MUGUN NUFI!

Chapter 3

by @nanahaleema11

*MUGUN NUFI*

     ©️ *Nana Haleema.*

*Page 3*

Sholly tana komawa d'akin da yake nata ta d'auki waya ta kira number Baban Husna bata jima tana ringing ba ya d'auka, sallama tayi masa suka gaisa kafin tace, "Baba gaskiya kasan yadda zakayi ka raba Husna da likitan nan dan shine yake juya mata tunani lokaci d'aya, d'azu zuwa tayi ta same ni take cemin wai ita ta gaji da wannan rayuwar ta daina kuma daga wajan sa ta dawo."

Daga can b'angaren Abba ya sauke numfashi yace, "Dr Ahmad Abdulsamad, mahaifin sa babban ma'aikaci ne a garin da kuke, yana da asibiti mallakin sa me suna Silver specialist hospital a cikin unguwar Gwarunfa dake Abuja,Shine wanda kike nufi ko?." Sholly da taji abinda bata sani ba daga bakin ta gyad'a kai tace, "Shine, wata biyu baya suka had'u shikenan ta fara san sa duk abinda yace mata ta bari tana bari, wani lokacin in tazo nan kaga manyan alhazai suna bin ta amma tace ita sam ba abinda ya kawo ta kenan ba sai nayi da gaske fa take sauraro na."

Daga can b'angaren Baba ya sauke numfashi had'i da yin murmushi yace, "Kada ki damu ki k'yale ta taje wajan sa duk sanda taso ni da kaina zanyi maganin abun."

"Amma Baba auren sa fa take so tayi."

"Aure!" Sai kuma yayi murmushi yace, "Aure tsakanin ta dashi har abada, Ya haramta a gare ta bazai tab'a zama mijin ta ba ki rubuta wannan ki ajjiye."

Wani sanyin farin ciki Sholly taji a ranta domin kuwa tunda taji ance baban sa mai kud'i ne taji ta sake tsanar kusancin sa dana Husna amma abinda Baba yace ya kwantar mata da hankali, "Toh Baba da naga wani abu ba dai-dai ba zan sanar da kai." Bai amsa ba ya kashe wayar tabi wayar da kallo tace, "Uba ya dinga saka y'ar sa bin maza ba don rashin kud'i ba, mu namu iyayen talauci ya sanya suka saka mana ido amma ita Husna ban san dalilin mahaifin ta na aikata hakan ba." Tab'e baki tayi ta ajjiye wayar ta shiga band'akin da yake cikin d'akin.

******

A.A kuwa ko a theater room d'in gabad'aya tunanin sa yana wajan Husna burin sa yaji ta bar Abuja har suka fito abinda yake zuciyar sa kenan, Mima na bayan sa suka biya ta labour room suka fita suka shiga office, ya wanke hannun sa ya sa hand sanitizer ya d'auki wayar sa da niyar neman number ta sai ya tuna ashe fa bashi da number ta itace take da tasa.

Dafe kan sa yayi ya furta, "Oh my god!" Ya fad'a yana zama a kan kujera yana tunani, Mima ta kalle shi ta zauna a gefen sa tace, "Dr i have a question." Sanin bazai bata amsa ba ya saka tace, "About the tablet da naga ka saka patient din da muka gani yanzu a labour room, naga ka saka mata tab a private part nata wanne tablet ne? Meye amfanin sa kuma?."

Banza yayi mata bai ko kalli gefen ta ba kansa na sama yana kallon ginin p.o.p d'in da yake office d'in gabad'aya hankalin sa da tunanin sa yana ga Husna, jin shiru ya saka tace, "Dr I'm talking to u fa, I'm sure kana jin me nake cewa." Nan ma bai motsa ba har ta fara zuwa wuya ta bud'e baki zatayi magana suka had'a ido tayi saurin mayar da maganar ta ya d'age gira d'aya yace, "what is private part?."

