba ta aro ba kou dan gudun kada ya wulaĆ™anta ta,musamman kuma data tuno asalin faruwar matsalar ma duk a dalilin Ummii É—in ne,hakan sai yasa ta kama mutuncinta,sai dai yanzu ba kamar da farko ba,dan ta É—an sauko har tana masa abinci da sauran hidimomi,kawai abunda ta rage kou ma ace ta daina shi ne doguwar magana da shi,za tai masa komai har ta gaisheshi,amma dariyarta gaba É—aya ta daina bari yana gani a sadaka,Iyami ma kuma tunda ta tafi,sau biyu kaÉ—ai ta leĆ™ota shima duka bata daÉ—e ba,a bakinta ne ma ta samu labarin Ummiinta har da saĆ™on gaisuwa,ba ta jira har ya dawo daga gurin aiki ya sameta za tai tafiyarta,duk dan gudun afkuwar wani matsalar,cikin wannan yanayin suka fara wani irin zama mara daÉ—i tsakaninsu,Tayyibah kullum za ta shigo kou ita taje su yini suna hira da wasa da dariya,sai dai kou itama Aya bata bari ta fuskanci irin zaman da suke ba,duk fara'arta da zaran dare ya yi ta ganta ita kaÉ—ai,kou ta duba taga lokacin dawowarsa ya kusa za ta fara É—aure fuska kou tai shigewarta É—akinta,sam ta daina shiga harkarsa akan abubuwa da yawa,shima kuma da yake soko ne ya biye mata ya fita sabgarta,gaba É—aya ya É—ebeta ya bawa banza ajiyarta,Ć™arĆ™ari idan tashi ta kawoshi nan zaita É“arin jiki da son yı mata magana,data gama ganoshi sai dai ta kalleshi kawai,da zaran ya gama samun biyan buĆ™atarsa shi kenan za su koma gidan jiya,a cewarshi fushinta da rashin magana ba damuwarshi bace,sanda suka kusan share sati uku a haka,ya gaji dan kansa ya fara saukowa tare da nemwn sulhu,ita kuma ta nuna masa ai yanzu ta fara nata fushin,duk yanda yai zaton al'amarinta sanda ya wuce nan,har gida yaje yai kwanakinsa ya barta ita kaÉ—ai,da ya dawo ya yi zaton zuwa lokacin ta sauko,amma har sannan tana kan dokin zuciya,Ć™arshe da yaga shi ne yake azabtuwa kou kuma dai huÉ—ubar Innarshi ya É—auko ohon masa,nan yace ta shirya ya mayar da ita gida ya san matsalarta,bayan ta haihu komai zai dawo dai² tsakaninsu,cikin zaĆ™uwa kuwa ta shirya da yake lokacin cikinta ya kama hanyar shiga wata na tara,ta yi zaton idan sunje gida zai kaita gurin Iyami,sai dai suna zuwa yace shima sam sai dai ta zauna nan gidan,duk kukanta da roĆ™o baisa ya saurareta ba yai wucewarshi Kano bayan ya kafa mata mugayen sharuÉ—anshi na bai yarda da fita ba kou da gidansu za ta,kuma bai yarda Iyami tazo ta zauna da ita ba tunda gidan ga mutane nan,idan ma wani abu ne ya taso ta nemi wani ta sanar masa a kirashi,iya takura da damuwa ta shigesu,domin gidan sam babu wanda ke shiga harkarta banda Baba Wada,a haka taita zaman haĆ™uri har kwanakin EDD É—inta suka wuce babu batun haihuwa kwata²...





*MAZAN FAMA GLOBAL COMMUNICATION..*


     ```Muna farin cikin sanar da Ć´an uwa tare da masoya cewa,wannan Company namu yana siyar da data akan farashi me sauĆ™i na networks da muke da su a Nigeria kamar haka:```


*MTN*

 

500MB—₦150 

1G—₦300 

2G—₦550 

3G—₦850 

5G—1,450 

10G—₦2,750. 


FOR DATA BALANCE 

DIAL:*460*260# or *461*4#


 *AIRTEL*


500MB—₦150 

1G—₦300 2G—₦550 

5G—₦1,4000 

6G—1,650. 


DATA BALANCE *140#


 *GLO* 


1.35G—₦550 

2.9G—₦1,050 

5.8G—₦1,500 

7.7G—2,050.


DATA BALANCE *127*0#


*9MOBILE*


2G—₦1,200 

3G—₦1,650 

4G—1,950 

6G—₦2,600 

7G—₦2,900. 


DATA BALANCE *228# 


contacts:***



Account â„–:6074981401 

Account name:Aliyu Muhammad Usman

Bank name:9 Payment Service Bank. 



#Follow

#Vote

#Comment

#Share

#Asli Smasher.