Chapter 20
by @azizat
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣2️⃣0️⃣
Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi aka ɗaura auren *Hudu Umar Hudu* da amaryar sa *Lubna Hussain* bisa sadaki naira dubu arba'in sannan aka ɗaura auren *Suhail Adam da Nafisah Hassan* bisa sadaki dubu ɗari. Ɗaurin auren da ya samu halartar manyan mutane daga ɓangaren Alhaji Inuwa da kuma Alhaji Hassan. Daga wajen ɗaurin aure aka wuce Bauchi don reception da za a yi.
Da gudu Rahma ta faɗo ɗakin Mama tana faɗin 'an ɗaura an ɗaura' yanzu Aabid ya kirani wai an gama ɗaurin aure.
Lubna na duƙunƙune kan gado wai kan ta ke ciwo. Maman ma ba ta ɗakin tana wajen jama'a ana ta hada-hadar yanda abincin da ake shiryawa zai tafi dai-dai.
Tuntuni Hood ya turo ma ta text *Alhamdulillah, officially Mrs Hudu Umar Hudu*
Rahma ta matsa gefen ta "ya dai amarya? Lafiya?"
"Jjjjust headache" ta amsa tana dafe kan ta.
"Barin kawo miki pracetamol toh"
Sai da ta fita a ɗakin ta sauke ajiyar zuciya hiran su da Khair daren jiya yana sake dawo ma ta. So yanzu duk abinda Khair ke koya ma ta za su dinga yi da Hood. Anya za ta iya? Ta tambayi kan ta...
Da shi ke ba wani hidiman da Lubna za ta yi ya sa ƙarfe shida aka yanke za a kaita saboda ma su shirin zuwa dinner da za ayi ƙarfe takwas na Nafy da Suhail. Motoci biyar ne su ka zo ɗaukan amarya. Sai da Mama ta gama ma ta addu'a sannan a ka wuce da ita ɓangaren Alhaji, a taƙaice ya mata nasiha inda ta dinga kuka saboda tunowa da Daddyn ta da ta yi. Da aka zo shiga mota da ƙyar aka raba ta da Mama saboda dukkan su kuka su ke yi. Ita kan ta Mama ba ta yi niyyar kuka ba sai dai yadda Lubnan ke ta kuka ya sa itama ba shiri ta fara hawaye. Ko lokacin auren Khadija ba ta ji irin haka ba. Lubna ta riga ta zama jinin jikin ta. Allah ne kawai ya ƙaddara ba ita za ta haifi Lubna ba amma soyayyar da ta ke ma ta soyayya ce ta uwa da 'yar ta.
Cikin mota Lubna na tsakiya sai Khair da mommy Sanah ƙanwar mommyn su. Ana tafiya Khair na ƙoƙarin bata haƙuri akan ta dena kuka musamman da ta tuna babban dalilin kukan na ta saboda rashin Daddy da Mommy ne a rayuwar su. Ita kan ta daurewa ta ke yi saboda kar ta nunawa ƙanwarta rauni amma da tuni ta fashe da kuka.
A haka aka kai amarya ɗakin ta. Wanda ciki da falon da Baban Hudu ke amfani da shi ne ya fita ya bar mu su, shi Hudu bai nemi hakan ba sai dai Baba da Umma ne su ka ga hakan yafi dacewa tunda dai ciki da falo zai wadacesu na ɗan zaman da za su yi fiyeda ɗan tsuguryar ɗakin sa da ya ke son su zauna a ciki da.
An shigar da amarya ɗakinta wanda ba wani tarkace ne a ciki ba. Gado ne a ciki wanda Hudu ya saka sabuwar matras a kai. Da kunya ace gadon da Baba da Umma su ka.....(ni dai ban ce ba😀)...
Sai da aka ɗan ma ta nasiha aka gaggaisa da mutanen gida sannan aka bar amarya da ƙawayen ta ko na ce en uwan ta. Cousins ɗin ta uku ne su ka tsaya za ayi sayan baki da su kafin su tafi saboda yawanci suna chan gida ana shirye-shiryen tafiya wajen dinner.