"I mean her cervix" ta fad'a kanta na k'asa. Tsaki ya jaya mik'e tsaye ya k'arasa inda fridge yake ya d'auki ruwa ya bud'e ya sha ya ajjiye ragowar ya k'arasa inda files suke yana duba next theater da zai shiga, kamar ya manta da ita a wajan sai daga baya taji maganar sa daga sama yace, "research on your self, U can go akwai patients suna jiran ki" ya fad'a ba tare da ya juyo ba.

Ji tayi kamar ta shak'e shi dana sanin tambayar sa ya kawo mata ziyara, tunda akace ya fara aiki da ita shikenan ko yaushe da fi'ilin da zai fito mata dashi wai a ganin sa batayi gogewar da zata fara aiki ba, turo baki gaba tayi tana hararar sa cikin kunkuni tace, "mutum sai bak'in hali komai baza'a ayi dashi cikin kwanciyar hankali ba." Juyowa yayi ya watsa mata banzan kallon da ya saka ta daina hararar sa ta mik'e tana niyar fita aka turo k'ofar aka shigo.

Ganin Wanda ya shigo ya saka ta yin murmushi shima yayi kafin yace, "badai patients ya tara miki ba?." Bata yi magana ba sai murmushi da tayi tana niyar fita ya kalle ta yace, "In kin huta zan shigo" ya fad'a da murmushi yana kallon ta. itama murmushin tayi tace, "to sai kazo" ta fad'a tana bud'e k'ofar ta fita.

Juyowar da yayi suka had'a ido da Ahmad yana hararar sa tare da jan tsaki, y'ar dariya Omar yayi kafin yace, "Yauwa d'azu me ya kawo wannan karuwar office d'in ka?."

Banza yayi masa bai kula shi ba badan baiji mai yace ba, "Magana nake maka fa Ahmad." D'ago kansa yayi ya kalle shi yace, "to me zance maka Umar? Meya kawo ta waje na kake tambaya nima kuma ban san me tazo yi ba kaga babu amsar da zan baka, ka kuma daina kiran ta karuwa sunan ta Husna".

"Na fad'a karuwa, ba karuwar bace zaka ce wani nace Husna banzan fad'a ba, Ahmad meye kai ka sauraron yarinyar nan dan Allah meye had'in ka da ita?, naga taimakon ta kake son yi kuma ta nuna bata so basai ka k'yale ta ba, Har ta fara biyo ka office kana zaman zaman ka zata zubar maka da k'ima da daraja, ka k'yale yarinyar nan amma kak'i kai ga sarkin son taimako" ya k'arasa fad'a a fusace yana kallon sa.

Nan ma banza ya sake yi masa har sai da ya fusata yace, "na fa gaji da wannan wulak'ancin naka ina maka magana kana share ni." Sai a sannan yace,

"Omar baza ka gane ba, yarinyar nan ba wani shekaru ne da ita ba bana tunanin ta kai 25 years a duniya, babu abinda ta sani na addini bata banbance tsakanin halak da haram, a yau na kuma tabbatar da akwai tasirin wani a cikin rayuwar ta kamar forcing d'in ta ake tana aikata abinda take yi badon tana so ba sai dan tsoro, bata da uwa wacce zata zaunar da ita ta nuna mata dai-dai da ba dai-dai ba, Omar in ba'a shiga rayuwar irin wad'an nan an taimaka musu ba rayuwar suwa za'a shiga?. Abinda kake tunani a kaina sam ba haka bane kai ka sani bana neman mata tausayin ta da nake ji kawai ya saka nake sauraron ta, kuma kasan wannan aiki nane dani da kai tunda muna da foundation akan hakan, duk cikin wanda muka taimaka babu wacce nafi jin tausayin ta kamar ita jin ta nake a jiki na kamar y'ar uwa ta shiyasa nake so na d'auke ta daga cikin wuta na dawo da ita waje mai sanyi domin na lura ita ba sana'a ta d'auki abin ba."

