Chapter 17
by @azizat
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣1️⃣7️⃣
"Why did you lie to me?"
Saukar da idon ta ta yi daga kallon da ta ke ma sa dan ta san ba ta da gaskiya.
"Lubna kin bani mamaki, wallahi gara ace ma Yunusa za ki aura da wannan. Mi ki ka gani a jikin sa? Mi ya ke da shi?. Yanzu kin zaɓi bare a kaina?"
"I'm sorry" ta faɗa a hankali, ba abin da za ta iya faɗi daya wuce hakan.
"Ni ba ma abinda ya fi ɓata min rai irin how foolish you made me look a gaban Alhaji. Kin san ya na ji kuwa da ya ke sanar da ni wai Hudu ki ke so. Ki yi tunani Lubna, i still have hopes in you"
Kamar zai yi wani maganan sai kuma yai shiru. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fita a ɗakin. Sai da ya fita daga ɗakin sannan ta ɗago. Gaskiya ba ta yiwa Abdallah adalci ba, since they one da su ka dawo gidan nan ya ke nuna ma ta kulawa. But then ya za ta yi da ran ta. Her heart felt nothing for him, nothing except what a sister feels for her brother. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da karatun da ta ke kafin ya shigo ɗakin.
"Da gaske dai Hudu ya fi ƙarfin ka" Nafy ta faɗa tana dariya. Harara ya watsa ma ta sannan ya wuce. Ya sani idan da ace Hajiya ta supporting ɗin sa ba zai sha wahalar samun soyayyar Lubna ba. Sai dai kash Hajiyar ta sa wata iriyar mace ce mai shegen kafiya akan abin da ta sa a gaba. Ya zubda hawaye a gaban ta ba sau ɗaya ba duk dan kawai ta amince da Lubna amma ta ƙi. "Wallahi ban yafe ba idan har ka auri Lubna" kalaman ta kenan a duk lokacin da ya je roƙon ta.
Gaskiyar Mama da ta ce ma ta sai ta toshe kunnuwan ta akan maganar Hood, idan ba haka ba kullum tana cikin damuwa dan daga yanzu har Allah ya sa a yi bikin su Hajiya da Nafy ba za su dena yaɓa ma ta magana akan Hood ba.
Yanzu ma indomie ta dafa za ta bar kitchen ɗin Nafy ta shigo.
"Lale matar Carpenter. Ki na ta nan ashe" Lubna ta harareta za ta wuce ta sake cewa " Na ji ance yau Hudu zai zo amma banga kin shirya komai ba. Ko abin sirri ne?" Kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta juyo ta ce " dont you get tired? Dddddda safe kkkkin yi magana na yi shiru, da rana haka. Ba ki da aiki ne sai zance na dddda Hood?"
"Allah ya ba ki haƙuri matar Hudu" sai kuma ta fashe da dariya. Lubna ta girgiza kai ta wuce ciki.
Ta na shigowa ɗaki ta ajiye plate ɗin hannunta tareda jan dogon tsaki. Wai yaushe Nafy za ta fita a hancinta ne. What's the big deal idan za ta yi soyayya da Hood? Ta bi ta damu mutane da zancen ba dare ba rana. A irin gulmanta ta kira Khair ta gaya ma ta komai. Jiya sun kwashe minti talatin su na jayayya da Anty Khair ɗin akan maganar Hood, har ita ma Khair ɗin ta ke ganin ta tafka shirme.
" yanzu Auta da Abdallah gara mi ki wancan baƙin?" Khair ta tambaya.
"Ni ma baƙa ce ai" amsar da ta bata kenan. Haka su ka yi ta ja inja ƙarshe Lubna sai katse kiran ta yi. Babu tamtama ta san Nafy ce ta turawa Khair hoton Hood ɗin idan ba haka ba ya aka yi ta san shi ɗin baƙi ne.
"Kin sa abincin a gaba sai ya yi sanyi ki ci kenan?" Mama ta faɗa lokacin da ta fito daga banɗaki.
"I lost my appetite"
"Nafy ko?" Maman ta tambaya ta na zama a bakin gado.
