KIBIYAR KADDARA

6

by @neesharjay1

Kwance nake kan sofa sakamakon ba skl yau. Shigowar shi kawae naji shida wata mata da yara biyu mace da namiji. Fara ce amma bata Kae haske na ba kuma bazata fini kyau bah bugu da kari cikin dake jikinta duk ya kara hargitsata dan a lkcn ya Kae 7months.


Bayan sun shigo parlour Hakeem ya tadani bayan sun zauna ya hade fuska yace"ba kince bana haihiwa ba toh Kinga ilayina nan, harda yaran nan da kike gani and this pregnant is also mine. So abunda nake so dake ki cigaba da kula da yaran nan idan wani abu ya same su ki kuka da kanki, itama bana so tana wahala duk wani aiki da kika sani na gda ki cigaba da yi as usual hope kin gane.


Kae kawae na iya daga mai couz am speechless. Ita kuma sae wani Kara shige mae jik take Kamar mage.


Kullum idan na tashi zan ma yara wanka in shiryasu su tafi skl. Ita kuma sae na tambaya wane kalar abinci take sonyin breakfast dashi. Haka na koma yar aikin gida komae ni keyi ni da gdana amma bani da iko dashi. 



Maganar zuwa club kam sae abunda ya karu dan kullum sae yaje wata rana harda wasu matan yake zuwa su tayashi kwana duk da Zeeey na nan da kuma ni.



Haka na cigaba da Kula da Ameer da Ameera har suka saba dani kullum tare muke kwana muyi wasa tare. Zeeey kuma kullum cikin jin haushi na take ko mae nayi bana burgeta idan kuma taso muguntar ta sae ta gaya ma Hakeem karya da gaskiya shi kuma baya tsayawa bincike sae dae kawae yyi concluding ya hau duka na.


Ana saura wata daya Zeeey ta haihu suka nmbar kasa acewar shi wae bazata haihu a Nigeria bah suka barni dagani sae Ameer da Ameera, ina kula da su kamar ni na haife su.



Watan da zasu dawo ana saura kwana biyu, na debo ruwan zafi na kae toilet,Ameer ya shiga bayan na fito na dauko Ameera, toh ashe yasa hannun shi cikin ruwan zafin ihun shi kadae naji har parlour da gudu naje amma am already late kayan shi na saka mishi muka tafi wani chemist din da ke kusa damu.



Ranar da su Hakeem suka, yana kallon hannun shi ya haj masifa tunda nake ba,a taba min dukan dayamin ba ranar daga karashe ya kira mae taxi ya bashi kudi yace gashi nan ya kaeni duk inda nake so shi ya sakeni. Abunda yafi bata min rae shine su fa yran bat hnyar arziki aka same su ba amma ba yanda na iya dole na bar mishi gida dan korar kars yamin.



::::::::::::::::::::::::::


"Let me guess" Sameer interrupted " kwana biyun da suka wuce koh"


Labeeb nodded and continued"bayan driver din ya bar compound din gidan nace mai ya ajiye ni abakin bushiyar da ka ganni,shi yasa nafi zama comfortable under the tree drenched by the rain that night. It was a sign of freedom. Wannan ne labarina.



Sameer was speechless for several minutes. He was a little confused about what next to say or do. He had wanted to hear all of this right? Daga karshe yace"i am really sorry Labeeba for all you went through. It is long sad story indeed. I can see that ikon Allah ne yasa na zo a wnn Daren da na taimake ki. How can I tell you it is well when you are already hurt to ur marrow?

"Ki barni na taimake ki Labeeba plss zan sama miki gurin zama a nan port Harcourt daga lbrn ki bakida kowa a abuja and koma wanki can only multiply ur troubles"


What is he saying?stay here again after all I have been Labeeba was insistent on going away and rejected Sameer's offer. Taso ta bar port Harcourt sbd pains din da tasha and couldn't see herself staying one more night in this town. Yanzu shekaranta 26 and now pushed out 10years after.




