SANIN GAIBU....

Page:8

by @maidambu41

SANIN GAIBU...!!

_Sai Allah_

ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023

*Mai_Dambu*

Page:8

"Gaskiya kan gara na kara shi akan haka, daga Makarantar zan dauke ta" murmushi Malam Musa ya mishi tare da cewa, "kar ka manta idan aka samu me yawa kar a manta da mu domin mu ma, mu dangwali arzikn yar mu" dariya ya saka yana faɗin "haba ai kaf duniya bani da masoyi irin ka, duk abin da na samu na ka ne." Ya fada suna tafawa. Da ace Malam Aminu yasa yadda Malam Musa ya tsani ganin shi da ba zai tab'a ɗaukar shawaran shi ba, amma baki daya bai da aiki sai daukar shawarar shi, bayan idan suka yi magana shi yake gayawa sauran abokan su, su kuma su gayawa Mai gari, haka yasa Mai gari ya saka a aka kira mishi Malam Musa ya ci mutuncin shi, domin ya zama mugun aboki me son ganin bayan abokin shi da munanan shawara.

.... Tunda ya bar gidan ya nufi makarantar, yara ke bin shi musamman yan mata masu tashen balaga. Abin ya basu mamaki yadda suka gan shi Bature dan gayu, kuma yana tafiya kamar mace a yangance, asalima shi mutum ne da bai da kazar kazar, haka yana nasaba da inda ya fito ne, duk da a dabi'ar shi babu maida hankali akan mulki, amma mulki da kasaita tana bibiye da rayuwar shi, hakan yana faruwa ne idan yana cikin damuwa, ko bacin rai tow hatta maganar shi na iya sauyawa. Aliyu Abu turab, dayawan mutanen da suka san tashin sa, suna mishi lakabi markabu iyalan gwamna, gadanga kusar yaƙi, bauna saniyar sake. Shigar shi makarantar ya hadu da malamai da suka zo daga Binji, wanda kana ganin su, kasan suma aiki suka zo yi, sallama ya musu ya wuce Office din Headmaster. Office din a rufe yake shi kan sa bai zo ba. Jingina yayi da bangon office din yana me sunkuyar da kan shi. "Burr-burrrrrrr" kara wata ya gulalliyar mashin kiran Yamaha ya shigo cikin makarantar, sau daya ya d'aga kai ya kalli headmaster sannan ya cigaba da tsayuwar shi, kafin headmaster ya shigo hayaniyar yara ya cika wurin. "Bata magana bata magana ohooo" dauke kai tayi kamar bata ga suna tsokanarta ba, sai a lokacin ya d'ago ya zuba mata ido, ita kanta yadda take tafiya zaka fahimci a takure take, sannan koda bai ga fuskar ta ba, ranta a b'ace yake. "Ita ce kenan?" Ya tambayi kan sa, wucewa aji tayi tana ta gaban shi. Kallon uniform ɗinta yayi yaga yadda yake daukar idanu, ba mamaki Mahaifiyar tana kula da ita. Nana ce ta bita da gudu ta kai mata duka, faduwa tayi ta mike tana kallon Nana ta ma rasa me zata ce mata, kawai ta juya tayi tafiyar ta. Shekaru goma baya haka ya ya faru da Ummu Mansurah. Murmushi yayi yana kallon su.

***

Kalambaina estate

Anan gidan Dr Sharif yake, tare da Amaryan shi Aunty Fareedah wacce suke kira da Aunty Mom.

