Book 2 (THRILLER)
by @realsmasher
💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*BOOK 2*
*♡DAUƊAR GORA¸.•💥*
(Cɪᴋɪ ᴋᴀ sʜᴀ ᴛᴀ)
Nᴀ
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••
*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..*
22
#Intermission!
•••Kamar cikin watan ramadhan lokacin tashe,haka muryoyi da yawa na yara da manyan gidan suke tashi cikin waƙe suna faɗin "Aya me fitsarin kwance,amalaala! Wace ce? Me fitsarin kwance.. Amalala.. Me fitsarin zaune.. Amalal.. Me fitsarin kwance!" Wasu na baiti yayin da wasu suke bada amshi,Aya dake durƙushe bakin ƙofar ɗakinta banda kuka babu abunda take kamar ranta zai fita,zuwa yanzu gaba ɗaya rayuwar ya fice mata a rai,musamman irin tozarci da wulaƙancin da take fuskanta daga danginta,abun yai mata yawan da ciwon zuciya yake neman kamata,a kullum rana tunda ta dawo gidan kuma maganar matsalar data samu ya bazu mutanen gidan suka sani,take cikin barazana/walaƙanci da tsokanarsu,har tunanin fita take kou wani uzuri ya kamata da dole zaisa ta haɗuwa da wani cikin mutanen gidan ba Baba Wada ba,Baba Wada da Allah ya kawoshi gidan dai² lokacin yana shigowa ya samesu sun cika ƙofar ɗakin,cikin wani irin ɓacin rai yai masu tsawa yana ɗaukan icce yai kansu yana faɗin "kun bar gurin nan kou sai na jima mutum ciwo?" Gudu kowa ya shiga yi,yara da manya sukai ɗakuna aka hau banko ƙofofi,cikin ɓacin rai Baba Wada ya tsaya tsakar gidan yana ɗaga murya ya fara faɗa yanda kowa zai jiyoshi yace "kun ci uwaku,shegun banza marasa mutunci.. Har wanda Allah ya jarabceshi abun tsokana ne a gurinku? Ku kunga naku ƙarshen? Kun manta da cewar ba'a gama yiwa ɗan Adam halitta har sai ya mutu? Ayan ba ƴar uwarku bace ne? Ina ce wani a waje za kuji yana tsokanarta ku tsaya kuyi faɗa da shi.." Faɗa sosai ya shiga yi kamar zai aro baki,Inna Larai dake masa wani kallo daga can gefe tace "yo idan mutum ya ji haushi ai sai ya daina abunda za'a tsokaneshi,amma da girmanta da bakinta ace tana tafe fitsari na bin jikinta" Baba Wada ya kalleta yana girgiza kai yace "illar jahilci kenan,har yau Larai kin kasa gane abunda Allah ya ɗaurawa bawa,da kuma wanda bawa yake yi yana sane" Inna Larai cikin ƙunan rai ta juyo tace "Malam ni kake cewa jahila akan wannan tsinanniyar yarinyar da ba'a tabbatar da asalinta ba?" Baba Wada cikin fushi ya nunata yace "Larai! Ahir ɗinki da kiran ƴar ɗan uwana mara asali.. Wallahi akan Ayatullah zan iya aikata abunda zai baki mamaki" wani irin shewa Inna Larai tayi tana sakin guɗa tare da tafa hannayenta ta kama ƙugu tace "ai wallahi Malam har yau banga abunda za kayi da zai ba ni mamaki ba,idan kuma akwai shi tou bismillah,akan dai wannan yarinyar ne kou? Tou ni kuma mu zuba ni da kai shege ka fasa.." Baba Wada yana girgiza kai cikin ƙosawa yace "haka kika ce?" Inna Larai tace "na faɗa ɗin,idan baka yi abunda kake faɗa ba tou baka haifu cikin Adama da Abubakar ba" runtse idanu Aya dake durƙushe tana jinsu tayi,gabanta banda wani mahaukacin bugu babu abunda yake tana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Baba Wada da ya gama kaiwa iya wuya yana kallon Inna Larai yace "Larai! Kije gidanku na sawwaƙe maki,na sakeki saki biyu.." Ba Inna Larai da taji saukar maganar kamar aradu ba,ba kuma Aya da tai saurin ɗago kanta hawaye na ci gaba da sauka fuskarta da yai ja ba,hatta Amado da ya shigo gidan ƙamewa yai daga bakin ƙofa ya kasa ƙarasowa,Inna Larai da maganar ya shigeta sosai saboda batai zaton hukuncin da Baba Wada zai ɗauka kenan ba,tace "ka me?" Yace "na sakeki.. Ki tattara ki bar min