Nine
by @takwalam
TSINTUWA
Nine
Top-notch 2023
Ayshatuuu
*Ta_kwalam is a home for jewelry, your best jewelry plug and introducing my Bridal accessories rent! For me a wedding is a one day celebration, for you to buy lots of costly stuff and after the wedding sun tashi a aiki! A saukake na kawo muku inda zakiyi renting kayan amare kuyi kyau, a kudi kalilan ki kece raini kawata, sannan ki Gama ki dawo dashi. You don't need to buy much. I'm a DM away!*
Muna shiga wani daki, ban ma tsaya na kalla dakin ba na zube saman carpet din dake shimfide a kowanne lungu na dakin, irin dai na da yadda ake carpeting gurin. Na saki wani numfashi me zafi, tare da mikar da kafata, wadda ta shigo Dani ta fito daga wata kofa tace
"Kin gaji ko?"
Na gyada Kai se tace na biyo ta, na bi bayanta zuwa wani bandaki, Ina zuwa tace na cire Kaya na, na tsaya Ina rarraba idanu Dan ni na manta rabon da Inna ta tayimin wanka, ganin Zan Bata Mata lokaci yasa kawai ta Fara cire min, nayi saurin saka hannu na na Kare kirji na da Babu komai, se na ga tayi murmurshi, ta cire min dankwali Kai na kamar bola saboda rabon da a taba shi tun kafin rasuwar Baba, ta tsaya tana kallon Kan nawa da ni Baki daya se muka ji ana Kiran
" Esther!"
Tayi saurin dauraye hannun ta fita tana fadin
" Yes Ma'am!"
Cikin turanci take tambayar ta wacece Boss ya kawo ta? Ta ce Mata ai Ina toilet, ta Fara fadin
" Shi dai Boss Bai rabuwa da kwashe kwashe! For goodness sake wacece ya samo wannan Karan, ya mayar min gida kamar wani orphanage, he's telling me yarinyar wanted to commit suicide! Bari na ganta"
Ta shigo ta same ni a tsaye se zazzare idanu nake, Abu na farko kafin isowar ta shi ne kamshin me sanyin gaske na fita daga gurin ta, doguwa ce Fara tas Yar gayu kyakyawar gaske, tayi ado Kuma irin very lousy kwalliyar nan, kana kallon ta kaga mace me Jin Dadi me Kuma izza! A take zuciya ta taji wani irin tsoro ta ta shige ni Haka Kuma naji ba lallai tayi kirki ba. Ta kalle ni wani irin mugun kallo disgustingly tace
" Kece?"
Nayi saurin tsugunnawa akan knees di na har lokacin hannu na na kirji na kafin nayi magana tace
"Esther what's she hiding?"
Esther tayi dariya tace
" Nothing of course!"
Bata amsa gaisuwar da nayi Mata ba balle ta Kara kallo na se tace har Kai na a aske a Kuma yimin shaving! Haka Easter ta aske Kan tas sannan tayi min wanka da komai, da na fito wata irin iska me sanyin Dadi ta shige ni, a take na lumshe idanu na, mai ta bani na shafa sannan ta dakko min komai sabo dal na saka, sede yunwa nake ji, tea aka hado min me kaurin gaske na kafa Kai na ko zafin bana ji na shnaye shi tas! Esther ta girgiza Kai ta koma se gata da abinci cikin plate shima da na zauna seda na cinye tas ki kafin na wanke hannu ga sanyin fanka Kuma dama su weather din su is favorable se bacci ya dauke ni bansan har lokacin da na dauka Ina baccin ba, lokacin dana tashi duhu ya Shiga sosae Kuma an maida ni Kan karamin gadon dake dakin. Na tashi Ina mitsitsika idanu na Dan ganin abinda yake faruwa, na tashi na koma toilet nayi alwala sede Babu zani balle hijab, na zauna nayi tsuru kamar me neman gafara, se gashi an shigo Esther ce,ta kalle ni tace
" Kin tashi?"
Nace
" Eh Zan yi sallah ne!"
Ta juya Babu jimawa se gashi ta dawo da hijab, ta nuna min gabas na tada sallah. Ina idarwa se naji an turo kofa ana fadin
" Sister!"
Na dago Kai na na kalle ta, tana Kan wheelchair se lokacin na lura Kama take da maman ta, wanann murmushin da ta fara min da nazo anan ta samu matsugunni cikin zuciya ta, har yau Hidaya bana manta wannan murmushin da tayi min, ta Fara kokarin wheeling Kan ta wajen da nake, nayi saurin tashi na fara tura ta saboda a zaman mu a asibiti da Inna na Saba tura ta zuwa lab ko dai wani gurin! Na zauna itama ta dube ni bakin ta a bude da ya fitar da hakoran ta kanana masu kyau tace
" Ina ta son Mamaa ta haihu Amma bata haihu ba, dama Daddy yace zai kawo min sister! I'm Maryam ina js2 bana tafiya Ina fama da matsala a spine di na!"
