Chapter 13
by @azizat
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... .............
0️⃣1️⃣3️⃣
*This page is solely dedicated to Anty Hauwa Jidderh❤*
Sai da ya juya ya ga ba ta shigo ɗakin ba, ya buɗe ƙofa ya ganta tsaye " ba za ki shigo ba ne?"
"Ba ka ce na shigo ba ai"
"To shigo"
Unlike ranan da ko zama ba ta yi ba, wannan karan cewa yai ta zauna. Akwai kujera one seater a ɗakin anan kuma ta zauna. Ya zauna a bakin gado ya ce "Lulu ya ku ka ƙare da supervisor ɗin ki?"
"Ya Allah! Hood, ba ka ga yadda ya ji daɗi ba. He said we are selling the software"
"Ai dama na gaya mi ki sayar da shi za'ayi"
Da murmushi a fiskarta ta ce " Thank you Hood"
" so, mun gama abinda ya haɗa mu, yanzu kowa yai hanyar sa ko?"
"Noo" ta faɗi da sauri
"Mi ya saura kuma?"
Ganin how serious he looks ya sa jikin ta yai sanyi. A hankali ta ce " i thought we are friends now"
Dariya yai ya ce " waya gaya miki? ai beautiful girls dont make friends with ugly guy like me"
"I'm i beautiful?" Ita kan ta ba ta san maganar ta fito ba.
Murmushi yai ya ce " i'm i not ugly?"
"Nooooo" ta faɗi da ƙarfi.
Ya tashi ya na dariya ya ce " gaskiya ne fa, saboda haka 'yar uwar ki ta ƙi ni"
"Sssssseriously, its a lie"
"Ko?"
"Allah" ta amsa
Wani kati ya ɗauko ya miƙa ma ta, sai da ta ƙarɓa taga ticket ne.
"OMG, i was hoping to buy it on monday"
Ya zauna ya ce " to na riga ki"
"Thank you very much Hood"
"Yaushe za ku fara exams?"
"Next week Monday"
"Allah ya bada sa'a" ta amsa da amin.
Ba wai katin na da tsada bane amma kuma the fact that shi ya siya ma ta is what makes her happy.
" sai mun haɗu saturday ɗin ko"
"Yeah sure" ta amsa ma sa
Ganin bai ce komai ba ya sa ta tambaye shi " you dont like the food i cook do you?"
" ni bance ba, dan yanzu zan ji sammaci a wajen Baba da Umma"
Dariya ta yi sosai shi ma yai dariyar.
"About that, Lulu i really appreciate it. Ke ce mace ta biyu da ta zo gidan nan saboda ni ta yiwa Umma da ƙannena alkhairi. Thank you Lulu"
"Who's the other girl?" Lubna ta tambaya curiously.
"Asiya" ya amsa a taƙaice
Ganin bai ƙara cewa komai ba ya sa ta ce " your ex?"
"Yes"
"Oh! Ina ta ke yanzu"
"Ta yi aure har da 'ya'ya"
"Kai kai, when did she marry?"
"Six years ago"
"Sorry" Lubna ta faɗi a hankali.
"Abba ana kiran wayar ka" muryar Umma ya katse mu su hiran.
Ya tashi ya fita itama Lubnan ta bi bayan shi.
Sai da ya gama wayan sannan Lubna ta sake yiwa Umma sallama.
Umma ta bata ɗari biyar wai kuɗin Keke.
Har ƙofan gida Hood ya rakota. Ya na cewa "machine ɗi na tana wajen gyara da na kai ki gida".
"Its Ok, Hood yaushe za ka bani labarin Asiya?"
"Idan mun haɗu watarana"
"Promise?"
"No"
"Plz nah"
"Ba ni na ce mi ki idan mun haɗu ba"
Su na tafiya su na hira wadda yawancin hiran akan program ɗin Tedx da za su je ne ranar Asabat.
Sai da ta shiga keke ya miƙawa mai keken kuɗi ta ce " so, are we friends now?"
" a sauka lafiya Lulu"
"Aaaaaah" ta faɗi yayinda mai keke ya ja kekensa.
....................................
A tsakar gida ta samu ana yiwa Nafy lalle. Ladidi da ke fige kaza a wajen kawai ta gaisar. Ta wuce dan shanya kayan da ta wanke
"Lubnan Hudu ya kike, na ji wai pepper chicken da ki ka yi da safe wai gidan su Hudu ki ka kai, ashe abin ya kai haka!"
Lubna ta cigaba da abinda ta ke yi.
"Lubna dan Allah yanzu Hudu Carpenter ya fi mi ki Ya Abdallah?"
Still Lubna ba ta yi magana ba.
