Page 10
by @ayushermuhd
*MUNƊO*
(MAI HAKURI)
Na Zee Yabour
Da
Ayusher Muhd🤸🏻♂️
*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️
Paid Book....
010....
Salame ganin ya sauko zaici abinci yasa ta fito kai tsaye zaure ta nufa ta leka hagu da dama bata hango Jauro ba, komawa tai sai dai ta kasa hakuri nan ta sake lekowa ko zata hango shi, fitulolin gidajen dake unguwar sun haska layin dama yana ɗaya daga cikin abinda ke ɓata mata rai gidajen unguwar kowa da fitilu banda nasu, shiyasa ko za'a mutu tace Jauro bai isa ya sa su saida gidansu ba a Layin saboda duk gidajen ƴan gayu ne banda nasu. Amma dan tai iyayi agun kawayenta ya sanya tace a unguwar take, tace bai isa ya saida ba. Can kuma ta sake lekawa tana hangoshi ya sake haɗe rai saboda yaje ya dade, tana kallansa takaici ne ma ya isheta gani take kamar ma baya sauri, tsaki tai tace "Ji wata tafiya da yakeyi sai kace wani ƙaramin yaro." Ganin ya kusa isowa kawai ta wangale ƙofar tace "Nikam Malam yi sauri mana ka kawo." Sauri yai ya ƙaraso ai hannun rigarsa ta jawo ta karasa shigo dashi tace "Haba sai kace me koyan tafiya?" Kallanta yai hannunsa ɗauke da leda kafin yai magana tace.
"Daka fita ka kira Kabiru Dogo?"
"In kirashi akan me?" Ya amsa fuskarsa na ɗauke da alamar tambaya. Ajiyar zuciya tai tace,
"Akan kwaso dabobbin nan mana, ko so kake su fasa bayarwa ne?" Ajiyar zuciya yai yace "Kinga bazanje a bani kuɗin marainiya kisana cinye mata ba, wancan ma da mukaci gashi nan har yanzu sakayya bata....."
"Kasan Allah baka isa ba, kai kasan sakayya na bin mu ni hankali na a kwance yake kuma Allah na tare damu koma menene laifin wanene banda kai? Kai yanzu banda rashin zuciya har zakaga abinda zai farantawa iyalanka rai amma ka musu bakin cikin samunsa? Ni da yaranka ne bakaso kaganmu cikin farinciki ko me?" Saman goshinsa ya shafa yace "Salame wai kinsan yawan dukiyar da ake magana ne? Kefa bakisan meke faruwa ba, wallahi Danejo da su Ardu bazasu barmu ba, shi kanshi Maccidon ba kyalemu zaiyi ba, ke wai dan Danejo ta barmu kina tunanin wannan karan zamu sake cin bulus ne....." Hannu ta ɗaga mai da sauri tace "Dakata Malam yaushe nace maka mu ci kudin yarinya? Ni da bakina kaji na faɗi hakan?" Shiru yai yana mata kallan mamaki, tace "Banda rashin imani ya ma za'ai kai tunanin cutarta nake shirin yi? Yarinyar nan kaf dinku har kai ba kaunarta kuke yi ba, abar tausayi ce, kai da baka taɓa ganinta bama ballesu, sai dai ai dai duk duniya bayan iyayenta da kakaninta batada wanda ya wuce sama da mu ɗin ko?" Kasa magana yai kawai sai kallanta da yake cike da mamakin kalamanta, itakam hankali a kwance tace "Kaiwa Kabiru magana mu tafi karfe hudun asuba kaga dai biyar da rabi zuwa shida mun isa cikin rigar Jiji ko kuma mu tafi uku mu isa biyar, shi kuma Salau sai ya koro dabobbin kamar yanda suka saba kiwo maimakon ya kaisu inda ya saba sai ya kawosu inda muka ajiye motarmu ta kwasar dabobbin."
"Maccidon fa da Munɗo muyi ya dasu?"
"Kaima dai wallahi Malam, ita ai muna isa zata shiga mota da ita za'ai komai fa ya zaai mu barta."
Hannu yasa a matse-matsin idanunsa yace "Ni gaba ɗaya ban gane ba shi uban kuma fa? Sannan ke wai dake ma za'a kikesan cewa ko me?" Murmushi tai tace "Nikam ai dole naje kanasan kace uwa zatabar ƴarta tai doguwar tafiya ne ita kadai ba mataimaki? Bayan na tabbatar wannan karan zata fara doguwar tafiya." Baki ya saki galala yana kallanta wai Salem ke wannan furucin? Murmushi tai ta ɗan riko hannunsa tace "Ni harna fara wani tunani ma wallahi, nan gaba muyi ƴar gida abin mu ko ya ka gani?" Nan da nan ya saki fuska yace.