"It's been two days Mama amma koyaushe ta ganni sai ta tsokaleni, i feel like punching her ssssstupid face"
"Na gaya mi ki dama sai kin toshe kunnuwan ki. Dan tsokala kam sai ma anzo hidimar biki"
"Mama ba yanzu za mu yi aure ba fa, sai na gama service"
"Haka ya ce mi ki?"
"No, amma haka na ke so"
"Allah ya nuna ma na"...
..............................
Duk yadda Alhaji yai akan ya zauna a kujera ya ƙi. Haka ya zauna opposite da Alhajin akan carpet. Kan sa a ƙasa su ka gaisa kafin Alhaji ya fara jawabi.
"Hudu na kira ka ne domin na ji ta bakin ka, wani shiri ka ke yi gameda Lubna?"
Shi yanzu mi zai ce? abinda tun text ɗin da Lubna ta ma sa sai kuma kiran sa da ta yi ta ce Alhaji na neman sa ba su samu zama da Lubna sun tattauna akan komai ba.
"Ina sauraron ka"
Ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ce " dama ina so zuwa ƙarshen watan nan ne sai na turo su kawu ayi maganar"
"Lokacin da ka aiko da tambayar izinin hira da Nafisa na ji daɗin abinda ka yi haka nan na yaba da halayen ka. Sai dai Lubna amana ce a gareni, yadda na ke ji da ita a raina ko Nafisa da ta ke 'yata ba na jin ta haka. Dan haka ne ma ba zan yi wasa da al'amarin auren ta ba"
Hood yai ajiyar zuciya yana kallon Alhaji.
" tsakani da Allah ka ke son Lubna ko dai akwai wata manufar a ƙasa?"
Wace irin tambaya Alhaji ke yi ma sa haka. Abinda zuciyar sa ta faɗi kenan kafin ya iya furta.
"Tsakani da Allah na so Nafisah, na juri zuwa wajenta domin nemawa kai na matsayi a zuciyarta sai dai kash, duk iya watannin da na ɗauka ina zuwa ban samu soyayyarta ba, ƙarshe ma ta sallameni. Na tafi da niyyar ni da Nafisa sai dai ko a lahira amma ba ni ba ita. Sai kuma Lubna ta shigo rayuwata, ban san Lubna 'yar uwar Nafisa ba ce sai da zan kawota gida bayan aikin da mu ka yi sai na ga ashe a gidan su Nafisa ta ke kuma ma wai 'yar uwar ta ce. Na yi ƙoƙarin nisan tar kai na daga gareta saboda alaƙarta da Nafisa sai kuma Umma ta nuna min hakan ba adalci ba ne. Mu ka cigaba da mu'amalar da ta haɗamu har daga ƙarshe na samu na gama ma ta aikin ta. A wannan lokacin sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin mu. Wasu lokutan na kan zargi kai na da son Lubna sai kuma na fasa ta hanyar tunasar da ni 'yar uwar Nafisa ce fa. Sai dai al'amarin zuciya sai a hankali. Ina son Lubna tsakani da Allah. Halayyarta da nitsuwar ta su suka rinjayeni gareta"
Alhaji ya ji daɗi da bai ɓoye ma sa komai ba sai dai can ƙasar zuciyar sa yana yiwa Hudu kallon kamar bai kai ya samu Lubna ba.
Lubnan sa da ya ke yiwa taken matar manya. Yana son Lubna ta ji daɗin aure, auren da ba za ta wahala ba. Kamar yadda yayarta ta ke America, itama ya na fata wanda za ta aura idan ma yana Nigeria to wani ne wanda ya zauna da ƙafafuwan sa, wanda zai riƙeta ba tareda matsalar ƙuncin rayuwa ba. Sai dai kuma Fatima ta fi shi gaskiya.
