Page 6
*MUGUN NUFI*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 6*
Bayan fitar Ahmad Mamy ta kalli Mima tace, "Mima zo na baki sak'o in kin tashi daga aiki ki kai min" ta fad'a tana yin ciki Mima ta mik'e a sanyaye dan tasan fad'a zata sha.
Tana shiga falon da Mamyn ta shiga kafin ta fara magana Mamy tace, "Mima ashe shirmen ki da rashin hankalin ki ya wuce inda nake tunani?, Har kina da bakin da zaki bud'e kice wai kin kama Ahmad da wata a gaban mahaifiyar sa da mahaifin sa, yanzu koda kama sun d'in kika yi da gaske ke ba me rufawa d'an uwan ki asiri ba ce?, Amma da yake ke shashasha ce mara hankali wace bata san abinda take yi ba kin b'are baki ba kunya babu tsoron Allah kina sanar da iyayen ki wannan maganar ko kunya furta ta ma baki ji ba, Kin ban kunya wallahi kin kuma bani mamaki, ki dena ganin dani da mahaifiyar Ahmad cikin mu d'aya kamar mu d'aya, maganar mu iri d'aya yau kika fad'i abu mara dad'i a kansa sai Mummy taji babu dad'i a zuciyar ta domin uwa uwa ce. A haka za'a aurar dake kina b'arar da duk maganar da tazo bakin ki?."
Tunda ta fara fad'an Mima tayi k'asa da kanta bata ce komai ba sai da taji tayi shiru tace, "Kiyi hak'uri bazan sake ba." Mamy tace, "Kima sake mana Mima, Allah ya baki sa'a, in ya dawo daga aiki ki tabbatar kinje har d'akin sa kin bashi Hak'uri in ba haka ba wallahi sai na sab'a miki" fad'a tana shigewa bedroom.
Numfashi Mima ta sauke tana kwab'e fuska fad'an da taso ayi masa sai gashi ita ake yiwa, shi koda yaushe baya laifi sai ita, fita tayi ta tarar Mummy ta tashi sai Dada kawai ta mata sallama ta fita daga falon zuciyar ta a cushe gabad'aya haushi take ji ganin abinda ta fad'a baiyi wani tasiri ba.
Ahmad kuwa tunda ya k'arasa asibitin yayi parking ya kifa kansa a kan sitiyarin motar ya kasa koda motsawa balle ya shiga cikin asibitin, abubuwa da dama ne suke masa yawo a zuciyar sa da kwakwalwar sa. Husna itace kawai yake ganowa a idon sa lokacin da take tsakiyar maza tana shan shisha, in ya tuna hakan yana jin zuciyar sa na masa zafi har yaji idanun sa na yaji kamar wanda ya shiga hayak'i. d'ago kai yayi ya jingina da kujera yana furzar da iska daga bakin sa ya sanya hannayen sa duka ya goge fuskar sa.
Wayar sa ya zaro ya shiga call log d'in nan yayi karo da number da ta kira shi jiya ya zubawa number ido yana kallo, wani b'angaren na zuciyar sa na bashi umarnin kiran ta wani b'angaren kuma yana hana shi, har zai danna sai zuciyar sa ta aiyana masa wata kila tana can tare dani a kwance. Ajjiye wayar yayi ya kulle idanun sa yana jin ina ma yana da ikon ajjiye abinda ya shafi Husna a zuciyar sa da tuni yayi ya huta.
Har aka bud'e gaban motar aka shigo aka zauna bai sani ba sai da Omar ya tab'a shi sannan ya d'ago ya kalle shi yace, "Yaushe ka shigo?." Omar ya zuba masa ido kana yace, "Ta yaya zaka San sanda na shigo ka zauna kana ta aikin tunani kamar ba kai ba. Wai damuwar jiyan ce har yanzu?." Numfashi Ahmad ya sauke numfashi kana yace, "Baza ka gane bane."
"Daman ai bana so na gane Ahmad, kalli fuskar ka fa yadda taji sha ga idanun ka ya tasa alamun baka samu bacci ba wait!, son karuwar yarinyar kake yi ko me?." Idanun sa ya watsa masa ya lumshe idanu ya bud'e yace, "Last warning." Omar yaja tsaki yace, "Sai na fad'a wallahi ba karuwan bace ba?, ka bani amsar tambaya malam son ta kake so me?."
