Page 10
*MUGUN NUFI*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 10*
Ganin suna kallon sa kowa baki a bud'e ya sanya shi yace, "Yeah da dai na nun Mima as my wife gwara na d'auko ta." Ran Anty Lubna ya b'aci ta d'aure fuska tace, "U are not serious Ahmad, yanzu akan k d'auki Mima jinin ka kuma y'ar uwar ka shine zaka ce gwara ka nuna karuwa?."
"Yes ya fi min" ya bata amsa hankalin sa kwance.
"To wallahi bazai yu ba baka isa ba" ta fad'a cikin d'aure fuska. Ya tab'e baki yace, "Sai a bar maganar gabad'aya zanje ni kad'ai duk abinda zasu ce su ce" ya fad'a yana wara hannyen sa alamin I don't care.
Ganin suna ta kallon sa sun rasa abin fad'a ya saka shi ya mik'e yace, "Byee" abinda ya furta kenan ya bar musu office d'in ko wanne baki a bud'e yana kallon sa har ya b'ace. Omar ya kalli Anty Lubna yace, "Anty kar fa mu k'yale shi yayi abinda yake so fa, a gani na mu samu Mima muyi mata bayanin komai ki ja mata kunne kar ta bamu kunya in lokacin yaso in yaso sai dai kawai ya ganta a wajan."
Anty tace, "Hakan yayi amma Jamil fa? Baka ganin anyi masa ba dai-dai ba?." Omar yace, "kowa na clinic yasan Mima d AA ba ma'aurata bane za'a nuna tane saboda rashin mafita, shima Jamil d'in ya sani amma in kuka gama magana da Miman ni zan same shi na fad'a masa ai ba wani abu bane ba."
Anty Lubna tace, "Hakan Yayi Omar ka same shi nima daga nan gida zan wuce na samu Mima muyi magana." Ya mik'e yace, "Shikenan Anty nima na wuce" ya fad'a yana fita ita kuma ta cigaba da aikin ta.
Ahmad kuwa tunda ya fita ya koma mota ya zauna jikin sa gabad'aya a salub'e yake baya jin kwari ko kad'an ko kunna motar ya kasa yi, iska ya fesar ya d'auko wayar sa ya shiga kiran number Husna amma a kashe ake ce masa, yaja tsaki ya jingina da kujera yace, "Ko meyasa ban karb'i number Abban ta ba oho" ya fad'a yana kunna motar ya fita daga gate d'in wajan.
Silver clinic ya nufa ya ajjiye motar sa ya fito a salub'e ya shiga ciki, kan sa a k'asa yake takawa a hankali ya wuce reception kenan wutar clinic d'in ta d'auke gabad'aya, duk da ba dare bane amma sai wajan yayi duhu sosai bai tsaya ba ya cigaba da tafiya ya d'auko waya zai kira masu kula da wajan yaji yayi karo da mutum anyi y'ar k'aramar k'ara tare da rik'e jikin sa, hannun sa ya saka ya rik'e k'ugun ta ba tare da ya san wacece ba duk a tunanin sa na taimakon ko wacece take k'okarin fad'uwa.
Idanun ta a runtse ta rik'e shi gam cikin tsoro da fargabar kar ta fad'i k'asa, khamshin turaren jikin sa da take shak'a shine ya bata tabbacin a jikin wanda tak ta zaro ido ta zabura zata bar jikin sa wutar asibitin ta dawo.
Had'a idanu sukayi ya kalle ta ta kalle shi ta zare jikin ta daga nasa tana raba idanu ya tab'e baki ya rab'a ta gefen ta ya wuce, dafe k'irji tayi bayan ya wuce ranar ta farko kenan da hannun sa ya kai jikin ta bada niyar duka ba hakan ya saka ta jin wani iri.
Zuciyar ta ce take buguwa sosai har tana jin sautin a kunnen ta, yanayin da ta tsinci kanta a ciki ne lokaci d'aya yake dawo mata cikin kanta har lokacin khamshin sa bai bar hancin ta ba. Ko me ta tuna kuma sai tayi saurin barin wajan tana dan dukan kanta kad'an.