gidana,na gaji da halinki haka nan,Allah ya bamu alkhairi" daga haka ya juya ya nufi ƙofar gida fuuu,Amado na kallon iyayen nasa amma ya kasa masu magana har Baba Wada ya fita,Inna Larai ta kurma wani ihu tana faɗin "na shiga uku ni Larai,yau ni za ka saka da girmana? Ni Wada zai tozarta ya saki saboda wannan annamimiyar magulmaciyar yarinyar?" Tana magana tana matsar ƙwalla,lokaci ɗaya kuma ta juyo kan Aya dake rarraba idanu tana nunata cikin ɓacin rai tace "duk abunda ya sameni akanki ne,tsinanniya baƙar kadara.. Mun yi fama da uwarki kema kin shigo kin hana man zaman lafiya,wallahi billahillazii yanda aurena ya mutu yau a dalilinki,kema kin bar gidan ɗana kenan,idan ba haka ba kuma sai na zama ajalinki.." Yanda take kumfar baki sosai Aya ta tsorata ta sake fashewa da kuka,Inna Larai da duk abunda ake tana ganin Amado ta juyo cikin ɓacin rai tace "Amado!" Ya juyo hankali tashe yana kallonta ya kasa amsawa,tace "ka saketa yanzun nan ba da ɓata lokaci ba,ka nuna mata cewar ni na haifeka kuma kana kishina,kana gudun ɓacin raina.." Girgiza kai Amado yayi zai magana,Inna Larai tai masa tsawa a haukace tace "ka saketa nace wallahi kou na tsine maka yanzun nan kabi duniya" Amado yana ɓarin baki yace "Inna dan Allah" a fusace Inna Larai tace "baza kayi ba?" Ya girgiza mata kai yace "a'a Inna.." Tace "saketa nace yanzun nan" yace "Inna ki saurareni dan Allah,mubi komai a sannu.." Inna Larai cikin zafin rai tace "tunda baza kayi ba kaje na yafe mata kai.. Allah ya isa nono na daka sha.. Allah ya tsi.." Da sauri yana zaro idanunsa yace "na saketa Inna..."
*
Dandazon mata ne majinyata dake fama da larurar VVF cike bakin ward ɗin sai hayaniya ake wasu na turereniya,mutumin dake sanye da kayan masinjoji ya tsaya yana cewa "dan Allah malamai ku dakata,daga wannan na gama amsar katin kowa,duk wanda ba'a karɓi nata ba,ta tafi domin baza ta samu ganin likita a wannan lokacin ba,sai dai nan gaba idan an sake bada dama" hayaniya mutanen da ba'a karɓa da nasu ba suka dunga yi har da masu zage² da faɗar magana,kafin kowa ya fara tafiya yana ƙunƙunin ansa sun zo an walaƙanta su,sanda mutane suka ragu sosai ya rage wanda aka karɓi katinsu da suke ta hamdala suna godewa Allah,a jere wasu irin manyan baƙaƙen motoci suka dunga shigowa cikin harabar babban hospital ɗin na Murtala Muhammad da gudu,hakan yasa mutane suka shiga ja baya suna kallonsu da basu hanya,gaban ward ɗin dake cike da mata masu fama da larurar VVF suka dunga yin parking,kafin wasu irin samudawan private security dake cikin baƙin suit suka dunga saukowa suna jeruwa gurin,yanda suke muzurai fuskokinsu sam babu alamun sassauci tamkar suna shirin ɗaukan rai,kallonsu kawai mutum yayi zai ji jikinsa ya kama rawa bare ka shiga harkarsu,Aya dake cikin taron mutane ta ɗago kanta a hankali tana sauke wahalallen numfashi me haɗe da ajiyar zuciya,cike da rashin wadataccen kuzari tabi jerin gwanon motocin da kallo,zuciyarta ne yai wani irin tsinkewa sanda ta tsayar da idanunta kan motar dake tsakiya,a hankali ta ɗan lumshe idanunta ta buɗesu akan mad black motar ƙiran Mercedes Benz maybach,duk da ba ta iya hango wanda ke ciki hakan bai hana gabanta faɗuwa ba,da ta rasa dalilin faruwar hakan,ganin kamar ana ƙoƙarin buɗe motar yasa tai saurin ɗauke kanta tana kai hannu ƙirjinta ta dafe tana faɗin "a'uzhu bikalimatillahit'tamaat min sharri maa khalaƙ.." Aya da zuwa lokacin tai mugun gajiya,in fact komai ya gama fice mata a rai,ga zaryan asibiti da suke ta faman yi,kou yau ɗinma Iyami ce ta takura mata sai sun zo,tunda taji ana