Chapter 10
by @azizat
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣1️⃣0️⃣
Faɗa Mama ke ma ta wanda ba ta ma lura da hancin ta da ke fidda jini ba. Sai da ta ga Lubnan ta jawo tissue ta na cusawa a hancin na ta sannan ta ga jinin.
" Ya Allah!" ta faɗi tareda saurin zama kusa da ita ta na ƙoƙarin duba hancin...
Bacci ne ya ɗauketa lokacin da ta sha paracetamol ɗin da Mama ta ba ta. Maman ma bubbuga bayanta ta ke yi har ta yi bacci.
Wayar Lubna da ake kira Mama ta jawo ta ɗauka ganin sunan da aka saving *Hood*
Jin sallamar ba na ta ba ne ya sa ya shanye duk wani masifa da ya ke son jibge ma ta. Ya amsa sallamar tareda gaisheta dan muryan ta manya ce.
"Ba ta jin daɗi ka kirata zuwa gobe" abin da Mama ta faɗa ma sa kenan ya ma ta addu'ar samun sauƙi sannan ya kashe wayar.
Tsaki yai ya ce "to Umma kin ji wai sakaliyar yarinyar nan ba ta jin daɗi"
"Ayya! ashe shi ya sa ba ta zo ba. Allah ya ba ta lafiya"
Shi kam ya san sakalci ne dan jiya lafiya ƙalau ta zo gidan su ai. Ta sa shi kawai ya ɓata lokaci wajen jiran ta. Ya gyara zaman hulan sa ya fice a gidan.
Lokacin da Lubna ta tashi fishi ta shigayi da Mama. Tun da ta ke ba wanda ya taɓa marinta, lokacin da mommy ke da rai ta taɓa dukan ta amma ban da mari.
Ko sallah ba ta yi ba ta ɗau jakar Laptop ɗin ta, ta sa hijab ta fito a ƙofar ɗaki ta yi kiciɓis da Mama za ta shigo.
"Ina za ki je?" Mama ta tambaya
"I'm going bbbbback to school" ta faɗi ta na avoiding idon Maman
Mama ta ƙarɓe jakar da ke kafaɗar ta ta ce "ba inda za ki je"
Lubna ta haɗe rai kamar za ta yi kuka ta ce "Mama plz let me go, so i wont cause trouble here"
Mama ta wuceta ta shige ɗakin ta na faɗin " ɗazu sirikina ya kira ki na ɗauka"
Da sauri Lubna ta juyo ta na faɗin " What!, sisisisiriki kuma!"
"Da alama ya na da kirki dan maganar sa ma a nitse ta ke"
Lubna da kan ta ya ɗaure ta zo wajen Mama da sauri ta na faɗin "Mama ni ni ni ni banida saurayi fa"
Mama ta ce " shi kuma Hood fah?"
Lubna ta kwashe da dariya dan jin abinda Maman ta faɗa.
Mama kam dama abinda ta ke so kenan sai itama ta biyeta ta fara dariyan. Da ƙyar Lubna ta tsaida dariyar ta ce " Mama yyyyou are funny wallahi, who tttttold you Hood is my boyfriend?"
"Mi ye aciki, my girl is old enough ai"
Dariya Lubna ta kuma yi sannan ta ce " what did he tell you?"
"See, its confirm now....."
"Allah Mama ni kam" ta faɗi ta na haɗa rai.
Mama ta jawota jikin ta ta ce " Lubna kin daina fushi da ni?"
Lubna ta yi shiru.
"Lubna, Hajiya ko me za ta faɗa mi ki ba tarbiya mai kyau bane ki dinga maida ma ta magana, imagine kina kiranta "Bitch" yanzu za ki so wani ya kirani da haka?"
Lubna ta girgiza kai
" to kin gani. Sorry i went extreme har na mare ki"
"It's Ok, i'm sorry too"
"That's my girl, yanzu gaya mi ni waye Hood?"
Lubna ta yi murmushi ta ce " first of all he's not my boyfriend"
Mama ta ce " ehemmm"
Lubna ta sanar da ita komai gameda Hood, sai da ta gama labarin ne ma ta tuno da ledar da Umman Hood ta bata. Ta yi sauri ta je ta ɗauko ledar ta miƙawa Mama. Ita kam ko dubawa ba ta yi ba haka ta ajiye shi jiyan. Sai da Mama ta buɗe ta ga chin chin da dublun ne a ciki na biki.
Mama ta ce " wannan Umman ko dai campaign ta ke wa ɗan ta ne"
Lubna ta turo baki...
.......................................
Sai da ta yi sallar Isha ta kira Hood sai dai bai ɗauka ba. Ta ajiye wayar ta na shirin kwantawa saboda Mama ta tafi sashen Alhaji dan kwanan ta ne. Kiran Abdallah ya shigo wayar. Kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka.
"My Lubna mi ya faru yau?, kin yiwa Hajiya laifi ne?"
"Well, Hajiya thinks ban dadadadace da kai ba, wai ka fi ƙarfina. So i told her i dont care"
Ajiyar zuciya yai sannan ya ce " my Lubna kar ki damu da maganar Hajiya. A hankali zamu shawo kan ta"
" well, no need ffffffor that"
"What did you mean?"
Shiru ta yi na ɗan wasu seconds sannan ta ce " it's obvious this thing wwwwwon't work between us, kasan tun asali ni da Hajiya ba ma shiri and she will never accept me"
"Look Lubna, idan har kina so na ba wata matsala. Alhaji will support us..."
"Dan Allah ka yi hahahahaƙuri, they're pretty girls out there sai wanda ka zaɓa"
"Lubna ke na zaɓa, ke na ke so. Na jima ina dakon son ki Lubna...."
Kashe wayar ta yi saboda bazata iya juran jin maganganun sa ba. Gudun kar ya kuma kira ya sa ta kashe wayar gaba ɗaya. Ta jima tana tunani kafin bacci yai gaba da ita.
Washe gari text ta turawa Hood akan za ta zo gidan su ƙarfe huɗu. Sanar da Mama ta yi akan daga school gidan su Hood za ta wuce daga nan za ta tawo gida. Mama ta ce ta gaida Umman sa.
As usual shigan da ta saba ta yi top da wandon jeans sai hijab dan ta san idan ba ta sa hijab ba ma Mama za ta ma ta faɗa.
Da ta isa gidan ta samu yaran sun tafi Islamiyya Umma na yanka alayyaho da za ta yi miyar dare da shi. Bayan sun gaisa Umma ta ma ta ya jiki ta ce da sauƙi.
Umma ta kira Hood ta ce ya zo yanzu. Ta san idan ta ce Lubna ce ta zo ba zai zo da wuri ba amma da ya ke nunawa ta yi ita ke kiran shi sai gashi cikin minti goma ya shigo gidan.
"Ashe Luluwa ce a gidan na mu" ya faɗi ya na ƙarasawa wajen da suke gyara alayyahon.
"Umma ki ki ki ce ya dena kirana Lulululuwa"
Umma ta kalleshi ta ce "to kaji ba na so"
" an gama Umma"
"Lulu ya jikin"
Lubna ta hararreshi.
Umma ta ce "je ki ya nuna mi ki aikin, kar dare yai"
Ta tashi ta zo wajen da ya ke zaune ta zauna.
Shi kuma ya tashi ya nufi hanyar falo.
Umma ta ce " ya kuma ka barta anan?"
"Umma wannan yarinyar wawuyace, ba bina za ta yi ba"
Umma ta ce " yau na ji shirme Abba, ka ce ta bika ne?"
Ya ɗan juyo ya ce " to Lulu biyoni"
Ta tashi ta bishi. Falon ba wani girma ne da shi sosai ba sai dai ya wadatu da kayan alatu dai dai gwargwado, akwai plasma tv babba, ga fridge, Kujerun ciki ma abin kallo ne dan su na da kyau. Akwai ɗaki acikin falon wanda ta na da tabbacin na Baba ne.