"Alhaji tunda ka damƙa min Lubna na ke kula da ita, iya shekarun da mu ka ɗauka tare na gane halayen ta kaf. Kuɗi ko kyau ko muƙami ba sa gaban ta. Tana son mutum mai ilimi tana kuma daraja mai ilimi, duk min talaucin sa ko munin sa. Hudu yana da ilimi, yana ɗaya daga cikin abinda ya ja hankalin Lubna gareshi. Za ka sha mamaki idan na ce ma ka za ta zauna cikin farinciki tareda Hudu fiyeda yadda za ta yi idan Abdallah ko wani mai kuɗin ta aura. Kuma tunda dai Hudun nan yai karatu kuma yana da sana'ar sa, mi ye zai sa mu ma sa kallon ƙasƙanci. Ba wanda ya san gobe fah"
Ya tuna kalaman Mama gareshi wadda a koda yaushe ta ke ƙara nusar da shi gameda al'amuran rayuwa.
"Yanzu mi ka ke da shi a ƙasa idan na ce zan baka 'yata Lubna?"
Bai gane tambayar ba dan haka ya ce " Afuwan Alhaji ban gane tambayar ka ba"
"Ina nufin za ka iya auran Lubna nan da wata uku?"
Wani ras ya ji a ransa. Bai taɓa kawowa Alhaji zai ma sa maganar aure ba, shi ya fi tunanin ma haƙuri zai ba shi akan ya rabu da Lubna.
Da ƙyar ya tattaro nitsuwar sa sannan ya ce " Ba na aikin gwamnati amma da sana'ar da na ke yi da buga-buga da na ke yi yauda kullum, Alhamdulillah akwai rufin asiri kuma na tabbata zan iya aure, na kuma ciyar da iyalina a ciki"
"Lubna ta na son karatu, kafin na ba ka 'yata sai ka min alƙawarin za ka barta ta ci gaba da karatu a duk lokacin da ta buƙaci hakan, ban ce ka ɗau nauyi ba, dan na san yau da gobe sai a hankali amma idan ka bata izini ni zan ɗau nauyin komai. Tsoro na kar ta bige da boko kafin aure a kai gandun da za ta ƙi auren gaba ɗaya shi ya sa zan yarda ta yi aure kafin ta cigaba da karatu. Ka gantan nan son bokon jaraba gareta"
Hood yai murmushi ya ce " Insha Allah Alhaji, Lubna sai ta ce ta gaji da boko amma ba zan hanata ba"
"To shikenan ka turo magabatanka mu tattauna. Allah ya shige ma na gaba"...
Idan aka ce zai iya kai kan sa gida a wannan yanayin zai muzanta. Yana tafiya gidan nasu na ƙara ma sa nisa a ido. Sau biyu ya na kusa buge mutane saboda irin gudun da ya ke fanfalawa. Ji ya ke kamar a wata duniyar ya ke. Shi Hudu ake maganar ya turo iyayen sa a ɗan ƙanƙanin Lokaci da su ka haɗu da Lubna wanda bai fi wata ɗaya da wani abu ba. Shekaru nawa su ka kwashe da Asiya su na soyayya magana ba ta yi zafi haka ba, ga Nafisa wanda shima yai ta sintiri a kanta kusan wata tara, sai Lubna wanda bai taɓa kawowa zai so ta ba balle auren ta. But then everything is moving fast. Yadda soyayyarta ya shigeshi farat ɗaya haka nan maganar aure ya shigo ciki gadan-gadan...
..............................
A maimakon auren Nafy da aka tambaya a Bauchi wannan karan Ningi Alhaji ya je ya samu 'yan uwan na sa inda anan magabatan Hudu su ka samesu. Alhaji Abdullahi dai ba yadda ya iya ne tunda Alhaji Hassan ya fahimtar da shi Lubna tana son Hudu amma har ga Allah ya so ayi 'yar gida, a haɗa mai sunanshi da Lubna. Musamman da Abdallah ya kawo ma sa kukan shi akan Lubnan kwanan baya. Sai dai kamar yadda Alhaji Hassan ɗin ya faɗa. Idan su ka aurar da Lubna ga Abdallah to sun yi son zuciya kuma kamar auren dole su ka ma ta, hakan kuma na dai-dai da sun ci amanar marigayi.
Dubu arba'in su ka bayar sadaki wanda tun daga nan su ka fara ganin alamun kamar talaka Lubna za ta aura. Saɓanin Nafy da aka kawo dubu ɗari a matsayin sadaki.
