Duk kyan Namiji

Chapter 19

by @azizat

*💮DUK KYAN NAMIJI💮*

............. ....👳.... ..............

0️⃣1️⃣9️⃣

Washe gari saboda gajiya ba ta tashi da wuri ba. Kusan shida da rabi ta farka. Nan ma ringing ɗin wayarta ne ya tasheta. Ta lalubo wayar ta ga numbar Ya Usman ke kiranta. Tsaki ta yi ta ajiye wayar sannan ta tashi ta shige banɗaki. Sai da ta yi sallah sannan ta fito daga ɗakin a hankali tana leƙe-leƙe. Wanka ta ke son yi kuma ba ruwan zafi. Gaskiya duk da ba wai sanyi ake ba ba za ta iya wanka da ruwan sanyi ba. Sai da ta fito falo ta fara bin tsarin gidan da kallo ko za ta ga ina ne kitchen. Caraf idon ta ya kai kan Usman da ke zaune akan kujera yana duba wani littafi.

"Amarya an tashi lafiya, na yi ta ƙwanƙwasa ƙofa ki tashi ki yi sallah ba ki ji ba"

Ta haɗe rai ta ce "ina ne kitchen?"

Da hannu ya ma ta nuni inda za ta bi. Kusan minti biyar sai ga ta ta dawo falon.

"Ina neman heater ko electric kettle"

Ya girgiza kai ya tashi ya shiga wani ɗaki wanda ta ke tunanin na shi ne. Sai ga shi ya fito da heater.

"Ki yi haƙuri Insha Allah zuwa sati mai zuwa za a gama gyaran kitchen ɗin ki" ba ta ce komai ba ta ƙarɓi heater ta shige ɗakin ta.

Tana wanka ta jiyo muryan Salma da Attahir ƙannenta. Tana ji su na tambayar sa ina ta ke, ya ce mu su tana bacci. Kafin ta fito ta ji suna ma sa sallama.

Da ta fito daga wanka ta shirya cikin wata atamfa ɗinkin riga da skirt wanda ya amshi jikinta sosai. Ba ta yi wani kwalliya ba sai ɗan powder da ta shafa da kwalli da ta saka a idon ta. Zama ta yi a kan gado tana duba hotonan biki da ƙannen ta su ka turo ma ta.

Sallamar sa ya ƙatseta ita ashe ta manta ba ta sa key a ɗakin ba. Ta amsa sallamar ƙasa-ƙasa wanda ba lalle ya ji ba. Bai buɗe ƙofan ba ya ce " su Salma sun kawo abinci, ki fito ki ci"

Yunwan da ta ke ji ya sa ko minti uku ba ta ƙara ba ta fita. A wajen dining ta samu warmers ɗin ta ɗau plate da ke gefe ta ebi iya abin da za ta ci ta wuce ɗaki.

Kwanan su biyar ba abinda ke shiga tsakanin su, ko ɗakin ta ba ya shiga iya kaci idan aka kawo abinci idan ba ta kusa ya mata magana daga ƙofa ta fito ta ɗeba abinci. Hidimarta daga ɗaki sai dining. Ba ta taɓa ko gaishe shi ba, shi ne idan su ka haɗu ya ke gaisheta amma still ba za ta amsa ba. Safe rana dare ake kawo mu su abinci. Abin mamaki ba ta taɓa kula da ya ake wanke kwanuka da warmers da ake kawo abincin a ciki ba. Ita dai ta ci abinci ta zo ta dire plate ɗin a inda ta ɗauka. Yau tana kwance ta ji shi ya na ƙwanƙwasa ƙofa. Kamar kullum uffan ba ta ce ba.

"Ki shirya da yamma za mu je mu gaida su Abba" ta ɗan ji daɗi ko ba komai za ta je taga 'yan uwanta.