Ta fada tana nuna min bayan ta anan na fahimci inda take nufi, nayi murmurshi nace
"Sunana Nafisa Salihu I've lost both my parents and I'm an orphan with nowhere to go, your father was my savior so I owe him a lot!"
Ta Kara sakin murmurshi tana min tambayoyin makaranta Ina fada Mata, se kawai gani nayi na saki jiki da kyau da ita, I feel safe a tattare da ita, tare dukka mukai dinner Ina ta Jin dardar Amma yadda Daddy da Maryam ke min yasa na Dan taba yayin da ita Mamaa Babu yabo Babu fallasa se Kuma wata itama tana gefen Daddy, ita ce second wife din shi Bata taba haihuwa ba kamar yadda Maryam ta fada min. Se da Muka gama cin abinci sannan Daddy yace Maryam tayi addua, tayi ya dube su yace
" Ga Amana na kawo muku, sunan ta Nafisa Ina fatan zakuyi hakurin Zama da ita, marainiya ce ba tada kowa..."
Mamaa ta katse shi da fadin
" Mu da muke Shirin tafiya overseas!"
Anty wato amaryar tace
" Su nema Mata Visa!"
Haka akai sati na daya na fara sabawa dasu, Daddy kamar yadda yace na rike su day kyau Haka na dauke su dukka iyaye na musamman Maryam muyi Wasa muyi dariya, muyi karatu tare wani Abu da na fahimta da ita ba tada kokari amma kuma tana son ta koya, hakan da na gani se nake koya Mata Wanda yasa shakuwa da bond din mu Kara karbuwa. Se wani Abu da na fahimta a rayuwa it's more of a lesson Kuma daga wannan lokacin na fahimci tabbas ya Kama ta duk runtsi duk wahala duk Kuma Dadi I should never give up! Maryam kyakyawar gaske ce, Dan tafi mahaifiyar ta kyau, iyayen ta har na da Anty A'isha wato kishiyar Mamaa na son ta kamar su maida ta ciki, mahaifin ta me dukiya ne komai ta bukata is at her disposal Amma kalla Hidaya se Naga she's crippled, Bata iya tafiya, idan da ace ana siyan tafiya da mahaifin ta ya karar da komai nashi Dan ganin ta taka da kafafun ta! Amma Kash Allah yake bayar wa ba kudi ko dukiya ba, na biyu Bata da kokari ko kadan she performs very bad a makaranta, ranar da na saka hannu na a cikin result din ta munin ya baci Kuma she badly wants to learn Haka dai nata rayuwar yake see Naga to ni Kuma kudi kawai babu, iyaye Babu to yawa kaddarar kenan Ina tafiya Ina Kuma gani, Ina ji why am I sad? Ita Kuma duk wannan flaws din she's still happy se kawai na cire wannan daga rayuwa ta nayi looking forward to a beautiful life ahead!
Zama nayi dasu shi ne wani karamin relief da Allah ya kawo min, a lokacin naji Dadi dukda takurawa da uzzurawa da Mamaa tayi min Amma ban damu ba, farin ciki na Maryam, Anty A'isha da Kuma Daddy, suna kula Dani sosae amma Mamaa ko haduwa ba na son Yi da ita ga dukkan Kaya na a dakin ta yake Dole kullum se naje Kuma Daddy yace kafin mu kwanta se min fadawa Mamaa Kuma se munje gurin ta ta dudduba assignment din mu, idan ba idanun Maryam Haka zata daddake ni kawai ta Yi satisfying kiyayyar da take min, a idanu na zata ce min ta tsane ni babban matsalar da take da ita yanzun a rayuwar ta shi ne ya bude idanun ta ta ganni a gidannan, dukda bana Jin Dadi Amma bana nunawa sede nace Mata tayi hakuri. A bangaren Daddy in dai zai fita to yadda yake tambayar Maryam whether she cares for wani Abu Haka zai tambaye ni Amma ni kuma se nace Babu duk abinda ya saya ma Maryam zai siya min. A wannan lokacin nayi wata uku kawai, idan aka ganni ba lallai a gane ni ba, nayi kyau na murmured kwanciyar hankali da nutsuwa ba Kama hannun yaro! Kamani na na asalin terawan yamaltu deba ya Fara fitowa, dukda banyi wannan bakin sosae ba Amma dai ni baka ce, ba nida tsawo sosae Amma dai ba Kuma can gajeriya ba, I've an average height, bani da jiki ko kadan Kuma har yanzun da nake hango 40y ai Kinga banyi kiba ba, wasu sun ce rashin aure ne Wai idan nayi aure zanyi kiba, wasu since Wai aikin da nake ne yasa ba zaa samu fat accumulation ba, whatever dai nasan iyayena dama Basu da kiba so Banda gene kilan.
