FreeArewaPen original
MUHABBATIL QALB
- 1views
- 81chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
*MUHABBATIL QALB**ASMY B ALIYU**Paid book**Free page*1....Drivern gidan su na danno hancin motar cikin babban compound ɗin gidan mai ɗauke da sashe har guda uku ta buɗe ido da mamaki take kallon motar Maina saraki dake fake acikin babban compound. Kara buɗe ido tayi tana kallon motar yaushe yazo? ta tambayi zuciyarta bayan ko minti talatin basuyi ba da gama waya dashi. Kai tsaye ta fice daga cikin motar, sashen dake can ƙarshe ta nufa da gudu duk da yayda ta kwaso zafin rana ga yunwa da take ji haka ta nufi entrance ɗin shiga part ɗin. Door bell ta danna ba'a ɗauki lokaci ba mai aiki tazo ta buɗe mata, ganin Hafsat yasa ta ba ta hanya tana gaisheta, bata ko kulata ba ta shige, kai tsaye stairs ta nufa tana haɗawa da gudu. Ɗakinsa ta nufa dake ɓangaren dama da sauri ta buɗe ƙofar dai-dai lokacin Muhammad Maina ya buɗe ƙofar toilet ya fito jikinsa ɗaure da babban towel fari sol. Da gudu taje ta ƙanƙameshi tana yi masa ihu. ware manyan eye's ɗinsa yayi masu kama da na cat yana kallonta, da wata kalan murya yake faɗin. "Sweet zaki kada mufa." Ta maƙe kafaɗa tana turo baki ta wani haɗe rai lokaci ɗaya ya riga da yasan laifinsa bai faɗa mata zuwansa ba. Komawa tayi kan soofa ta zauna ranta a ɓace ta tallabe fuskarta da hannayenta duka biyu. Hakan da tayi yasa Maina Saraki sakin wani irin kayattacen murmushi, hannayensa ya haɗe duka biyu da ido yake bata hakuri. Maƙe kafaɗa tayi alamar bazatayi ba, ya cije lips. Warware towel ɗin ya shiga yi ta fiddo da dukkan idonta da gudu ta nufi ƙofa ya bita da kallo still da wani irin murmushi cikin fuskarsa. Har ta sauka ƙasa babu kowa cikin parlorn. Wani irin murmushi ne kwance cikin fuskarta, tana ƙaunar Maina Saraki da dukkan zuciya da ruhinta. Kai tsaye part ɗin su ta nufa. Mama ce a parlorn tana shirya lunch Asma'a ce zaune akan rug tana bitar karatunta na hadda. Dakyar Hafsat Saraki ta gaisheda Mama da suka haɗa ido da haka ta nufi part ɗin su, Asma'a ta taɓe baki ta cigaba da abunda takeyi, Mama ta ƙaraso cikin parlorn tana faɗin. "Kije ki ɗibi abinci lokaci na tafiya kin san Shantima bai son jira nasan kuma shi zai kaiku Islamiyya tunda driver tare da Baffan ku zasu fita." Daga haka Mama ta nufi stairs Asma'a ta turo baki tana faɗin. "Mama nifa bana son jelop rice dan Allah nayi wainar fulawa mana?" Wani kallo Mama keyi mata tana faɗin. "Har yaushe kikayi wainar kuka tafi islamiya?" Da sauri Asma'a ke cewa. "Minti nawa ne Mama? dan Allah." Ta faɗa mata cikin sanyi murya, Mama ta girgiza kai tana cigaba da tafiya take faɗin. "Ni dai babu ruwana saboda kin san halin wanda zai kaiku islamiyyar." Kwashe books ɗinta tayi tabi bayan Mama. Kusan biyu da rabi ta fito daga parlorn ta nufi part ɗin Ummah, Hafsat ce kawai a parlorn tana waya, kallo ɗaya Hafsat tayi mata ta cigaba da wayarta, kai tsaye ɗaki...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.