Abokai sun zo da wuri dan bayan Isha su ka zo aka yi sayan baki sannan su ka wuce gida saboda tuni an fara tafiya wajen dinner ɗin.
Khair dai ta ce sai ta je dinner taga iyayin da za ayi a chan. Mama kam dama ba ta da niyyar zuwa alhinin rashin Lubna kaɗai ya isheta.
Ƙarfe bakwai na yamma Usman ya shigo gidan. Bai ganta a falo ba dan haka ya wuce ɗakin ta. Tana zaune kan sallaya tana addu'a ya shigo.
"A yi addu'ar da mu" ya faɗi tareda rufo ma ta ƙofar.
Sai da suna cin abincin dare a dining ta ce " Yaya ba za ka je dinner ɗin bane?"
"Ki na son zuwa ne?" Ya tambaya yana tsareta da idanu. Ta yi saurin cewa " A'a"
"To idan ba za ki je ba na je wajen na yi mene? Ko kin amince na je na zaɓo budurwa zugegiya"
Hararan sa ta yi wanda sai da ya fara dariya ta ji haushin hakan.
Ba su wani jima a falo kallo ba kowa ya shige ɗakin sa dan Usman ya nuna alamun gajiya.
Ta jima ƙofar ɗakin sa tana tsaye ta kasa ƙwanƙwasawa. Tun tafiyar sa Ningi ɗaurin aure ta ke fafatawa da zuciyar ta akan hukuncin da ta ɗauka wanda zai fishsheta.
*"Suhail ya yi aure zai zauna da matar sa su raya sunna cikin soyayya ba tareda ya ma tuno da wata Aisha Walidah ba, ta ya kuma ita tana da mijin za ta tauye ma sa hakkin sa ta riƙa kwasan zunubi a kan ta"* hiran da ta yi da zuciyar ta kenan.
A karo na uku ta daure ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. Daga ciki ya ce " yes come in"
Jallabiya baƙa ce a jikin shi yana tsaye kan darduma, da alama sallah zai yi dan ga alamun ruwa a fiskar sa.
Ganinta ya sa shi murmushi ya ce " Lafiya Aisha?"
" shi ne yaya nima ba za ka kirani mu yi nafilar tare ba" ta faɗa a shagwaɓance.
Ya lumshe ido ya ce " ki na son mu yi sallah tare ne?"
"Da alwalata na zo" ta faɗa a ɗan kunyace...
Sai da su ka idar da sallah raka'a biyu yai mu su addu'o'i sannan ya tashi, wayar sa ya ɗauka ya ce " sai da safe Aisha tah"
Har ya kai bakin ƙofa ta ce " Yaya kuma ni kaɗai zan kwana anan ɗin" chak ya tsaya yayinda farin ciki ya mamaye shi lokaci guda, dama ya gwada ta ne ya ga ko hasashen sa gaskiya ne.
Da sauri ya dawo kusa da ita ya ce " da gaske kin amince da ni Aisha?"
Ta rufe idon ta da dukkan tafukan hannunta tana murmushi...
..............................
Ƙarfe goma Hudu ango ya shigo ɗaki cike da farin ciki da annashuwa. A takure ta ke chan ƙuryan gado lokacin da ya shigo ɗakin tun tafiyar su Aneesa ta tashi ta yi sallah ta takure a wajen. Tsoro da fargaba su ka cika ta. A hankali Hood ya ƙaraso wajen da ta ke ya tsuggunna yana kallon yadda jikinta ke ɓari.
"Finally my Mrs me"
Dariya maganar ta bata amma tsoro ya sa ta kasa yin komai.
Ya jawo hannunta guda wanda ya sha ƙunshi ya manna light kiss a wajen ya ce barin ɗan watsa na yi alwala ko. Ido ta ƙwalalo jin maganar alwala. So maganar Khair ta tabbata. Ta yi saurin jawo wayarta lokacin da ga shiga banɗaki ta danna numbar Mama.
