MUHABBATIL QALB

7

by @asmybaliyu

*MUHABBATIL QALB*

*PAID BOOK* #300

*Free page*


_Asmy b Aliyu_


*Account Detail's*

0004157137

*Jaiz Bank*

*Asma'u Buhari Aliyu*

Shaidar biya ta

***


*Katin wayar MTN*.

*** *Shaidar biya ta* *** *View WhatsApp*


7...


Ganin ya ɗauke hanyar unguwar yarima zuwa gidansu matar da zai aura yasa ta juyo tamkar zatayi kuka take faɗin. "Yaya ba gida zaka saukeni ba.?" Yace "Sai na gama zance da matata." Tamkar zatayi kuka take faɗin. "Toh ni wallahi bacci nakeji Yaya." Kuma daman tasan xuwa xancen Shentima sai sukai goma basu fito daga gidansu Aunty Safeenah ba. Yayi parking gefen hanya yace. "Sauka sai ki samu abun hawa ki tafi gida." Ya faɗa fuska babu walwala. Ta zaro ido tana ƙara riqe handling ɗin motar take faɗin. "Toh ni yanzu a ina zan wani samu abun hawa?" Shareta yayi ya tada motar a fusace har suka kai gida babu fara'a acikin fuskar Asma'a ko kaɗan. Yana gama parking cikin compound ɗin ta fice daga motar tamkar zata tashi sama, kai tsaye entrance ɗin shiga gidan ta nufa. Wayarsa ya fiddo dan kiran Safeenah. Maman su Safeenah ce kawai a parlorn ita da kananen Safeenah, da fara'a Maman su Safeenah keyi mata sannu da zuwa, dole Asma'a ta saki fuskarta ta karasa ta duƙa har ƙasa tana gaishe da ita ta amsa tana tambayarta ya gidan dasu Hajiya? Ta faɗa mata cewar kowa yana lafiya. Ɗaya daga cikin ƙannen Safeenah tasa ta kawo mata ruwa, sai kuma ga Aunty Safeenah ta fito daga ɗakinta da hijab har ƙasa a jikinta. Black beauty chaculate ce tana da kyau sosai. Na gaisheta ta amsa tana tambayata kwana biyu ban leƙo ba, na faɗa mata cewar makaranta ce babu hutu. Daga haka ta nufi ƙofa tana faɗawa Mamansu zataje ta shigo da Yah Shantima. Kusan awa ɗaya Yah Shentima baice na fito ba har na gaji da zama saboda wanka kawai nakeso nayi. Maman su Aunty Safeenah ta dubi ƙanwar Aunty Safeenah mai suna Sakeena wacce zasu zo shekaru ɗaya da ita tace. "Sakeenah kuje ɗakin ki mana." Sakeena ta miƙe tsaye nabi bayanta duk da Sakeena bata da fara'a kamar Aunty Safeenah, muna shiga ɗakinta ta nufi hanyar toilet ta barni, ni kuma na zauna akan doguwar soofa tamkar zanyi kuka. Bata daɗe ba ta fito ta haye kan bed ta jawo wayarta kirar Iphone 7 ta shiga yin wayarta tana wani maƙe muryarta. Wani kallo na riqa yi mata ganin taki kulani yasa ban daɗe ba a ɗakin na koma wajen Mama dake zaune a parlor. Sai kusan goma da rabi Aunty Safeenah ta shigo anan ne Mamansu ta haɗa min turarruka da sabulai tace na gaishe da Maman mu. Aunty Safeenah kuma ta rakani har bakin mota ta buɗe min front seat na zauna ta rufe, anan ɗin ma sai da suka ɓata fiye da minti goma dan jaraba ko meye na nanewa juna sudama sun kusa yin aure. Ai kuwa ko sai da safen da take yi banza tayi mata har suka fita daga cikin gate ɗin gidan su. Ashe yah Shantima ya kula da share Safeenah ɗin da Asma'a tayi, wani irin kalar kama mata kunne yayi da yasa ta saki wani irin ihu da dukkanin karfinta take kiran sunan Mama. "Ashe rashin kunyarki ya tashi daga kaina har yazo kan matata?" Ya faɗa a tsawace, cikin fashewa da kuka take faɗin. "Toh me nayi mata kuma? babu fa abunda nayi Yaya." Cikin ɓacin rai yake cewa. "Shine tana yi maki magana kina wani shareta?" Hawaye na rolling a cikin fuskarta tana turo baki take faɗin. "Ni nagaji da magana wallahi." Kwafa Shantima yayi har suka kai gida Asma'a bata ko kalli inda yake ba. Suna shiga Mama nayi mata magana bata kulata ba ta nufi ɗakinta ranta na suya gamida murzawa ƙofar key. Mama ta girgiza kai dan ta san daman za'ayi haka tunda tace Shentima yaje ya ɗakko tasan zasu kai wannan lokacin basu dawo ba. Washe gari duk da baccin dake cikin idonta haka ta nufi part ɗin Inna kusan ƙarfe 7:00 na safe dan tasan yanzu Inna na kan neman wayarta. Door bell ta danna yarinyar da keyiwa Inna share-share ta buɗe, murya can ƙasa Asma'a ke faɗin. "Hibba Inna ta tashi ne?" Hibba ta girgiza kai tana faɗin. "Eh tana ɗaki." Ɗan ajiyar zuciya ta sauke ta shiga cikin parlorn can bayan TV ta aje wayar Inna ta juya ta koma part ɗinsu. Zata kwanta Mama ta turo ƙofar ɗakin na ta, tana riƙe da ƙofar take faɗin. "Ki tashi ki wanke innerwears ɗinki gasu nan kusan kala nawa kike tara sabida ke baki san ciwon kanki ba." Tana murza idanuwa take cewa. "Mama basu da yawa fa, duka bra 3 da kuma..." Mama ta katseta rai a ɓace take faɗin. "Bana son musu ki tashi kawai nace." Haka ta nufi toilet tamkar zatayi kuka saboda ta tsani wanki a cikin rayuwarta. Mama ta ɗaga murya yadda zata jita take faɗin. "Zan dawo nan da minti goma na gani idan kinyi." Kuka ne kawai Asma'a batayi ba saboda takaici. Koda Mama ta dawo tana cikin toilet ɗin tana wanki, ganin wankin takeyi yasa Mama ta fito daga toilet ɗin tayi ficewarta.