Tun ranar juma'a ya shigo Sokoto, amma yaki zuwa gidan Mahaifiyarsa. "Yaya Abdul!" "Na'am my angel me kike so?" "Home work aka bamu ban fada da wuri ba kuma yau zamu yi submit din shi" shafa kan ta yayi yana faɗin. "Na'imatullah me yasa baki gaya min tun jiya ba, na gani." Murmushi tayi, ta zuge jakar Yayanta me suna Hamidu yana zuwa ya make kanta. "Bata da hali aikin ta kenan ba zata fada tana da home work ba sai za a tafi school." Murmushi Abdul yayi ya ce mishi. "Kowa da kalar rayuwar sa" gyada mishi kai yayi, ko babu kome Aunty Fareedah da Yaranta suna saka shi farin ciki, madadin gidan su da ba barikin soja bane amma bin doka da oda sai a slow, gashi babu dan raha da farin ciki irin na gidan Aunty Fareedah. "Sannun ku babban Yaya da kanen shi" yar fara a yayi yana faɗin. "Aunty Mom kin ga yau Hamid bai rungume Ni ba" "oya wuce kayi rungume shi" "ayi hakuri na manta ne" yazo ya rungume shi ta baya. Abin da ya rasa kenan a cikin gidan su, yana buƙatar kulawa kodan irin laluran shi, fitowar commissioner of education, yasa suka juya yana saka links din hannun rigar shi. "Mr Hakim ka manta yau zaka koma bakin aiki? Ko so kake Hajiyar ku ta cinye ni danye?" Kallon mahaifin su yayi ya ce. "a'a idan na karya zan wuce." "Yaya kai zaka kai mu school?" "Kuna so ne na kai ku?" "Eh muna so, zan nunawa Jalilah nima Yayana yana sona" make keyarta Hamid yayi yana fadin "ke dai" kafin ya karasa ta ce mishi " baki da hali, sam baki da wani abu sabo, ko basu bane?" Ta mike da kofin tea ɗinta, ta nufi kitchen. Iyayen suka zauna. "bani Jakarta" mika mishi jakar Hamid yayi, ya saka mata. "Mamarka tace kaki maganar aure duk yarinyar da ta nima maka sai kace baka so" a hankali ya fara shan tea da Auntu Mom ta hada mishi. Yana sauraron mahaifin su, haka ma Hamid da ya nutsu yana sauraron mahaifin su. Wannan yana daga cikin abin da ya kara sakawa Alhaji Sharif Hamidu, kaunar matar shi Hajiya Fareedah, domin tarbiyyar Yaranta daban yaƙe, da ace a gidan Hajiya Dawlah ce, da yanzu yaran sun fara mishi shakiyanci da rashin hankali, ita kuwa Fareedah ko fada yake ba zaka tab"a jin tayi magana ba, asalima sai tayi shiru daga baya sun had'e a oda room, ka ga yadda yake susucewa yana bada hakuri. Tasan kan mijinta, wannan yanayin har Yaran ko fada yake musu, zasu yi shiru daga baya zaka ga sun bishi daki har suna kuka yayi hakuri, karshe kuma shi zai koma rarrashin su. Shi yasa gidan yake zaune cikin farin ciki. Haka Abdul shima dabi'ar gidan Aunty Fareedah ya kama shi, koda Hajiya Dawlah ke fada ba zai taba magana ba, tana gamawa zai ce mata kiyi hakuri. "Yana da kyau kayi aure, ka samu me kula da kai." "In Sha Allah zan yi yadda kace ayi hakuri" daga haka suka ci gaba da karyawan su, yana gamawa ya mike. "Hamid kace Widad ta fito mu tafi" "ok Sir" ya fita, "Abba ka daina mishi fada a gaban mu, mu kanen shi ne. Ba dadi" kallon Aunty Fareedah Dr Sharif yayi ya ce mata. "I did something else?" "Gaskiya ya gaya maka, kuna bukatar kebe wa ai" "Allah ya huci zuciyar Ubana ba zan kuma yiwa ɗan dan uwanka fada ba a gaban ku, don Allah kaso shi yadda yake son ku. Ya shirya ya bata da kowa saboda ku." "In sha Allah Abba, ke kucilili muje " ya kwalawa Widad kira, ta fito dauke da water bottle, ta nufi hanyar waje. Domin ya dauki jakarta, gaba ya shiga shi ya shiga baya. Suka nufi makarantar. Kiran Mother ya gani gaban shi ya fadi, ya taka birki da sauri. kallon shi suka yi. "Yaya lafiya?" "Lafiya lau yan uwana. " Haka ya cigaba da tafiya be dauki kiran ba, har suka isa makarantar, daga nan ya juyar da kan motar zuwa g.r.a gidan mahaifiyar shi. Tun a bakin kofar bayan ya ajiye motar yake jin tashin muryan ta.duk sai ya diririce. "Na zata zama zaka yi har abada a can, Nace na zata shiga cikin Fareedah zaka yi ta kuma haifarka, ni baka damu da ni ba, sai ita yadda ta tsafe Ubanka shi ne zata tsafe min kai na rantse da Allah baku isa ba, nace baku isa ba" yadda take bala'i kamar zata doke shi bai saka ya ce mata cikanka ki ba. Haka ta gama yana kallon Kannen shi, kowannen su harkan gaban shi yake, a gefen shi Taufiq ya dauki wayar shi da kayan makarantar shi ya fita sannu wannan bai ce mishi ba, tana mita Afiyyah ta fito itama ko kashi yafi shi daraja, haka ta fita sai cewa tayiwa Uwar "Hajiya na tafi" "tow" kallon ta yayi bayan sun fita ya ce mata"kiyi hakuri" bayan ya hàdiye wani yawu me daci, taya za a ce kanen ka babu shakuwa da soyayya a tsakanin ku. "Ka karya ka wuce aiki" "tow" har ya mike ta kalle shi."kana shan magani kuwa?" "Eh ina sha" "tow ya batun aure?" A duburce ya juya yana kallon ta. "Nace ya batun aure?" "Hajiya dama-dama- dama" "Abdulhakim na baka kamfani na ka rike bawai don ban san ciwon shi ba ne, iyalin zaka ajiye kamar kowa sai a wuce wurin" zama yayi yana saka hannun shi a tsakanin cinyar shi ya ce mata." Hajiya yan matan yanzu suna da buri, Hajiya rayuwata babu buri dayawa, babban burina na samu macen da zata so ni, bayan nan mu gina rayuwar mu cikin farin ciki da jin dadin, bana son tashin hankali idan kika matsa na auri yan matan zan aura amma babban matsalar farin cikin da nake son samu bai zama dole ba, ki kara min lokaci, kafin ayi min aikin karshe ina sha Allah zan gabatar da matar da nake so " shiru tayi tana kallon shi, so take tayi magana amma kuma wani bangare na zuciyar ta yana gargadin ta, da tausassa mishi. "Alright zan duba al'amarin aikin da zaa maka zai dauki 4 to 5yrs Inci gaba da ganinka babu d'a babu mata? Akwai adalci a nan?" Kamar ya fashe da kuka ya ce. "Hajiya likita bai miki bayanin yanayin ba ne?" "Idan ya min bayani sai na dauka? Ko ce maka aka yi can believe da abin da suka ce? Look ina son naganka cikin iyali da wadata wanda haka ba zai samu ba, sai kayi aure " "tow hajiya " zanyi yadda kika ce.