"In son nata nake sai me?." Omar yace, "Baka isa ba domin kuwa ba ajin ka bace inda wannan a ranka ka gaggauta ajjiye shi a gefe domin ba abu ne me yuwa ba." Tsaki Ahmad yayi baice komai ba dan sake b'ata masa rai yake yi.
"Ka ajjiye wannan damuwar kaje ka duba patients d'in da suke jiran ka." Nan ma ya sake masa banza ya kalli gaban sa kamar me tuk'i, Omar zai sake magana ya hango Husna da d'aya daga cikin masu sharar asibitin yana nuno mata motar Ahmad.
Omar ya kuma fusata yace, "Ka gani ko? Ta kuma biyo ka, Ahmad meyasa baza ka raba kanka da yarinyar nan ba zata b'ata maka suna a asibitin nan wallahi." Zaiyi magana kenan tayi knocking d'in glass d'in gefen da Ahmad yake.
Dak'yar ya iya d'ago kai ya kalle ta ita kuma bata ganin sa kasancewar glass d'in motar bak'i ne sosai, d'auke kai yayi daga kanta ya mayar da kansa ya jingina da kujerar ganin haka Omar ya sanya shi sauke glass d'in side d'in da Ahmad yake zatayi magana ya riga ta yace, "Bud'e bayan motar ki shiga" ya fad'a a fusace dan a lokacin yake son yi mata iyaka da Ahmad.
Kamar jira take ta bud'e ta shiga hawayen idanun ta suka zubo lokacin da ta kulle motar tace, "Kayi Hak'uri Dr na sab'a alqawarin dana d'aukar maka, ba laifi na bane laifin zuciya tane, ko kad'an bana son dabi'ar da nake yi ni kaina amma zuciya ta tak'i karb'ar hakan ka yafe min dan Allah."
Kuka yaci k'arfin ta babu wanda ya kula ta kafin su kuma cewa wani abu ta kuma cewa, "Wallahi tun ranar da nazo nan kace min na koma Kaduna naso komawa Sholly ce ta hana ni, na shiga d'aki naita kuka k'arshe nasha maganin da zai saka ni bacci nayi bacci. Banda gani na da kayi a wajan abincin nan wallahi bana fitowa ina kulle a d'aki ka yarda dani Dr."
"Ke ba abar yarda bace Husna sau nawa kina yi min alk'awarin kin daina bin maza?" Ya fad'a muryar sa a sanyaye yana kallon ta ta mirror. Goge ido tayi tace, "na daina tun ranar da mukayi magana ban sake ba sai jiya......" Sai kuma tayi shiru suka had'a ido ta mirror yayi murmushin takiaci tace, "Ina da wata lalura Dr da in ta tashi bana iya sarrafa kaina jiyan ma haka ta kasance a gare ni" ta fad'a tana kifa kanta a cinyar ta tana kuka sosai.
Omar da yake sauraren ta yace, "Wacce lalura ce da ta wuce son zuciyar ki?." Ta d'ago tace, "Ina fama da matsananciyar sha'awa in ta tashi bana sake gane komai sai na bayan na bada kaina ga wani, ku amince dani wallahi ji nake kamar zan bar duniya in ban kasance da namiji ba" ta fad'a kanta a k'asa haka kawai tasamu kanta da jin kunyar abinda take fad'a.
Murmushin takaici Ahmad yayi da yake kallon ta ta mirror yace, "Kunya? Daman kin san kunya?." Kasa bashi amsa tayi kanta a k'asa har lokacin hawaye na cigaba da zuba daga idanun ta.
"Kayi Hak'uri na bud'e idanu ne kawai na tsinci kaina a wannan rayuwar, bani da me bani shawara, bani dame cemin ban yi dai-dai ba sai da na sanka a rayuwa ta. Ka yafe min daga yau d'in nan zan bar garin nan koda na koma can bazan sake sauraron kowa ba."
