MUGUN NUFI!

Page 9

by @nanahaleema11

*MUGUN NUFI*


    ©️ *Nana Haleema.*


*Page 9*


A b'angaren Husna tunda aka tashi daga islamiyya ta dawo gida ta kulle kanta a d'aki take kuka kamar ranta zai fita, ba kukan komai take ba sai kukan tausayin kanta da kuma takaicin rayuwar ta. Wacce irin rayuwa mahaifin ta ya saka ta a ciki? Meye nufin sa na saka ta tana bin maza?, bata da me bata amsa hakan ya saka ta cigba da kukan ta cikin rashin samun mafita.


Abubuwan da aka koya musu a islamiyya ya dinga yi mata yawo a cikin kanta, an musu bayani akan abinda ya shafi tsarki da kuma sallah bata tab'a sanin ana wani abu wai shi wankan janaba ba sai a d'azu gashi bata gama rik'e yadda aka koya ba sai yawo abin yake mata a zuciyar ta.


Share hawayen idanun ta tayi ta kalli saman rufin d'akin a fili tace, "Yace ibadah bata yuwa sai da tsarki, gashi ya koya tsarki amma ban fahimta sosai ba, na shiga uku ni Husna Allah ka taimake ni kar na mutu ban tuba ba." ta fad'a tana sake fashewa da kuka me tab'a zuciya. A iya zuwa islamiyyar da tayi iya na yau ta fahimci abinda Baba yake sanya ta ba dai-dai bane a addini amma bata jin zata iya dainawa domin gangar jikin ta tak'i bada had'in kai a kan hakan.


Bud'e k'ofar d'akin akayi aka shigo hakan ya saka ta kalli wanda ya shigo taga Baba ne ta d'ago tana kallon sa har ya k'araso ya zauna kafin yayi magana tace, "Baba abinda nake aikatawa kake cemin shine dai-dai ga rayuwa ta shine zina ko?." Tsuke fuska yayi yace, "Waye yace miki zina ce?."

"A islamiyya."

"Mtswww kinga in islamiyyar nan zata b'ata min ke wallahi sai ki daina zuwa babu lallai babu dole, daga zuwan ki har sun ce miki zina kike yi bayan ke ba zina kike ba kina morar kuruciyar ki ne."


Ta d'ago idanu tace, "Amma Baba ance duka babu kyau Allah ya haramta ya kum....." kafin ta k'arasa yace, "Kee! Yi min shiru ko na fasa miki baki, su malaman islamiyyar sun fini san ki ne ko kuma sun fini ilimi ne? Shi wanda ake cewa babu kyau shine zina amma ke ba zina kike ba tunda baki da aure kina da ikon zab'awa rayuwar ki abinda kike so, bana son shirme ki tsaya ki nutsu nine na haife ki bazan tab'a cutar dake ba."


Idanu ta share badan ta amince da abinda yace ba ya kuma cewa, "Abokin kine yazo yake son ganin ki gashi nan zai shigo." Girgiza kai tayi tce, "A'a Baba bana son sake ganin su duka k'awaye na da abokai na zan canja su, ka manta abinda Dr yace?."


"Zaki sanya na zagi baban Dr dan uwar sa, ya isa ya hana ki huld'a da abokan ki ne? Asma'u ki dawo hankalin ki bana son shirmen banza" ya fad'a a fusace yana nuna ta. Shiru tayi bata ce komai ba ya fita yana fita Mahmud yana shigowa d'akin nata.


"Babyyyy!" Ya fad'a yana k'arasowa inda take ya zauna yana kallon ta yace, "Meya samu cute face d'in nan tayi ja haka?, kar kice min kuka kike tayi."


Kawar da kanta gefe tayi ya saka hannu ya dawo da fuskar ta ta ya rik'e hab'ar ta yace, "me ya faru ne? Kin taho baki sanar damu ba, yanzu kuma kin zauna kina ta kuka meya faru?." Kwace fuskar ta tayi daga rik'on da yayi mata ta sake mayar da face d'in gefe. Murmushi yayi ya zuba mata idanu bai san meyasa kome tayi burge shi take yi ba hakan ya saka shi cigaba da kallon ta yana murmushi.


"Ga key na motar ki gata can na dawo miki dashi, da kayan ki a ciki wanda kika bari" ya fad'a yana ajjiye mata key d'in motar a gefen ta. Hannayen ta duka ya rik'e yana murza fatar hannun a hankalin yace, "Come on baby ki saki ranki please, face d'in ki bata kyau in babu murmushi ki fad'a min abinda kike so zan miki."