    *SAMEER*


Muhammad Sameer Isah ne cikakken sunan sa. Dane ga Alh. Isah maigidan glass haifaffen jihar kebbi ne a bagudu . Babbanasuwa ne da duniya ta sanshi ba kasar da baya zuwa domin kasuwancin sa. Matan sa biyu hjy Haleema itace uwar gidan sa sae hjy sa'adatu itace amaryar sa . Hjy Haleema na da yara shida Bashir shine na farko sae Sumayya, Maryam,Okasha,Asiya sae autar su Atika. Hjy sa'adatu kuma tana da yara 8 Yusuf ne farko sae Ahmad, Zaynaba,Sameer,Ruqayyah,Rumaisa,Abdurrahmnsae auta islaam.


Suna zaman lpy sosae sae dae matsala daya kakarsu da ta haifi babansu tana raye har yanzu kullum cikin masifa take batadahkr ko kadan abu kadan fada shi yasa yaran gdan ba mai shiga sabgaarta dama² Sameer suna dan shiri b sbd shine mae sunan kakansu kuma yafi mata alkairi.



Sameer was still single at 32 years, bawae dan he is not hard-working ba , ya karanci sociology and criminology a Cyprus yyi joining Army immediately after is NYSC was a matter of choice aka mishi transfer zuwa port Harcourt kuma a wnn Daren ne ya hadu da Labeeba.





"Karki damu ina zuwa" bata ce komae ba ya fita dag hotel din. Booking flight din abuja ya mata kana yaje y siyo mata trolley ya dawo.


Bayan ya tayata shirya kayanta suka fito ya ajiyeta airport ya bata 100k da zatayi amfani dasu bayan ta sauka tamai godiya ta bashi no wayanta kana sukayi bankwana ta tafi.



 *‰‰‰‰‰‰*



Da misalin karfe 7:30pm flight dinsu yyi landing a abuja. Gidan mama Sarah ta tafi direct sunyi matukar mamakin ganin ta dan ita har ta fitar da rae da Kara haduwa da ita a duniya bayan sun gaisa ta huta ta basu lbrn abunda ya faru tun ranar da tabar gidan cikin kuka mama Sarah tace"kiyi hkr wlhi nima sae bayan kin tafi nayi da nasanin barinki na tafiya dan Allah kiyi hkr Labeeba"



Labeeba tace"ba komae mama kin min abunda uwata zata iya ma yarta ni ba abunda zance sae Allah ya saka da alkairi. 


Mama Sarah tace"uncle's dinki sun zo neman ki ba adadi kabeer ma ya dawo yace kuma ki kirashi duk lkcn da kika dawo ga no dinshi nan daya bari" t fada tana Mika ma Labeeba wayarta


Da sauri tace"Alla mama wlhi naji ddi kice bayan tafiyana abubuwa da yawa sun faru, Allah sarki Fareed inshallah zanje gidan nayi kwana biyu"


Nan suka cigaba da lbrn yushe rabo haka ma bayan sunyi dinner suka suka cigaba da firar su.




Washe gari da safe ta shirya taje gidan uncle Ahmad abun ya matukar bata mamaki yanda taga gaban gudan ya koma duk flowers din sun bushe wasu ma gaba daya babu su a ranta tace lallai cikin shekara goma abubuwa duk sun canza. Bayan ta shiga gidan tana tuna nin taji hayaniyar yara amma shiru. Knocking tayi daga ciki Aunty Azeema ta tambaya waye 


Labeeba tace"Aunty Azeema nice Labeeba"



Da sauri tace "Labeeba"


Tace "ehh bude ki gani"


Tana budewa kuwa taga Labeeba dince kallonta tayi sama da kasa kana tayi hugging dinta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya itama Labeeba bata San lkcn da fara nata kukan ba a haka suka shiga parlour Aunty Azeema taje ta dakko mata ruwa da drinks (a Raina nace kut su Azeema an shiryu anbi God ko ontop🤭 dariya muka saka gaba daya 🤣🤣 harda rike ciki)


Bayan ta ajiye mata tace"dan Allah dan girman ya rasulillahi dan kaunar da kike ma Annabi ki yafe min nasan na miki laifi na zalunceki zanluntar da nasan da wuya ki yafemin amma dan Allah kiyi hakuri Labeeba" ta karasa fada tana Kara fashewa da wani sabon kuka😭(hmmm sae kace dae sabuwar amarya😆)


Labeeba ta share hawayenta tace" na yafe miki ni tunda dade aunty Azeema idan ban yafe miki ba wa zan yafe ma bani da kowa fa sae ku "

(Jar uba Aisha idris tace wlhi da itace baza ta yafe ba bayan duka da wahalar da ta bata☹ uhmm nidae ba ruwana bance komae ba kar naji kunya🙃)


Godiya ta mata daga nan suka shiga fira Labeeba ta bata lbrn rayuwarta bayan barinta gdan har aurenta a port Harcourt.



