ASHE BA SO BA NE?

11-12

by @yarmutanargungu

 馃崜馃崜馃崜馃崜

         馃崜馃崜

           馃崜

           11

Picts din Usman ta gani tare da abokansa, da alama hotunan daurin aure ne na abokinsu. Sai dayan pics din Usman ne shi kadai 

Yana sanye da ash shaddar ( getzner ) dinkin babbar riga wanda ya sha aikin hannu. Wani tsadadden agogo baki kirar Rolex ke a tsintsiyar hannunsa na hagu. Kafafunsa na sanye da black loafers na kamfanin Gucci. A saman kansa kuma, akwai hula mai kala ash, white da black. All in all, a gaskiya Usman yayi kyau matuka

     Take Hauwa taji zuciyarta tana bugawa da karfi. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kara kurawa hoton ido.

Usman mutum ne mai matsakaicin tsayi wanda bashi da kiba sosai. Shi kalar wankan tarwada ne wato chocolate. Yana da manyan idanuwa. Hancinsa dogo ne, yayin da bakinsa matsakaici.Sajen fuskarsa yayi yanayi da na shahararren dan film din Indian Zain Imam

Ajiyar zuciya Hauwa ta sake saukewa, ta San Usman yanzu yayi mata nisa. Amma kuma wata zuciyar na rada mata cewa ta kira shi. Sannan dayan bangaren na cewa ka da ta kira shi, duba da abubuwan da suka faru a baya.

Kasancewar Hauwa yarinya ce mai son Kai, tafi amincewa da maganar zuciyarta ta farko. Sai ta kira. Ta na fa ra ringing...


ARGUNGU

Usman yana wurin aikinsa na kamfani, kasancewar yanzu shi production manager ne na kamfanin sarrafa shinkafa ( su oo na son suji wane kamfani ne, LOL 馃槣)

Wayarsa da ke aje kan desk din ofishinsa ce ta fa ra ringing, ya zura hannu ya dauka, lambar da ta kira ba suna. Kallo daya yayi wa lambar zuciyarshi ta buga, domin ko daga bacci ya falka ya san mai wannan lambar.

Wata zuciyar na cewa ya dauka, wata kuma na cewa kar ya dauka saboda matar aure ce fah. Amman be san meyasa zuciyarshi ta rinjaye shi da dauka ba. Sautin muryarta da yaji, take wani sanyi ya ratsa zuciyarsa. Shi kanshi wannan al'amari ya bashi mamaki, saboda a tunanin shi ya dade da binne soyayyarta daga zuciyarsa.

"Hello?" Yaji tace domin ja wo hankalinsa

Ita kanta Hauwa ta fa ra waswasin kodai ba Usman ya dauki wayar ba? Domin dakyar zai dauka bayan abunda ya faru

Gyaran murya taji 

daga dayan bangaren layin, sannan muryar Usman dauke da sallama...



***********


      馃崜馃崜馃崜馃崜

         馃崜馃崜

           馃崜

          12


"Sai ta amsa Sallamar sa tare da cewa, "dan Allah ina magana da Usman ne?"


"Eh kina magana da Usman ne, amma ban gane mai magana ba. Wacece dan Allah?"

Ya fada in a serious tone.


Hauwa: kana magana da Hauwa


Usman: Hauwa... Hauwa..ban gane wace Hauwa ba?


Hauwa: Wadda kuka hadu a cikin group din AMINAN JUNA?


Ta fadi hakan ne cikin mamaki, sabo da a tunaninta Usman ya manta da ita. Hakan ya sa jikinta yayi sanyi.

Usman: hello? Hello?

Muryan Usman ce ta dawo da ita daga tunanin ta.


Hauwa:  Hauwa ce fah, har ka manta Dani ?


Usman: kinsan yanayin rayuwa,abubuwa sun yi wa mutum yawa,wani lokacin ba komai mutum yake iya tunawa ba...


Cikin ransa wani dadi yake ji Hauwa ta kira...amma wata zuciyar na fada mishi Hauwa matar Aure ce fah,me zai sa ta kira shi?


Wannan ne ya rage farin cikin da ke zuciyar shi...


Hauwa: haka ne, gaskiya. Kwanaki da yawa,amma ban yi tsammanin zaka iya mance Hauwa daga Zamfara state ba...


"Fadar haka ya sa Usman ya gane cewa magana Hauwa ta fada mishi, cikin ruwan sanyi. Sai jikinshi yayi sanyi...


     Usman: Allah sarki,Hauwa Ashe kece,ya gida ? Ya mai gidan naki? Da fatar kowa na lafiya...ban gane ki ba ne,ki yi hakuri sabo da nayi loosing contacts kuma kinsan ana cewa "abun da ba naka ba,kayi nesa dashi."


Hauwa: tayi shiru...San nan tace ai mun rabu da shi.


Usman: yana zaune bai San lokacin da ya Mike ba! innalillahi wainna ilaihir raji'un,meya faru? Ya rasu ne?

Hauwa: himm, Usman labari ne mai tsawo...

Dama na Kira ne in baka hakuri akan abubuwan da su ka faru a baya...

Dan Allah ka yafe min,ban San ko alhakinka ne ke bii na ba...


Usman: haba Hauwa, wannan wace irin magana ce ? 

Kamar baki yadda da kaddara ba? Auren dole aka yi Miki,ba laifinki bane,dan haka ni ban rike ki da komai ba...

Hauwa: nagode sosai Usman, zuciyar ka mai kyau ce 

Usman: ba komi Hauwa,sai anjima.





Duk da Usman bai so aje wa ba,yayi hakan ne sabo da tausayin ta.


*****************************

        *

        *

        *

Bayan ya aje waya,sai kuma ya ce bari ya Kira Nasir...


Nasir: wallahi yanzu nake cewa bari in Kira ka,sabo da kwana biyu bamu yi waya ba.


Usman: Allah sarki,Nima yanzu wani albishir na Kira in fada maka...


Nasir: tasamu kenan,na dade ban jika cikin farin ciki ba... Yana maganar tare da dariya


Usman: himm...kai dai bari, ai dole kajini cikin farinciki, yanzu muka gama magana da Hauwa...



Nasir: wace Hauwa? Ko kayi sabuwar budurwa ne?


Usman: dadina dakai akwai shirme wani lokacin,wace budurwa kuma... Hauwa dai wadda ka sanni da ita Yar Zamfara.


Nasir: what! Usman kana da hankali kuwa? Matar aure ce fah,kasan zunubin yin hakan kuwa?!


Usman: easy mana,wai me ka dauke ni ne dan Allah?! Jahili ko mahaukaci? Kasanni kasan halina,be kamata kayi min wannan zaton ba!


Nasir: I'm sorry abokina ,Kai dinne naji kana wani batu na daban, please explain to me


Usman: haba ko kaifah.Dazu Hauwa ta kirani take bani hakuri akan abubuwan da suka fa ru... "Toh Kai Ina ruwanka da wani Auren ta ya mutu?!

Kar dai ace min...




Yar mutan Argungu 鉂わ笍