Wannan abu ya ƙara kawo habaici da dariya wa Lubna. Nafy har cewa ta ke da Lubna ta bashi dubu goma cikin kuɗin ta ya cikata sadaki dubu hamsin za a fi ganin sa da ɗan daraja. Lubna ba ta damuba ita damuwar ta auren da aka sa tareda Nafy that means very soon za ta zama Mrs Hudu Umar Hudu. Da ta yiwa Hood complain akan ya bari ta ƙare service tukunna sai cewa yai " Lulu na jima a matse fa haƙuri kawai na ke yi da azumi da ke taimakona" ba ta gane maganar sa ba sai ma cigaba da roƙon sa da ta ke yi. Shi kuwa ya ce bai ƙi a ɗaura mu su aure a ranan ba.
Da farko Hajiya ba ta ankara rana ɗaya aka yanka bikin Lubna da na Nafy ba sai daga baya. Ai kuwa ta tada jijiyar wuya akan ba zai yiwu ba, dole ko dai a fara na Nafy kafin Lubna ko kuma ayi na Lubna kafin na Nafy amma ba za ta yarda ayi rana ɗaya ba. Alhaji yai biris akan ba za a janye ba. Akan haka har ƙara ta kai Ningi sai dai chan ma ba wanda ya goya ma ta baya sai ma cewa da su ka yi da Lubna da Nafy duk ɗaya ne ba abinda zai sa a raba bikin su.
Sau uku Hood ke zuwa hira a sati wanda ba wani jimawa ya ke yi ba saboda gudun sheɗan. Akwai ran da ya zo lokacin ta ƙarɓo result ɗin ta tana nuna mi shi feeling very excited. Ya ƙura ma ta ido ya na ji a ransa kamar yai kissing ɗin ta he almost did. A lokacin har sheɗan na raya ma sa ka fa biya sadaki ai ba matsala sai dai yai saurin ɗauke tunanin a ransa. Lokacin da ya ƙarɓa result ɗin haka ya haɗa da hannunta ya riƙe ya na kallo. Ranan dole ba shiri ya tafi saboda yadda yakejin tsananin sha'awarta a Lokacin. Su biyu ne a falon Alhaji su ke hiran dan Alhajin baya gari. Tun daga lokacin ya chanja tsari saboda sheɗan babban munafuki ne kawai dan an bada sadaki sai ya dinga kissimawa mutum ai yanzu an zama ɗaya aure ne kawai ba a ɗaura ba za a iya yin wasu abubuwan. Yadda yai haƙuri ya jure iya shekaru dan dai lokaci kaɗan da ya rage a kawo ma sa amaryar sa zai yi haƙuri.
A ɓangaren Lubna kuwa jin abin take daban, wai ita ce za ta yi aure. The only good thing shine a kullum ƙara ƙaunar Hood ta ke yi dan ba za ta ce So ba tukunna. She still insist that she only like Hood not love.
Suma chan iyalen Alhaji Inuwa shirye-shiryen biki ake yi na Walidah da Suhail a ɓangaren Suhail Alhaji Inuwa shi ne komai na shi sadaki shi ya biya gidan da za su zauna shi ya bayar kuɗin da ake haɗa ma sa lefe shi ya bayar ba abinda ya assasa da kan sa to mi zai yi shida ko aiki bai fara ba.
Walidah kam kullum lalacewa ta ke yi, har lokacin tsanar Usman ta ke gashi ƙarin haushin ma shi Usman dama mai tsatstsauran ra'ayi ne. Tana ji ranan Abba ya na yiwa Ummi magana akan wai Usman ya nace akan wai gidan da ya ke ginawa za su zauna duk da kuwa ba a gama ƙarasa gidan ba, wai idan ta shigo a hankali za a gama komai. Bayan da Abba ya ce gidan sa da ke new GRA za su zauna. Idan ta je school ta ga Nafy kaman ta je ta shaƙeta ta ke ji. Wai saboda ita Suhail ya ƙi ta. Gaba ɗaya ba ta wani shiri a bikin. Yayun ta da ƙannenta kaɗai ke rawar ƙafa a kai. Ita kam da Abba zai janye wannan haɗin da sai ta fi kowa farin ciki a duniya.