************************

*SULTAN ABUBAKAR 111 INTERNATIONAL AIRPORT SOKOTO*


Ya jingina bayansa jikin motarsa yana sanye ne cikin (traditional attire) wanda sukayi masa matuƙar kyau. Sanye yake cikin wani bakin glass wanda ya ɓoye ainahin kwayar idanunsa, ƴan matan dake wurin babu abunda suke yi sai kallon sa. Mintuna ƙalilan ya rage jirgin su Maryam Saraki ya sauka wacce ta taho ne tun daga Lagos dan kawo kayan lefensa da tagama haɗawa. Yaron dake yi masu hidima ne ya fara zuwa da akwatunan a jirgin ƙasa wanda tun a jiya ya iso garin Sokoto. Ita kuma a yau ne ta biyo jirgin sama ta taho garin. Tun daga nesa ya hangota ya ƙara faɗaɗa murmushi a cikin fuskarsa, cikin sauri ya nufeta ya karɓi trolley ɗin hannunta suka bawa juna wani irin side hug. Tare suka jera zuwa mota, ya buɗe bayan booth ya saka jakar trolley ɗin sannan yazo ya buɗe mata back seat ta shiga ya mayar da ƙofar ya rufe ya nufi ɓangaren driver ya zauna tare da yiwa motar key suka bar cikin airport ɗin yana ɗaukar hanyar unguwar da yake da zama wato (Sama Road) "Yanzu ke kaɗai kika biyo hanyar nan ina Hooda? na zata tare zaku taho." Maryam Saraki na danna wayar hannunta tana ƙoƙarin kiran maigidanta take faɗin. "Hooda makaranta kasan Babanta bazai bari tayi fashi ba duk da na faɗa masa kwana biyu nima zanyi na koma." Ba tare da ya juyo ba yake cewa. "Wannan ba hujja bace haka kurum ki barota cikin samarin yayanki suna takura mata." Dariya tayi tana faɗin. "Ai ita ɗaya ce a gidan ka manta baban nasu ya maida su boarding school?" Da mamaki Maina Saraki ke faɗin. "Duka yaushe akayi hakan? Gaskiya bani da labarin nan." Murmushi tayi tana cewa. "Toh yaga ƴaƴansa zasu karya masa yarinya shi yasa ya kai su." Dariya sosai Maina keyi wanda ya manta yaushe rabon da yayi dariya irin wannan. "Ai gara da ya kai su boarding ɗin suje can suyi da maza ƴan uwansu." Maryan saraki ta girgiza kai tana faɗin. "Bazaka gane Hooda bane Maina, ta fiye son girma da tsare gida itama ai dan haka suke nuna mata cewa su maza ne." Har suka kai gidansa suna hirar yaran Maryam Saraki. Ɗayan ɗakinsa ta sauka wanka tayi ta gabatar da sallar azzahar. Tare suka yi lunch ɗin da yayi masu takeaway ɗinsa. Tana lura da duk wani motsin ƙanin nata taga ba ƙaramin ramewa yayi ba, duk yadda ta sako masa zancen Hafsat dan ta bugi cikinsa taji ko akwai matsala sai dai yayi murmushi ya faɗa mata komai lafiya ta manta shi barister ne mai zaman kansa. Ta rigashi zuwa duniya ne kawai amman bazata yi masa wayau ko dabara ba. Ta san karya kawai yake faɗa mata dan tasan mugun zurfin cikin Maina zaiyi wuya ya faɗa mata damuwarsa kuma taji daɗi da Hajiya ba tayi masa zancen yadda sukayi da Hafsat