Yadda yake murza fatar hannun ta ya fara shiga jikin ta ta kasa kwace hannun ta ta lumshe idanun ta, ko magana ta kasa yi, ganin hakan a tare da ita ya sanya shi yin murmushi ya cigaba da abinda yake yi yace, "Fad'a min" ya fad'a muryar sa can k'asa tare da matsawa kusa da ita yana hura mata iskar bakin sa a fuskar ta.


Yana kallon yadda tsigar jikin ta take tashi kafofin gashin hannun ta na bud'ewa, kiss ya mata a kumatu hakan ya saka ta bud'e ido suka had'a idanu yana kallon idanun ta yace, "Kice wani abu." Zare hannun ta tayi daga cikin nasa jikin ta a sanyaye ta bud'e baki tace, "Ka tafi."

"Meyasa Baby?."

"Bana son ganin ku dukkan ku ka tashi kaje."


Murmushi yayi kad'an ya mik'e yace, "na tafi, in kina nema na koda yaushe k'ofa a bud'e take" yana gama fad'ar hakan ya fice dan yasan dak'yar bata neme shi ba domin ya gama karantar ta.

Yana fita ta kalli sama yanayin ta yana cigaba da canjawa a hankali. Mik'ewa tayi ta isa inda kayan ta suke ta bud'e ta d'auko kwalbar kayan mayen ta guda d'aya ta kafa kai ta shanye ta ajjiye kwalbar ta k'arasa kan gado ta kwanta ba jimawa bacci ya kwashe ta.


Duk da baccin da yayi mata mugun yawa amma hakan bai hana fitinanniyar sha'awar ta tashin ta ba, lokaci d'aya taji duniyar na juya mata ba shiri ta farka a firgice idon ta na kullewa sabida bacci, duk da sanyin a.c d'akin amma gumi take yi jikin ta ya soma mugun rawa ta danna wayar ta taga k'arfe goma na safe lokacin. Mik'ewa tsaye take so tayi amma tasan baza ta iya ba sabida yadda take jin kanta yayi mata mugun nauyi ga bacci da yake d'aukar ta.


Tana daga zaunen ta cire komai na jikin ta ta rufe jikin ta da bargo jikin ta na rawa numfashi ta ya fara fita dak'yar. A lokacin Baba ya lek'o d'akin a hankali ganin yanayin da take ciki idanun ta sun k'afe ya sanya shi murmushi yana girgiza kai tare da cize baki cike da mugunta ya shigo d'akin a hankali kamar b'arawo ya d'auki wayar ta ya fita har lokacin bata sani ba bank'arewa take a cikin bargo tana wani irin nishi tana juya kai.


Number Mahmud ya nema ba b'ata lokaci ya tura masa text ya dawo mata da wayar ya ajjiye ya koma bakin k'ofa yana kallon ta, k'wafa yayi ya b'ata rai yace, "A haka rayuwar ki zata k'are a lalace a azabance matuk'ar ina numfashi bazan bari ki samu jin dad'in rayuwa ba, zan iya k'arar da duk abinda na mallaka dan ganin na tarwatsa rayuwar ki" ya gama fad'a ya fice ya barta ya koma b'angaren sa yana kallon duk me shigowa ta taga.


Yana kallon shigowar Mahmud ya faka motar ya shiga cikin gidan da sauri shi kuma ya saki labule yana murmushi. Mahmud yana shiga d'akin nata ya mayar da k'ofa ya rufe ya shiga ciki da sauri ya yaye bangon ya ganta a sume idanun ta a k'afe babu komai a jikin ta. Sanin abinda yake damun ta bai b'ata lokaci ba shima ya shiga cikin bargon ya jawo ta had'uwar jikin ta da nasa ya sanya ta jan dogon numfashi alamun ta samu abinda take nema.


Sun jima a haka sun d'auki lokaci me tsaho kafin su dakatar da abinda suke aikatawa ko motsin kirki Husna bata yi ba bacci ya sake d'aukar ta a inda take kwance, shine ya mik'e ya shiga band'akin ta yayi wanka ya fito ya mayar da kayan jikin sa ya zauna a gefe yana kallon ta. Shi kam Allah ya sani bazai iya rabuwa da Husna ba yana son ta yana kishin yaga wani a tare da ita zai iya aikata komai akan duk wanda yayi gangancin rab'ar ta. Kiss ya mata a goshi gashin ta da yake a haukace ya gyara mata sannan ya fice yana jin nishad'i na ratsa shi.


*Abuja.*


Haka kawai ya farka sukuku baya jin wani kwari a jikin sa duk da nishad'in da ya kwanta dashi, a haka ya shirya ya tafi national hospital. Aiyuka ya tarar da yawa haka ya samu yayi abinda zai iya yana cikin aikin ya samu mail ya duba sai kuma ya fita direct ya wuce CBN quarter's.