............................
Tunda maganar Hood da Lubna ta kankama Lubna ta kasa zuwa gidan su, ta kan dai kira Umma su gaisa amma ta kasa zuwa. Sai lokacin da za ta tafi camp inda aka turata Kaduna Mama ta ce ta je ta mu su sallama. Unlike before da ta ke sakewa a gidan yanzu kam da ta zo kunya ya hanata sakewa da su. Ita abinda ya bata mamaki ma shine yadda ƙannen Hood ke nuna tsananin farin cikin su akan wai yayan su Hood za ta aura, jin ta su ke kamar 'yar gold...
"Har yau dai ba ki iya gyara gado ba ko?, idan kun fito daga camp ɗin nan dole mu fara training ɗin ki daga nan"
Da fushi-fushi shagwaɓa-shagwaɓa Lubna ta ce " Mama to ke ɗin ne gyaran gadon ki kamar idan an gyara ba za a kuma kkkkwana a kai ba"
"Dama ta ya za a bar gado a yamutse. Matsa ki gani da kyau ki koya" ta ƙarɓi bedsheet ɗin daga hannun ta. Lubna ta rungumeta ta baya tana cewa " Mama I will miss you alot, har sati uku zan yi ba tareda ke ba fa"
"Za a zo ayi rabuwan da za a jima ba a ga juna ba ai"
"A'a nikam kullum sai na zo"
"Hudun ne zai barki?"
"Mama ni kam....."
.................. ................
Lubna na camp aka kawo lefen Nafy. Akwatuna shida ne da manyan jakukkuna biyu. Ranar kar kaga Nafy ba ki har kunne. Mama kam ta sha habaici musamman da aka gama baje kayan aka gani aka kuma tabbatar da an narka kuɗi wajen siyan kayan. Cikin lefen harda sarƙan gold guda biyu. Mama kam ko a jikinta a kullum addu'ar ta yadda ta ke ji a jikin ta Hudu alkhairi ne ga Lubna Allah ya tabbatar da hakan.
Kawo lefen Nafy da sati ɗaya wanda har lokacin ba a dena zuwa ganiba. Nafy ta ce da Mama da ke goge falo "Mama da yanzu kin bari Lubna ta amince da Ya Abdallah da lefen da zamu haɗa mi shi sai ya fi nawa. Inaga Hudu Carpenter idan ya iya biyan sadaki ba lallai ta samu lefe ba" maganar ta yiwa Mama zafi amma ta dake kamar bai dameta ba ta ce " tunda Hudu ya biya sadaki ai Alhamdulillah. Sauran abubuwan idan bai da halin yi mun yafe dan mu ba kayan da zai tsole ma na ido"
"Sai a kaita da kayanta na gida kenan, tarkacen jeans da Tshirt da ta ke sawa"
"To Nafy mi ye a ciki? Ina dai ashi za ta yiwa kwalliyar"
Nafy ta yi dariya ta ce " ni kam har yanzu ina jajanta abin nan, wai da gaske Lubna Hudu Carpenter za ta aura"
"Wai dan Allah na tambayeki Nafisa. Miye aikin Suhail?"
Nafy ta yi murmushi ta ce "a Malaysia yai karatu fa, aikin sa a sama, nan ba da jimawa ba. Ya na aure zai fara zuwa office"
"Sai me dan ya yi karatu a Malaysia. A'a ba Malaysia ba America ne. Ki dai nitsu ki kuma yarda, ko a yanzu Hudu ya fi Suhail daraja, tunda shi yai karatu kuma yanada sana'a har ma da sana'arsa ake ma sa inkiya. Suhail fa? har yanzu bashi da aikin yi sai garari. Cima zaune kawai. Na tabbata duk lefen nan da aka kawo ba sisin sa a ciki. Amma Hudu da gumin sa zai haɗo lefe koda kuwa akwati ɗaya ne. Which is indeed a sign of bravery" tana gama faɗin haka ta bar wajen, Nafy sai faman huhhura hanci ta ke yi dan ta ji zafin maganar mama...