A watanni na hudu a Jos nayi uzu biyar Wanda ya hada da Wanda nazo dashi ya tashi quarter of the Quran, I was so excited da hakan. Kawai se Maryam ta Fara wata irin rashin lafiya, zazzabi me zafin gaske ta wuni ta Kuma kwana dashi, a take likitan ta Dake Massachusetts yace su taho, wannan tafiyar yasa Daddy yace Mamaa ta zauna zuwa wata daya Dan saboda influence din sa sunyi Mana alkawarin visa, Haka Mamaa ta zauna wadda naso har zuciya ta ace Anty A'isha ce ta zauna Amma se Daddy da Maryam da Kuma Anty A'isha har da Esther Suka tafi. Ya rage da ga driver, Mamaa se ni se wata Fati da aka samo ta dinga Mana aiki kafin muma mu wuce Massachusetts.
To ke dai kin sani ya lafiyar kura balle tayi hauka, da idon mutane ma duka na take, ta zage ni ta Kuma hantare ni balle daga ni se ita? Ai se abinda yayi gaba, ta cigaba da uzzura min yadda Baki tunanin ga visa yaki fitowa, aikin da Esther takeyi Baki daya shi nake Amma ban damu sosae ba a gani na matsugunni ma da Suka bani menene aiki? Balle tarin illimin da na samu wajen lesson teacher di na da Kuma na islamiyya. Idan nayi aiki na gaji Haka Zan dawo daki na kwanta bayan nayi waya da Maryam saboda kullum se ta Kira munyi waya, Haka Daddy ya dinga tambayar ko akwai matsala? Wannan abun ya Kan saka na shiga daki nayi ta kuka Hidaya, na Kan tuna nawa iyayen, Nima suna so na Amma Haka suka tafi suka barni ba Dan sun so ba.
Wani yammaci Mamaa tayi bakuwa, tunda ta shigo take hura hanci tana daddaga Kai, dama kana kallon ta Babu rahmar musulinci a fuskar ta ko kadan! Taci uban fixing na Kai da yatsu gata gansame miya kyace basamudiya ce, I still vividly remember how she looks because that woman will never make it to heaven! Never!
"Waccan yarinyar fa?"
Mamaa ta nisa cikin bacin Rai tace
" Wata orphan ce Boss ya kawo!"
Ina daga can gefe Ina jin maganar kasa kasa, nasan magana ake Amma na kasa fahimtar me suke fada, kallo na da suke lokaci zuwa lokaci yasa nasan da ni suke!
"Kika barta Kuma! Har kin manta yadda akai da A'isha kenan? Ki Gama raino Boss ya aure! Are you insane?"
Mamaa ta dubeni idon ta ta kada yayi jawur da alamu har yau abin na koma Mata zuciya tace
" Bansan ya Zan Yi ba Deborah! Na rasa abinda ke yimin dadi, I hate to open my eyes and see that useless fellow!"
Tayi dariya tace
"Shi ne kike ta zaune da ita?"
"To ya zanyi Debo? Boss has a special interest akan ta, Haka Maryam, yanzun kullum Maryam se sunyi waya kafin suyi bacci fa!"
Debo tayi rolling idanun ta tace
" Wai your only daughter Kika Bari tana Wasa da wancan trash din? Kinsan ya upbringing din ta yake? Haba Mana Khalsi?"
"Meye abun Yi?"
"Very easy! Tare zaku wuce Massachusetts da ita ko? Ok sell her off!"
Cikin rashin fahimta Mamaa tace
"To whom?"
Deborah ta gyara zaman ta tace
" Akwai mutane masu sayan mutane su cire organs din su suyi discarding mutum da ya rage!"
" Organ harvest?"
Ta jiniina Mata Kai, Mamaa tayi shiru tana Jin murya ta na tashi na karatun suratul mujadala, kullum ne Ina cikin tilawa, tana Jin tausayin sayar Dani Amma shi ne abinda zatayi ta fitar Dani daga cikin zuri'ar ta Baki daya!
TSINTUWA is not free, Pay N400 to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza