ƘADDARATA CE A HAKA

Na goma

by @maikosai53

P_10



A gigice Munira ke jijjiga Nuriyya, amma sam ko gezau ba ta yi ba. Hamza dake tsaye bisa kansu wanda shigowarsa kenan da kiran wayarsa da Munira ta yi, shi ma zuciyarsa cike da jimami da alhinin abin da ya sami abokin na sa yake Magana, “Munira samo ruwa a kofi muga”

 Munira ta sauke kan Nuriyya dake cinyarta ta mik’e da sauri ta nufi kicin, ba ta d’au lokaci mai tsayi ba ta dawo hannunta rik’e da kofin ruwa, ta mik’a masa. Ya amsa yana mai tsiyaya ruwan cikin tafin hannunsa kana ya soma yayyafawa kan fuskar Nuriyya.

Ya yi haka sau wajen hud’u amma ba ta motsa ba, hakan ya sa ya ce su fito da ita su wuce asibiti kawai.

 Suna isa asibitin a ka amshesu, yayin da wani likita ya ja ragamar kula da ita.

 Tsawon mintuna arba’in, har lokacin kuma ba ta farfad’o ba. Munira kuwa babu abin da take yi sai kuka da sasshek’a, tsoronta d’aya shi ne ka da ta rasa k’awarta ta.

Hamza ne ke ta dauriya da k’arfin halin rarrashinsu, amma duk da haka duk sun gaza yafawa zuciyoyinsu ruwan salama.

 Tsawon awa biyu ken an likitan na fama da Nuriyya, wacca har lokacin ba ta farka ba. Zuwa wannan lokacin hankalinsu Munira ya sake tashi ainun. Kar dai a ce itama ta mutu? Idan ta mutu su kuwa yaya za su yi? Wannan wace iriyar k’addara ce ke d’awainiya da su? Daga wannan sai wannan.

Ahmad ya shigo jikinsa a sanyaye yana mai tambayar ya mai jiki? Inna ce ta amsa masa da sauk’i yayin da su gwaggo suka kasa furta mishi komai.

 Ya kalli Hamza dake rakub’e zaune kan benci ya ce da shi, “Me likitan ya ce a game da hakan?”

Hamza ya sauke wata b’oyayyiyar ajiyar zuciya kana ya ce, “To har yanzu dai shiru babu wani bayani.”

Ahmad ya bud’e baki da nufin Magana isowar likita wajen ya katse masa maganar, likita ya dubesu kana ya ce,”Ina son ganinku a office” 

Daga haka ya wuce hanyar office na shi, yayin da su kuma suka mara masa baya.

 Yana zaune kan kujera, yayin da suma suka sami waje suka zauna da jiran jin abin da likitan zai ce da su.

 Likita ya kallesu bayan ya ajjiye wata takarda da ya yi wani d’an rubutu a kai.

 “Ba wata matsala ba ce mai yawa, amma tana da buk’atar samun hutu da kwanciyar hankali, kuma in sha Allahu nan ba da jimawa ba za ta farka."

Suka sauke ajjiyar zuciya tare, tare da yiwa likitan godiya kana suka fice baya ya damk’a musu takardar magungunan da za su siyo dan a yi amfani da su wajen ba ta.


 LEGOS


A b’angaren Nasir kuwa lokacin da jirginsu ya kama da wuta, suna kan saitin tsakiyar wani daji ne, cikin k’udirar Allah kuma sai ya kub’utar da shi Nasir d’in yayin da yana cikin jirgin ya ji kamar an jefo shi k’asa. Iskar da take kad’awa ce ta bugeshi har ta farkar da shi daga suman da ya yi. 

 Gurin tsit ba ka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye dake tashi, da tashin sautin iska dake kad’awa, yayin da bishiyoyin wajen keta faman kad’awa. A daddafe ya tashi zaune ya jingina jikinsa da wani dutse, nan ya soma jin kansa na wani irin sarawa tamkar zai fashe, jikinsa ya fara kakkarwa tamkar mazari. Haka ya daure ya mik’e yana d’ingishi ya soma tattakawa da sawayensa har Allah ya kawo shi bakin wani rafi, d’iban rowan ya shiga yi yana sha yana watsawa fuskarsa da jikinsa. Ya d’aura alwala ba tare da fahimtar ina ne gabas ba ya tada ik’ama ya soma gabatar da sallah a zaune, nan da nan kuma wani barcin wahala ya yi awoon gaba da shi bayan ya idar da sallar.


