Chapter 22
by @azizat
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣2️⃣2️⃣
Da wuri ta tashi ta kimtsa gidan saboda zuwan su Harira. 'Yan sauran chanjin da ke hannunta ta sa Muhsin yaron maƙotan su ya siyo ma ta naman ɗari uku, tarugu da tumatir na ɗari da coke biyu, ta sa coke ɗin a fridge. Tana gyara naman tana ƙunƙuni, yanzu haka ba ta da cash ko naira ɗaya babu a hannunta chanjin naira hamsin da Muhsin ya dawo ma ta da shi ta ce ya tafi da shi. Daɗin ta ma gobe idan ta shiga school za ta cire kuɗi a account ɗin ta. Ba abinda ya tsaya ma ta a rai irin yadda tunda su ka yi aure Suhail bai ba ta ko ƙwandala ba. Satin auren su na farko daga gidan su ake kawo abinci. To tunda ta fara girki kuma ita ke sa kuɗin ta ta ke siyan kayan miya da 'yan ƙananan abubuwan da ba za a rasa ba. Tana da kayan gara ba ta da matsalan kayan abinci sai dai kuma kayan miya fa? da kuma kayan marmari na yau da kullum.
Ranan da ta fara ma sa maganar kuɗi ya ce ma ta ya kashe kuɗin sa a wajen hidimar biki. Abba kuma sai ƙarshen wata zai fara bashi allowance. Takaici ya kawo ma ta har wuya maganar Mama ya sake dawo ma ta lokacin da ta ke tambayar ta *miye aikin Suhail?* Ta sani tun farko dama ya ce mata sai sun yi aure zai fara aiki amma kuma da ta shigo gidan sai ya chanja magana da cewa sai ya gama service zai fara aiki. For the mean time Abba zai dinga bashi allowance duk wata.
Jiya da ya dawo ya ke ce mata ya cika Jigawa, Anambra da kuma Abuja har yana murnan saura ƙiris su shiga camp kuma yasan Abuja za a tura shi. Ita kam kallon shi kawai ta yi ta rasa abun cewa. Yana nan ma ba kullum ya ke neman ta ba balle kuma baya nan. Wallahi indai wani garin ze je service to ƙafar sa ƙafar ta.
Sai da ta haɗa girki wadda farar shinkafa da miya ta yi sannan ta shiga wanka. Domin ko kaɗan ba ta so manyan ƙawayenta su zo gidan ta su sameta a wargaje, so ta ke su zo su ganta a amarya wadda ta ke cikin jin daɗi da kwanciyar hankali.
Ta fito daga wanka tana ƙoƙarin shafa mai warin wiwi ya fara buso ta.
"Wiwi kuma a gida na?" Ta tambayi kanta yayinda ta gyara ɗaurin towel ɗin ta ta fito falo. Zaune daɓas ya ke a tsakiyar falon yana zuƙar wiwi hankalin sa kwance.
"Suhail!" Ta faɗa da ƙarfi. Ya ɗago jajayen idanun sa yana kallon ta. Tabbas jiya taji wari a jikin sa makamancin wannan da ta tambayeshi ya ce gidan ƙwallon da ya je ne ya zauna kusa da wani da ke sha shiyasa taji warin, ashe yaudarar ta yai, tunda gashi ta ganshi muraratan yana sha.
Ba tareda ya ce komai ba ya cigaba da zuƙar wiwin.
"Yanzu dan Allah dama Suhail ba ka dena shaye-shaye ba. Ka ce min sigari kawai ka ke sha kuma ka dena. Amma...."
"Daɗina da ke yawan ƙorafi. Ke ba kya gajiya da yawar magana ne?" Ya faɗa da kakkaurar murya.
"Wallahi ka fice min a falo. Ƙawayena za su zo kuma ba ka isa ka kunyata ni a gabansu ba ehe"
Ya ƙyalƙyale da dariya ya ce "sannu mai gida" sannan ya cigaba da abin da ya ke yi. Haushi ya kamata, taja dogon tsaki ta koma ɗaki. Ta kira Harira ta tambayesu ko sun taso daga gidan Lubna, su ka ce suna cin abinci tukunna, sai a lokacin hankalinta ya ɗan kwanta. Atleast kafin su zo za ta san yadda za ta yi da Suhail ya bar gidan.
Sai da ta ji fitar motar sa daga gidan sannan ta fito falo dan ta share wajen da ya ɓata. Ganin ƙaton plate da aka ci abinci a ciki da kuma empty bottle na coke ya sa ta fasa ihu ta yi kitchen da gudu. Ta buɗe food warmers da ta zuba abinci a ciki. Naman cikin miyan an tsamesu saura yanka biyu shinkafar dai da sauranta zai ishe su ci.
Sai da ta gama zagin Suhail tas sannan ta fito ta gyara wajen da ya ɓata. Tareda fesa air freshner saboda warin wiwi da ya buɗe falon.
