Duk kyan Namiji

Chapter 5

by @azizat

*DUK KYAN NAMIJI*

............. ....👳.... ..............

Please follow me on

Wattpad: Azizat_Hamza

Arewabooks: Azizat Hamza

Free book

0️⃣0️⃣5️⃣

Hudu sai da ya yi wata huɗu a Portharcort kafin ya zo gida. Ranar da ya zo gidan su Nafy da murnar shi ya zo rabon da ya ga gimbiyar sa wata huɗu ta gota. Yadda yai missing ɗin ta ita kwata-kwata ta manta da batunshi ma abu ɗaya ke tuna ma ta shi. Dama tun yana Bauchi duk wata ya na tura mata katin dubu biyu na subscription hakanan ko da ya tafi bai fasa ba. A ɓangarenshi ya na ƙoƙarin kiranta amma ba ta taɓa kiran shi ba hakanan ba koda yaushe ta ke ɗaukan kiran sa ba.

Ya na zaune amma hankalin sa na kan hanyar fitowar ta, ya san ta saba jimawa amma yau saboda ɗokin ganinta ko wanni minti gani ya ke kamar awa ɗaya. Da tsakar dare su ka sauka a garin Jos jiya anan ya kwana sai da safe ya hau mota ya taho Bauchi. Tun tasowar sa ya kira ta ba ta ɗauka ba ya tura ma ta text akan zai zo da yamma, bai ga reply ɗin ta ba amma still ya ma ta uzuri may be tana school tunda yau Alhamis.

Ya san Nafisa ta na da kyakykyawace, haka nan ta fito daga gidan arziƙi amma Allah ne shaidar sa tsakani da Allah ya ke son ta. Tun ranar da ya fara ganinta a shagon abokinsa ya ji ta kwanta ma sa, yana son ta sosai. Abokansa sun sha discouraging ɗin sa akan Nafisa, wai ɓata lokaci ya ke yi ba zai iya auren Nafisa ba. Ya kan ba su amsa da cewa nifa *Namiji ne* ina da lafiya ina da sana'a sannan dai-dai gwargwado na yi karatu to mi ye za a ce wai wata mace tafi ƙarfin in neme ta.

Lokacin da Nafy ta fito gaba ɗaya ɗaure fiska ta yi tamau kamar me shirin dambe. Ce ma sa ta yi bacci ta ke ji, a gajiye ta ke dan ba ta jima da dawowa daga lectures ba. Duk wani murnan sa sai ya koma ciki saboda yadda ta ke ma sa magana ma kamar dole. Da ƙyar su ka yi hiran minti sha biyar ta ma sa sallama ta tafi wai kan ta na ciwo. Ya jima zaune a wajen ya na tunani kafin daga bisani ya tashi. Wajen machine ɗin sa ya nufa ya ɗauka tsarabar doya da manja da ya kawo ma ta, ya miƙawa Mai gadi akan ya shiga mu su da shi.

Mama ke girki a kitchen Lokacin da Ladidi ta shigo da buhu da kuma jarkar turkey wanda cike ya ke da manja.

"Mama Hudun Nafisa ne ya aiko da tsarabar patakol"

Kafin Mama ta amsa muryan Hajiya ya doki kunnen su " kul Ladidi, kar ki ƙara haɗa Nafisa da Hudu kin ji ko"

Ladidi ta amsa da to. Hajiya ta fara kunce buhun ta na faɗin "idan ba kinibibi irin na yaron nan ba ina shi ina Nafisa"

Doya ne manya guda takwas acikin buhun, da ka gansu ka san za su yi daɗin daka sakwara.

"Ko ance ma sa nan gidan yunwa ne oho"

Mama aikin ta ta ke yi ba ta ma nuna alamar ta ji abinda Hajiyar ke faɗi ba balle ta tanka ma ta. Ladidi kuwa kallon mamaki ta ke wa Hajiya.

Sai da ta yi hanyar ƙofa sannan ta ce "Ladidi ki yanka doyan nan kaɗan ki soya min da ƙwai yanzu ina jiran ki". 

Ladidi ta amsa da toh yayinda Mama ta yi murmushi har sai da haƙoranta su ka fito.

Sai da ta fita sannan Ladidi ta yi dariyar da ta ke gimtsewa tuntuni...