 KANO, ASIBITI.


Cikin sauri ya shigo d’akin gami da sauke wata ajjiyar zuciya, wanda ya yi daidai da farfad’owar Nuriyya.


Munira dake zaune gefen gadon Nuriyya ta kalleshi tana mai furta, “ An ganshi ne Hamza?”

 Ya dubeta kafin ya ce, “Wallahi har yanzu lalube ake ta yi, babu gawar da ba mu duba ba amma ba ta sa ba ce ba, sai dai kawai mu ci gaba da addu’a”


Da k’yar Nuriyya ta iya bud’e bakinta saboda nauyin da ya yi mata, ga wani irin sarawa da kanta yake yi mata. “Munira” ta furta a hankali, wanda ba da ban Muniran na kusa da ita ba da ba za ta iya jiyowa ba.

Munira ta waiga tana mai kallon Nuriyya kana ta ce, “Sannu kin farka, bari na kirawo likita”

 “ A’a barshi Munira bana so, ni dai kawai ki gaya mini da gaske ne Nasir d’ina ya mutu? Da gaske ne ya yi hatsarin jirgin sama ya k’one k’urmus ba a ga gawar shi ba?”

 Sai da ta d’an numfasa, a zahirin gaskiya ba ta son b’oye mata komai, domin ko ba dad’e ko ba jima za ta san gaskiyar al’amarin gwara a yita yanzu a k’are kawai.

 “I abin da a ka sanar da mu kenan. Su Hamza duk sun je filin jirgin amma an tabbatar musu da cewa a na nan ana bincike domin gano inda raguwar mutanen suka yi, kuma in sha Allahu za a gano Nasir da ransa ki kwantar da hankalinki.”

Ta sanya hannuwanta biyu ta dafe kanta saboda tsananin sarawar da yake yi mata,ta shiga halin kid’ima da d’imuwa jin abin da Muniran ta sake cewa. Ta rasa wani abu za ta yi dan jin sauk’in bak’in cikin da ta riski kanta a halin yau, sai kawai ta kurma ihu gami da fad;’in, “ Wayyo Allah na! Na shiga uku na lalace! Na ga ta kaina ni Nuriyya, shi kenan na rasa Nasir d’ina farin cikina wanda yake sona”

Kuka mai tsananin gaske da wasu irin surutai take yi. Munira ta sake matsawa kusa da ita, tare da sauke mata hannun nata da d’ora a kan, kana ta ce, “Haba Nuriyya! Ki yi hak’uri dan girman Allah, ki rungumi k’addararki, Allahn da ya k’addara haka shi zai yaye mana komai, idan ma har da gasken ya mutu to shi ya fimu sonshi ai shiyasa ya karb’i kayansa, ki yi hak’uri.”

Kalmomi ne masu tarin yawa a bakinta, sai dai bakin ya mata nauyi yadda har ta gaza furtawa Muniran su, sai kuma kawai ta tsince kanta da maganar zuciya wanda maganar hart a fito fili, duk da yawancin maganar tamkar sab’o take yi, ganin haka ya sa Hamza ficewa dan sanar da likita ta farka. Koda likita ya iso a yanayin da ya risketa ssai kawai ya zuk’lk’ula mata allurer barci, take kuwa barci ya yi awon gaba da ita.


Ba ita ta farka ba sai gabanin magrib. Ta bud’e idanuwanta a hankali tare da saukesu kan Munira dake zaune kan sallaya tana laziminta.

 “Da gaske na rasa Nasir d’ina Munira? Da gaske Nasir ya tafi ba zai sake dawo wa ba har mu yi rayuwa tare da ni da shi, kamar yadda ya alk’arwanta min?”