"Magana na ke mi ki fa"
Sai da ta gama shanya kayan ta zo gaban Nafy ta ce " stop meddling with my life Nafisah. Hood or Abdallah the choice is mmmmmmine not yours"
Nafy ta kwashe da dariya ta na maimaita sunan da Lubna ta kira Hudu carpenter da shi wai HOOD.
Ladidi da ke gefe ta ce " ina son jin masifan Lubna Sai dai ita daga ta fara faɗa sai turanci gaba ɗaya ka rasa gane kan zancen" Barira da ke yiwa Nafy lalle ta sa dariya.
.........................
Ta na kwance ta na ɗan karanta handout ɗin ta amma zuciyar ta ba abinda ke tuno ma ta sai hiran su da Hood. Maganar sa da ya ce *beautiful girls dont make friends with ugly guys Like me* shi ya fi ɗaukan hankalinta.
'He thinks i'm beautiful' ta faɗi a ranta. Just thinking about that makes her blush. Ba wai directly ya ce she's beautiful ba kamar yadda Abdallah da Younus ke gaya ma ta, amma just the fact that he thinks she's beautiful is making her happy.
A haka Mama ta shigo ta sameta. "Wannan farin ciki na san baya nasaba da gidan suriki na da ki ka je yau"
"Kayya Mama, Ni gidan su Hood na je ba gidan su wani ba"
"Ayya ƙawar Hood"
"Mama ki yiwa Ladidi faɗa she's too nosy"
"Mi ta yi?"
"She went and tttell Nafisa that i made pepper chicken for Hood"
" to abinki Lubna mi ye a ciki, na ga itama Nafyn dambun kaji ta sa a mata saboda Suhail da zai zo gobe"
"Mama its two different things, ita ta yi wa Suhail ni na yiwa Umman su Hood as an appreciation"
Dariya Mama ta yi ta ce " duk kanwar ja ce ai"
.................................
Ranan Monday Lubna ba ta zo gidan ba balle ta ga takaici. Yadda Nafy ta sa aka gyara gida kamar wani Sarki ne zai zo. Ita kan ta takanas ta je saloon aka ma ta gyaran gashi da kwalliya. Ƙarfe takwas na dare Suhail ya zo gidan su. Da safe ya iso amma saboda kinibibi dole ta sa ya zo a ranan saboda a cewar ta ta missing na shi sosai.
Ƙarin bushasharta ma Alhaji baya nan. A falon sa ma ta sauke shi inda aka baje ma sa kolin kayan da aka tanada musamman saboda shi. Ranan bakin Nafy har kunne. Haka ta sa duk ƙannen ta sai da su ka zo su ka gaida Suhail. Aabid ma da gulmansa sai da ya je su ka gaisa. Cikin gatse Nafy ta yiwa Aabid magana
" Aabid na iya zaɓe ko?"
Ya ce " lallai Masha Allahu"
"Ka sa baki a maganar Lubna itama ta zaɓi mai kyau dan na ga kamar idon ta na da matsala"
" kin san Lubna special girl ce, ta fi son unique things"
"Ko?"
"Yeah" ya amsa ya na ɗaga gira...
Sai da ya ci ya sha sannan ya je ya gaida Hajiya. Su na zaune ta ce barin kira Mama ku gaisa. Ta shiga ɗakin Mama ta samu ta na duba wasu takardu.
"Mama ga Suhail ya zo zai gaishe ki"
Mama ta ce " to ina zuwa"
Sai wani shanƙamshi ya ke yana magana da ƙyar. Abu ɗaya Mama ta karanta a tattare da shi, idon shi babu kunya kwata-kwata. Zargin ma Shaye-shaye ta ma sa...
Su ka gaisa ta shige ɗakin ta, dan yadda Hajiya Zainab ke hararanta ma ba zai bari ta ma sa tambayoyi ba.
Duk abinda ya faru Aabid ya kira Lubna ya gaya ma ta. Ita kuwa ko a jikinta.
Washe gari Mama na girki a kitchen Nafy ta shigo idon ta duk a kumbure saboda rashin barci.
"Mama ki ka ce Ladidi ta taso ni"
" Nafy yanzu yadda ku ka bar kitchen ɗin nan kun kyauta. A ƙalla ko ba za ku wanke kayan da ku ka ɓata a daren ba sai ku tattare su waje ɗaya. Amma na shigo kitchen ɗin nan yau da safe na tadda shi kamar bola, Kwanuka har a ƙasa."
"Mama gajiya mu ka yi jiyan amma ai nace Ladidi ta wanke yau da safe, dan dai ke da sassafe ki ke aikin ki shiya sa ki ka taddasu haka"
"Shi kenan ya yi kyau"
Har ta juya za ta fita sai kuma ta dawo ta ce " yawwa Mama, yanzu maganar Lubna ba za ki sa baki ba"
Mama ta juyo ta ce " wace magana kenan?"