"wallahi tun ranar da na fara ganin ta take bani tausayi har kawo yau taimakon ta nake so nayi ba wani abun ba kuma kaima kasan sai a hankali komai zai bar jikin ta ba yanzu ba. Wanda suka gabace ta ya akayi fama dasu ka manta ne?." ya fad'a cikin murya mai sanyi yana kallon Omar d'in.

Ajiyar zuciya Omar yayi yace, "bance kar ka taimaka mata ba Ahmad amma ka daina zak'ewa akan lamuran irin su, ba fata nake ba amma zata iya kasancewa turo ta akayi wajan ka dan tayi wasa da hankalin ka kasan kuma tsaf zata iya, ta daina zuwa inda kake zuwan ta kusa da kai babbar illa ce ga rayuwar ka dana dangin ka da kuma mahaifin ka, kar ka manta Abbah babban mutum ne a garin nan samun matsalar ka d ita har shi sai ya shafa, kai karan kanka ma illa zatayi maka domin ana ganin k'imar ka ba a iya Nigeria ba kad'ai ka sani. ka duba project d'in da aka baka d'azu wanda ka jima kana mafarkin samun sa sai gashi yazo har inda kake, yawan ganin ku tare za'a iya amfani dashi wajan b'ata maka suna wanda baza ka iya goge shi ba shiyasa nake baka shawara ka dinga baya-baya da ita."

"Haka ne naji, amma mutanen da kake magana a kai sun san aiki nane hakan ko?."

"Nima na sani amma mutane basa raina abin magana, in ka duba duk cikin wanda aka taimakawa babu mai zuwa inda kake sai ita."

"To naji."

"Bai laifi."

Mik'ewa Ahmad yayi ya d'auki rigar sa ya mayar ya fara had'a kayan da zai fita dasu, "Badai tafiya ba?" Omar ya tambaya yana kallon sa, "eh to zan fara sallar azhar yanzu sannan zan dawo ina da patients k'arfe uku." Girgiza kai Omar yayi tare da yi masa jinjina yace, "An gaishe ka Ahmady kana k'okari sosai sai dai Allah ya biya ka." Murmushi yayi kad'an yace, "Amin, har da kai kaima" ya fad'a yana shiga toilet d'in dake office d'in.

Ana yin azahar Mima ta bar asibitin bata sake bi ta kansa ba domin mugun haushin sa take ji a zuciyar ta in ta tsaya sauraron sa ji take zata iya shak'o wuyan sa.

 Ahmad sai bayan magariba ya koma gida ya daidaita parking d'in motar ya fito,a hankali yake takawa zuwa cikin gidan inda yake jiyo hayaniya da alama mutanen gidan sun kawo ziyara kamar bazai shiga ciki ba sai kuma ya fasa ya shiga, da sallama ya bud'e k'ofar falon ya shiga yana kallon wanda suke zaune a falon, "likitan likitoci, sannu masu aikin Allah" wani daga cikin wad'an da suke zaune ya fad'a yana kallon Ahmad.

Maimakon yayi magana sai yayi murmushi ya wani kwab'e fuska ya nufi inda Mummy take zaune tana jifan sa da murmushi, yana zuwa ya zauna kusa da ita tare da kwanciya a kafad'ar ta ya saka hannu sa ya zagaya ya rik'e kafad'un ta yace, "Mummy I'm so tired" ya fad'a yana lumshe ido. Shafa kansa tayi tace, "Sorry Ahmady na kana k'okari sosai".

"Tabdijam dallah malam tashi sai ka karya mana uwa k'aton ka dakai kazo ka wani kwanta a kafad'ar ta" Wata mace ta fad'a a alama Yayar sace tana hararar sa, "Wai Mummy daman har yanzu Ahamdy bai daina kwanciya a jikin ki ba? Wallahi Mummy ke kika sangarta shi yaro sama da shekara talatin da wani abu amma abinda yake yi Tasleem bata yi ita da take auta" wani ya sake fad'a shima yana kallon Mummyn tasu.