Tun ƙarfe huɗu ta shirya tana zaman jiran sa amma sai biyar da rabi ya zo. As usual daga bakin kofa ya ce " Idan kin shirya ki fito mu tafi" ta tashi da sauri ta duba kan ta a madubi ta gyara fiskarta sannan ta fita, a falo ta sameshi yana danna waya ya sa ka jumpa ash color. Kamar wanda su ka yi haɗin baki itama shaddar da ta sa ash color ce, ji ta yi kamar ta koma ɗaki ta chanja kaya sai dai kuma ta matsu su tafi dan haka ta dake.

Already ya fito da motar sa daga garage dan haka. Su na fita shiga su ka yi bayan ya kulle gidan. Ba wanda ya ce da wani ci kan ka, sai da su ka iso gidan ya ce " bayan Isha za mu dawo" ba ta amsa ba ta fice daga motar ta shige gida ba tareda ta jira shi ba.

Sosai su Ummi su ka yi murnan ganin su, musamman da basuga wani alamar matsala a tareda su ba. Ƙarfe takwas da rabi Salima ta shigo ta ce wai inji Ya Usman ta je su tafi. Kamar ta kurma ihu haka ta ke ji. Ta dai daure ta fito.

A hanyar dawowa ma ba wanda yai wa ɗan uwan sa magana har su ka isa gidan su.

"Gobe za a fara aikin kitchen ɗin ki" ya faɗi lokacin tana shirin shiga ɗaki. Ba ta ce ƙala ba ta shige ta barshi tsaye.

Ƙarfe goma tana bacci bayan ta karya ƙaran buge-bugen Carpenter ya tasheta (🙄 dont tell me its Hudu Carpenter...Lol). Ganin ba halin komawa bacci ya sa ta fara chatting a wayar ta. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya ratsata lokaci guda bayan hotunan Pre-wedding pics ɗin Suhail da Nafisa da ta gani. Sun yi bala'in kyau tare, hankalin ta ya kai matuƙar tashi ƙarshe dai kashe wayar ta yi ta fara hawaye. Shi kenan ta rasa Suhail. Usman ya cuceta.

Ranan ko abincin rana dana dare ba ta fito ta ci ba. Wuni ta yi kuka har sai da idon ta su ka kumbura.

Tana ji kusan ƙarfe tara Usman na cewa ta buɗe ƙofa amma ta shareshi. Jim kaɗan sai ga shi ya shigo ɗakin, mamaki ƙarara a fiskarta ashe yana da key ɗin ɗakin amma idan ta kulle baya shigowa.

"Ki fito ki ci abinci" ya ce da ita fiskar sa ɗaure.

"Na ƙoshi" ta amsa ma sa da dashashshiyar muryan ta.

" tun abincin safe ba ki sake cin wani abu ba kuma ki ce kin ƙoshi"

"Ni ka bar min ɗaki" ta faɗa da ɗan ƙarfi.

A hankali ya tako har ƙarshen gadon inda ta ke duƙunƙune cikin bargo.

"Mi ya sameki?"

"Babu" ta faɗi tana ƙara matsawa gefe

"Kin san Allah Aisha idan ba ki tashi kin ci abinci ba zan saɓa mi ki."

"Ni ka barni ana cin abincin dole ne"

"Yau za ki ci na dole kuwa" fita yai daga ɗakin sai ga shi ya dawo da tray a hannun sa. Tea ne a Mug sai jollof ɗin shinkafa da ya ji kifi a plate. Ya ajiye a kan drawer da ke gefen gadon ya ce "tashi ki ci"

"Ni kam ka bar ni na kwanta dan Allah"

Ya rungume hannayen sa ya ce " duk take-taken ki tsoron kar na kusanceki ne ko. To wallahi idan ba ki tashi kin ci abincin nan ba, a daren yau zan maida ke mace" tana jin haka ta yaye bargo ta jawo abincin ta hau ci, shi dariya ma ta bashi. Sai da ta cinye ya kawo ma ta paracetamol ta sha sannan ya kwashe kayan ya fita da su. Ta jima tana tunanin ko zai dawo ɗakin amma har bacci yai gaba da ita ba ta gan shi ba.

