DAHLIAS: HAUSA NOVEL

3

by @noorulhuda

“Amma kana ganin zaka kula da business ɗin yadda ya kamata daga nan? Ka tabbata kana da full control a kan companyn sannan komai zai tafi bisa tsarinka dukda baka nan?”


Engr ya ajiye tumblern ruwan daya gama sha bisa table sannan ya dubi Baba Sada.


“Eh Yaya Insha Allah. I trust my teams, za suyi komai yadda ya kamata. Sannan anyi test-running Control Software ɗin last month a Redmond bayan munyi designing, it is quite good. Bill Gates ma yayi commending sannan companies da yawa sunata showing interest. I believe zata taimaka wurin monitoring komai na companyn. Kuma zan rinƙa zuwa Insha Allah, a ƙalla once in a week. Nayi tsare tsare da yawa, everything will run smoothly as planned bi iznillah.”


“To Alhamdulillah, don har na fara tunanin Ahmad ya dawo ya tayaka running. But tunda kace tsarin yana da kyau matuƙa shi kenan. Allah Ya sanya mana albarka Ya dafa mana.”


Su duka suka haɗa baki wurin amsa addu'ar. Yanzu su biyar ne kaɗai a parlourn, sai kuma Hajiya Fatima data bada himma tana kallon labaran rana da ake watsawa a tashar Channels. Matansu na parlourn Mum suna tasu hirar abun sha'awa. Wannan rashin jituwar da akan samu tsakanin faccaloli, sam basu santa ba. Kan mazajensu a haɗe yake, to akan me zasu rarraba nasu? Yaransu kuma sun bazu a gidan suna bajakolin wasanni. Ƴan ƙananan na parlourn yara suna kallo, wasu suna waje suna wasa da keke da sauran kayan wasanni, wasu kuma suna tare dasu Mus'ab suna buga games.


“Ahmad...Ahmad ko ba dan ya tayani running business ba ya kamata ya dawo gida haka. Shekaru biyu kenan fa yana aiki da South Korea. Da yace min aikin yarjejeniya zaiyi dasu na wata uku to daga baya yayi renewing contract ɗin ya ƙara wasu wata ukun. Haka fa yayita renewing har aka ci shekaru biyu. Shi kenan kuma a haka za'a ƙare? Ya kamata ya dawo yayi aure yayi settling haka. Ko ya kuka ce?” Dad ya tambayesu. Tun tuni yaso su tattauna wannan maganar amma basu samu haɗuwa ba sai yau.


Yanzu Hajiya Fatima ta tsoma baki cikin hirar tasu

“Ai ni dama tsayawa nayi naga iya gudun ruwanka dan kar in saka baki ku da jikokina ku tsane ni. Yo ai duk ku kuka janyo da kuke harba ƴaƴanku ƙasashen waje. Duk yawan jami'oin da muke dasu basu ishekuba sai kun kaisu ta masu fararen kunnuwa. Kune Harvard, kune Oxford, kune Cambridge yo ba dole a rinƙa riƙesu ba. Anga ƙwaƙwalwa da hazaƙa, ai dole a hanasu dawowa.”


Amma yanzu magana suke a inda ya samu aiki, ba inda yayi karatu ba. Sai kawai sukayi shiru dukansu. Idan tana irin wannan faɗan, ba'a ce mata uffan, don ko ka faɗa ba tasiri yake a kanta ba.


“Yanzu ai sai ku tilasta masa ya ajiye aikin kuma lallai ya dawo cikin wannan watan. Ku saka musu rana, shi da Husna, yana dawowa sai aure kawai. Sannan ka damƙa ragamar companyn naka a hannunshi, ya tayaka kasuwancin na ɗan wani lokaci.”


Duk sunyi na'am da umarnin mahaifiyarsu. Uncle Bello da yaso yayi magana abar Ahmad yayi aikinshi har sai lokacin daya ajiye a karan kanshi. A ganinshi, gwara kawai a aura mishi Husnan sai ta bishi South Korea, suje can su cigaba da rayuwarsu. Kowa ya sani suna ƙaunar junansu, sannan ko da ta kama za ayi biki, zasu iya yin abinsu babu angon, dukansu TURAKI ne, tuwona maina. To amma ance abinda babba ya hango, yaro ko ya hau rimi ba zai gano ba. Sannan ba wannan ne karo na farko da Hajiyar take zartar da hukunci a al'amuransu ba, kuma basu taɓa ganin ba daidai ba matuƙar dai umarninta suka bi. Shi yasa kawai ya haɗiye maganar bai furta ba.