Tsayawa ta yi ganin bai ce ta zauna ba.
"A kaina za ki tsaya?" Ya faɗi ya na ƙoƙarin cire hular sa.
Ta zauna kusa da shi da ya ke a two seater ya zauna.
Ta fito da laptop ɗin ta ta buɗe. Bayanin project ɗin ta ma sa ta kuma nuna ma sa aikin da ta fara.
"Wannan duk shirme ne" ya faɗi ya na danna laptop ɗin.
Sai da ya gama taɓe-taɓen sa sannan ya ce ina zuwa.
Ɗakin sa ya wuce ya je ya ɗauko na shi laptop ɗin. Sai da ya kunna ya ce. "ki dinga gani ki na yi a naki laptop ɗin"
Sun jima su na aikin ya na yi ya na ma ta bayani. Kusan awa ɗaya da rabi sai laptop ɗin Lubna ya fara warning ba chaji.
" barin kkkkkashe sai gobe na zo mu cigaba"
Hararanta yai ya ce "zaman ki na ke yi kenan, buɗe kunnen ki ki ji da kyau, dan su Umma na ke mi ki wannan abun ba dan ke ba. Ba macen da zan sake ɓata lokacina a kanta idan ba Umma ba kin ji"
Lubna ta yi ajiyar zuciya ta ce " to yaushe zan dawo?"
"OYO" ya faɗi ya na ƙoƙarin kashe na shi laptop ɗin
"Plz Hood" yadda ta yi maganan ya sa shi saurin ɗagowa ya kalleta.
"Wai in tambayeki mi ya sa ba kya kiran complete suna na ne?"
"Adam,Idrees,Nooh,Hood,younus, Ishaq, Isma'eel,..."
"Ya isa haka na san kin san sunayen Annabawa. Miye gamin tambayata da wannan?"
Ta yi murmushi ta ce "all names are beautiful if you call them right"
"Hood" ya maimaita.
"Thank you" ta faɗi sannan ta maida laptop ɗin ta cikin jaka ta fito.
Kitchen ta je Wajen da Umma ke tuƙa tuwo ta na mata sallama. Umma ta ce ta tsaya ta ci tuwo.
"Umma ni zan fita" Hood ya faɗa.
"Har kun gama?"
"A'a Umma wuta aka ɗauke" Lubna ta ba ta amsa.
Sai gashi kuwa kaman haɗin baki sai aka kawo wutan.
"Masha Allahu, Abba je ka ƙarasa ma ta tunda an kawo wuta"
Ya haɗe rai ya ce " Umma maghriba ta doso fa"
"wuce Lubna kije falo zai zo ya ƙarasa mi ki"
Lubna ta ce toh.
Sanda ya shigo ta na ƙoƙarin jona charger laptop ɗin.
Ya na zuwa ya ranƙwasheta a ka.
"Ouch, it's painful"
"Shegen bakin ki da za ki ce wa Umma ba mu gama ba. An gaya mi ki a yau za mu gama komai ne?, ana coding komai Lokaci ɗaya ne?"
Yai tsaki ya zauna "daga yau kar ki kuma zuwa gidan nan idan na gama mi ki aikin zan kira ki"
murya ƙasa-ƙasa ta ce " to ta ya zan ga yadda ka ke yi har na koya?"
Hannu ya kai zai ma ta wani ranƙwashin ta yi saurin tarewa.
"Na dai gaya mi ki"
Gaba ɗaya sun shagala da aikin sai da aka fara kiran sallar maghrib su ka ankara. Hood ya ce yanzu kam ta tafi sai Sunday tunda dare ya yi. Ba ta musa ba ta ɗau Laptop ɗin ta ta fito. Umma ta ce ai dole ta yi sallah ta ci abinci. Lokacin yaran gidan sun dawo. Ba ta musa ba ta yi alwala ta yi sallah da ta idar aka kawo ma ta abinci.
Tuwon shinkafa da miyar taushe.
Ta ɗan yi shiru tana kallon abincin.
Umma ta ce " ba kya cin tuwo ne?"