Da safe ƙarfe bakwai ta fito falo ba ta gan shi ba dan haka ta wuce kitchen dan taga aikin da aka yi jiya. Tsaye ta gan shi jikin sink ɗin da aka sa yana wanke-wanke. Allah sarki ashe duk iya kwanakin nan shi ya ke yi. Ta ɗan matsa kusa da shi ta ce " kawo na wanke"

" ya ciwon kan?"

"Ya aka yi ka san kai na na ciwo?"

"Ba wanda zai yi kuka irin wanda ki ka yi kan sa bai yi ciwo ba"

" da sauƙi" ta faɗa a taƙaice. Ba ta matsa a wajen ba ta sa hannu ta fara tayashi yana wankewa tana ɗaurayawa.

"An gama kawo mana abinci da ake yi, mi za ki karya da shi ba yau?"

"Duk abinda akwai"

"gidan ki ne fa sai abinda ki ka so ki ci, ki faɗa idan babu shi a gidan sai na fita na siyo" ta ɗan yi murmushi wanda ya fitar da kyaunta sosai.

Sai da su ka gama wankewa ya ce ta nemi abinda za ta ci zai shirya kitchen ɗin tunda yanzu anyi kitchen cabinet.

Tana tsaye ya fara ebo kaya daga store yana jerawa. Tana tsaye tana kallo idan taga ya sa wani abu a wajen da bai dace ba ta ce "ya Usman kar ka sa a wajen ka sa a chan" ƙarshe dai itama sa hannu ta yi su ka shiga shirya kitchen ɗin tare, zuwa ƙarfe sha biyu kitchen ya fito sarai ya kyau.

"Barin je na yi wanka" ya faɗi tareda barin kitchen ɗin. A gurguje ta dafa mu su jollof ɗin spaghetti da macaroni da ya ji bushashshen kifi. Tana jerawa a kan dining ya fito sanye da jeans da shirt.

"Sannu da aiki Aisha" ya faɗi yana zama a kujera.

Aisha ya ke kiran ta tun da ta san shi, da shike shi ne asalin sunan ta.

Da ta gama jerawa ta ce "Ya Usman ga abinci"

Har ransa ya ji daɗin haka sannan ya ce " ke fa"

"Zan yi wanka tukunna"

"To zan jira ki"

Hakan kuwa aka yi sai da ta yi wanka ta shirya sannan su ka ci abincin a tare a dining table kowa da abinda ke tunani a ran sa. Ita dai tun jiya da ta yi kuka a kan Suhail ta sawa ran ta ƙoƙarin yakice son shi da ya mamaye ma ta zuciya. Nasihohin da Ummi ta mata da su ka je gida ya sa ta ke son haƙura da duk wani plan ɗin ta ta koyawa kan ta son Usman.

Da su ka gama,ta je ta wanke kwanukan sai da ta dawo za ta wuce ɗaki ya ce " Aisha zo nan" ba mu su ta dawo ta zauna opposite da shi.

"Tsakanina da ke ko ba aure akwai zumunci. Ina son ki Aisha fiye da yadda ki ke tunani. Ba zan tursasa mi ki ba amma dan Allah ki dena gudu na ni fa yayan ki ne. Idan kina tunanin ko akwai abinda zan mi ki. A'a i will wait har sai lokacin da ki ka amince mi ni. Dan Allah ki bar ƙunshe kan ki a ɗakin nan kin ji"

"To" ta faɗa a hankali

"Sannan ina neman alfarma, akwai abokai na da za su zo gobe, ko zan samu ki ɗan girka mu su wani abu?"

" Allah ya kawosu lafiya" ya amsa da Amin...

.................................

Saura kwana takwas a ɗaura aure Lubna da Khair su ka dawo Bauchi. Shirye-shiryen biki sai daɗa kankama ya ke yi. A da a Bauchi za a ɗaura auren saboda za'a haɗa dana Walidah to tunda an riga an yi nata sai aka maida ɗaurin auren su a Ningi.