"Wai baza ka tashi ba sai nazo na make ka?" Wanda ya fisu girma a ciki ya fad'a da alama shine yayan su gabad'aya.

D'agowa yayi ya kalle su kafin yace, "Mummy wai ina ruwan su dani ne duk dun takura min babu wanda yake tausayi na sai ke da Mamy kowa fad'a da masifa" ya fad'a cikin shagwa6a sosai yana sake mayar da kansa kafad'ar ta.

"Wai ina ruwan ku dashi ne,? Yaro ya dawo daga aiki tun safe sai yanzu ya gaji ai kamata yayi a barshi ya huta amma kowa ya fara kawo masa suka ko ruwa bai sha ba." Kallon kallo sukayi kafin macen ciki tace, "Wai Mummy wannan sangamemen ne yaro?, Kalle shi ba inda yayi auren wuri yana da y'ar shekara sha kaza amma shine yaro?, Daman ai Mummy indai aka cee Ahmad bakya ganin laifin sa."

"Yaro ne mana Lubna tunda baiyi aure ba yaro ne ni a waje na ko autan Mummy" ta fad'a tana kallon sa da murmushi. Kiss ya mata a kumatu ba tare da yace komai ba.

 Babban cikin su ya mik'e a fusace ya janye shi daga jikin ta yana fad'in, "Naga ranar da zakayi hankali wallahi abinda kakeyi ko Tasleem bata yi". Sai a lokacin yayi dariya wanda suma mutanen falon dariyar suke yace, "ni kun saka min ido wallahi, kowa kishi yake dani dan kawai Mummy tafi so na".

"Mtswww aure zamu yi maka wallahi kaje can ka k'arata" Anty Lubna ta fad'a tana hararar sa, shima kallon ta yayi yace, "in kin gaji da gani na ai sai ki aurar dani tunda a akan ki nake" ya fad'a yana murgad'a mata baki kamar yadda yara suke yi. Sai kuwa tayi dariya sosai sannan suka fara gaisawa cikin raha da wasa da dariya.

Abbah da Abie ne suka shigo falon da Mamy da ta fito daga kitchen sai Mima da Tasleem da suka shigo suma duka da sallama, aka amsa na kan kujera suka zame k'asa suka zauna aka bar iyayen a kan kujera a lokacin Dada ma ta iso.

Dada ta banka masa harara tace, "Su rasa kunya an dawo kenan?." Kallon ta yayi ya wara mata idanu ya d'auke kansa. "Ka yiwa uban ka gashi nan a zaune" ta fad'a tana nuna masa Abie da hannu. Bai sake kallon ta ba sai had'e rai da yayi dan yaga Mima na kallon sa.

Abbah yace, "Kiyi hak'uri Dada, kai Ahmad ka shiga hankalin ka." Baice komai ba Abbah ya kuma cewa, "Kamar yadda nace ku taru a wannan lokacin magana ce akan k'anwar ku Mima." Damm gaban Mima ya fad'i ta d'ago ido ta kalli Mummy da Mamy suka mata alamu da ta kwantar da hankalin ta.

Abbah ya kalli Ahmad yace, "Ahmad me ka sani akan ma'aikacin ka Jamil?." Ahmad ya kalli Abbah yace, "ban san shi da wani abu mara kyau ba a dai cikin hospital."

"To ma sha Allah, muma ta b'angaren mu babu wata matsala da muka gani shiyasa na tara ku ku zama shaida."

Abbah ya d'ora da fad'in, "Jamil shine saurayin Mima na hud'u da za'a yi musu baikon auren, ku bawa y'ar uwar ku shawara ta shiga hankalin ta a wannan karon in komai yayi nisa ta dawo tace min bata son ko a aiko min shi shima yace ya fasa wallahi baza mu sake bata dama ba zamu aura mata wanda muka ga dama." Mima ta dafe k'irjin ta hawaye suka fara zubo ta ta jiyo muryar Abie yana fad'in, "Kina jin abinda ake fad'a miki ko? Wannan karan babu sake baki dama kina cewa bakya yi lokacin mu zai fara."