"Wai da gaske kikeyi?" Ta dan sake murmushi tace,
"Kai dai wallahi kai ta maidani mara kirki ƴan uwanka da nawa duk ba ɗaya bane? sannan ƴan uwanka sune suka mana hallaci har muke zaune a nan ko ba da dukiyarsu bace muka zo birni? Na dade inaso in saka musu sai yanzu Allah yai, in ka dawo ka saida dabobbin kasa mata kudinta a banki harsai ta kusa aure. Kai Maccido ya yarda dakai meyasa zaka nuna baka yarda da kanka ba?"
Yanzu kam ya gama gamsuwa da maganganunta, yace "Ungo ledar nan bari nai maza naje gun Kabiru kafin wani abin ya samu Maccido."
Tana tsaye tana kallanshi harya fita sannan tai tsaki ta kad'e hannunta, waje ta leka ta harari kan titi tace "Nima na kusa sa fitilu a gidana." Ta kara zabgawa wajen harara sannan ta koma ciki nan da nan ta hau lissafin abubuwan da suke bukata tai tsaki tace "Matsalar gidan namu dan tsugul ne a tsakiyan manyan gidaje amma in mukai bene ai shima zaiyi girman...." Toshe bakinta tai saboda dariyar dataji tana neman kwace mata. Salau kam sai daya tada ragowar burodin nan tas ya kuma shanye lemon kwalbar da kwai sannan yaji wani daɗi ya kamashi, mika yai ya ɗan kishingid'a ɗan baccine ya ɗauke shi saboda ba kowa a falan.
******
A b'angaren Munɗo kuwa ko abinci kasaci tai, kuka kawai takeyi tana rokon su barta taga Baffanta amma sunki kulata, tun tana kuka da karfinta har tazo ta kasa tana rokon mutuwarta tazo kowa ma ya huta. Ita ba ibadah ta iya ba kuma ba addu'a ta iya ba balle tahi, hawaye kawai ke zubowa a idanunta batasan daɗin duniya ba ko kaɗan, kaf duniyar nan mahaifinta kadai sai Danejo take jin daɗin su toh menene amfanin rayuwarta in Baffanta ya mutu?
A haka wani wahalalen bacci ya ɗauketa, kamar a mafarfi taji ana cewa "Munɗo! Munɗo!!" Idanu ta buɗe da kyar ihu ta nemi sakawa Danejo tai saurin toshe mata baki, a hankali tace. "Nice Danejo."
Ta kwanta da rana sam batasan har dare yayi haka ba dan muryar Danejo kawai taji bata ganin komai. Cikin sauri ta rungumeta ta saka wani irin kuka tace "Danejo dan Allah ki fita dani inga Baffana ko mutanen nan zasu kasheni, wallahi inbanga Baffa ba mutuwa zanyi."
Tausayinta ne ya kamata ta sani duk duniya Maccido ne gatan ta, duk yanda tasan Salame tasan zata cinye dukiyar nan sai dai tasan koma menene can zaifi nan kuma saboda darajar dukiyarta zata kula da yarinyar. Ajiyar zuciya tai ta ɗago ta tace "Tashi muje babanki zaki gani sai dai karki kuskura kiyi magana da karfi."
Cikin sauri ta ɗago ta share hawayenta ta mike tana kamo hannunta. Danejo ta haska ƴar karamar fitila ta ɗan kalleta tace "Kwasomin kayanki nagani." Nan ta fito dasu ta kallesu jitai zuciyarta na sake ɗaci, yanzu kaf kayan nan babu wasu kayan kwarai banda wanda ta dinka mata kwanan nan, to basu isa suyi mata ɗinki ba sai a fara cewa ai sankai ne Maccido dan yaga shine da kuɗi yake wareta yana yi mata, in kuma yai mata a boye a kwace ace wai sun mata yawa ko kaɗan. Hawayenta ta share ta kalli kayan dake jikinta wanda shine wanda ta bata kwanakin baya tace "Kibar wannan ɗin kawai yafi kyau."
A hankali suka fito, kukan tsintsaye kawai ke tashi, b'ɓangaren Maccido sukaje Danejo ta tsaya a waje tace ita ta shiga ɗakin da aka kwantar dashi zata tsaya ta dinga dubawa dan kar wani ya gansu. Da gudu ta shiga yana kwance a kan dan ƙaramin gado sai fitilar kwai dake gefen ɗakin, hannunsa kawai ta riko ta fara hawaye. Ya sani sarai itace ji yake zuciyarsa na sake karaya dan dole ya daure yai abinda ya kamata.
"Munɗo ya isa hakan nan ba gani nan lafiya lau ba?"
Hawayenta ta sharr tana kallansa tace "Baffa Allah a'a baka warke ba, dan da ka warke da na ganka kazo ganina." Fuska ya ɗaure yace "Danejo zata kaiki gun Kawun ki zaku wuce dashi, ni in na samu sauki zan zo na ɗaukeki sai mu sai gida a can muyi zaman mu ni dake." Kai ta girgiza da sauri tace "Baffa aradun Allah bani iya zama a inda baka nan, koma menene za'ai min anan gwara amin inda kake kawai."