Mama da ke bacci wanda ba ta jima da baccin ba wayarta ya shiga ƙara. Ta sa hannu ta lalubo wayar ta ƙara a kunne.
Jin muryan Lubna ya sa ba shiri ta tashi zaune " Innalillahi! Lubna mi ya faru?"
Muryan Lubna na rawa ta ce " Mama i'm scared, Anty Khair ta ce its a little bit painful. Mama please tell him not to do anything today. I'm not ready" ta ƙarashe maganar tana share hawaye.
"Kai Lubna da wauta ki ke ai sai ki sa na samu heart attack da irin wannan kira"
"Mama plz"
"Kinga, ki saki ran ki ba komai, duk abinda Khair ta gaya mi ki ki mance da shi ki yiwa mijin ki biyayya kin ji"
"Mama is it really painful?"
"No" Mama ta faɗi kai tsaye dan ta san matuƙar ta amsa da eh to yau Hudu ya shiga uku da kuka.
Sai da ta tabbatar da hankalin ta ya kwanta sannan ta kashe wayar.
Sanda Mama ta ajiye wayar wani nannauyan ajiyar zuciya ta sauke dan duk da ta san irin tarbiyan da ta yiwa Lubna amma duk da haka ganin kiran ya tada ma ta da hankali.
Sanye da Jallabiya fara ya fito daga bayin wanda har lokacin tana takure a kan gado zuciyar ta fal da wasu-wasi. Ga dai abinda Khair ta faɗa ma ta gashi kuma Mama ta ƙaryata hakan.
Gyaran muryan da yai ne ya fargar da ita. Ya ƙura ma ta ido yana kallon yadda ta ke zaune a firgice.
Ki tashi ki yi alwala.
" na yi sallah" ta faɗi da sauri.
Takowa ya farayi yayinda jikinta ya fara rawa. Sai da ya zauna kan gadon ta fara wiki-wiki da idon ta.
"Mi ya sameki?, why are you acting like you just saw a ghost?"
"Please Hood dont do anything, i'm not ready"
"Ban gane ba?"
"Dan Allah i know we are mmmmarried now but i still need time to get uuuused to all of this"
"Lubna" ya faɗa da salo mai kashe zuciya. Ya kai hannu zai taɓata ta yi saurin matsawa gefe tana hawaye. Da ya ƙara matsawa sai gashi ta ɓare baki tana kuka.
"Na shiga uku ni Hudu! Lubna mi ye haka?" Ba ta kulashi ba ta cigaba da kukan ta. Ganin da gaske ya ke yi ba shiru za ta yi ba ya sa shi cewa " shikenan ki ba abinda zan miki. Barin shigo mi ki da abinci sai ki ci"
"Na ƙoshi" ta faɗa da muryan kuka.
Hakanan ya ɗau sallaya ya ma ta saida safe ya fita.
(Mrs Hudu Umar Hudu, you better stop this nonsense ko kuma ki ga fushi na ehen🙄)
Washe gari da safe ya shigo ɗaki su ka gaisa, sai da su ka karya tare sannan ya fice a gidan saboda har lokacin akwai sauran en biki da ba su tafi ba.
Su Aminah ne su ka tayata zama suna tayata ƙarɓan baƙin da ke zuwa gaisheta both en uwa, en unguwa da en gulma.
A bangaren amarya Walidah ma daren jiya sun raya sunnah da angonta. Lokacin da ta tashi sai wani nan-nan ya ke yi da ita, shi da kan sa ya haɗa ma ta ruwan zafi ya taimaka ma ta tayi wanka. Daga ƙarshe ya je ya haɗa mu su breakfast ya kawo. Ita kam gaba ɗaya kunyar sa ta ke ji. Ko da kaɗan ne ta san yanzu kam Usman ya samu matsayi a ranta wanda da sannu za ta koyawa zuciyarta son shi da kuma kyautata mi shi.