Nan take aka saka ranar bikin. Nan da watanni biyu masu zuwa. Daga haka aka rufe babin matsalar aka shiga wata. Sun cigaba da hirarrakinsu da tattauna matsalolinsu har sai da aka kira sallar la'asar. Bayan sunyi sallah sai suka haɗu akayi addu'ar neman alkhairi da tsari daga dukkanin sharri a sabon gidan nasu da suka tare. Daga haka kuma suka fara haramar tafiya. Engr bai so ba, yaso sai sunyi maghriba sai su tafi to amma ba yadda ya iya, Hajiya bata son tafiyar dare, kuma a ganinta dukda a jirgi sukayi tafiyar ya kamata a barsu su huta da kyau. Daga Jalingo zuwa Abuja sannan a taho Kano, ba tafiyar wasan yara bace.


Mum tayi musu packaging ragowar abincin ranar da aka dafa, musamman snacks da fruits. Har gate suka raka su, suna tsaye motocinsu suka fice ɗaya bayan ɗaya.Washegari lahadi a gida suka wuni. Dad ma ba inda yaje.


Ranar Monday aka saka Zuhra a primary school, St. Lious. Safwan da Mus'ab kuma St. Thomas aka saka su. Cikin watanni uku shirye shiryen da Dad ya fara na buɗe branch a Kano ya kammala. Company ya samu karɓuwa yadda ya kamata, Alhamdulillah. Kayan da aka sarrafa a Kano, su ake aikawa jihohin arewa sannan a fitar Nijar da Chad. Waɗanda kuma aka sarrafa a Jalingo, su ake fitarwa Cameroun, sannan a turasu Lagos daga nan a fitar ƙasashen waje.


Tick tock! Tick tock! A hankali hannun agogo ke motsawa, sakanni suna komawa mintuna, su kuma mintuna idan suka cika sittin sai su bada awa, awanni ashirin da huɗu kuma sune kwana. Komai na cigaba da tafiya cikin Ƙudirar Ubangiji, babu abinda ya tsaya. Kullum rana zata fito daga gabas ta kuma faɗi a yamma. Ruwan River Niger na cigaba da gudana. Kwanaki na ƙaruwa su bada watanni. Watanni na canjawa su zama shekara. Shekara kuma ta rikiɗe ta zama shekaru dake naɗe al'amura da yawa cikin kundin tarihi kamar dawowar Ahmad Turaki Nigeria da kuma aurenshi da Husna Turaki, kammaluwar karatun Mahmoud Turaki a Jami'ar Harvard, buɗe companyn TURAKI HOLDINGS, tafiyar Mus'ab da Safwan Turaki Jami'ar Harvard, kammaluwar karatun Zuhra Turaki na secondary da kuma shigarta Jami'ar Bayero, fitowar result ɗin exams ɗinta na first semester da kuma zuwan da tayi yau ta duba result ɗin.


★★★★★★★★

Malam Idi na yin parking ta fita daga motar. A parlour taci karo da Mum zaune kan ɗaya daga kujerun parlourn cikin shiga ta alfarma. Wayarta na kare a kunnenta na hagu tana amsa kira.


“Mum na dawo” Zuhra ta faɗa a hankali tana zama a gefen Mum.


Dr Nafisa ta ajiye wayar a kan hannun kujerar bayan ta katse kiran


“Sannu Zuhra. How far? Ya result ɗin?” Ta tambayeta yayinda ƙwayar idanunta ke yawatawa a kan fuskar ƴar tata, ƴarta ɗaya tilo.


“Alhamdulillah” Ta ɗanyi shiru tana haɗe siraran yatsunta tana lanƙwasawa. “5.0 points naci.”


“Ohhhh Masha Allah! Alhamdulillah! That's my girl!” Sai ta matsa kusa da ita ta rungumeta tana shafa kanta. “You've made me proud Zuhra, Allah Ya miki albarka.”


“Amin Mum...Thank you.”


“But me yake damunki ne? What's wrong naga duk kin yi wani iri?” Ɗagota tayi daga jikinta tana sake bin fuskarta da ido.


“Nothing wrong Mum, kawai kaina na ɗan ciwo ne amma I'll be okay Insha Allah. Bari naje na shirya.” Sai ta fara ƙoƙarin miƙewa.


“A'a Zuhra, anya zaki iya fita a haka? Kiyi zamanki kawai ki huta. Sai na dawo.”


“Aa ba komai Mum, zan iya zuwa. I'll be much better...please Mum yanzu zan shirya.”