Ahmad ya sauke numfashi yace, "A hotel d'in da kika sauka akwai wani abu naki da kika bari me mahimmaci?." Hawaye ta share tace, "Kaya nane kawai sai mota ta." Baice komai ba ya kunna motar ya juya ta ya fita daga asibitin, Omar ya kalle shi yace, "Ina zamu je?."
"Kaduna" ya bashi amsa yana kallon titi.
Da matuk'ar mamaki Omar yace, "Amma ni da kai muna da patients da yawa a ciki suna jiran mu."
Tak burkin motar yayi da k'arfi yace, "Fita!." Omar ya cize baki yace, "Muje." Ya kalle shi da jajayen idanun sa yace, "Kar ka sake min wata magana" ya fad'a yana jan motar da k'arfin tsiya.
"Shine yake saka ni aikata komai ba yin kaina bane, yace min indai na daina abinda ya saka ni sai ya kashe ni, sai ya tsine min sai ya lalata rayuwa ta, bani da yadda zanyi abinda yace shi nake yi. Ban san meyasa ba koda nace na bari da na kwana na tashi zan ji abinda yace d'in shi nake so nayi, na rasa ya zanyi" surutai take kawai ita kad'ai tana hawaye da alama ta manta a inda take sai da taji muryar Ahmad yace, "Waye shi wanda yake saka ki d'in?."
Firgita tayi ta koma jikin k'ofa ta rakub'e tana raba idanu ta kasa furta komai, yana kallon ta ta mirror sai ya share ya cigaba da tuk'in sa.
D'uf motar tayi ba abinda ake ji a ciki tafiya kawai suke kowa da abinda yake sak'awa a zuciyar sa, sun jima suna tafiya kafin su shiga garin Kaduna, cikin unguwar su ya nufa ya faka a dai-dai k'ofar gidan su a lokacin Baba yake fitowa daga gidan.
Bud'ewa sukayi duka suka fito Baba da ya lura dasu ya kalle su ya kalle ta zatayi magana yayi saurin tare numfashin ta yace, "Asma'u na kece?."
Kallon su tayi ta kalli mahaifin nata har zatayi magana taga ya k'araso wajan da sauri ya kama hannayen ta duka biyun yace, "Asma'u ashe zan kuma ganin ki cikin kwanakin nan?, ina kika shiga Asma'u na?, Me kika nema kika rasa daga gare ni kika zab'i wannan gurb'atacciyar rayuwar?" Ya fad'a yana jijjiga hannayen ta kamar zaiyi kuka.
Kallon kallon ake tsakanin Ahmad da Omar da kuma Asma'u, Husna da kalaman mahaifin ta ya daskarar da ita sabida zallar mamaki ta kasa furta komai sai kallon fuskar sa da take yi. Sakin hannun ta yayi ya kalli su Ahmad yace, "baka yi kama da irin samarin da take kulawa ba, a ina kuka samo ta?." Omar yace, "Sunana Omar wannan kuma sunan sa Ahmad Abdulsamad shugaban kungiyar da take tallafawa mata da suka saka kan su a cikin wannan sana'ar, kuma shine shugaban say no to rape foundation, ni mataimakin sa ne."
"Shiyasa nake ta tunanin inda na san fuskar sa ashe a talabijin nake gani, barkan ku da zuwa kuzo mu shiga ciki" ya fad'a yana nuna musu gate d'in gidan alamun su shiga. Ba yadda suka iya suka shiga har cikin set room d'in da yake gidan suka zauna har Husna. Da kansa ya kawo musu ruwa da lemo ya ajjiye musu ya zauna yana fad'in, "Sannun ku, nagode da kuka dawowa min da Asma'u gida."