Washegari da su Lubna su ka dawo aka kawo kayan auren ta. Akwatuna uku ne da kit. Kayan ciki kam ba ƙarya kaya ne masu tsada kuma na zamani na yayi, dan har su Khair sun yaba kyan kayan duk da bashida yawan na Nafy. Ita kam Lubna bai dameta ba, koda ta ji Nafy da Khair suna ta chachar baki akan dariyar da Nafyn ke yiwa kayan Lubnan ba abinda ta ce.

Ba abinda Lubna ta shirya yi a bikin banda Waliman da Mama ta ɗau nauyin za a yi. Ita kuma Khair ganin Nafy za ta yi bridal shower ya sa itama ta ce dole Lubna ta yi.

"Stop competing Anty Khair" Lubna ta faɗi lokacin da ta ke faɗawa Mama za a yi bridal shower.

Gadan-gadan biki sai matsowa ya ke yi. Yayinda ake ta buga gasan tsari tsakanin Khair da Nafy. Kowa so ya ke ya fi ɗan uwan sa kece raini. Ita Khair haushin Lubna ba za ta yi dinner ba ya sa dole su kece raini a wajen bridal shower duk da kuwa Lubnan ba ta da ƙawaye.

Saura kwana huɗu aure aka je aka yiwa amarya Nafy jere a gidan ta da ke railway. Gidan ya haɗu ba laifi, falo ne haɗe da master bedroom sai wasu ɗakunan guda huɗu da kitchen da store. Farfajiyan gidan ba shi da wani girma dan ba zai ɗauki mota ya fi uku su shiga ba. 'Yan jere su ka dawo suna yaba gidan. Nan aka fara tambayar batun kayan Lubna inda Mama ta nuna mu su jeren kaya ba yanzu ba, shiyasa wasu abubuwan ma ba a siya ba sai daga baya. Wasu tsakani da Allah su ka ji tausayin Lubna yayinda wasu ke ta Allah ya ƙara tunda ita ta gani ta ji zata iya.

Rana ba ta ƙarya. Yau ne bridal shower, tun daga safiya 'yan mata da zawarawa da matan aure ke cincirindo a gidan. Sosai gidan ya cika. Duk da rasuwan da aka yi bai hana 'yan uwan mommy sun zo wannan biki ba, autar marigayiya Maryam guda.

Wata farar gown mai kyau Nafy ta saka. Ta bazo gashinta baya wanda ya sha gyara. Ta rataya wani baƙin ribbon wanda a jikin shi an rubuta *bride to be* da farin rubutu. Ƙawayen ta kam harda gayyan soɗi wanda su ka zo. Ankon pink material su ka yi. Wanda ba su samu yi ba ma sun sako pink saboda shine theme color of the day.

Amarya Nafy ta yi kyau ba ƙarya. A farfajiyar gidan aka shirya komai inda nan ma ba ƙaramin faɗa aka yi ba kafin Nafy da Khair su ka yadda za a yi komai tare a wajen...

Kasancewar Lubna ba mai kwalliya ba ce ya sa ainihin kyaunta ya fito lokacin da make up artist ɗin ta gama tsara ma ta kwalliya. Wani blood red designer dinner gown Lubna ta sa, wanda ba ƙaramin kuɗi Khair ta kashe ba wajen siyan shi a New york. Ta zo da shine da niyyar Lubna ta sa a wajen dinner ɗin ta, to kuma Malam Hudu ya ce ba dinner, ko anyi sai dai amarya ta je ita ɗayan ta.

Gashin Lubna ya sha ƙananun kitson bare-bari wanda jelar gaban ke taɓa ƙashin wuyan ta a duka gefe biyu. Wani sarƙan gold Mama ta sa ma ta a wuya wanda ya ƙara fito da kyan kayan. white shine kalar kayan ƙawaye da 'yan uwa na side ɗin Lubna wanda hatta Rahma ƙanwar Nafy wanda ta ke matsayin babbar ƙawa shi ta saka, tunda Lubna ba ta da ƙawaye, dama gayyar cousins ɗin su ne a wajen sai ɗaiɗaikun en makarantar su da su ke mutunci sama-sama.