Munira ta mik’e tare da nunke sallayar kana ta isa ga Nuriyya ta soma furta, “ Haba Nuriyya wai mene ne haka ne? Dan Allah ki yi hak’uri ki sanyawa zuciyar salama ki yayafa mata ruwan sanyi ko itama ta samu ta yi sanyin”

 “Ki yi hak’uri fa kike cewa Munira? Kin san kuwa me kike fad’a haka? Ta yaya za ki ce na yi hak’uri alhalin Nasir d’ina ya tafi, farin cikina ba ya nan. Ki na tunanin zan iya rayuwa ni ma babu shi ne? Nasir ya yi min alk’awarin samun farin ciki, annushuwa da walwala, ya yi min alk’awarin sona har k’arshen numfashinshi, ya min alk’awarin zai zauna da ni mu rayu tare mu mutu tare, me ya sa zai tafi yanzu ya barni ni kad’ai, me na aikata masa da zai bar ni cikin kewarsa?” Ta rushe da wani irin kuka.

 Munira ba ta hanata ba har sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru kana Munira ta ce, “ Dan Allah Nuriyya ki daina wad’an nan kalaman, me ya sa ba za ki iya yadda da k’addararki ba ne? Ki barwa Allah komai dan Allah”

 “Da gaske wannan d’in k’addarata ce? Me ya sa za ta zo min a wannan k’aulin lokacin da na rasa k’anwata, mahaifina kuma yana kulle gidan yari? Me na aikata mata haka da za ta dinga zuwar min da abubuwa masu nauyi?”

“Ki yi hak’uri komai zai zo da sauk’I, kuma Allah da ya baki Nasir ya da’ukeshi zai sake ba ki wani wanda ya fishi ya maye gurbinsa.”

 “Babu shi, har gaban a bada babu wanda zai maye min ngurbin Nasir d’ina.”

Munira na shirin Magana Ahmad ya shigo, yayin da k’arar wayarsa ta katse musu maganganunsu.

 Ya d’aga wayar yana mai karawa a kunnensa. “To” kawai ya ce yana mai sauke wayar daga jikin kunnen na sa.

 Ya kalli Munira bayan ya yiwa Nuriyya sannu da jiki kana ya ce, “Zan je na duba wata gawa ne, an sanar da ni na zo an sami wata gawa ko shi ne.

 Hamza da Ahmad abokanan Nasir na unguwa, Ahmad malamin makaranta ne, yayin da Hamza ke fannin ma’aikacin soja. Tafiyar Nasir kuwa ta samo asali ne dalilin wani aiki da zai kaishi Lagos a kan wani mutumi da ya d’auke shi a matsayin lauyansa da zai tsaya masa shi ne kuma suka sami hatsari.

Jim kad’an sai ga Ahmad ya shigo shi da Hamza. Ahmad ya zauna gefen gadon da Nuriyya ke kai sai kawai ya fashe da kuka, da man shi Allah ya hore mishi saurin kuka, domin kuwa yana da raunatcciyar zuciya. Yayin da Hamza ya shiga yi ma sa fad’a sosai a kan kukan da yake yi, ta yaya zai sake d’aga hankalin mutane shi da zai zama mutum na farko wajen kwantar musu da hankali? Tun da har yanzu ba a tabbatar da Nasir d’n ko ya mutu ba.

Cikin sauri Nuriyya ta d’ago jajayen idanuwanta ta d’orasu kan Hamza, kana ta ce, “Haba Hamza ta yaya za ka ce haka? Ta yaya za ka ce a kwantar mana da hankali ko mu mukwantar da hankalinmu alhalin har yanzu Nasir bai dawo ba, Gawarwaki nawa a ka gani amma babu ta Nasir sannan ka ce hankali ya kwanta? Gaskiya ni ba zan iya ba, ba zan iya ba, ba zan iya jure hakan ba.” Ta k’arashe tana mai buga kanta da jikin k’arfen gadon da take kai. Da azama Hamza ya fice dan kiran likita, yayin da Munira ta shiga k’ok’arin rik’eta amma tana fizgewa.


A tare suka dawo, Hamza da likita da kuma malam jinya guda biyu.

 Wad’anda su suka taimaka wajen rik’eta likita ya mata allurer barci. Kowa da irin kallon tausayin da yake yi mata, cikin kwana d’aya har ta wani rame ta zaftare sai ka ce ba Nuriyya ba.


Maikosai✍🏼