FreeArewaPen original
ƘADDARATA CE A HAKA
- 1views
- 22chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Ni Marubuciya ce, kuma ina matuƙar alfahari da kasancewata haka. Ina girmama alƙalami, saboda alƙami yafi takobi. Ina sonku masoyana,na gode.😘
Sample · Babin farko
P__1 Bisimillahir Rahmanir Raheem. Zaune take gefen kan lafiyayyan gadonta. Hannuwanta duka biyu shimfide bisa kan kyakkywan kuncinta. Kallonta a haka kaɗai ya isa ya gamsar da kai cewar lallai tana cikin matsananciyar damuwa. Hawaye ne suke gangarowa daga cikin kurmin idanuwanta zuwa kan dandamalin fuskarta. " Me ya sa gwaggwo da Baffa za su yi mini haka?? Me ya sa suke son saka ni cikin Wani hali? Me ya sa ba za su bar ni na aure Wanda zuciyata ke da muradi ba? Su ne maganganun da ke reto a cikin zuciyarta. Kuma tabbas tasan lallai babu mai amsa mata waɗannan tambayoyin sai su. Hakan ya sakata miƙewa daga zaunen da take zuwa tsaye tare da saka kai ta fice daga d'akin. Gwaggwo na zaune kan kujerar tsugunno a tsakar gida,tana yankan farce, ta kalle ta tare da furta, " Gwaggwo don Allah ki daɗa yiwa Baffa bayani akan lamarin nan nasan idan yaga kin daɗa dagewa akan batun zai duba lamarin nan nawa don Allah. Ni Wllh ban san me ya sa bakwa son aurena da yaya Nasir ba? Wai Gwaggo wani laifi ya aikata muku haka da ba za ku iya amsar shi ba? Me ya yi muku da ba zaku ƙauna ce shi ba?" Gwaggo ta dubeta a karka ce kafin takai ga cewa, " Ai hakan da kika yi yana da kyau kizo ki tutsiye mahaifiyarki akan wani ƙaton gardi ko? Kema ai za ki iya zuwa ki sami shi gyatumin naki ki yi masa magana ,sai ya fi jin maganarki ma akan ni, sai dai ina so ki sani tunda muke bamu ta'ba ƙin wani d'an Adam ba, amma ki sani munsan mahimmancin *alƙawari*" Tana kaiwa nan ta mayar da magananta kan yankan farcen da take yi ba tare da ta ƙara ce mata komai ba. Ita kam ganin yadda Gwaggon ta harzuƙa ya saka ta miƙewa ta koma d'akinta , tabbas tasan da man Gwaggon na ta ba za ta ta'ba goya mata baya ba, amma ta bawa zuciyarta amanna da abin da take son aikata wa yanzu. Cikin sauri ta miƙe tare da faɗawa bayi shaf-shaf ta watsa ruwa ta fito, ko mai ba ta tsaya shafawa ba da yake garin ana zafi, kayanta ta sanya tare da zarar mayafinta ta fice. Har lokacin Gwaggo na zaune inda ta barta, kallonta ta yi kana ta ce " Gwaggo ni zanje wajen Inna , ba dad'ewa zan yi ba" " Ki yi sauri dai ki dawo, in kika jima har Baffanki ya rigaki dawowa to tabbas zance ban ma san kin fita ba. Kin ji ko?" Zun'buro baki ta yi kana ta ce , " Kai Gwaggo! To ayi mini sassauci kada a ce haka" " Oho miki ki tsaya kar ki tafi" Gwaggo ta fad'a. " In banda ma kisa baiwar Allah surutu ni banga uwar abin da za ki je yi a can ba" " Ni dai na tafi, sai na dawo " Ta fad'a tana mai ficewa daga gidan. " ki gaisheta " gwaggon ta fad'a tana d'an daga sauti yadda za ta jiyota.********** Tafiya take yi sannu a hankali duk da wani sashe na zuciy...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.