Bayan sallar azahar Mima ta gudu gida kuma ta samu kiran Anty Lubna daman, a falo ta baje ta zauna kusa da Anty Lubna da take zaune a falon ita kad'ai dan Dada ta yiwa zaman falon yaji tunda aljana Basira ta kawo mata ziyara.
"Anty Lubna gani" ta fad'a tana zama kusa da ita. Ta kalle ta tace, "Ki fara hutawa mana ina nan har yamma."
"A'a fad'a min dai Anty."
"Naji kina khamshin Auta, a ina kika samo turaren sa?."
Zaro ido tayi ta dan sosa kai alamun mara gaskiya tace, "Bafa turaren sa bane kawai khamshin ne yazo iri d'aya." Anty Lubna tayi dariya tace, "To naji. Kiran ki nayi sabida ina so zaki min wani taimako amma a sirran ce kuma in kin san baza ki bani had'in kai ba ki fad'a min."
Mima tace, ,"Anty me zai hana ni kin baki had'in kai? Fad'i ina jin ki Yaya ta."
"Akwai bak'in da Ahmad zaiyi daga k'asashe da yawa ranar monday kuma suna son suga matar sa da y'ar sa, kin sani na sani kowa ya sani bashi da aure karanbani irin nashi ya saka yace musu yana da mata last had'uwa da sukayi yanzu sunce suna son ganin ta a taron. Na yanke shawara zaki je matsayin matar sa Alina kuma matsayin y'ar ku, amma bana son Ahmad yasan zaki je event d'in matsayin matar sa, zamu taimake shi ne nida ke matsayin mu na y'an uwan sa."
Mima da take sauraren Anty Lubna ta bud'e baki jin abinda tace har ta kai k'arshe ta dafe k'irji tace, "Anty me kika ce? Ni Ayshatou naje wajan taro a matsayin matar sa?, abinda bazai yu ba kenan ba ai Anty, kuma kince bai sani ba naje wajan ya samu hanyar dizga ni kamar yadda ya saba ko?."
Anty Lubna tace, "Wanne irin dizgi kuma Mima? Wallahi bazai miki komai ba sai ma godiya ki rubuta ki ajjiye wannan."
"Gaskiya Anty bazan iya ba kar rai yazo yana b'aci a wajan dan kin san bazan k'yale ba in yayi min gwara a hak'ura yafi." Anty tace, "Babu fa abinda zai faru ki bani had'in kai ki gani mana."
Shiru Mima tayi tana tunani kafin tace, "To Jamil fa? Tunda maganar asibiti ce ai kinga gabad'aya za'a had'u har dashi a wajan." Anty tace, "Omar zai masa bayanin komai nasan kuma zai fahimta, bafa wani abun za'ayi ba zaki zauna a kusa dashi ne kawai."
"Toh shikenan" ta fad'a tana mik'ewa tayi cikin gidan.
Bai dawo ba sai magariba kamar koda yaushe ya shiga part d'in sa ya yi wanka ya shirya ya shiga masallaci akayi sallar i'sha sannan ya shiga cikin gida, babu kowa a babban falon ya kalli inda Dada take zama yayi murmushi tunawa da abinda ya faru ya k'arasa inda ake ajjiye abinci ya zuba d'an kad'an ya koma kan kujera ya zauna ya fara ci a hankali, Tasleem ce ta fito tana fad'in, "Yaya Dr shine ko ka neme ni ko?."
Kallon ta yyi da murmushi a fuskar sa yace, "Sorry fav na gaji da yawa ne" ya fad'a yana nuna mata kusa dashi alamun ta zauna.
Ta zauna tace, "kasan me Yaya Dr?." Girgiza kai yayi alamun a'a tace, "An zab'e ni a cikin wanda zasuyi national debate." Wara idanu yayi ya had'd'iye abincin da ya zuba a bakin sa kana yace, "Woww! Fav national debate fa? Ohhh congratulations my dear friend" ya fad'a yana mik'a mata hannu suka gaisa.
Tana murmushi tace, "Nayi choosing topic d'in da aka bamu zan fara joting a kai sai ka taya ni." Yace, "Meye topic d'in?."
"Water is better than air."
Wara ido ya kuma yi ya ajjiye abincin hannun sa ya rik'e hannun ta duka biyun yace, "Who told u water is better than air?."
Ta turo baki tace, "On my own, a gani na kamar ruwa yafi iska amfani." Girgiza kai yayi yace, "Kin basu topic d'in?." Ta Girgiza kai alamun a'a yace, "To ki canja ya koma air is better than water."
Cikin shagwab'a tace, "Like how?."
"Fav ana iya rayuwa babu ruwa amma baza a iya rayuwa babu iska ba." Gani yayi kamar bata yarda ba ya saka yace, "imagine a kulle ki a falon nan a kulle windows da door a kashe a.c a kuma kashe fans, a ajjiye miki abinci da kuma ruwa zaki iya zama?."
Ta girgiza kai tace, "Babu inda zanyi ji iska ai zafi sai ya kashe ni." Yayi murmushi yace, "Basai ki sha ruwa ba."
"To ai bazan iya shan ruwan bama in ba iska, babu ta inda oxygen zai fita fa."
"Good girl. Now u understand air is better than water?."
Murmushi tayi ta d'aga kai suka tafa tace, "Ina farin ciki sosai da ka zama Yaya na mai sona." Ya d'an kwab'e fuska kad'an kana yace, "Awwwnn." Ta kalle shi tace, "I love u so much My Fav."
"I love u much" ya fad'a Yana murmushi itama haka.
Hakan ya faru a kan idon Mima jin yadda kalmar i love u ta fita tar a bakin sa kamar bature sai gaban ta yayi mugun fad'uwa ta dafe k'irji ta sake kallon sa taga lokacin sun sake tafawa da Mima sai kawai taji zuciyar ta ta raya mata ina ma itace, cikin bala'in sauri kawar da tunanin ta samu tayi ta k'araso wajan lokacin Tasleem ta koma ciki shi kuma ya cigaba da cin abincin sa.
Zama tayi nesa dashi ta kalle shi yana sanye da three quarter wanda ya rufe iya guiwar sa gabad'aya sauran k'afar sa a bud'e yake gashi ya kwanta a k'afar gata fara tass har tafi fuskar sa hasken kamar baya taka k'asa. Gajiya yayi da k'are masa kallon da take ya d'ago suka had'a ido ya zabga mata harara ya d'auke idanun sa.
Tab'e baki tayi tace, "Kar ka mutum ya d'auka ina kallon sane dan yayi kyau ko yana da kyau a'a, ina kallon wanda yake neman alfarma ta a matsayin na kasance matar sa a wajan taro sabida na cancanta ta." Sarai yaji me tace amma ya share kamar bai ji ba ya lumshe ido ya bud'e domin ba kowa ya jawo masa ba sai Anty Lubna.
Jin yayi mata banza yak'i kula ta ya sanya ta mik'e tsaye tana juyawa tace, "Na cancanta shiyasa ake so na fito a matsayin matar wani, duk da ba'a yi dani amma ana so a nuna ni tunda na cancanta an san na isa." Sai da ta bashi dariya yayi murmushi har hak'oran sa suka bayyana jin wai ta cancanta, ya kalle ta gefen ido yana so ya gano cancantar amma bai gani ba ya sake yin murmushi amma bai nuna da ita yake ba sai ka rantse film d'in da yake kallo ne yake bashi dariya.
Mima ta k'ulu ranta ya b'aci zatayi magana ta jiyo ana cewa, "Yau Mima da Auta ne a inuwa d'aya?." Kallon wajan sukayi duka kafin ya mik'e tsaye yace, "Mamy me kika ce?."
"Cewa nayi yau kai da Mima ne a waje d'aya a zaune?."
Kallon falon yayi suka had'a ido da Mima yace, "Ba tare kuke da ita ba daman?." Mamy ta harare shi tace, "Ban sani ba." Ya tab'e baki yace, "I thought tare kuke dan ni ban ganta bama sai yanzu" ya fad'a yana ajjiye plate d'in hannun sa ya shiga cikin gida cikin taku a nutse hannayen sa zube cikin aljihu.
Mamy tayi dariya ta kalli Mima da ta kwab'e fuska tace, "Ina ma ku kasance ma'arauta naga yadda zaman nan naku zai yu."
Mima tace, "Allah ya tsarii gatari da saran shuka ai wallahi nafi k'arfin sa, dan Allah ki daina fad'a Mamy." Mamy ta kalle ta tace, "Ke dai kika sani, kije Mummy na so ta ganki Dada ma haka." Cikin gidan Mima tayi tana k'unk'uni ita kuma Mamy ta zauna.
Ahmad ma wajan Mummy ya je ya zauna kusa da ita ta ja masa kunne tace, "Tun jiya nake so na kama ka sai yanzu Allah yayi." Ya runtse idanu yace, "Mummy me nayi to?."
"A gaban idanun Mamyn ku zaka cewa Mima munafuka mai bak'in hali? Kai baka san uwa bace duk yadda kuke da ita in ka fad'i abu mara dad'i akan Mima sai taji babu dad'i?."
"To Mummy ai ba k'arya nayi ba gabad'aya halayyar ta daban dana mutanen gidan nan, ga gulma, ga munafurci, bak'in hali, da bak'ar fuska duka ita kad'ai." Mummy ta sake murd'a kunnen sa tace, "Na dai fad'a maka Allah ka sake ranka zai b'aci."
Yana jin zafi a kunnen sa hakan ya saka shi yace, "To Mummy bazan sake ba." Sakar masa kunne tayi ya turo mata ido bakin sa a gaba kamar yaro k'arami. Hannu ta kawo zata doke bakin yayi saurin mayar dashi tayi k'wafa sai yayi murmushi ya kwanta a kafad'ar ta.
A lokacin Mima ta shigo da sallama ta k'araso kusa da Mummy tace, "Mummy na gani." Mummy ta kalle ta cikin nutsuwa da kulawa tace, "Mima mai ya same ki kike ramewa haka? D'azu muke magana da Abbahn ku yake cewa me yake faruwa yaga sai rama kike nace zan tambaye ki."
Kai ta sunkuyar jikin duk ta duk yayi sanyi tace, "babu komai Mummy ina fama da zazzab'i ne cikin kwanakin nan da ciwon kai shiyasa." Mummy ta dafa ta tace,"Ban amince da abinda kika fad'a ba Mima, kin san nasan meye a zuciya ki kiyi hak'uri ki jure ki kuma daure ki cigaba da addu'a kinji?."
Idanun ta ya kawo ruwa ta goge ta d'agawa Mummy kawai alamun to domin bata san me zata ce ba, "kar kiyi kuka mana Mima, kiyi hak'uri Allah yana sane da komai." Tace, "to Mummy zanyi in sha Allah." Mummy tayi murmushi tace, "Yauwa y'ar albarka."
Ta mik'e tace, "Mummy bara na lek'a Dada." Mummy tace, "To a gaishe ta yau tayi yaji bata lek'o main parlor ba gabad'aya."
Fad'ar hakan sai Ahmad yayi y'ar dariya yace, "Aljanu." Mummy ta doke shi a kai tace, "Baka da kirki fa." Ya kuma yin murmushi sosai Mima ta kalle shi itama sai ta samu kanta da murmushin domin yadda ya masa kyau a fuska dole ya burge ka, yadda yake yi da Mummy kamar k'awar sa hakan na burge ta sosai.
Fita tayi Mummy ta kalle shi tace, "Ina tausayin rayuwar Mima wallahi, Allah ya kawo mata mafita ya sanya wannan auren ya yu kar ya watse kamar na baya." Maimakon ya amsa sai yace, "Uhum Mummy ina da aiki fa yanzu a national hospital."
"To agogo Allah ya kiyaye."
Mik'ewa yayi kana ya durk'usa ya mata kiss a goshi ya fice yana dariya.
*Kaduna.*
Baccin asara Husna tai tayi ba ita ta samu kanta ba sai bayan sallar magriba sannan ta farka, ciwon kai da ciwon jiki dasu ta tashi ta kalli kanta da kuma yanayin da take ciki, Dafe kai tayi tunawa da abinda ya faru ya sanya ta yin k'aramin tsaki ta mik'e dak'yar tana dafa bango ta shiga band'aki.
Ta jima sosai sannan ta fito gashin kanta k'amas babu alamun yaga ruwa ta saka doguwar riga ta saka hijjabi ta kalli gabas da niyar sallah, kanta taji yayi mugun sarawa hakan ya saka ta yin baya ta zauna tana zare idanu jikin ta yayi mata mugun sanyi. Agogo ta kallah taga k'arfe bakwai har da wani abun ta yamutsa fuska tana tunanin Sallah nawa ce ma ta wuce ta.
Maimakon ta mik'e ta tayar da sallar sai tayi baya ta kwanta tana sauke numfashi, wayar ta ta hango a gefen gado ta mik'e ta rarrafa ta d'auko dai-dai lokacin kira ya shigo cikin wayar, ganin me kiran ya saka ta d'auka ta saka ta a speaker daga can b'angaren yace, "Asmee."
"Uhum" ta furta kawai tana lumshe idanu. Yace, "Ina son ganin ki Asmee ya za'ayi?."
Turo baki tayi tace, "Ina Kaduna."
"Wow nima kinga ina hanya zan wuce Abuja k'arfe bakwai na safe jirgi na zai wuce Spain please ki daure ki raka ni."
Numfashi ta sauke bata ce komai ba ya sake cewa, "please my Asmee wallahi nayi kewar ki sosai." Yatsine fuska tayi tace, "Tohm."
"Wow thanks u Asmee, yanzu zan shigo Kaduna sai mu k'arasa, kina gida?."
"Uhum."
"Okay oh ready daman passport d'in ki na hannu na kuma akwai visa last time da muka je bata k'are ba zan siya miki ticket yanzu kawai gobe mu wuce."
Bata jira me zaice ba ta yanke wayar ta mik'e tsaye kanta na mugun sara mata, gabad'aya ji take k'asar ta ishe ta in ba barin ta tayi ba hankalin ta bazai kwanta ba hakan ya saka ta jawo trolly ta fara zuba kaya ta gama ta kulle ta d'auki wayar ta lokacin da taji kiran sa, mayafin doguwar rigar ta yafa ta fesa turare a jikin ta ta jawo jakar ta fito daga d'akin.
A falo ta had'u da Baba yana zaune yana kallon ta ganin ta da jaka ya sanya shi yin murmushi ya saki fuska da kulawa yace, "Husna ina zuwa haka?." Tace, "Baba gidan nan yayi min zafi zan wuce Abuja yanzu daga nan gobe zan wuce Spain."
Jin abinda tace ya saka shi jin sanyi a zuciyar sa yace, "Sai kin dawo my daughter." Kai kawai ta d'aga masa ta fice ya bita da kallo har ta b'ace yace, "Ba ke ba Ahmad Husna yafi k'arfin ki, sai nayi silar jefa tsanar ki a zuciyar sa bazan tab'a k'yale ki kiyi karatun islamiyya har ki fahimci meye addini ba a haka nake so k'are ba arabi ba boko, Zaki yi nisa da Ahmad baza ki sake ganin sa ba, bazai sake kallon ki ba balle kije kusa dashi, ki sauka a Spain lafiya MUGUN NUFI na kullum a kanki k'aruwa yake."
Kyakykyawan murmushi ya kuma yi ya d'auko wayar sa ya shiga videos sai ga video Husna da Mahmud na d'azu ya bayyana ko wanne cikin su tsirara babu mai suttura suna sab'awa Allah, murmushi yayi yace, "Wannan video shine makami na, dashi zan jefa tsanar ki a zuciyar wanda kike so, dashi zan raba ku duk son taimaka mikin da yake yi yaji kin fita a zuciyar sa, dashi duka duniya zata k'yamace ki tsumma ya fiki daraja Husnaaaaa!" Ya fad'a yana jan sunan yana murmushi mai cike da ma'anoni da dama a cikin sa.
_Nima dai na fara tantama akan Baba._🤔
Share it sabida Allah🤗👏