Ahmad ya kalli Husna zaiyi magana Baba ya tare shi yace, "Ba sai kace komai ba Ahmad, ina rok'on ka dan Allah ka sanya Asma'u a cikin wanda zaku tallafi rayuwar ta ta inganta, bamu rasa ci da sha da suttura ba ku duba gidan da aka haife ta amma na rasa me Husna take nema har ta kai kanta ga halaka. Mahaifiyar ta ta rasu tun tana k'arama na kula da tarbiyar ta dai-dai gwargwado duk da ba kamar uwa ba. Na saka ta a makarantar boko da ta islamiyya ban sani ba ko a can k'awayen banzan suke wanda suke hure mata kunne wallahi tana fara girma in ta shirya da niyar ta tafi makaranta ashe ba nan take zuwa ba, nayi dukan nayi horon amma a banza" yayi shiru ya goge hawayen idanun sa ya cigaba da fad'in,
"Ita kad'ai Allah ya mallaka min a duniya amma Asma'u ita take k'ok'arin zama ajali na a duniyar nan, dangin maman ta gabad'aya ta raina su bata jin maganar kowa balle taje inda suke su kuma laifi na suke gani suna ganin kamar ni ne nake zuga ta nake d'ora ta akan turbar banza. Ta yaya za'ayi na haife ta na kuma saka ta yawon duniya? Dan Allah hankali zai d'auki wannan?" Ya fad'a yana kallon su.
Tare suka girgiza kai alamun a'a ya cigaba da fad'in, "Ina rok'on ku da ku taimaka mata ta dawo turba mai kyau kodan ta gana Allah lafiya in ta bar duniya, tunda har ta yarda ta biyo ku kuna da tasiri a wajan ta dan Allah kuyi amfani da wannan tasirin ku taimaka min a daina zagi na a unguwa ana ganin kamar laifi nane" ya fad'a cikin kuka sosai.
Jikin su yayi mugun sanyi kwarin guiwar taimakawa Husnan ya shiga jikin su dukkan su Ahmad ya tausasa murya yace, "Ka daina kuka Baba in sha Allah zamuyi iya bakin k'ok'arin mu wajan ganin ta bar turbar da ta d'auka amma kaima muna buk'atar taimakon ka." Ya goge idanun sa yace, "Ko meye kuce zanyi."
"Saka idon da kake mata ina so a ninka shi sannan a raba ta da duk wata kawa ko aboki da suke zuwa inda take. Muna da islamiyya da muka bud'e wacce muke saka irin su muna da branch a nan Kaduna kuma a nan bayan ku take babu nisa zanje yanzu nayi mata register gobe in Allah ya kaimu zata fara zuwa in sha Allah komai yazo k'arshe. Amma Baba ka cigaba da mata addu'a ita take buk'ata itace sinadarin da zata shiryar da ita."
Baba yace, "Addu'a muna yi Ahmad duk sati sai an sauke alqur'ani akan hakan, akwai rubutu ma daka aiko dasu dan bata nan ne ban bata tasha ba amma yanzu tunda gata yanzu zata fara sha." Ahmad yace, "Da taimakon Allah komai yazo k'arshe tunda itama tana son barin abun a zuciyar ta itama."
Sak Baba yayi kafin yace, "Da gaske tana so ta bari ita da kanta?." Ahmad ya kuma cewa, "Eh Baba da kanta tazo har office d'in mu na wannan foundation d'in tace min tana so ta bar harkar amma tana jin tsoro, na tambaye ta tsoron me take ji ta kasa bani amsa sai taita kuka, dalilin hakan ya saka na fahimci a akwai kamar blackmailing cikin lamarin ta."
Baba ya kalle ta yace, "Tsoron me kike ji Asma'u? Waye yake tilasta ki?, fad'i waye yake saka ki har kike jin tsoro?." Kallon sa kawai take bakin ta ya kulle ta rasa abinda zata ce sabida mamaki da al'ajabi, gaban ta kuwa sai fad'uwa yake tsoro na sake dabaibaiye ta.
Ganin hakan ya saka Ahmad yace, "Ko ma waye zamuyi maganin sa da rok'on Allah. Yanzu da mun bar nan islamiyyar zamu wuce zan mata register zan dawo na kawo mata komai tunda akwai niya a zuciyar ta Allah zai bamu sa'a."
"Nagode Ahmad, nagode muku Allah ya yiwa rayuwar ku albarka ya inganta ya kuma tsare ku daga sharrin mak'iya."
Murmushi sukayi dukkan su suka amsa da amin kafin Omar yace, "Babu komai an riga da an zama d'aya da izinin Allah komai zai wuce." Murmushi Baba yayi yace, "Da kun cika min buri na wanda zan iya cewa shine na k'arshe a duniya." Ahmad ya murmusa yace, "In sha Allah zai cika. Zamuyi sallah kafin mu wuce."