Tuni Nafy da jama'arta su ka hallara a wajen da aka kafa tanti, yayinda kiɗa ke tashi da ƙarfi a wajen. Domin DJ Joyce su ka adana a wajen.

Ƙannnen Hudu kaf ɗin su sun zo harda wasu cousins ɗin sa en ƙauyen Kangere, da ma na cikin birni. Kowa ɗokin ganin amaryan Hudu ya ke, saboda ance Hudu 'yar gayu zai aura. Kuma sun tabbatar da hakan tun daga ƙofar gidan su, balle da su ka shigo gidan su ka ga irin mutanen da ke ta shige da fice a ciki. Tun lokacin ana yiwa Lubna kwalliya su ka zo, tun a lokacin Aminah ta ɗauki hotunan Lubna ta fara turawa Hudu. Da aka gama kwalliya ma aka sha hotuna tareda su. Su na ɗan kaffa-kaffa da wasu cousins ɗin Lubna da ke mu su wani gani-gani. Da ke Lubna ta gaya mu su white za a sa ya sa kowanne a cikin su ya sa fari ko kuma dai kowacce akwai wani abu fari a jikin adon da ta yi. 

Minti shabiyar bayan fitar su Nafy wajen taron sannan Lubna da tawagarta su ka fito. Kasancewa ba ta saba saka high heel shoe ba, ya sa ta ke taku a hankali dan tsoron faɗuwa. Takun ya ƙara ma ta swags, su Batool da Aisha na gaban amarya su ma cikin shigar white su na burbuɗa flowers a wajen da Lubna za ta taka yayinda 'yan biyun Mama Usman da Umar ke recording komai a video, suma kuma shigar farar shadda su ka yi. Abin ya ba da kala sosai. Tunda su ka nufo gurin wajen aka ɗauka tafi da shewa abinka da taron mata. Yadda Nafy ta ƙwalalo ido waje ka ce idon za su faɗo ƙasa. Wani turnuƙin kishi da baƙin ciki duk ya haɗu ma ta lokaci guda. Na farko ita kanta gown ɗin Lubna ya tafi da ita, ga shi kasancewar Lubna baƙa kalar kayan ya amsheta sosai. Na biyu ita ta sa white yayinda tawagar Lubna su ka saka fari, kenan ta shiga cikin su itama. Idan ba dan ribbon ɗin bride to be da ke jikin ta ba sai ka ɗauka itama 'yar bayan Lubna ce. Suna haɗa ido da Khair ta kashe ma ta ido. Hawaye ne kawai ba ta yi ba ta daure ta cigaba da murmushin yaƙe dan kar a gane ɓacin ranta. Sai da aka zaunar da Lubna a kujerar da ke gefen ta sannan ta ce "wato cin fuskan da za ku min kenan, kun san fari zan sa amma ku ka ce a sa fari"

"I dont know yyyou are wearing white until now"

Lubna ta amsa ma ta. Tsakani da Allah ba ta sani ba saidai Khair ta sani, kuma dalilin cewa a sa white kenan.