A hankali ya murd'a handle d'in k'ofar ya shiga ya tarar da Anty Lubna ita da Omar suna tattaunawa akan wani case na fyad'e da suka samu a Kano. Da kallo suka bishi ya samu waje ya zauna yana fitar da numfashi a hankali kafin ya kalle su amma baice komai ba.


Anty Lubna tayi dariya tace, "Auta ya dai?." Iska ya fesar ya gyara zaman sa yace, "I don know." 


Omar ya tab'e baki yace, "Kin manta ne wai? Ai duk inda rago yake aka samu Ahmad an gama komai yayi yace wash na gaji." Dariya Anty Lubna tayi tace, "Wai haka?." Yace, "haka kawai yau na tashi a haka ban san me yake damu na ba, I think it's about Husna."


"You see, Husna! Husna!! Always Husna, wait Ahmad wai ba munyi solving problems d'in ta bane ba jiya? Mun mata abinda zamu iya duk abinda tayi wannan kuma ita taso, akan me zaka dinga saka damuwar ta a zuciyar ka bayan kasan ayyukan da suke gaban ka?."


"One minute Omar, who's she?" Anty Lubna ta fad'a tana kallon Omar.


"Wata prostitution ce wacce....." Ahmad ya dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Don't call her prostitution again" ya fad'a yana kulle idon sa alamun bai ji dad'in abinda ya fad'a a kanta ba.


Omar yace, "Na fad'a karuwa, ba karuwar bace ba?." Anty Lubna tace, "kuyi min bayani mana me yake faruwa ne wai?, Wacece ita?, Then meye a tsakanin su da zai damu dan an kira ta prostitution?."


"I think yana son tane" ya fad'a yana hararar Ahmad.


"What!?" Ta fad'a tana kallon su duka biyun. Ahmad yace, "Look, I'm not in love with her, but I'm Compassionate her life."


"Anty Luba yarinyar nan da ake magana tana daga cikin wacce taje office ta same sa tace tana son ta daina abinda take yi but she can't, he want to help her but sai ta watsar aka daina ganin ta daga baya ta dawo Allah ya saka masa san taimaka mata a zuciyar sa yeah munji wannan yin Allah. Anty ta shiga rayuwar sa har office d'in sa na clinic take zuwa tace zata daina but bata d'auki hanyar hakan ba, caught the stroy munje har garin su jiya Kaduna an mata register ta shiga school tace kuma ta daina to meye had'in sa da ita yau kuma da zai tashi da damuwar ta?."


Anty Lubna da taji me Omar yace tace, "Meyasa taimakon ta bai biyo ta office d'ina ba ya wuce naka directly? I think wannan issue d'in is under my office?". Omar ya ware hannayen sa ya tabe baki yace, "because she love him".

"Who told you?" Ahmad ya fad'a yana kallon sa.


"I saw it in her eyes, ai ba makaho bane ba." Anty Lubna tace, "Kayi min bayani Ahmad meye a tsakanin ku?."


"Nothing except taimako, tun lokacin da na ganta nake jin ta a jiki na kamar Tasleem, ina jin ta a jiki na kamar y'ar uwa the reason why na shiga rayuwar ta ina so na d'auko ta daga wuta na dawo da ita waje mai sanyi. Anty bata da mahaifiya Maman ta ta jima da barin duniya, mahaifi kad'ai ne da ita then akwai enforcement a cikin life nata sabida komai nata tana yi ne a tsorace. Hankali na bai kwanta da zaman ta a Kaduna ba sam ina ji a jiki na kamar a can mai saka ta yake."


Anty Lubna tace, "I heard dis, abu ne mai kyau dan kaso ka taimaka mata abubuwan da ka lissafo a kanta tana buk'atar a taimaka mata, but ya zama dole ka nutsu ka dawo hankalin ka ka daina shigewa rayuwar ta, kana da matsayi babba a Nigeria gabad'aya kowa ya san ka shiga rayuwar ta da kake dai-dai yake da tab'uwar darajar ka."


"Help me to tell him what I'm trying to say" Omar ya fad'a yana d'aga kafad'ar sa. Ahmad ya zuba musu fararen idanun sa kafin ya d'an lumshe su ya bud'e yace, "Amma mutane sun san ina da my own foundation akan irin su right? Why mutane zasu zarge ni a kan ita kad'ai?."