D'aga kai tayi alamun eh tana share hawaye Abbah ya kalli Dada yace, "Dada gobe iyayen yaron zasu zo kuma gobe za'a tsayar da ranar auren, wanne lokaci kike ganin ya kamata a saka?." Dada ta sauke numfashi tace, "To naji kuna ta wani kafa mata sharud'a shiyasa nayi shiru azo inda zanyi magana, duka wanda kuka ga bata aura ba tace bata so shima haka daman fa Allah bai rubuta mijin ta bane, shi wannan d'in shima da kuke zance in ba mijin ta bane sai hakan ta faru. Sharud'a ba naku bane addu'a itace taku ita kuma ya kamata kuyi mata."

Shiru sukayi dukkan su dan sun sani daman Dada bata tab'a ganin laifin Mima komai tayi shine dai-dai, Dada ta kuma cewa, "zancen ranar aure sanda kuka yanke dai-dai ne." Abie yace, "Shikenan to Dada zamu jira muji da kwana nawa suka zo in mun ga zamu k'ara sai mu k'ara in za'a rage a rage."

"Ba laifi" Dada ta furta kawai.

Yaya Mustapha yace, "Allah ya kaimu lokacin ya sanya alkhairi." Duk suka amsa da amin. Kallon Ahmad Abie yayi yaga ya kulle idanun sa kamar mai bacci da alama ba sauraron su yake yi ba yace, "Ahmad." D'ago ido yayi ya kalli Abie yace, "Na'am."

"Yan uwan ka maza duka sunyi aure sun barka ga k'anwar ka ma tana niyar tafiya ta barka, da Tasleem kake so mu had'a ku ne?."

Ambatar Tasleem da Abie yayi ya saka shi waige-waige a falon ya hango ta tana fitowa daga kitchen hannun ta rik'e da ruwa da wata roba k'arama me kyau tana kallon sa da murmushi, murmushi shima ya mata har hak'oran sa suka bayyana ya kalli Abie yace, "zanyi." Abinda yace kenan a tak'aice yana mayar da kallon sa ga Tasleem.

Anty Lubna tayi karaf tace, "Badan wannan Jamil d'in ba ai ni da Mima naso a had'u su auren kaga shikenan an huta anyi maganin masu ganin hanjin juna" ta fad'a tana kunshe dariya. Duff annurin fuskar sa ya d'auke ya kalli Anty Lubna bai ce komai ba dan in badan yaya take a wajan sa ba babu abinda zai hana bai make ta ba.

Dada tace, "Allah ya kiyaye me jika ta zatayi da wannan abin kamar ragowar aski? Ai tafi k'arfin sa tuni." Had'a ido sukayi ya tabe baki baice komai ba. Duka dariya sukayi banda Mima da har lokacin take hawaye.

Tasleem tace, "Yaya Dr wannan naka ne" ta fad'a tana mik'a masa robar hannun ta. Murmushi ya mata sosai ya karb'a ya bud'e ya kalli abin ciki ya kuma kalle ta sai ya rufe ya ajjiye a gefen sa.

Ganin hakan ya saka ta yin ihu da murna tace, "Na fad'a miki Yaya Mima babu abinda zai min kika ce in na bashi alale sai ya kusa kashe ni gashi bai min komai ba." Mamy tayi dariya tace, "Dan dai ke d'in ce kawai Tasleem amma waye zai gwada wannan gangancin shida ko kallon abin baya so." Anty Lubna tace, "Hajiya Tasleem ki daina murna ai a ci yayi shine zaki tsalle."

"Nan fa d'aya ai ko babar Tasleem baza ta saka shi yaci ba balle ita" Dada ta fad'a tana kallon sa.