Amarya Nafy an yi dinner lafiya sai dai ta ji haushi da Alhaji Inuwa da kuma Alhajin su ba su halarcin dinner ba. Ta sa ran zuwan Alhaji Inuwa zai ƙarawa taron armashi saboda dole idan ya zo ƙusosin ƙasa da jaha su halarci dinner sai dai kash ba ta samu hakan ba.
Washe gari Lahdi aka yi launcheon daga ƙarfe sha ɗaya zuwa ƙarfe uku wanda abokan ango su ka haɗa. Wannan hidimar kam zallar en mata da samari ne su ka yi cincirindo a wajen.
Ƙarfe takwas motoci goma su ka zo ɗaukan amarya. Ba laifi amarya Nafisa ta ɗan koka Lokacin da za ta rabu da Hajiyar ta. Fal cikin ranta ta ke fatan su isa gida a watse a bar ta da angonta. Suhail mai kyau, su samu raya sunnah abinda ta ke buri a koda yaushe...
Ƙarfe sha ɗaya na dare Suhail ya shigo. Da 'yar gasasshiyar ƙazar sa. Bayan sun yi nafila raka'a biyu sannan su ka zauna su ka ci kaza da yoghurt. Idon amarya a buɗe ya ke dan haka ba ɓoye-ɓoye ko noƙe-noƙe ta fara amsa saƙon da angon ke aika ma ta, sai da ta birkita shi da wasanni sannan su ka shiga raya daren. Yanayin da ya ke ciki ya sa ta ɓoye mamakin ta bisa ɗan abinda ta gani...
Washe gari ƙarfe bakwai saura ta farka, ganin Suhail shame- shame a gefenta ya sa ta gane shi ma bai tashi ba tuntuni. Ta ɗan bubbuga kafaɗar sa wanda ya buɗe ido da ƙyar saboda baccin da ke cin sa.
"Heartbeat ka tashi lokaci ya tafi fa ba mu yi sallar asuba ba"
"Ma yi daga baya bacci na ke ji" ya faɗa da muryan bacci.
Ta cigaba da tashin sa amma shiru, ƙarshe filo ya ɗauka ya kwanta a ƙasa. Tana son tashi ta tsarkake jikinta musamman gaɓoɓinta da ke ma ta ciwo sai dai kuma ba ta son ruining dream na ta. Kamar yadda ta ke karantawa a ko wane novel ango shi ya ke ɗaukan amarya ya kai ta banɗaki ya gasa jikin ta haka itama ta ke da wannan mafarkin a ranta. To ko dai ta koma bacci ne itama har lokacin da zai tashi saboda kar ta rasa wannan dama wanda sau ɗaya ya ke zuwa wa mutum. Ta koma bacci wanda a zahirin gaskiya ba baccin ne a idon ta ba.
Ƙarfe goma da rabi aka fara buga gate ɗin gidan wanda ya jawo Suhail farkawa. Itama ɗin ta farka saboda bai fi awa ɗaya ba bacci ya saceta. Jallabiya ya sa ya fita. Daga gate ɗin ya ƙarɓi abincin da ƙannen sa su ka kawo ya shigo da shi. Ɗan banzan yunwa ya ke ji saboda aikin da yai daren jiya ya rarike ma sa ciki sosai. Kai tsaye ya ajiye abincin a tsakiyar falo ya ɗeba a plate ya fara ci.
Shiru-shiru Suhail zai zo bai zo ba kuma ta ji shigowar sa falo. Daga inda ta ke zaune akan gado tana zaman jiran tsammani ta fara ƙwala ma sa kira " heartbeat...heartbeat... Suhail" amma shiru ganin fa za ta iya dawwama a haka ya sa ta taso ta fito falon da leƙa shi. Mamaki ƙarara a fiskarta lokacin da ta ga Suhail ya tisa abinci a gaba yana ci.
"Heartbeat ko brush fa ba ka yi ba" ta faɗi tana ƙarasawa wajen sa.