"We know aikin kane but mutane basa raina abin magana, kar kaga wai kana zaune lafiya baka da abokin fad'a wallahi wani yana nan yana neman hanyar da zai bi wajan ganin ya nemo abinda zai tozarta ka a duniya. Wata k'ila ma amfani ake da yarinyar dan a cutar da kai you have to be careful Auta, zuwan ka inda take matsala ne, zuwan ta inda kake matsala ne ka bar min komai a hannu na zan dinga bibiyar ta ina fad'a maka information but, in na same ta bata mayar da hankali akan barin abinda take aikatawa ba zamu zare hannun mu daga kanta har kai dole ka bar lamarin ta ka yarda?."


Zuba mata ido yayi yana sauraron ta har ta kai k'arshe, shi Anty Lubna ce bai amince da ita ba sabida ta cika fad'a da yawa yanzu tana ganin wani mistake a lamarin Husna shikenan zata watsar shi kuma ba haka yake so ba gaskiya.


"Kayi shiru ko baka amince da abinda nace bane?." ta fad'a tana kallon sa. Iska ya fitar yace, "No amma....." ta dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Abinda Omar ya fad'a gaskiya ne kenan son ta kake."


Girgiza kai yayi yace, "I'm not, is okay na baki go ahead." Ta koma jikin kujerar ta kwanta tace, "Good. Any gist?."


Ahmad yace, "We have guests from America on Monday." Anty tace, "Wow me zasu zo yi?."

"Zasu zo wai su karrama ni matsayi na na wanda nayi karatu a country after na gama manufacturing maganin kuma zasu gayyace ni can."


"Ma sha Allah, kaji labari mai dad'in gaske, to me za'a shirya?" Omar ya fad'a. Ahmad ya yatsine fuska yace, "It's very big event fa, sunyi inviting mutane da dama daga outside countrys and cikin country d'in nan ma sun gayyata ciki har da president."


Anty Lubna tace, "Abu me dad'in ji Auta, ya kamata mu fara shiri tun yau kaga yau Thursday 3days ya rage mana."


Ahmad ya sauke numfashi yace, "Akwai matsala ne." Dukkan su suka kalle shi suka ce, "Ta me kuma?."

"Last time da muka had'u nace musu ina da mata da baby dis time sunce definitely matata da babyn su kasance a wajan, kun san yanayin turawa da matan su in nace bata zo ba zasu ga kamar ban d'auke ta da mahimmaci ba, illar k'arya kenan" ya fad'a yana yamutsa fuska.


Anty Lubna tayi dariya tace, "To ai Kaine kamar me aljanu ace har yanzu babu wacce kake so, for now ya kamata ce kayi aure har da yara ma kalli Omar fa yaran sa biyu amma kai ko matar baka da." 

"Anty mu samo solution wannan duka a tattauna daga baya."


Omar yace, "Ni a gani na mu samu taje matsayin matar ka." Ahmad ya harare shi yace, "U are not serious, wata kawai bamu san ta ba tazo ta tsaya kusa dani muyi holding hands ban san wace ba? Impossible."


Anty tace, "To a samu ta gida mana." Ahmad yace, "Wace?."

"Ga Mima" Omar ya fad'a yana kallon su. Anty Lubna tace, "very good idea Omar, Mima ita kad'ai ta dace da tsawaya matsayin matar ka a taron."


Wani irin kallo yake musu na baku da hankali dukkan ku yace, "Mima! Mu fito front of peoples ciki har da wanda b y'an k'asar nan ba na nuna Mima as my wife? Muyi holding hands in ta kama we hug each other, never, ever! Abu ne da bazai yu ba gwara na hak'ura da ko meye da dai wannan banzar yarinyar ta tsaya matsayin mata a gare ni, ni Ahmad wannan ai zunubi ne a gare ni" ya fad'a cikin zallan takaicin da yake cin zuciyar sa.


Anty Lubna tayi dariya tace, "For the first time naji kace Mima, ka iya pronouncing Mima kamar a bakin ka aka yi sunan. Malam Auta in ba ita ba wa zaka samu?."


"Tasleem" ya fad'a yana kallon wani wajan daban. Dukkan su dariya suka fara yi jin wacce ya ambata wai Tasleem yarinyar da secondary bata kammala ba. Sai da suka gama dariyar sannan Anty Lubna tace, "Ai kana nuna musu Tasleem as your wife wallahi sai su kama ka dan wannan child abuse ne, ina kai ina Tasleem Ahmad?."


Shiru yayi jin abinda tace ya kuma san haka ne dan gaskiya tayi karancin shekaru da yawa ya kalle su ya d'aure fuska yace, "okay in ba Tasleem ba zan nuna Husna as my wife." Kallon juna sukayi kafin su kalle shi a tare suce, "What!?."


Share it sabida Allah 👏🤗