sanarwar za'a yiwa masu larura irin nata aiki kyauta,ganin irin lokacin da suka ɓata a gurin kuma hakan baisa an karɓa da katinsu ba,tana ƙoƙarin hana kanta kukan da ya zame mata jiki,ta juyar da kanta ta kalli Iyami da sanyayyan yanayinta tace "Iyami mu tafi gida dan Allah.. Kinga kowa ya tafi sai mu kaɗai,kafin ai mana wulaƙanci gara mu tattara mu bar gurin nan" jikin Iyami a sanyaye tazo ta riƙe hannunta,tana gyaɗa mata kai a hankali tace "tou Shalele! Tashi mu tafi,kada mu rasa abun hawa ma" gyaɗa kai Aya tayi tana share hawayen da suka sauko fuskarta,Iyami ta dauƙi ledarsu data ɗebo zannuwa tana sauke ajiyar zuciya,underneath addu'ah take Allah ya taimakesu ya fitar dasu daga cikin wannan ƙangi da jarabawar,while Aya kuma tana ta aikin share hawayen da baza ta iya cewa ga dalilin saukarsu ba,har sun fara yin nisa da barin gurin sun kama hanyar fita daga cikin asibitin,ɗaya daga cikin private security dake tsaye gaban motar ya biyosu da ɗan hanzari yana cewa "Hajiya!" Daga Iyami har Aya a tsorace suka juya suna kallonsa gabansu na faɗuwa,yace "ana magana" Iyami tayi ƙarfin hali tace "da mu kake?" Yace "ehh!" Cikin tsoro Iyami tana karyar da muryarta tace "bawan Allah kayi haƙuri! Idan mun maka laifi ne,ɗan Allah ka yafe mana,wallahi ba da saninmu muka aikata ba" yana girgiza mata kai yace "no! Ba laifi kukai ba,Boss ne yace a tsayar da ku" Iyami ta kalli Aya dake kuka sannan ta kalleshi tace "tou waye shi ɗin kuma?" Yace *"Dr A.Y GHULAM MOHIUDDIN.."*
*
Kyakkyawan matashi ne fari dogo da bai wuce 35 years ba,duk da a zaune yake hakan bai hana na tantance tsayinsa ba,kallo ɗaya za kai masa ka tabbatar da kasancewarsa wani jinsi daban ba na Hausa/Fulani ba,a zahiri ka kalleshi bai yi kama da kowane ƙabila namu nan africans ba,sai dai ga wanda yake da lura zai iya kiranshi da arab,har hakan yasa kayi saurin yanke masa hukunci nan take kace bai san me kalmar (zo) yake nufi ba,fuskarsa dake ɗauke da baƙin kakkauran sajenshi daya haɗe har gemunshi,tare da baƙaƙen cikakkun girarenshi da dogayen eyelashes wanda za kayi zaton mascara akasa aka tashesu,a hankali yake tauna tattausan lips ɗinshi da suke da ɗan duhu ba masu kauri can ba sun yi kalar onion pink da su,fuskarshi yake squeezing alamun akwai wani abu dake cizon ranshi,yayin da yake feso numfashi daga cikin dogon hancinshi da ya ƙawata fuskarshi da bakinshi,duk da sanyin AC's dake aiki a office ɗin,amma hakan bai hana gumi ya shiga sakkowa daga cikin kyakkyawan baƙin sumar kanshi da gemunshi me laushi/santsi da wani irin sheƙi irin na larabawan asali ba,zaune yake cikin office ɗinsa,yai mugun nisa a cikin duniyar tunanin da bai san sanda ya shiga cikin kanshi ba,almost a week kenan da yaga fuskarta,kuma accidentally ya hangeta lokacin yana fita daga hospital,su biyu ne ita da wata dattijuwa da yake kyautata zaton mahaifiyarta ce,ita tana kuka ita kuma matar tana mata magana cikin yanayin damuwa,tun daga ranan komai yake yi hoton kyakkyawar fuskarta da brain ɗinsa yai capturing kawai yake masa flashing,after then ya ganta again a cikin masu larurar VVF,sai dai abunda ya ɗaure masa kai kuma yake yawan tambayar kanshi game da al'amarin yarinyar shi ne "wace ce ita? Me yake kawota cikin masu larurar *YOYON FITSARI?"* Ajiyar zuciya ya sauke yana buɗe lumsassun brown idanunsa da sukai wani irin oily sun ɗan canja launi saboda damuwa,haka nan zuciyarshi take tuhumarshi *ABDUL-ADL!* Me ya haɗa ka da tunanin yarinyar da baka sani ba? Shin idan matar wani ce fa? Me yasa za ka damu da ita? Mene ne alaƙarka da ita?"