"Idan na ci zan yi, kin san a chan turai haka su ke yi sai sun karya tukunna su yi brush"
"To ka gama ka zo ka min wanka"
"Dama tun tashin farko da kikayi ba ki yi wankan ba" ya faɗa yana tauna bredi.
"Kai na ke jira ka min"
Bai ce komai ba ya cigaba da cin abincin sa, sai da yai nak sannan ya tashi ya shige ɗaki itama ta yi saurin bin bayan sa. Da ƙyar da naci ya taimaka ma ta ta yi wanka wanda kusan komai ma ita ta yi da kan ta...
A bangaren Lubna dai ranan lahdi ma Hood a falo ya kwana ita kuma ta kwana a ɗaki. Ranan litinin da ya kasance gida an watse duk en biki sun tafi, ya chanja takun sa.
Da wurwuri ya kawo grilled chicken da apple juice da ya san tana so. Kafin maghrib su ka ci su ka ƙoshi. Kai tsaye masallaci ya wuce dan sallar maghrib yana tafiya yana jin nishaɗi tattare da shi.
Ƙarfe takwas da rabi ya shigo gidan kallo ya samu tanayi a laptop ɗin ta. Bai ce da ita ƙala ba ya shige banɗaki yai wanka tareda ɗauro alwala. Sai da ya fito ya ce "Lubna kin yi sallah" sai a lokacin ta tuna ba ta yi sallar Isha ba.
Ta girgiza kai.
Ya ƙaraso ya kashe laptop ɗin ya ce " prayer first"
Lokacin da ta ɗauro alwala ta fito zaune ta sameshi kan sallaya yana jan tasbaha dan haka ta ɗau wata sallayar ta tada sallah a bayan sa. Sai da ta gama addu'o'in ta za ta tashi ya ce "Lubna when will you be ready?" Gaban ta ne ya faɗi, ita gaba ɗaya ta ɗauka ya haƙura sai kaman wata ɗaya haka (kutmelesi🙄)
"I still nnnneed time" ta faɗi tana wuri-wuri da ido
"Do you hate me?"
"Noo" ta faɗi da ɗan ƙarfi
"Ba kya son na samu nitsuwa ne?"
Ta sunkuyar da kan ta ƙasa tana wasa da bakin sallayar
"Ba kya son haɗa jiki da Hudu Carpenter ko?"
Ta zaro ido tana kallon sa.
Ya ɗan matso kusa da ita ya ce " to minene?"
"Its...its painful right?"
Sai da ya ɗan dara sannan ya ce " gaskiyar Alhaji da ya ce sai na daure dan akwai ki da shagwaɓa. Wa ya gaya mi ki its painful?"
"Anty Khair" ta faɗi a hankali.
"Let me prove her wrong" ya faɗi tareda tashi tsaye ya ce " tashi mu miƙa godiya wa ubangiji"
Bayan sun idar da sallar raka biyu ya jima yana kwararo mu su addu'a kafin ya ɗan ma ta tambayoyi musamman gameda tsarki wanda ta amsa daidai gwargwado.
Su na idar wa ta shiga banɗaki. Yanayin kallon da ya ke ma ta kaɗai ya sa jikinta yai sanyi. Tana dai tsaye a banɗakin ne amma ba abinda za ta yi. Har yanzu fargar abin ta ke. Ta jima a bayin kafin ta wanke fiskar ta ta fito. Tana fitowa ta ganshi tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannayen sa. Ta ɗan dafe ƙirjinta sannan ta ce " you sssscared me"
Ba ta ankara ba yai sama da ita bai sauketa ba sai kan gadon su.
Kissing ɗin ta ya shiga yi a hankali. A hankali dukkan wani lungu da saƙo na jikinta ya fara amsa saƙonnin sa. The feeling is new to her, she was enjoying every bit of his touches his kisses and caresses. Idan wannan ne ai gaskiyar Mama its not painful. Sosai ya dinga romancing ɗin ta wanda hakan ya jawo ma ta kasala. Ko lokacin da ya ke addu'ar saduwa ba ta farga ba, sai da ya shigeta sannan ta ji MAZA.
"Wiwi ta ke ma sa kuka da asubahin washe gari, shi har kunya ya ke ji dan ya san ba makawa su Umma sun jiyo kukan ta. Kai Lubna akwai raki.
A inda ta ƙudunduna chan gefen gado ya ke so ta tashi ya taimaka ma ta ta yi wanka amma ta ƙi.
"Hayaty ki tashi, i promise komai zan mi ki"
"You liar, Anty Khair is right after all"
Ya ɗan yi murmushi ya ce " Lubna my love, my life, my everything. Allah ya mi ki albarka"
"Mugu" ta faɗi tana sake ƙudundunewa. Ganin da gaske ba tashi za ta yi ba ya sa ya ɗauketa da ita da bargon duka. Tana ɗan ƙara tana bugan bayan sa amma bai sauketa ba. Sai da ya warware bargon sannan ya zaunar da ita cikin faffaɗan bahon da ya tara ma ta ruwan zafi a ciki. Tunda ba bathtube ai sai a yi na gargajiya. Ƙara ta saka tana ƙoƙarin ta shi yai maida ta da ƙarfi tareda haɗe bakin su. Cizon sa ta ke son yi amma ta kasa. Hawaye ya dinga bin idanun ta. Sai da ya ga ta daina mutsu- mutsu sannan ya janye lips ɗin sa.
Har lokacin tana sheshsheƙar kuka...
Bayan ya tabbatar ruwan zafi sannan ya fara ƙoƙarin yi ma ta wanka. Ai kuwa ta tuɓure ba ta so. Ya ce " ko ki bari ko kuma na maimaita abinda na yi jiya" da sauri ta fara girgiza mi shi kai.
Kamar wata ƙaramar yarinya haka ya ma ta wanka ya sake ɗaukota ya maida ta ɗakin, ita kam sai kumbure -kumburen fiska ta ke yi...
Da sauri ya fito da bedsheet ɗin da ya wanke yana shanyawa yana tsoron kar Umma ko Baba su gan shi. Ai kuwa sai da ya gama shanyawa yana ɗaukar bucket zai koma ciki Baba ya fito daga ɗaki zai fita sallar asuba. Da sauri ya shige sashin su yana jin kunyar kan sa. Ba wai dan wanke bedsheet ɗin da yai ba sai dan dalilin wanke bedsheet ɗin.
Lubna tsabar raki a zaune ta yi sallar asuba. Sai sannu ya ke ma ta Ita kuma haushin sa ta ke ji.
Tana idar da sallar asuba ta koma ta kwanta shima ɗin da ya ke a gida yai sallah bayan ya gama azkar ɗin sa ya zo ya kwanta gefenta ya rungumeta jikin sa yana godewa Allah da wannan kyauta da ya ma sa...
Ƙarfe goma Mama na zubawa Alhaji abincin sai ga kiran Lubna. Alhaji ya miƙa ma ta wayar sannan ta amsa kiran.
"Mama you lied, you said its nnnnot painful. Last night was..."
"Kul Lubna, wannan sirrinki ne ke da mijin ki. Bai kamata wani ya ji ba duk kusancin ku kuwa"
"But Mama...."
"Yanzu kinga kin girma, ki rage raki da shagwaɓan nan dan Allah"
Kukan sakalci tasa ma ta, Mama ta ce " kin ga yadda na koya mi ki kula da kan ki kar ki yi sake da ko ɗaya a ciki kin ji"
"Mama we are not doing it again" ta faɗa a sakalce.
"Kin ga zamuyi magana sai an jima" ta faɗi gameda katse kiran.
Alhaji yai 'yar dariya ya ce " Maman Lubna ke da 'yar ta ki ce"
"Yallaɓai ai Lubna ba de raki ba"
"Allah ya ba su zaman lafiya"
Mama ta amsa da amin tana ƙara godewa Allah da ya sa Lubna ta kai darajar ta gidan miji.