ASHE BA SO BA NE?

7-8

by @yarmutanargungu

๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“

         ๐Ÿ“๐Ÿ“

           ๐Ÿ“

           07


"Hankali tashe Nasir ya ke ihun neman taimako! ga abokinsa kwance kamar gawa...

Nan da nan aka dauki Usman sai general Hospital Argungu!" 

    Bayan an karbe shi,likitoci sun yi aikin su yadda ya kamata."

Haka Nasir ke Kai da kawo, hankalin sa nakan dakin da aka shiga da abokinsa.!

  

"Fitowar likita ne Nasir ya zo da sauri... doctor ya jikinshi...? Da fatar ba abunda ya same shi? " Zo muje office" abin da doctor ya ce mishi kenan.

"Bayan mun shiga office likita ke sanar min cewa Usman ya kamu da hawan jini (hypertension). Wannan shine abun da nasani game da Usman mama..."

  

**** **** **** ****

Ajiyar zuciya mama tayi! San nan ta dafa kafadar Nasir tana cewa "Nasiru samun aboki nagari yana da wuya a wannan zamanin, Allah yayi maka albarka ya kuma sa zumunci ku ya daure har abada.!

"Amin mama, Allah ya bashi lafiya."

Amin ga takardar sallama nan likita ya ba ni.


Bayan sun koma gida Nasir yayi musu sallama ya wuce gida. 


   After 2 days

Alhamdulillah Usman ya ji sauki sosai Masha Allah! Sai dai fushin da mama ke yi da shi...

Yau bayan sallar Asubahi direct dakin mama ya wuce,ya tura kofar dakin bakin shi dauke da sallama...

Mama na kan sallaya tana lazimi 

  " Mama ina kwana "?

Da Kai mama ta amsa mishi gaisuwar sa" 

Kusan minti biyar babu Wanda ya ce komi.


Usman nason yin magana amma bai ga fuska ba,a hankali ya tako har zuwa wajen ta,ya daura kansa a kafafunta ...danshin da mama taji ne,ya sa ta mai da hankalin ta wajensa. Ya mugun bata tausayi sabo da rabon da taga kukan yaron ta tun yana karami...

  Su biyu Allah ya ba ta,Amina sai Usman. Tun ya na primary school mahaifinsu ya rasu,haka ta ke kula da yaranta,ta sa ma musu ilmin addini da na zamani,yanzu haka Amina tayi Aure, shi kuma Usman ya gama N.C.E aiki yake nema,Amma har yanzu shiru " kamar an aika bawa garinsu," tunda kasar tamu ta zama wa kasani ne waya sanka!"

   

Haka bai sashi jiran gawon shanu ba,". Yana saro tufafi yana sayarwa. Sabo da sana'oin hannu su na da matukar muhimmanci acikin al'ummar mu.


Rike hannun ta da yayi shiya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi...

" Mama dan Allah ki yafe min wallahi fushin ki a gareni masifa ce! Ta ya zan yi barci mai dadi bayan uwa na fushi da danta...


" Waya ce maka uwa na fushi da danta, tana dai son danta yabar biyewa zuciyarsa ne,sabo da Kar ta Kai shi ga halaka,ba ka tunanin halin da zan shiga idan wani abu ya same ka? Amma ni ba fushi na ke yi ba!

   "Oya tashi muyi magana cewar mama,bayan ya tashi zaune ta fara da cewa "Usman Aure kake so ko? Sun kuyar da kansa kasa yayi,duk da akwai fahimtar juna tsakanin shi da mahaifiyarsa,amma ya ji kunyar wannan tambayar...


"Bakomi Hausawa sun ce " shiru ma magana ce " kwanciyar ka asibiti ma ya nuna min cewa Dana ya isa Aure cikin dariya mama ta gama zancen...


 " Mama ban so dan Allah kibari... Fuskarsa Asanyaye Ya fadi Haka 

" To shikenan tun da ba ka so a fada amma ka zama jarumi,ba abu kadan mace za ta yi ma ka ba,kazube mana ...


" Please mama naface banso yakare maganar kamar zaiyi kuka.


" To na bari Allah ya baka mace tagari wadda taffi Hauwa...


*** **** **** ****


      ๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“

         ๐Ÿ“๐Ÿ“

           ๐Ÿ“

           08

" Haka rayuwa ke tafiya,kwanaki na wucewa har ankai ga satuttuka,ahankali har mun kai watanni,sannu sannu mun shiga shekara ,haka kwanakin mu ke tafiya ba tare da mun farga ba."

  ZAMFARA STATE

        gusau


Zaune suke acikin falo kowa ransa a bace yake! Abba ne ya kalli gefen da Hauwa take zaune rike da baby'n ta a hannu tana faman kuka. " Hauwa wannan shine tambayata ta karshe da zan yi miki, me ya hadaki da mijinki har ya yi Miki wannan dukan ya kuma hadaki da saki!? 

 " Abba wallahi ban yi mishi komai ba" shikenan tashi ki tafi, ammah idan na bincika ke ce ba ki da gaskiya sai ranki ya baci!? ๐Ÿงโ€โ™‚๏ธ


" Abba gaskiya bai kamata mubar wannan maganar ba, dole ne na dauki mataki akan abin da ya yi wa kanwa ta! Yaya Ahmad ne ke wannan maganar cikin fushi!!!

   "Ahmad tunda Abban ku ya ce abar maganar ba sai a barta ba, saki uku fa ya yi mata, ka ga kuwa aikin banza ne tsayawa cece kuce, ko wayyi nagari kansa... Allah zai saka ma ta! Kuma ba za a rike diyar sa ba, tunda abun rashin mutunci ne a mayar masa da jaririyar sai ya shayar da ita. Cewar Ummi wadda ranta bace take maganar!!!


   "Haba Umminsu ai "in rai ya baci hankali ake sawa a nemo shi" abar yarinyar a wurin mahaifiyar ta, har ta cika shekarun da addini ya ce, ina ga wannan shine adalci ga jaririyar. Abba ne ke wannan jawabin...


Haka dai aka tsayar da magana,yaya Ahmad ya wuce gidansa...


A daki kuwa Aisha ce zaune rike da baby Haneefa diyar Hauwa tana jijjiga ta.

  Budar bakin Aisha sai cewa tayi...