Har ya isa gida zuciyar sa a sanyaye ta ke, bai taɓa ganin Nafisa haka ba, ko farkon zuwan shi wajen ta ba ta haɗa rai kamar na yau ba. Ya na tuno dariyar ta lokacin da ya ce ma ta shi Carpenter ne, har tsokanar sa ta yi wai idan ta tashi aure ba an sai ma ta gado da kujeru ba shi zai buga ma ta.

Yau kam ya karaya da al'amarin Nafisa, tun kafin ya tafi ya fara ganin changes a wajen ta amma hakan bai girgiza shi ba. Sai dai yau kam ya karaya.

Har ya shigo gidan hankalin sa ba a jikin sa ya ke ba.

"Abba lafiya?" Umma da ke jan ruwa a gindin rijiya ta tambaya.

Ya ƙaƙaro murmushi ya ce " ba komai"

"Ban gane ba komai ba, shigowa fa ka yi ba ko sallama"

" tunanin zuci ne sai ya min kaman na yi sallamar. Barin shiga ɗaki kaina ke ciwo"

Bin shi ta yi da kallo har ya shige ɗakin sa. Ta san akwai matsala dan hankali kwance ya fita a gidan.

Hudu ya sa a ransa idan Nafy ba ta kira shi ba, ba zai kira ta ba.

........................................

Haɗuwar saurayi da budurwa ya na zuwa ta kowanni yanayi. Wasu a biki za su haɗu, wasu a Makaranta, wasu a motar haya ko keke, wasu a waya ko social media duk dai.

Hakance ta faru domin kuwa a ranan da Hudu ya zo Nafy ta haɗu da Saurayin da ta kira da Jasim ɗin ta.

Fitowar su daga lectures su ka tsaya maganar wani group assignment da aka ba su. Walida Inuwa 'yar ajin su ce yadda ta ke ji da kan ta haka Nafy ke ji da kan ta. Shi ya sa ma basa shiri, Ita Nafy na ji da kyaunta yayinda Walida ke ji da kuɗi. Mahaifin Walida ɗan siyasa ne, ya riƙe muƙamin minister hakanan ya yi takarar senator amma bai ci ba. Har mota Walida ke da shi hakan ya ƙara sa ma ta ɗagun kai. Idan ba maganar yadda za su yi assignment da su ke yi ba, ba abin da ke haɗa Nafy da Walida banda kallo.

Su na cikin magana Walida ta ɗau waya. Kwatance ta yiwa mai kiran na inda su ke sannan ta katse kiran.

Hafiz ya ce yanzu dai inaga kowa zai haɗa ɗari uku-uku saboda a samu a haɗa komai cikin lokaci kafin ranar da za mu yi defence.

Nafy ta fara lalumar jakarta dan ta biya na ta kuɗin tun a lokacin. Dubu biyu Walida ta fito da shi a purse ɗin ta ta miƙawa Hafiz. "Ga shi ka kawomin copy na idan ka gama" ya san mi hakan ya ke nufi dan ba yau ta saba biyawa mutane kuɗin abu ba idan hidimar aji ta haɗa ta da mutane.

"Ranki shi daɗe an gode"

Ta juya ta bar wajen.

Nafy ta bita da harara ta na faɗin "sai shegen girman kai"

Magana su ke da Zuby wanda ke mitar an haɗa ta group ɗin unserious wata mota ta yi parking ɗan nesa da su. "Hasbunallahu wa ni'imal Wakil" Nafy ta faɗi lokacin da kyakyawan saurayin ya fito daga mota ya nufo su. Nafy shagala ta yi da kallon saurayin. Gaskiya ba ƙaramin tafiya yai da ita ba. Ta na son farin namiji kamar yadda ta ke farar mace. Ga shi wannan ya haɗa duk abubuwan da ta ke so, ga tsayi, dogon hanci, uwa uba baƙin gashi mai salƙi mai yalwa. Shegen larabawa ya ke ko kuma idan ta rage zumuɗin ta kirashi bafulatanin usul.

Wajen su ya ke nufowa kafin ya ƙara wayar sa a kunne wanda maganar da ya yi ya sa ya chanja hanya. Nafy ta bi shi da ido taga inda zai yi sai ta ga wajen Walida ya nufa. Ta haɗiye yawu moƙot.