"No Umma ba na cin miyan ne, spinach kaɗai na ke ci, amma spinach da gyaɗa ya na ɓaɓaɓata min ciki"
"Ayya ba komai, bari Amina ta zo ta mi ki wani miyan"
"No Umma ki barshi kawai"
Sai da su ka yi sallama sannan ta fito anan ƙofar gida ta haɗu da Baba da Hood su na hira da alama tare su ka dawo daga masallaci. Ta gaida Baba sannan ta ce za ta wuce. Baba ya ce " Babangida ka kaita gida ma na ai dare ya yi"
"Baba za ta hau keke ne fah"
"Ni kuma na ce ka kai ta ba"
Ba mu su ya ƙarasa wajen machine ɗin sa ya tayar.
Lubna ta yiwa Baba godiya sannan ta ƙarasa wajen da Hood ke zaune akan machine ya na jiran ta.
Sai da ta hau sannan ya ce " ina za ki je?"
"Fadaman Mada" ta amsa ma sa.
Tun da ya dawo gida bayan gama service na shi sau ɗaya ya je anguwan nan ma saboda wani abokin sa da zai sauke ne a wajen.
Sai da su ka shiga anguwan ta fara ma sa kwatancen gidan. Nan ƙwaƙwalwarsa ta ɗauka 'ba dai gidan su Nafisah ba?' Ya faɗi a zuciyarsa.
"Lulu a gidan Alhaji Hassan Ningi ki ke?"
"Wow ashe ka san Alhajin mu"
Wani wawan tsayawa yai wanda sai da Lubna ta tsorata.
"Sauka" ya faɗi a taƙaice
"Why?"
"Ki sauka na ce!" Ya daka ma ta tsawa.
"Ba zan sauka ba sai ka kaini gida, ko kuma ka maida ni gidan ku" ta faɗi zuciyar ta ya na bugawa da ƙarfi dan ta tsorata da tsawar da ya yi.
Ko me ya tuna, sai kawai ya tada machine ɗin su ka cigaba da tafiya har ƙofan gidan su sannan ya tsaya.
Ta na sauka ta ajiye jakar ta a bayan saboda idan ta ɗauke tafiya zai yi dan ta lura kamar a takure ya kawota gidan. "Thank you Hood"
"Ɗau jakar ki zan wuce" ya faɗi da kakkausar murya.
"What's wrong?, ka san Alhaji ne? Did he do something bad tttto you....?"
"Innalillahi...Hudu Carpenter" muryar Nafy ya katseta.
Daga gidan ta fito da alama ma wata hidima za ta je dan ta sha kwalliya.
"A'a ko dai ido na ne"
Ta ƙarasa wajen su ta na haska fiskar Hudu da wayar ta. Hudu ya sha mur fiskar shi ko kaɗan babu annuri.
Ta kwashe da dariya ta ce " don't tell me Hudu dan ka rasa ni shi ne ka fara neman Lubna?"
"Nafisa what's happening?" Lubna ta tambaya looking confused.
"au saboda Hudu Carpenter dama ki ke yiwa Ya Abdallah jan aji. Lallai a gaishe ki Lubna, gaba ɗaya ba ki da taste Wallahi. Hudu Carpenter za ki haɗa da ya Abdallah"
Hudu ya ɗau jakar Lubna ya ajiye a ƙasa tareda faɗin. " sai da safen ku"
Ya ja machine ɗin sa ya tafi zuciyar sa cike da ƙuna...
Lubna ta kalli Nafy ta ce "Nafisa what's this bullshit all about? How did you even know him?"
"Dan uban ki za ki ce ba ki san Hudu Carpenter ba. Duk iya zamaninsa da ya ci a gidan nan"
Ta sake fashewa da dariya ta na faɗin "kai lallai dole na sanar da su Harira"
Lubna ta yi tsaki ta ɗau jakar ta ta shige gidan...
"Mama waye HuHuHudu Carpenter ?" shi ne tambayar da Lubna ta yiwa Mama lokacin da ta shigo ɗaki.
©AzizatHamza2020