Ga mamakin mutanen falon sai suka ga ya bud'e robar ya gutsiri alalen ya saka a baki yana taunawa ya kalli Tasleem sannan ya rufe robar ya ajjiye, mik'ewa yayi ya rik'o hannun suka fita daga falon kowa ya bisu da kallo cike da zallar mamakin sa.

Abbah yayi dariya yace, "lallai Tasleem ta cire tuta akan ta yaci abinda bai tab'a ci ba tunda yazo duniya." Mamy tace, "Gaskiya dai ya nuna mana akwai banbanci tsakanin mu da Tasleem."

Dada da ta cika da mamaki tace, "Gaskiya dai ya mana bazata, to ko dai rik'on ta yake yi?." Kowa yayi dariya a wajan Mima ta mik'e tayi ciki suka bita da kallo ganin yadda ta canja gabad'aya. Lokacin sallar i'sha ne yayi hakn ya sanya kowa ya tafi masallaci aka bar matan Mummy ta mik'e tabi bayan Mima.

A kwance ta same ta tana aikin kuka ta zauna a kusa da ita tace, "Kuka ba shine maganin damuwar ki ba Ayshatou addu'a itace maganin matsalar ki a koda yaushe, nasan kina jin tsoron abinda zai biyo baya kamar yadda yake faruwa ko wanne lokaci ko?." D'ago kai tayi cikin kuka tace, "Mummy ina jin tsoro kar wannan lokacin ma na b'atawa su Abbah rai, ki duba yadda ran su ya b'aci a wancan lokacin in aka sake maimaitawa kina jin hukuncin da yace zai d'auka a kaina. Wallahi Mummy ban tab'a samun d'aya daga cikin masu neman aure na nace suzo suce sun fasa ba hakan nan suke zuwa ni kuma sai naji kamar an zare min su daga zuciya ta, ina jin tsoro Mummy kar wannan lokacin ma hakan ta faru."

Mummy ta d'ago kanta ta d'ora a cinyar ta tace, "Kin tabbata kina son Jamil d'in?." D'aga mata kai tayi alamun eh Mummy tace, "To ki ta addu'a kina neman zab'in Allah in kinga hakan ta kasance to ki saka a ranki shima ba mijin ki bane, hukuncin da iyyen ki suka yanke kuma matuk'ar kika auri wanda suka baki to daman shine mijin ki wad'an can babu mijin ki a cikin su, ki daina kuka addu'a zaki dinga yi kinji?."

Hawaye ta share kana tace, "Lokacin Habib ban san me na masa ba yace baya sona ya fasa a lokacin auren mu sati uku ya rage, aka zo kan Nasir shima sai da biki ya rage kwanaki yace ya fasa, aka zo kan Zuhair shima sai da biki yazo yace ya fasa Mummy in hakan ta faru akan Jamil ina jin Allah bai kaddara zanyi aure ba."

Mummy ta d'ago ta tana kallon idon ta tace, "kar ki sake cewa haka Mima, kome ya faru dake Allah ya riga da ya rubuta hakan kuma dole sai ya faru domin babu Wanda ya isa ya canja kaddarar sa a duniya, k'addarar ki kenan Mima ki daure ki cinye jarabawar zaki ga sakamako mai kyau da Allah zai baki. Ki rik'e addu'a da neman zab'in Allah wata ran sai dai ki tuna kiyi dariya kawai amma fa sai kin daure. "

"Toh Mummy zanyi in sha Allah. Abinda yake d'aure min kai a lamarin dukkan su in suka tashi rabuwa dani sai sunce sabida kare ran su da rayuwar iyayen su zasu rabu dani badan san ran su ba, na kasa fahimtar matsalar daga ina take Mummy."

"Addu'a itace maganin komai."

"Zan yi Mummy."

"Ko kefa. Tashi kiyi alwala kiyi sallah kizo kici abinci" Mummy ta fad'a tana mik'ewa ta fita itama ta mik'e ta shiga band'aki zuciyar ta cike da tunani.

Share it fisabinillah👏🥰

#Wattpad @Nana Haleema