ba saboda yanzu Maina zai ɗauki mataki dan zai yanke hukunci ne koda Baffa zai yi fushi dashi. Tun yana karami baya ɗaukar wulakanci komai kankantarsa. Wani irin tausayin kanin nata ya rufe ta lokaci ɗaya. Sai kusan 2:00pm suka fito suka ɗauki hanyar zuwa Gusau a motarsa da manyyan akwatunan kayan lefensa a ciki. Suna tafiya suna hira tana tsokanarsa ya duba kayan saboda yau da safe yaron da ya kawo kayan ya koma dan jiya sai bayan isha'i suka iso. Ƙarfe biyar dai-dai ya kunno kan hancin motarsa acikin Saraki mantion, babu kowa aciki compound ɗin gidan, ganin motar Baffa acikin rumfar adana motoci ya tabbarwa da Maina Saraki cewa Baffa na gidan. Maryam Saraki ce farkon ƙofa, Hajiya ce ta buɗe ƙofar da mamaki kwance a cikin fuskarta take kallonta, haka tana kallon Maina Saraki dake bayanta. Wani irin murmushin kaunar uwa ne kwance cikin fuskarsa. Ya baiwa Hajiarsa hug side murya can ƙasa yake faɗin. "I really miss you Hajiya." Ya faɗa yana riƙe da hannunta. Kallonsa kurum take tana kallon irin ramar da yaron nata yayi, wani abu taji yana dan ne mata zuciya. Ta kalli Maryam Saraki tana faɗin. "Tafiyar yamma haka baki faɗa min zaki zoba.?" Da murmushi a fuskarta take faɗin. "Wallahi kuwa Hajiya Maina kawai ya san da tafiyar nan, daman kuma kayan lefensa na kawo masa." Nan take fara'ar dake cikin fuskar Hajiyan ta ɓace ba tareda tace komai ba ta juya ta koma cikin parlorn tabar su Maina a bakin ƙofar. Mai aikin Hajiya ta karɓi jakar kayan Maryam Saraki ta kai mata ɗakin da take sauka. Da fara'a Baffa ke faɗin. "Kune da yamma haka?" Maryam ta zauna cikin rug tana gaishesa, ya amsa da fara'a yake tambayarta ina matarsa da abokaninsa? ta faɗa masa suna lafiya itama lefen Maina ta kawo, Baffa yayi Allah ya sanya alkhairi. Anan cikin parlorn aka riƙa shigo da manyyan akwatunan kayan lefen masu tsadar gaske. "Ai kawai a kwashesu akai su ɓangaren Inna." Hajiya tayi maganar babu fara'a cikin fuskarta. Da sauri Baffa yace. "A'a ki fara gani tukuna sai akai can ɗin." Da sauri ta katse Baffan tana faɗin. "Ai naga kayan tun a waya basai na gani ba Baffa Allah yasa albarka." Duka ƴaƴan nata suka kalleta, da wani yanayi cikin fuskar Hajiya haka aka kwashi kayan zuwa ɓangaren inna. Lokaci ɗaya kuma jikin Maina Saraki yayi sanyi, dakyar ya miƙe zuwa ɗakinsa. Itama Maryam bin bayansa tayi, tana rage kayan jikinta Hajiya ta shigo ɗakin ta zauna gefen gado tana kallon Maryam Saraki rai a ɓace take faɗin "Ashe baki da hankali?" Da sauri Maryam ke faɗin. "Meya faru kuma Hajiya?" "Saboda rashin hankali duk wannan uban dukiya kuka narke wajen haɗa wannan lefen kin san yarinya nan yanzu bata son auren." Hajiya ta ƙarasa maganar