Da ɗan gudu tayi hanyar matattakalar benen. Tun sanda aka kai lefe kusan kullum sai Mum tayi mata hirar bikin. Bikin ƴar aminiyarsu ce, Hajiya Bilkisu. Duka ankon ƙawayen amarya da suka fitar saida Mum tayi mata, a cewarta koda amaryar bata santa ba, koda amaryar ba ƙawarta bace to ya dace ta shiga cikinsu ayi bikin da ita albarkacin amincin dake tsakaninsu iyaye. Ko yau kafin ta fita dubo result, sai da ta tuna mata kamun da za ayi. Bata kyautawa Mum ba idan taƙi zuwa bikin saboda wata damuwarta da bata san yadda akayi tayi mata katutu a ƙoƙon rai ba, sannan bata san rana ko lokacin da zata kau ba.


Cikin minti biyar ta shirya cikin ankon da ƴan mata zasu saka. Atamfa ce blue black da akayi mata zane da jajayen flowers. Doguwar riga akayi mata irin mai buɗewa daga ƙasan nan. Ɗaurin ɗankwali tayi simple, ta shafa powder ta goga wet lips sannan ta yafa madaidaicin mayafin daya dace da kayan. Safwan ne ya tuƙa su zuwa The Afficent, inda za'a yi bikin. A gefen titi yayi parking, suka fita daga motar suka shiga ciki shi kuma yayi reverse ya juya ya tafi gidansu abokinshi dake Sultan Road ɗin. Amininshi ne, tare suke karatu a Harvard.


Filin The Afficent da aka tsara aka kuma ƙawata shi da kayan adon zamani cike yake da mutane. Su ba suyi abin nan da ake kira african time ba, da zaka ga an saka biki ƙarfe biyu a kati amma sai ƙarfe huɗu tayi ko tsare tsare da decorations ɗin gurin ba'a gama ba. Speakers ɗin dake kowacce kusurwa a filin na fitar da kiɗa cikin sauti mai taushi. MC na riƙe da mic tana ɗebewa mutane kewa don kar a gaji da jiran amarya tunda lokacin bata ƙaraso ba. Can wani table Dr Nafisa ta hangi Hajiya Mariya tare da ragowar aminan nasu. Table ɗin nasu ta nufa, taja kujera ɗaya ta zauna bayan sun gaisa sannan suka cigaba da hira.


Zuhra Turaki bata bi Mum ba. Gefen data hangi ƴan mata sa'anninta masu kalar ankonta ta nufa tayi musu sallama tare da sassanyen murmushi sannan taja kujera itama ta zauna. Ba tafi minti talatin da zama ba muryar MC ta karaɗe ko ina na filin.


“Amarya ta ƙaraso! Ƴan matan amarya aje a shigo mana da ita. Oya! Oya! Bridesmaids amarya fa na jira.”


Ƙasa Zuhra tayi da kanta tana cigaba da latsa wayarta. Bata so ta haɗa ido da Mum balle ta aiko mata da irin wannan kallon da zai miƙar da ƙafafunta tsaye ya kuma turata cikin jerin ragowar ƴan matan daketa miƙewa suna fita domin shigo da amarya.


“Sai kije biki ki zauna shiru ba uhm ba a'a. Duk kusancinki da amarya bazaki shigo da ita filin biki ba. Ƴar takawar nan da amare keyi da freinds ɗinsu idan aka kira ba kya zuwa. Koda yake idan da na biye ta taki bikin ƙawayen naki ma ba zuwa zaki yi ba. To wallahi tun wuri gwara ki gyara. Haka kika ga Jidda nayi a biki? Idan fa ba kya shiga cikin bikin mutane ana yi dake babu wanda zai shigo ayi naki dashi wallahi.” Zuhra ta tuna faɗan da Mum tayi mata a bikin Fatima, best friend ɗinta a secondary school. Tun daga lokacin duk sanda suka je biki sai tayi mata wannan faɗan. Yanzu ma data ƙi yarda ta ko kalli sashin da Mum ɗin take, ta san faɗan take ɗumamawa da tiririn zuciyarta tana kuma tunanin yadda zata wullo mata shi ya daki goshinta cikin sauƙi ba tare da ya huce ba😂


Tana ji DJ ya saka waƙa mai taushi, irin waƙoƙin da ake sakawa domin shigo da amare. Ƴan matan amarya sun jeru a layi biyu, sun saka amaryar a tsakiya. Taku sukeyi cikin nutsuwa da gayu mai birgewa. Ta san Mum na can daga seat ɗinta tana tunanin ina ma tana cikinsu! Ina ma ita ce a sahun farko! Ina ma...Ina ma...Ta san yau tun a mota Mum zata maimaita wannan faɗan nata. Wata ƙila ma ta ranƙwasheta ko ta murɗe mata kunne kafin su isa gida. Faɗan Mum akwai shi da cin rai. Ranƙwashinta da zafi. Idan ta murɗe maka kunne sai kaji kamar ka saki fitsari saboda azaba. Zuhra Turaki ta san waɗannan duka amma kuma basu ne a gabanta ba, ta yadda zata haɗu da Umar Faruk kawai take. Ta san ba abu ne mai sauƙi ba, kuma ba lallai ya yiwu ba. Abu ne da take buri.


“Result ɗinka baiyi kyau sosai ba. Ka faɗa min matsalarka, I'll be glad to help.” Haka take so ta faɗa mishi. Yana fashi sosai. Zata iya ƙirga sau nawa ta taɓa ganinshi a lectures. Amma duk lecture da yaje yana miƙa hankalinshi ne gaba ɗaya ga lecturer. Yana yin note ko yayi jotting. Babu alamar daƙiƙanci a tare dashi. Bata san tushen matsalar ba, amma koma mece ce bata damu ba,so take ta taimaka mishi.


“Taimakonshi kike so kiyi? Ko dai kusanci kike so ki samu dashi? Ko kuma so kike ki shiga rayuwarshi?” Wata murya tayi amsa kuwwa cikin ƙwaƙwalwarta tana tambayarta. Maƙogaronta taji ya bushe, yawunta ya ƙafe, sai kawai ta janyo Faro ɗin da aka ajiye tare da drinks a gaban kowane seat ta buɗe ta fara sha. Da gaske ya kamata ta nemi amsar wannan tambayar.


An cigaba da gudanar da biki. Ango yazo da tawagar shi bayan an kama amarya. Ƙawayen amarya ne suka sake fita suka shigo dasu bayan amaryar ta canja kaya da kwalliya. Zuhra Turaki ta fita? Aa! Tana zaune a seat ɗinta tana faman saƙawa da warewa. Ƙwaƙwalwarta tayi nisa gurin neman amsar nan. Bata ko kalli abincin da caterers suka raba ba. Haka yayi ta zama har suka sake dawowa suka kwashe abinsu. Maghriba ta gabato, duhun dare ya fara mamaye hasken ranar daya daɗe da disashewa amma Zuhra bata samu ko birbiɗin amsar ba. Kiran Safwan daya shigo wayarta ne ya katse mata tunaninta


“Hello” Tace dashi bayan ta ɗaga wayar


“Mum ta kira ki not reachable. Tace ba yanzu za'a tafi ba akwai abinda za tayi. So ko dai ki fito ki jirata a mota yanzu ko kuma ki karɓo min kati na shigo dan bazan zauna ni kaɗai a nan ba kamar maye.”


Ƴar dariya ce ta suɓuce mata sannan ta mike daga seat ɗin “Bari na fito yanzu dama zaman ya ishe ni.” Tana katse wayar ta nufi hanyar fita. Sai yanzu kuma yadda zasu kwashe da Mum yau ya dameta. Tana zuwa motar zata roƙi Safwan ya bawa Mum haƙuri ko kuma ya ɗauke hankalinta da wata hirar ta yadda zata manta laifin data matan. Bata lura ba sai kawai ji tayi bam! Tayi karo da wani a ƙofa, Ita zata fita shi kuma ya sako kai zai shiga. Mukulli da wayar hannunshi suka bada wani irin sauti lokacin da suka daki ƙananan duwatsun (gravels) da aka baza a ƙasan gurin. Tsugunawa tayi ta ɗakko su sannan ta miƙa mishi bayan ta duba taga babu abinda ya samesu. Yana daskare ƙiƙam kamar wanda yayi suman tsaye, ya saki baki da hanci y ido duka yana ƙare mata kallo.


“Sorry ban lura ba. Ga shi.” Shiru bai amsa ba.


“Ga shi. Sorry ban lura bane.” Ta sake maimaitawa cikin sanyinta. Sai sannan ya farfaɗo. Ya miƙa hannu ya karɓa yana sosa ƙeya ita kuma ta gifta shi ta fice daga gurin. Ya bita ya karɓi number wayarta ko kuma address ɗinta ya kamata ya tambaya?


★★★★


Assalamu alaikum readers❤️ ya kuke ya gida da kowa kowa🤗I am very sorry bana baku updates a kai kai...I am very busy ne wallah😭amma zan ƙoƙarta Insha Allah. Thank you very much❤️❤️

Masu voting da sharing ina godiya sosai da sosai❤️Allah Ya bar ƙauna.


#ZuhraTuraki

#UmarFaruk


©Noorul Huda