"To ga band'aki nan, Asma'u shiga ciki ki karb'o musu abinci" ya fad'a yana kallon ta. Ahmad yyi saurin cewa, "A'a Baba mun gode sauri muke." Omar ya kalle shi kawai dan shi har ga Allah yunwa yake ji.
Ciki Husna ta shiga jiki a sanyaye sukayi alwala sukayi sallah suka yi masa sallama da niyar zasu je su dawo, har bakin mota ya raka su yana godiya sai da ya daina ganin motar su a layin sannan ya sauke numfashi fuskar da ya aro ya saka ta yaye daga fuskar sa ya juya ya shiga cikin gidan.
Da k'atuwar dorina ya shiga falon ya kalli matar sa fuska a d'aure yace, "Ina Husna?." Da mamaki take kallon sa tace, "Ta shiga d'akin ta, wannan bulalar fa?." Bai jira yaji me zata ce ba ya bar mata wajan ya shiga d'akin Husna ya mayar da k'ofa ya kulle.
A zaune take a gefen gado tana kuka tana ganin sa ta zabura ta mik'e jikin ta na mugun rawa tana ja baya yana biyo ta, "Har kina da k'afar da zaki je neman taimako?, har kina da bakin da zaki ce zaki bar abinda nake so kiyi ko?, yaushe kika fara sab'a abinda nake fad'a miki eyeee?" Ya fad'a da muguwar tsawa yana zaula mata bulalar a gadon baya. Ihu tayi ta canja waje tana sosa bayan ta tana kuka tace, "Har ciki raina ina so na daina Baba, shekara sama da biyar ina abu d'aya shiyasa naje neman taimako ko taimakon su zai saka ka janye tsinuwar ka a kaina."
Husna! Wallahi kika daina abinda kike yi sai na yi gunduwa-gunduwa da naman ki, Husna wallahi sai na tsine miki kin shiga duniya, sai nayi miki addu'ar da Allah zai cilla ki a wuta ya k'ona ki" ya fad'a da kakkausar murya yana kallon ta.
Zatayi magana ya fara dukan ta ta ko ina ta ihu yana sake k'ara mata, sai da yayi mata sama da goma sannan ya k'yale ta ya kalle ta yace, "zasu kawo miki uniform yanzu ki karb'a kar kuma ki nuna musu na dake ki, ki amsa musu zaki je makarantar ki nuna musu kina son zuwa wallahi kika yi akasin haka sai na lahira ya fiki jin dad'i" yana gama fad'ar hakan ya fita a fusace.
Yana fita Anty ta shigo ta rungume Husna da take ta kuka fatar jikin ta duk ta tashi taji ja sabida duka, kuka Antyn take itama tana bubbuga bayan Husnan. "Na gaji Anty wallahi na gaji, ki taimaka min kinji Anty, in kin ga Baba yana rarrashi na yana min magana mai dad'i sai in nace zan fita daga gidan nan ne, amma da zarar na dawo sai fad'a yace na koma inda na fito, wallahi na gaji." ta fad'a tana sake fashewa da kuka.
"Addu'a Husna ita zaki dinga yi, ina so ki sani kuma abinda mahaifin ki yake sanya ki ba dai-dai bane sab'on Allah ne, Allah ya haramta ya kuma ce kada mu kusance shi, Husna kika mutu yanzu baki tuba ba kina cikin tashin hankali, gashi ko sallah baki iya ba Husna baki a banbanci da karifi tunda sallah itace take banbance tsakanin musulmi da kafiri. Husna ki shiga islamiyya zaki gane duk abinda kike aikatawa babban laifi ne, kuma....." kafin ta k'arasa ta jiyo amon maganar sa yace, "ki tattara inaki inaki ki bar min gida na sake ki saki uku!."
Abinda ya sanya su firgita dukkan su suka kalli inda yake tsaye a gigice.
_Tabbas akwai Lauje cikin nad'i._⛹♀️⛹♀️
Share it Fisabinillah👏🥰