Zuby ta ɗan tsikareta "Nafy lafiyar ki kuwa, wannan kallon da ki ke ma sa ai sai kisa ya kife"

"Zuby Jasim ne, wallahi Jasim ne"

Zuby da maganar ta bata haushi ta ce "Allah ya shirye ki"

Duk ajinta duk yadda ta ke ƙin Walida amma yau kam ta ajiye komai. Ta na ganin Walida da saurayin sun yi hanyar wajen motar ta yi saurin cewa Zuby ina zuwa.

Da sauri ta cimmusu lokacin Walida na shirin buɗe ƙofa.

"Walida ki tsaya dan Allah"

Walida ta juyo a darare " ya akayi?"

Nafy ta sauke ajiyar zuciya ganin shima saurayin ya tsaya bai shiga Motar ba wanda kallon ta ya ke yi.

"Na ce kinga mu ne group 1 ya kamata ace kafin ranar defence mu ɗan yi practice kar mu zo a samu matsala"

Walida ta ce " hala kin manta group 3 fa mu ke"

Nafy ta wayance ta ce " still Walida, ina tsoron kar ayi irin ta last presentation na mu, ba mu shirya ba, aka zo presentation mu ka fara inda-inda"

"Ok ba matsala" ta faɗi a taƙaice.

Ganin ba ta samu abin da ta ke so ba ya sa ta yi saurin cewa " ranka shi daɗe ina wuni"

Ya amsa fiska a sake " lafiya sister"

A take a wajen ta dropping duk wani pride na ta ta ce " dan Allah idan ba matsala ko za ka sauke mu a bakin gate ni da ƙawata" ta yi maganar ta na nuna Zuby.

"Ba matsala ku shigo"

Kar ma ta matsa daga wajen Walida ta hanashi ɗaukan su ya sa ta yi saurin ƙwalawa Zuby kira. Zuby dai tun tafiyar Nafy ta ke kallon su zuciyar ta cike da mamakin Nafy. Da ta ƙaraso Nafy ta mata alamar su shiga. Zuby na shirin musu Nafy ta galla ma ta harara.

Sai da su ka fito bakin gate ya tambayesu wani anguwa za su je. "Fadamar mada" Nafy ta faɗa da sauri a Lokacin da Zuby ke shirin cewa ya barsu a nan za su hau keke.

Walida ma da ta haɗe rai tuntuni ta ce " Ya Suhail, ka barsu anan za su hau keke ai"

Jin sunan *Suhail* da Nafy ta yi saura kaɗan ta fasa ihu saboda daɗi.

"Oh ashe dama haka ki ke yi idan kin zo da taki motar ba kya ɗaukan mutane balle ki rage mu su hanya"

"To Ya Suhail...." ta wani turo baki.

Har ƙofar gidan su Suhail ya kawosu wadda Nafy ke ma sa kwatance cikin karya murya.

Ta ma sa godiya sannan su ka fito.

"Kin bani mamaki Nafy, irin wannan shishshigi haka, daga ganin mutum hankalin ki ya tashi, ki ka sani ko saurayin Walida ne"

"And so what Zuby, na ganshi kuma ya min, idan ma saurayin Walida ne to sai dai ta yi haƙuri dan wallahi sai ya zama nawa"

Tsabar haushi Zuby rasa bakin magana ta yi ko gidan su Nafy ba ta shiga ba, ta tsare machine ta wuce na su gidan dan tsayawa neman Keke a wajen ma ɓata lokaci ne.

Nafy ta shige gida hankalin ta kwance, ban da tunanin Suhail ba abinda ke ran ta.

Ganin Suhail ya shagalar da ita zancen wani Hudu zai zo wajen ta yau. Lokacin da ya aiko ta je ma ji tayi gaba ɗaya ta tsaneshi. Ba abin da za ta yi da Hudu bayan ta haɗu da irin saurayin da ta ke so, irin mijin da ta ke burin aure. Da ƙyar ta iya fita. Nan ma sai da Mama ta ma ta magana akan ba daɗi walaƙanci tun ɗazu Hudu ke jiran ta sannan ta daure ta fito...

Tunda Hudu ya tafi ta fara kiran 'yan ajin su tana neman info akan Suhail shin Yayan Walida ne ko saurayin ta. Rashin samun gamsashshiyar amsa ya sa ta cilla wayar tana tsaki...

©AzizatHamza2020