***

Kwara

Dukkan familyn sun hadu, a cikin su har da Sultanah karama da Sultanate, babu abin da suke bukata kamar Sultan Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari ya zartas da hukuncin shi akan Aliyu.

"Binciken da aka yi, ni na yanke hukuncin a duk inda aka ga Aliyu a kashe shi, shi ne adalcin da zan iya samarwa " ya fada a matukar sanyayye. "Gara a kai shi kotu domin zan daukaka kara." Ta fada cikin kwarin gwiwa. "Badi'atul Noor!" Baffanta ya daka mata tsawa. "Kayi hakuri Baffa batu ne na D'a nasan idan da Marigayi ko mahaifina suna raye za a samar mana da adalci tare da zakulo gaskiya. A daren ranar tana bangaren Sultanate sannan ta turowa Baba karami sako, yazo ya dauke ta. Sannan bayan nan mutuwar ta, ta turo min sako Ummina ki taimakawa Abu turab kar ya ci kome da za a kawo mishi an shirya ciyar da shi guba, ga sakon nana cikin wayata. Sannan kafin mutuwar ta, inda aka kashe ta daban inda aka ajiye gawarta daban, hujja ta karshe kashe Kabirun Gajiyah da shi idanun shi ya gane mishi kisan da aka yi, sannan itama Gajiyah aka illata lafiyarta yadda ba ta san waye akanta ba." "Badi'atul Noor hujjar kare danki ne duk wannan surutun?" Kallon Hajiya Suhailah yayi kafin ta ce mata. "Bani da buri ko yau Abdulrahman ya fadi Yarana sai naso su zauna a cikin gidan nan, balle kuma kun ga wani a cikin su bayan Baba karami? Ku sani ina shiru ne kawai don bana son magana, Uwa madubin goben D'anta Na amince da duk hukuncin da zaka yi, a cikin hukuncin har da sauke ni a matsayina, tare da sauwake min matukar zaka janye kalaman ka akan shi na bar kome na cikin gidan nan na yafe kome, amma daga ranar da gaskiya tayi halin ta, tabbas a lokacin zan zartas da nawa hukuncin....

ASHRAF, SANIN GAIBU,TSINTUWA is not free, Pay N400 ONE, TWO N800, THREE 1K to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza