Na sha ɗaya
by @maikosai53
*ƘADDARATA CE A HAKA*
©Maryam Abdulaziz_Maikosai(Matar Abdul)
P_11
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Wane asibitin ne” Ummi ta ce tana mai mik’ewa tsaye, yayin da ta kashe wayar tana mai sauke ajjiyar numfashi.
A gaggau ce ta zari hijabinta tare da d’aukar kud’i ta fice daga gidan bayan ta sanya mukulli ta rufe shi. Kai tsaye asibitin da aka kwantar da Nuriyya ta nufa. Ba ta sha wani wahalar gano d’akin da aka kwantar da ita ba saboda Munira da ta zo ta tafi da ita daga bakin gate.
Ta k’arasa inda Nuriyya ke kwance, ta zauna gefen gadon tare da kamo hannunta cikin tausayawa ta soma fad’in, “In sha Aallahu za ki warke, za ki tashi babu abin da zai sameki. Ina jinki a cikin zuciyata kamar yadda nake jin d’ana Nasir, in sha Allahu ba zan rasaki ba ‘yata.”
Dukkansu suka zuba mata idanuwa cike da tausayawa suke kallonta. Ga ta a cikin tashin hankalin rasa d’anta wanda ma ko gawarsa ba ta gani ba har yanzu, amma it ace keson kwantarwa da wata hankali.
“Hasbunallahu wani’imal wakil”
Shi ne abin da ya dawo da hankulan mutanen dake cikin d’akin. Ummi dake gefen Nuriyya ta sake saita idanuwanta kanta, Nuriyya ta ware k’wayar idonta tas a kan cikin idanuwan Ummi, ta soma yink’urin ganin ta mik’e zaune amma hakan ya gagara, domin ji take gaba d’aya gab’ob’in jikinta a rik’e suke sun mata nauyi mai yawa, ga kanta da yake mata wani irin ciwo.
Da sauri sauran jama’ar suka k’araso bakin gadon suna masu aika mata da sannu.
Da gudu-gudu hawayen cikin idanuwanta suka soma ambaliya saman kuncinta. Ta sake k’urawa Ummi idanuwa kana ta ce, “Shi kenan Ummi na rasa Nasir d’ina, Ummi kema kin yarda da abin da suke fad’a cewa Nasir d’ina ya mutu?”
Ummi ta tallafo kan Nuriyya, tana mai girgiza kanta kana ta ce,” Ko kad’an Nuriyya, ki yi hak’uri ki ci gaba da addu’a in sha Allahu za a ganshi kuma a raye kin ji. Idan har ba ya raye to ki zamto mace mai tawakkali mai yarda da k’addaarta a duk yadda ta zo mata, ki sa ni Ubangiji ya fimu son shi shiyasa ya d’auke mana shi a lokacin da muke da buk’tarsa.”
Cikin kuka Nuriyya ta ce, “K’addara? Wace irin k’addara ce haka Ummi da har za ta rabani da muradin raina? Da gaske k’addarata ce a haka Ummi? Dan Allah ki tsayar min da ita haka Ummi, kina kallo ta d’auke min Suhaimata, ta kuma sanya min hijabi tsakanina da Baffana ki kalli inda ta kai mini shi, sannan kuma yanzu ta zo za ta raba ni da Nasir d’ina, me ya sa haka? Wane irin abu na aikata mata haka da take zuwar min da zafi haka Ummi? Me na yi…”
Kuka mai k’arfi ne ya tokare mata sauran kalmomin da take son amayarwa, Yayin da Ummi ta sanya tafin hannunta ta rufe mata baki tare da furta, “ Ya isa haka Nuriyya, ka da ki kuskura ki sake irin wad’an nan zantukan, ita k’addara ai tana kan kowa mai kyau da mara kyau, ki kasance baiwa mai amsar ko wacce iriyar k’addara, wacca za ta yi k’ok’arin ganin ta cinye duk wata jarrabawa da Ubangiji mahaliccinta zai yi mata. Ki mayar da komai naki ga Allah hak’ik’a shi kuma zai dafa miki ya fitar dake ga duk halin da kike ciki.”
“To ummi amma…” K’arar wayar Hamza ta katse mata kalamanta, inda suka tokare mata a mak’oshi. Hamza ya amsa wayar tare da furta, “Ok sir, yes sir” Kana ya sauke wayar yana mai dubansu kafin ya furta, “Headquater ne suka kirawo ni, tare da sanar da ni an bani daman a shirya za a had’ani da wasu abokanan aikinmu za mu bi sawun Nasir, inda zamu je can Legos d’in daidai inda abin ya faru ko Allah zai sa a dace.”
“A’a Hamza da kun hak’ura, ni ina jin tsoro ka da aje a yi biyu babu ko d’aya.” Cewar Munira da take rakub’e jikin gadon Nuriyya.
Nan fa Ummi ta shiga goyan bayan kalaman Munira yayin da Nuriyya ta kafe a kan lallai sai Hamza ya bi sawon masoyinta. Nan dai a ka sami matsayar cewar Hamzan zai bi sawunsa, yayin da Ahmad zai tsaya tare da su, har Allah ya sa su Hamzan su dawo.
Ko da zai tafi, har gida yaje ya yiwa Ummi sallama tare da neman addu’arta a kan Allah ya sa su yi nasara a kana bin da suka je nema, ita dai Ummi cikin ranta fad’i take yi 'daman ya barshi kawai ya yi zamansa. ' Yayin da ya je asibiti su ma ya yi musu sallama.
Yau take sati guda cif da d’age shari’arsu Baffa, kuma ayau ne za a sake zama, inda gwaggwo da Ahmad da Munira suka ziyarci zaman koton.
KOTO
Shigowar alk’ali ita ce ta sanya mutanen dake cikin koton mik’ewa dan ba shi girmansa. Hankalin Baffa kuwa a tashe yake ganin bai ga Nuriyya a cikin koton ba, ga shi babu damar tambaya. Har alk’ali ya zauna a ka soma gabatar da shari’ar bai fargaba sai dai jin ambato sunansa da alk’ali ya yi shi ne ya ankarar da shi cewar a koto yake fa gaban alk’ali.
“Shin ka yarda da laifin da ake zarginka das hi?” Alk’ali ya watsawa Baffa tambaya.
Baffa ya sunkuyar da kansa k’asa ya rasa abin da zai ce da alk’ali, domin shi tabbas ya san ya sanya hannu a kan takardar da ta kawo shi wannan koto, to amma shi har ga Allah bai san da wata munak’isar bad a babu abin da zai saka ya sanya hannun.
“A’a ya mai girma mai shari’a” Baffa ya ji hakan ta sub’uto daga bakinsa ya furta.
“Kenan ba ka sanya hannu kan takardar ba?” Alk’ali ya sake tambayarsa.
“Na sanya, sai dai ko kad’an ba takardar shigo da jabun magunguna ba ce ba” Cewar Baffa.
Alk’ali ya yi wasu ‘yan rubuce-rubuce kafin ya d’ago da kansa ya kalli mutanen wajen kana y ace” Ko lauyan wanda ke kare hak’k’ok’in mutane na da abin cewa?”
“ I ya mai girma mai shar’a” Lauyan ya fad’a yana mai mik’ewa tsaye, ya gyara zaman rigarsa kana ya soma da,” Ya mai girma mai shari’a ina so wannan koto mai albarka da ta yi dubu da zaluncin da aka yiwa bayin Allah, wasu sun mutu, wasu sun rasa wasu sassa na jikinsu, wasu na kwance a gadon asibiti ba su san inda suke ba suna kan gabar halin rai ko mutuwa da ta yankewa wannan bawan Allahn hukunci daidai da abin da ya aikata, ta yadda bai ji tausayin al’umma ko kad’an ba na halin da mutane za su riske kawunansu idan sun sha magungunan ya rattaba hannu a kai. Duba da ga shi rashin gaskiyarsa ta sa lauyan da zai kare shi ma babu shi, domin kowa ya san abin da ya aikata tsantsar zalunci ne, na gode ya mai shari’a”
Ya k’arasa fad’a yana mai komawa inda yake ya zauna. Alk’ali ya sake Magana da,
“Ko iyalan malam Abdullahi sun samo lauaynsu?”
Ahmad ne ya tashi tsaye yana mai furta, “A’a ya mai girma mai shari’a, dalilin hakan kuwa ya samo asali ne ga wani iftila’I da su iyalan Dr. suka tsinci kawunansu.” Ya kwashe komai ya sanarwa da alk’ali, ya sake rissinawa kana ya ce, “ Dan haka muna sake neman alfarma da rok’on wannan koto da ta sake d’aga mana k’afa a karo na biyu ta sake d’age zaman, in sha Allahu a zama na gaba za mu gabatar da lauyanmu, na gode.” Ya fad’a yana mai zama.
Sai da alk’ali ya dad’e sosai kafin ya d’ago ya ce, ” Wannan koto mai alfarma ta sake d’aga wannan zama bisa jin koken iyalan malam Abdullahi zuwa nan da d’aya ga watan julin da za mu shigesa. Haka nan koto na umartar da a ci gaba da ajjiye dr. gidan kaso kamar yadda ta bayar da umarni a wancan karon.”
“Koto” Alk’ali ya fad’a yana mai buga ‘yar k’aramar gudumarsa. Nan kowa ya mik’e dan fita daga koton.
Baffa kuwa hamdala ya yi domin godiya ga Allah da ya sa a ka sake d’aga zaman koton, watak’ila nasararsa ce take zuwa shiyasa Allah ya k’i ba su damar zartar mai da hukunci, sai dai k’wak’walwarsa cike take fal da tambayoyi kala-kala amma babu wanda zai yiwa, da haka ‘yansanda suka tasa k’eyarsa dan mayar da shi gidan yari.
Maiƙosai✍🏼