ƘADDARATA CE A HAKA

Na biyu

by @maikosai53

P__2


   " Amma me? Yaya Nasir kada ka ce mini za ka rabu da ni, ka da ka ce min ka shirya rabuwa da ni plz don Allah, kar ka sake na ji wannan gubar maganar daga bakinka"

  Nasir ya ce " Haba my one ni fa ban ce zan rabu dake ba, kuma ban shiryawa hakan ba ko da da second daya ne, ina sonki my one har abada kece matata duniya da lahira kin ji share hawayen ki" ya ƙarasa cikin sigar san kwanatar mata da hankali.

   "Shi kenan har naji dad'i, da zuciyata ta fara harbawa da sauri da sauri, ni ma ina sonka kuma ko wanne bugun numfashina yana fita ne tare da naka"

  Sai da ya ta'ba saitin zuciyarsa sannan ya ce " Wow! Godiya nake yi sarauniyata, wai ina zuwa hakane ma? Ni ban tambaya tun farko ba"

Murmushi ta yi kana ta ce " zanje wajen Inna, bari na wuce"

 Shi ma murmushin ya yi kan ya ce,

  " Ki ce za ki hana kakus sakat, to muje na dan taka miki"

 Turo baki ta yi kafin ta ce,

  " Au haka ma za ka ce, ba na son rakiyar "

  "Tuba nake ranki shi dad'e muje ko"

Har ƙofar gidan Inna ya rakata sannan suka yi sallama ya wuce shi ma yana jin cewar in sha Allahu babu wanda zai raba shi da my one ɗin sa.

  Gidan ta shiga haɗe da yin sallama, zaune ta hango inna tana aikin gyaran lamsir dan Inna akwai masifar san kwaɗon lamsir shiyasa koyaushe take cikin cin sa da aikinsa.

   Ƙarasawa ta yi wajenta tana fad'in " Oh! Inna ke kam kullum cikin aiki bakya gajiya, yawan aiki fa yana jawo tsufa da wuri, ki bari ki tsufa ni kam ba ruwana wllh" ta ƙarasa tana dariya ƙasa-ƙasa.

  Inna ta kalleta kana ta ce " NURI kinci gidanku, yarinyar kamar Aku, cha-cha haba ,yo to in ban yi aikin ba kanki zan yi , zama waje ɗaya ai babu dad'i "

  Haɗa rai ta yi kafin ta ce " Ni dai Inna kinga kin yi fura ki ba ni. (tana tsananin San fura) kuma nasha gaya miki ni ba suna na NURI ba in ba za ki ce *NURIYYA* ba to ki barshi mana an yafe mene ne wani Nuri ko daɗin ji babu.

 " Yo ni na ga ikon Allah haka nan na yi niyya kuma na iya faɗa, kisa zare da allura ki dinke bakin ka ji min 'ya da tsurfa" Cewar Inna.

  Nuriyya ta ce " Ni dai ki ba ni fura nasha inda akwai" ta ƙarasa tana turo bakinta.

  "In kuma na ce Babu fa" Inna ta fad'a.

Cikin washe baki Nuriyya ta ce "Ah! nasan ma akwai don Allah ki ba ni

  Inna ta ce " Allah ya aiki na yi 'yar nema je ki dakko tana firinji"

  Miƙewa ta yi ta ƙarasa falon ta bud'e fridge din ta dakko, ai kam ta yi sanyi sosai. Kusa da ita ta dawo ta zauna ta hau Shan kayan ta ba tare da ta ƙara cewa innar komai ba.

  Sai da ta shanye furar tatas sannan ta kalli Inna ta ce " Inna don Allah ina roƙonki ki yi mini wani abu guda d'aya, kinsan duk abin da za ki faɗawa Baffa ya yi baya tsallakewa, ke kaɗai za ki gaya wa Baffa yaji , don Allah Inna kisa baki ya amince da aurena da yaya Nasir don Allah"

   Inna ta ce " Me? In yi me ? Rufa mini asiri, kin san halin Baffan ki indai ya yi magana baya canzawa ko ni bana iya dakatar da shi, dan haka ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddarar ki

  Cikin marairaicewa Nuriyya ta ce " Inna don Allah ki yi magana da shi nasan in kika saka baki to zai canza maganar shi"

  Inna ta ce " kayya dai 'yar nan bar halin Baffan ki , ki yi dai haƙurin da na ce za ki ga riba mai yawa aciki"

   "Inna ni fa na riga na gaya muku yaya Nasir nake so , kuma shi kad'ai nakejin zan iya rayuwa da shi, dan Allah Inna ki yi wani abu a kai"

   "Allah me iko , har ya kawomu lokacin da yarinya za ta ce ga wanda takeso, mu sa'adda akai mana auren munsanma mazajen namu ne ma, kuma kinsan dai ba kyau karya alƙawari , dan haka kin san babu yadda Baffan ki zai karya alƙawarin da ya d'auka, ba dan ma tsaye-tsaye da shirirta irin tasa ba , da su dangin Idirisun sun so ace tuntuni aka yi auren, amma ya biye miki sai kinyi karatu ga shi nan ai"

  "Inna ba alƙawari tsakanin aure, idan 'ya'yan suka taso basason juna fa, haba inna yanzu zamani ya sauya, kuma idris ɗin da kike gani abokin yaya Nasir ne nasan zasu fahimce juna sosai, kuma ni Inna ba fa son shi nake yi ba, na riga na gaya masa tuntuni"

  " Shi ke nan , naji Nuri ta, zan yi iyakar ƙoƙarina wajen shawo kan na shi"

  Cike da farin ciki Nuriyya ta rungume Innar ta ce " kai Inna wllh kin ga mai mini komai innata Allah ya tsundu min ke a aljanna"

  Inna ta ce " Naji ɗaga ni uwata, daman kinzo ne dan ki lallasani kawai ko"

  Nuriyya ta ce " Wa? Wace ni? Ina sam, ni ina na kema da ƙwarin ƙashin da zan iya karya 'yar tsohowa.

 “Au haka kika ce to na fasa.” Cewar Inna.