*
Kyakkyawan murmushi Aya ta saki tana kallon Amado dake zaune gabanta yai fuskar damuwa,tace "me kace?" Yace "Ƙanwata please! Ya kamata muyi magana,ki yarda na mayar dake ɗakinki muci gaba da zama,ke yanzu ba abun kunya bane ace kin bar ɗan uwanki kin auri bare? Me yasa baza mu gyara tsakaninmu mu zauna da juna ba? Kou hausawa suna cewa da sabon gini gara yaɓe.." Da sauri Aya ta tari numfashinsa tace "wani ginin kenan,amma wani idan kace za kai masa faci tou zai iya jangwalo aikin da sai ka gwammace rusheshi tun farko.. Kamar yanda ka rabu da ni a baya,ka ƙaddara mun rabu kenan har abada.. Tsakanina da kai a yanzu har zuwa nan gaba sai dai zumunci,bayan nan babu wani alaƙar aure kuma,ba zan iya zama inuwa ɗaya da mutumin da mahaifiyarsa ba ta ƙaunata ba...." Yace "Aya please.." Cikin wani irin dakewar zuciya tace "dan Allah Ahmad mu bar maganar nan iya nan.. Idan kai ba ka tunanin me zai faru ni ina yi,shin ka manta mahaifiyarka ba ta sona? Kou ka manta akaina ta yi furucin za ta tsine maka?" Yace "ban manta ba Aya.." Tace "tou dan Allah karka sake tado da maganar nan,ni da kai daga yau ka ƙaddara bamu taɓa sanin juna ba,bamu taɓa zama da juna ƙarƙashin inuwar aure ba,ina so ka ɗaukeni matsayin ƙanwarka kamar yanda kayi a can baya pleaseee.. Kuma ma ni a yanzu ina da wanda yake sona ba dan wani abu nawa ba sai saboda Allah.." Amado yace "yanzu Aya wani ya fini? Bare har ya fi ɗan uwanki jininki?" Da sauri ta gyaɗa mashi kai tace...
*#Alhamdulillah! I'm done with free part,na ji mutane suna ta cigiyan ci gaban littafin nan,duk da akwai wanda suka san it's not for free,sannan na yi write-up ƙarshen book 1,so ga masu buƙatar ci gaba da wanda basu fara ba suka tsaya jiran document,za ku samu littafin DAUƊAR GORA! Na ɗaya kyauta. For 2 & 3 na kuɗi ne normal ₦500,SP 1k,za'a tura kuɗin ta wannan account ɗin 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank,kou a tura zuwa ***-Usman Hauwa Muhammad,Opay wallet. Mutanan Nijar/Mali zaku turo dala ɗari,SP jakka ɗaya,ku tura shaidarku zuwa ***. My sister idan baki da halin biya duka a yanzu,za ki iya making payment na book 2 akan ₦300,idan mun zo book 3 shima ki biya ₦300,idan kuma za ki biya ne duka lokaci ɗaya a maimakon ₦600 na yi discount nace ku biya ₦500,please idan baki shirya ba ina haɗa ki da girman Allah kada ki ɓatama kanki lokaci nima ki ɓatan,rayuwar nan me sauƙi ce,ba na wulaƙanci ba ni da abokin faɗa,dan Allah kada ki yi min magana idan har ba ni kou novels ɗina kike nema ba,ba na ajiyar paid books ɗin mutane,nawa kawai nake iya ajiyewa,stop asking me na baki book ɗin wata writer,na san akwai mutane da yawa da suke da contact na online writers,duk wacce kike nema kou books ɗinta,kina tambayar contact ɗinta za'a baki.. Masu ƙananun magana akan book na kuɗi ne,duk ina kallonku kuma ina jinku,kawai i don't have lokacin kula maganarku,bance zan maku free book ba dama bare kuce na yaudareku,duk wanda littafi na yaiwa zai iya siya,wanda kuma baiwa ba please ya kalleni kawai ya barmin abuna,babu dole a cikin rayuwar duniya,attoohh! Ga wanda suka shirya kuma suke jiran na gama free part,za ku samu Book 2 & 3 akan farashi me sauƙi,dan anyi payment a tabbatar anyi screenshot,sai a turo evidence of payment ta wannan number ***.*
#Kaɗan kenan daga cikin DAUƊAR GORA! Kashi na 2.. Shin wane ne Dr A.Y GHULAM MOHIUDDIN ɗin nan ne? Kuna zargin Aya za ta samu damar ganin likita? Wane ne ABDUL-ADL dake tunanin Aya? Da gaske Amado ya saki Aya kenan? Idan har haka ya faru me kuke zaton zai faru a gaba? Anya kuna tunanin Amado zai haƙura da Aya kou ita Ayan ta iya auren wani namiji daban? Mu haɗu cikin littafi na 2 masoya domin gano bakin zaren..
#Follow
#Vote
#Comment
#Share
#Asli Smasher.