Aunty Azeema tace"Allah sarki Labeeba ni naja miki duk wani abu da kika shiga da ban sa Ahmad ya koreki ba da ba abunda zae faru nima Kinga bayan tafiyarki uncle dinki ya bani 1.5m na fara business haka na fara in samu a hankali sae wnn frnd din tawa Binta tace na bata kudin da na tara zata basuwa a siyo mana kaya a Dubai sae mu saka a shago. Bayan na bata bayan sati biyu ta dawo tace wae flight din ya samu aircraft bayan da na iya sae tunda itama da nata kudin aciki. Amma kin San mae ya faru daga karshe?"






Labeeba tace"aa'?"


Tace"ashe karya takeyi gaba daya kudin guduwa tayi dasu tunda ga wnn lkcn ko mae n fara baya samun albarka sae na tuna ashe haqqin kine ke bina shima uncle dinki daga baya aka koreshi daga gurin aikin sa uncle dinki kabeer ma da ya dawo ya samu baki nan yace ma Ahmad bazae Kara mishi mgn ba har sae ya nemoki duk inda kika shiga . Haka ya shiga neman ki kullum cikin saran yake idan yafita zae ganki"





Labeeba tace"Allah sarki yanzu ai komae ya wuce"



Suka cigaba da hirar su har akayi sallahr suka tashi.




Bayan sallahr Asr suka shiga kitchen Labeeba ta hada musu abinci mae dadi suka jera a dining.




Da misalin karfe 8pm uncle Ahmad ya dawo gda. Mutuwae tsaye yyi ganin Labeeba yace"Azeema wnn kamar Labeeba ko"



Azeema tace"bama kamar bane itace"



Da gudu Labeeba tayi hugging dinshi ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya shima kykan yakeyi sae da yyi mai isarsa kana ya shiga lallashin Labeeba itama Azeema kukan takeyi.




Bayan sun zauna Ahmad yace"Labeeba banyi tunanin zaki Kara dawowa gareni ba dan na miki abunda baza ki taba yafe minba naci amanar da mama ta barmin shi yasa komae nawa baya albarka alhakinki sae bina yake yi. Kabeer ma cewa yyi idan ban nemo ki ba bazae taba yafe min bah kullum tunanina idan na fita zan ganki har tsawon shekara goma amma shiru. Yaran da muke hauka akan ke kika hana mu samu ashe ba haka bane har yanzu gashi ko ciki Azeema bata taba dauka bah duk ALHAKIN (na Nabiya sani) ki ne ke bibiyar mu dan Allah ki yafe mana dan Allah"




Labeeba tace"ni damatun tuni na yafe maku uncle"


Yace"nagode"



Wayarshi ya dakko ya kira Kabeer ba dadewa sae gashi yaxo



Labeeba dake tsaye bayan labulen kofar tayi sauri ta fada kanshi. Shi har ma yaji tsoro wlhi kuma bae ganeta ba.


Ta turo baki gaba tace"uncle Labeeba ce fah”


Yace"taya zan gane haka"


Sae ta dunkule hannunta 🤜🏻 shima ya kawo nasa suka buga🤜🏻🤛🏼 tare da ware wa suka taba.



Yayi hugging dinta yace"my bby kin girma sosae Allah"


Tace"wlhi ni bawani girma da nayi shekarana 26 fa kadae"



Yace"Kae duniya harkin kae 26 lallai bari mu kama girman mu"


Dariya tayi suka zauna tare.



Larinta ba ta koma basu gaba daya suka tausaya mata sosae tareda neman gafararta again. Suka cigaba da lbrn cike da kunar juna.