"Wai cikin Ya Abdallah da Ya Yunusa duk ta rasa wanda za ta zaɓa sai Hudu carpenter"
"Nafy miye a ciki?"
"Mama Hudu carpenter fah"
"Mi ye aibun shi? Ko dan tsohon saurayin ki ne?"
" Allah ya kiyaye, dama chan shi kaɗai ya ke abinsa. Bai taɓa birgeni ba"
"To Miye matsalar?" Mama ta tambaya
" wai na ga dai su Ya Abdallah duk sun fishi fasali ne, ko ba komai ta auri wanda za ta kalle shi ta ji daɗi a ranta ma na"
"Kyau shi ne jin daɗi?"
Ganin Mama ta ƙi ba fa support sai ma ƙoƙarin gasa ma ta magana da ta ke ya sa ta ce " shi kenan Mama, dama wai naga 'yar uwata ce ina son ba ta shawara amma tunda ke ma ba ki damu ba, shi kenan" tana faɗin haka ta fita daga kitchen ɗin.
Mama ta girgiza kai ta ce " har yanzu Nafy ba ki san minene aure ba"....
..............................
"Suhail ina maganar yarinyar da ka ke nema ne?" Alhaji Inuwa ya tambaya.
"Ta na nan Abba"
" to kace ma ta za ka fito" ya zaro ido ya na kallon Abban.
"Alkawarin da ka min yana nan ban janye ba"
"Abba kwanana uku da dawowa ta fah, a ɗan ban lokaci"
"Ba wani lokaci Suhail, nan da wata ɗaya ma ban ƙi ka yi aure ba. Dole in tabbatar da nitsuwar ka kafin na baka aiki"
"Shikenan Abba zan ma ta magana"...
"Amma Alhaji ba ka ganin ba a yiwa Walidah adalci ba kai kan ka kasan Suhail ta ke so" Hajiya Bilkisu ta faɗawa mijin ta.
"Bilki kenan, ina ganin Usman yaron kirki da mutunci in bawa Suhail auren ɗiya ta. Ashe ban shirya ma ta kwanciyar hankali ba kenan"
"Amma Alhaji ba lallai Walidah ta amince da Usman ba"
"Shi ma ɗan uwanta ne, a haka za su saita kan su idan aka yi auren" da haka ya rufe zancen....
Duk yadda ta so 'yar ta ta fahimci zancen ta kasa, kuka kawai ta ke wiwi akan Alhaji baya son ta. Zai bari Suhail ya auri bare akan ta.
"Haba Walidah na gaya mi ki Abban ki mafi alkhairi ya ke nema mi ki shi ya sa ya yanke wannan hukunci"
"Suhail yaya na ne, miye rashin alkhairi a gare shi. Na ga zumunci za 'a haɗa"
"Usman ma ai yayan ki ne, kuma shine mafi chanchanta da ke"
"Ki bar rarrashinta Bilki, idan ta gama kukan na ta na shirme za ta haƙura"
Muryan Abba ya doki kunnen ta.
Ta tashi ta bar ɗakin da gudu tana kuka.
"Alhaji ba za a bawa Suhail lokaci ba ko zai chanja halayen sa kafin nan itama Walidah ta gama karatu sai a mu su aure"
"Ban shirya wannan chachar ba. Ta auri Usman ta samu kwanciyar hankali. Tun yaushe mu ke jiran ya chanja halin sa amma ya ƙi. Idan yai auren ma gani ko zai chanja tunda ya ce yana son yarinyar"
" to Allah ya sa"
Tunda Walidah ta shiga ɗaki ta ke kuka. Tun tasowarta ta ke son Suhail duk da ba wai ta taɓa sanar da shi hakan ba ne amma alamomin da ta ke nuna ma sa kaɗai ya ci ya gane hakan. Lokacin da Usman ya gayawa Abba ya na son ta, da Abba ya ma ta maganar ta ce ita Suhail ta ke so, tun lokacin ta ke tunanin komai zai zo da sauƙi amma sai gashi ƙwatsam wai Suhail Nafisah zai aura ita kuma ta auri Usman. Dukkan su 'yan uwan ta ne sai dai Allah na gani tafison Suhail. Da chan su na mutunci da Usman sai dai tunda ya sako zancen soyayya ta tsaneshi domin Suhail ta ke so...
.....................
Weekend ɗin ƙarshe da ta zo gida kenan saboda exams da za su fara ranan monday. Dama a irin wannan lokaci Mama na yi ma ta cake, chin-chin da dambun nama saboda ta riƙa ci, ta san halin ta abinci bai dameta ba sai ta wuni ba ta ci komai ba idan ta na karatu.