"So kike mu dawamma a rigar nan a wannan rayuwar? Akwai abubuwa da dama da nakeso na faɗa miki sai dai yanzu bazan iya sanar dake ba har sai nazo zan faɗa miki, kiyi hakuri da rayuwar da muka jefaki a ciki, Munɗo kin cancanci rayuwa tajin daɗi sai dai kalli yanda aka maidake? can ɗin da zaki kiyi hakuri har na zo bazan dauki lokaci ba zaki ganni."
Kai take ta girgizawa yace "Tashi ku wuce kuma kika kuskura kikai gaddama in nai fishi dake bazan sake miki magana ba."
Zata sake magana ya kauda kai hakan yasa ta mike, tana fitowa Danejo taja hannunta suka fita ta baya. Can jeji suka je suna tafe kayoyin cikin ciyayi su na karzar musu Ƙafa saboda duhu bawani ganin hanya suke yi sosai ba. Sai da sukai tafiya sosai har Danejo taji numfashinta yana fita da sauri yasa suka tsaya, sai a lokacin ta saki hannun Munɗo wacce ta sake kamo hannunta tace "Danejo bana san zuwa ko ina dan Allah."
Rungumeta tai tace "Maccido zai zo ya ɗaukeki ba da daɗewa ba, kedai ki fara tafiya shi namiji ne inyace zai fita bamai ganinsa amma kefa? Ko su kuke ku dawwama a haka?" Nan ta hau cewa "A'a" Danejo ta ɗagota tace "To kiyi hakuri ku fara tafiya kinji ko?"
Kai ta ɗaga suka samu wata bishiya suka zauna abinka da fulani ko tsoro ma basaji.
Sannu-sannu Danejo taga dare sai sake shiga yake basu zo ba bayan kuma ance suzo a ranar a kwashe wajen biyu na dare yanzu kuwa ta tabbatar biyun tayi ita batasan sun canza shawara ba tunda ba waya garesu ba. Tsoro ne ya fara kamata badai mutanen nan kin yadda sukai ba? Ko kuwa sun tashi daga unguwar ne Salau bai gansu ba? Anya ba komawa zasuyi ba? Ita dai sai kwancewa da warwarewa take, ita kam Munɗo hawaye kawai take tana tunanin yanda zatai rayuwa a wani kauyen da ba Baffanta a cikinsa.
Har ta gama karaya dan sun sake sama da awa agun kawai ta yanke shawarar komawa tun kafin ma asan Munɗo bata ɗaki. Fitila ta hango ana hasko inda suke, nan da nan daɗi ya kamata, kallan Munɗo tai tace "Sunzo ɗaukarki, inaso ki sani zaku tafi da dabbobi masu yawan gaske wanda mallakinki ne Maccido ya damka musu kafin yazo su siyar su fara kula dake kafin yazo. Idan yazo in kika sake girma zai sanar dake abinda ya ɓoyewa kowa dake kauyen nan ciki kuwa har dani. Dan haka karki yarda su cutar dake dan arzikin da zaki tafi dashi ya isheki kiyi rayuwarki mai ɗaɗi, in har kikaga zaman yafi na nan wahala in Salau yazo kice ya dawo dake." Kai ta ɗaga mata kafin tace "Amma ina naga dabba ba ma dabobbi ba Danejo? Kin manta banda ko ɗan maraki a rugar nan?"
"Me yasa kikaga duk abinda ƴan kauyen nan sukeyi a kanki ba wanda ya kasheki har yanzu? Meyasa kikaga Ardo na hanasu ƙona ki? Ke kanki kinsan in a gunsu ne kisa ba wani abin bane, sai dai Maccido ya sadaukar da duka dabobbin ki a maimakon su barki ki zauna anan, yanzu kuma yace kwashesu duka zai yi tunda basusan darajarki ba."
Gaba ɗaya ita bata gane mai Danejo ke cewa ba tambayoyi ne fal a bakinta sai dai kafin tai magana Salau ya karaso yana hakki yace "Danejo kinju shiru ko? Ai shawara aka canza, nan ya sanar da ita yanda suka tsara tace "To shikenan yanzu ni zan koma na kwanta kamar ban fito ba kai kuma ka kora dabobbi kiwo kamar yanda kuka saba, motar tana can?" Yace "Eh." Ta sake rungume Munɗo ta fara tafiya, sam bata san yana binta a baya ba sai dataji karar tafiya ta cikin ciyayi, juyowa tai cike da mamaki ta sauke idanunta kan Jauro.....
ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)🔥
RAFEEQ🔥
MUNƊO🔥
ZAMANIN MU AYAU🔥
FATHIYYA.🔥
DOMIN SIYAN GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR ƊAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita da sunan
Asma'u Buhari Aliyu
***
SAI KI/KA ISAR DA SHAIDAR BIYA TA ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
***
***
***
***
Zee Yabour
Da Ayusha Muhd