sounding so very angry. Da taushin murya Maryam Saraki ke faɗin. "Dan Allah kiyi hakuri Hajiya komai zai zama dai-dai." Hajiya batace komai ba tabar mata room ɗin a fusace. Wata irin ajiyar zuciya Maryam ɗin ta sauke taci gaba da abinda takeyi. Daga Maryam har Maina kowa shakkar haduwa da Hajiya yake yi musamman ma Maina da yasan zai sha faɗa sosai. Bayan magrib ya shiga suka gaisa da Abba dasu Ummah sa'anan ya nufi ɓangaren Inna wacce babu kowa a parlorn sai karar TV. Ɗakin Inna yayi knocking yaji shiru sai ya tura ƙofar ɗakin nata babu kowa a ɗakin amman yaji karar ruwa a toilet, a hankali ya riƙa jin murya ƙasa-ƙasa a ciki, kai tsaye ɗakin ya nufa, mamaki ya kusa kasheshi, daga ita sai ƴar ɓingilar riga ta (body hook) wacce iyakarta cinyoyinta, kallo ɗaya yayi mata yasan da namiji take yin wayar. Mamaki kusan sandare shi yayi a tsaye, jin motsi yasa ta juyo da sauri sukayi ido huɗu dashi, wani irin zaro ido tayi gamida miƙewa tsaye da sauri ta katse kiran ta goge lambar. Yana tsaye yana kallonta fararen cinyoyinta yabi da kallo, rabin kirjinta duka a waje saboda daman zai yi wuya kaga Asma'a Saraki da suturar kwarai ajikinta dan har zaneta yake yi har kafa doka yayi kar ya ƙara ganinsu da english wears amman yana mamakin taurin kai irin nata, duk cikin ƙannensa itace fitsararra haka itace batada tsoro. Duk tsoronsa da ƙannensa keyi ita idan zaiyi tsawa na minti biyu kafin minti biyar ta manta hargaginsa. Turarensa duk ya gama cika ɗakin, a yadda yake ta kowa zuwa gabanta yasa kirjinta yayi wani kalar bugawa. Makurewa tayi a jikin bango tana tsuke baki. "Bani wayar." Ya faɗa da coolness watau babu tsawa cikin muryar. Da sauri ta tura wayar cikin bra ɗinta, wajen da ta jefa wayar yabi da kallo yana mamakinta, bata idar da goge duka abunda takeso ta goge a wayar ba. Rumfa yayi mata da hannunsa numfashinta taji yana yin kaɗan haka taji iskar dakin gaba ɗaya ya canza mata. "Na taɓa yi maki wannan kalar wasan?" Ya faɗa da mugun tsawa, ta kallesa ido cikin ido tana cewa. "Dafa ƙawata muke wayar." Hannunsa taga yana ƙoƙarin kaiwa wajen ai da sauri ta saki ihu gamida zubewa ƙasa, shi kuwa ihun nata ne ya gigitashi har yasa ya nufi ƙofar fita yana cikin karo da bango. Lallai wannan yarinyar daga shaiɗan sai ita a shaiɗanci. Shi kuma abunda yasa ya fito kar Inna ta same su a haka bai san kalar tunanin da zatayi ba. Har ya nufi ƙofar barin parlorn yaji muryar Inna tana yi masa magana. Tsayawa yayi cak gabansa na wani irin bugu....




(Complete Decuments)

*WAMINAL HUB*#500

*NIDA RAHEEMA*#300

*ALBI(my heart)*#500


#Asmy b Aliyu

#maina saraki

#Asma'a saraki

#Team Muhabbatil qalb

#Haske Writers Association.....