Tun jiya jumu'ah da Hood ya ce zai zo ya ɗauke ta su tafi taron Tedx da za a yi ta rasa nitsuwar ta. Rasa kayan da za ta sa ta yi. Normally idan za ta je events irin haka ta fi saka normal shigan ta, riga da wando, sannan ba ta ma saka hijab. Sai dai yau daban ne, tareda Hood za su je.
Ta fitar da kaya sun yi kala goma amma ta kasa zaɓa a ciki. A haka Mama ta shigo ta sameta.
"Da alama ba za ki je program ɗin nan ba, tun yaushe ki ka yi wanka amma kin ka sa shiryawa"
"Mama i dont know what to wear"
Mama ta yi murmushi saboda ta san dalilin da 'yar tata ta kasa zaɓen kaya. This is the first time da Lubna ta damu da shigar da za ta yi kafin ta fita wanda Maman ta san saboda Hood ne.
"Mama ki tayani dubawa ma na"
"Ki sa kayan da Khadija ta kawo mi ki wancan zuwan su"
"Wanne a ciki?"
"Baƙin, kin san baƙin kaya ya na mi ki kyau"
ta tashi da sauri ta buɗe closet ɗin ta na neman kayan.
Sai da ta fito da su Mama ta ma ta sallama saboda makaranta da za ta je.
A gaban mirror ta tsaya tana kallon kan ta bayan ta saka kayan. Riga da wando ne na pakistan duka baƙi, rigan ya na da adon flowers kalar gold sai gyalen wanda shima ya na da flowers ɗin. Ta ɗan yafa gyalen saboda ta na ganin idan ta yi rolling ba zai yi kyau ba.
Takalmin ta flat shoe ta ɗauko wanda shi ma ɗin golden color ne. Ba ta da purse ko jaka irin kalar, dan haka ta ɗauko purse ɗin Mama kalar gold ɗin.
Ta jima a gaban madubi ta na tunanin mi za ta shafa a fiskar bayan powder da ta shafa. A hankali ta ɗau kwallin Mama ta fara ƙoƙarin sawa. Tun kafin ta kai tsinken ma idon ta ya ciko da hawaye. Ta yi ƙoƙarin sawa hannunta na rawa wanda hakan bai yiwuba sai ma hawaye da idon ya fara yi. Yau ga ranan iya kwalliya, tunda ta ke sau ɗaya aka taɓa sa ma ta kwalli, lokacin bikin Khair wanda make up artist ɗin da ta yiwa Amarya ce ta ma ta itama.
Ganin ta ka sa saka kwallin ya sa ta haƙura ta jawo tissue ta goge idon. Wayar ta yai ringing ta tashi ta je ta ɗauko.
"Ki fito na iso" abinda Hood ya gaya ma ta kenan ya katse kiran.
Ta sake zama gaban mirror ta na tunanin mi za ta sa. Chan ta ga lipstick ɗin Mama ta ɗauka. Ta goga a lips ɗin ta. Gani ta yi lips ɗin ta sun yi wani ja bau. Ta ɗau tissue ta sake gogewa. "Idan Mama ta sa ya na ma ta kyau fa" ta faɗi a zuciyar ta.
Ta ɗauko wani pink ta sake gogawa shima ta ga bai yi ba. Kiran Hood da ya sake shigowa ya sa ta ɗau wayar da purse ta fita daga ɗakin da sauri.
Da Ladidi kawai ta haɗu a falo
"Lubna ke ce yau da sa jan baki! lallai za a yi ruwa da ƙanƙara"
Lubna ta harareta ta fice da sauri.
Har za ta buɗe ƙofar gate ɗin sai kuma ta fito da wayar ta ta kalli kan ta a screen ɗin wayar. Ga dai pink lipstick ɗin da ta shafa na nan amma ba yawa. Ta sa harshe ta lashe lips ɗin dan ta ga kamar bai ma ta kyau ba sai dai kuma jan bakin 24hrs ne bai fita ba. Ta dai yi ajiyar zuciya ta fita a haka.
Ya na zaune akan machine ya na danna wayar sa ta fito. Shigar shi dai da ya saba yai farar jumper da hula. Sai da ta ƙaraso ya ɗago ya kalleta.
"Sorry i kkkkkept you waiting" ta ce da shi
"Lulu jan baki ne haka!" Ya faɗi ya na dariya.
Wani iri ta ji da ya faɗi hakan, ta sa bayan hannunta ta fara ƙoƙarin gogewa.
"Ki bar shi ma na, ya mi ki kyau fah"
Batasan lokacin da murmushi ya suɓuce ma ta ba.
Ya tada machine ɗin ya ce " mu tafi ko?"
Ta ɗaga ma sa kai tareda zuwa ta hau bayan sa ta na murmushi. Ya ja machine ɗin sa su ka bar wajen...
©AzizatHamza2020