Khair da Harira ne MC a wajen idan. Abin ya bada kala sosai, an yi dancing competition, kitchen game, fashion,rapping competition da question and answers kafin a ka zo aka fara bada gifts. Dakarun Mama wato Umar da Usman su suke tsaye wajen da ake ajiye gifts ɗin Lubna saboda gudun sata. Duk wanda ya zo zai faɗi sunan sa da alaƙar sa da amarya. Wasa-wasa sai ga gifts ɗin da ake ajiyewa Lubna suna ninka na Nafy a yawa. Fiye da rabin 'yan uwan Alhaji a wajen Lubna su ke ajiye gifts ɗin su, tausayin Lubna su je ji tunda ance mijinta talaka ne. Ƙawayen Mama ma wajen Lubna su ke ajiye gifts ɗin su. Wata ƙawar Mama bayarabiya Hajiya Latifat ta ajiye sinkin doya guda biyu ta ce amarya ta dakawa angonta sakwara da shi, gaba ɗaya wajen aka kwashe da dariya. Sai ga shi da aka gama ajiye gifts, na Lubna ya ninka na Nafy sau biyu. Harta wajen da ake ajiye kyautar kuɗi, Lubna na da envelope guda sha takwas ita kuma Nafy na da sha biyu. Hajiya kan ta jikin ta yai sanyi ba ta tsammanci 'yan uwan Alhaji za su ma ta haka ba su ka nuna sun fi damuwa da Lubna, ga uwa uba 'yan uwan Lubna na Yobe da ba ƙaramin kara su ka mata ba. Aka ci aka sha, Amaren biyu su ka fito su ka ɗan taka wanda Nafy rawan ta ke amma zuciyarta kamar zai fito saboda baƙin ciki.

Tun daga ƙarfe goma na safe sai ƙarfe biyu na rana aka gama taro inda mutane su ka tafi kowa da souvenirs da aka raba a wajen...

Ranan Jumu'ah aka yi walimah a haraban gidan inda Malama Juwairiyya ta wa'azantar ta kuma faɗakar.

Rana ba ta ƙarya yau ta ke asabar kuma ranan ɗaurin aure. Tun da sassafe mazan gidan su ka wuce Ningi. Abdallah dama tun da aka fara hidiman biki ya tafi Ningi. Cikin gida kam tun da safe aketa ɗaura sauke na abincin da za a ci da ya ke akwai reception da za ayi a Bauchi da zaran an gama ɗaura aure...

Jin sa ya ke tamkar a mafarki wai yau ɗaurin auren sa. Ba abinda ya ke hangowa irin tsantsagwaryan soyayyar da ya shirya narkawa Lubna a zaman su na aure, irin soyayyar da ya ke muradi da kuma fatan yiwa duk macen da ya aura. Duk wani tsare-tsaren tafiya an yi shi wanda ƙarfe takwas na safe su ka kama hanyar Ningi don halartar ɗaurin aure...

Tana kallo a falo ya fito sanye da jumper kalar sky blue. Yana gyara zaman hular sa ya ce "Aisha bari mubwuce ɗaurin aure ko"

Yai kyau ba ƙarya hakanan shigar ta fito da shi sosai.

"Dan Allah Yaya Usman kar ka je" ta faɗi kamar za ta yi kuka.

Kallon mamaki ya bita da shi, cikin sati ɗaya zaman su ya chanja tana ma sa girki, sannan su ci tare idan yana gida. Hakanan su kan zauna su yi hira sama-sama musamman idan suna zaune a falo su na kallo. Tun jiya da ya ce ma ta zashi Ningi ɗaurin auren Suhail ya ga yanayin fiskarta ya chanja.

Sai da ya zauna daf da ita sannan ya ce " miya sa bakya so na je?"

" ba komai" ta faɗi tana maida kallon ta ga TV.

"Saboda ɗaurin auren Suhail ne?"

Ta yi shiru

"Ki yi haƙuri, kinga Suhail ya zo ɗaurin aurena bai dace ace ni na ƙi zuwa na sa ba. Kuma Abba ba zai ji daɗi ba yanzu haka ni su ke jira mu wuce"

"Shi kenan to" ta faɗi tana sauke ajiyar zuciya.

Murmushi yai ya ce "rufe idon ki"

Ta tsaya kallon shi.

"Rufe mana Aisha tah" wannan karan sai ta rufe.

A hankali ya matso sosai kusa da ita ya mata light kiss a lips ɗin ta. Haɗuwar da lips ɗin su yai ya sa ta buɗe ido da sauri.

Kashe ma ta ido ɗaya yai duk sai kunya ya kamata. Ta tashi zata bar falon da gudu ya riƙo hannunta ya ce "ki kular min da kan ki"...