....................................
"Yaya, har yanzu ba ka ɗauko min mota ta ba, gobe fa zan fara shiga school" ta faɗa cikin sakalci.
Murmushi yai sannan ya kurɓi zobo mai sanyi da ta ma sa sannan ya ce " motar ki ai tun satin baya ta ke gidan nan"
"Da gaske Yaya?"
Ya ɗan langwaɓar da kai gefe ya ce " ni kam har yanzu ba za a chanja min Yayan nan bane? Kowa a gidan ku haka ya ke kirana kuma na zo nan kema ki kirani da haka"
Ta ɗan hararashe shi ta ce " to mi zan kira ka?"
"Ba irin sunan masoya ɗin nan, kamar Baby, sweetheart, darling"
Dariya ta farayi saboda yadda ya ke kiran sunan yana lumshe ido.
"Da gaske idan ba a chanja min suna ba zan kawo miki ƙanwa mai kirana da baby. Ina waccar student ɗina mai damuna da text ɗin nan ya ma sunanta? ....Lawiza ko Lawisha ne ma?...."
Hawayen da ya gani a idon ta ya sa shi saurin tsayar da maganar. Yai saurin tashi daga kujerar da ya ke ya zo kusa da nata ya tsugunna ya fara goge ma ta hawaye. Hawayen kawai ke zuba amma ba kuka sai ajiyar zuciya da ta ke saukewa.
" my Queen ba kya son kishiya ko?"
Ba ta yi magana ba sai ya fara ƙoƙarin tashi.
"Relax Mrs Usman, wasa na ke mi ki, ni da ke mutu ka raba Insha Allah. Ashe dai ana sona tunda har kishi na ake yi" ta yi saurin rufe fiskar ta tana murmushi.
Shima murmushin yai sannan ya ce " take your time my Queen, duk lokacin da ki ka ga ya dace kya chanjamin sunan" ya kissing goshin ta ya koma ya zauna. Shi ne ya ƙarasa cin abincin amma ita kunya ya hanata. Sunkuyar da kai ta yi tana wasa da yatsunta lokaci zuwa lokaci tana satan kallon mijin ta wanda cikin ƙanƙanin lokaci ya siye zuciyar ta. Koda ba ta furta ma sa ba tasan abinda ta ke ji akan sa babu tantama SO ne.
Sai da ta gama gyara dining ɗin sannan ya kawo ma ta key ɗin mota. Ganin ba key ɗin motarta ta da bace ya sa ta kalle shi da mamaki ta ce "ba tawa ba ce"
"Mu je garage ki ga motar ki" ya faɗi yana kama hannunta.
"Yaya! sabuwar mota!"
"Yes baby nah. Kyauta ce daga gareni. Ina ƙoƙarin chanja mota maganar auren mu ya taso sai na ajiye batun mota a gefe. To yanzu abubuwa sun lafa kuma wani kasuwanci da na haɗa da abokina Salisu shekara ɗaya daya wuce mun samu alkhairi, shi ne na siya mi ki wannan"
"Yaya ai da nakan ka chanja tunda nima inada tawa"
"Abba ne ya siya mi ki wancan kuma ta kusa shekara uku kina hawanta. Wannan mijin ki ne ya siya mi ki. Idan na ƙarasa fencing gidanmu sai a ɗauko wancan sai ki dinga hawa duka biyu"
"Thank you Yaya au ssssweet" ta faɗi tana toshe bakin ta
"Ɗan sake maimaita sunan na ji" ya faɗi yana jawota jikin sa.
"My sweet husband" ta faɗi tana ƙara shigewa jikinsa.
Murya ƙasa-ƙasa ya ce " My Queen mu je ɗaki a min thank you ɗin nan da kyau"....
...............................
Tana idar da sallar azahar ta ji sallamar su Harira. Ta yi saurin cire hijabi ta fito falo ta buɗe mu su ƙofa.
"Har muna shirin komawa mu ka ce ƙila ana chan ɗaki ana amarci" Harira ta faɗi tana ajiye jakarta
Nafy ta yi 'yar dariya ta ce " Harira wallahi ba ki da kyau. Amarci kuma na yaushe"
Amira ta ce "ai Nafy ba ki san mi muka gano a gidan su cousin ɗin ki ba"
"Mi?" Nafy ta tambaya da sauri ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri saboda fargabar abinda za su ce.
"Kin san yadda Hudu ya iya soyayya!. Abin ba a magana Nafy. Dama Ustazan nan sai a hankali kana ganin su kamar ba su san komai ba wallahi su suka san soyayya" Harira ta cigaba da bata labarin abinda su ka gani a gidan Lubna.
Zuby ta ce "a ɗan tsurkukun sashin sun nan Allah kaɗai ya san soyayyar da su ke zubawa junan su. Ikon Allah kenan kin ƙi Hudu ita kuma 'yar uwarki ta so shi. Ni sai yau dana gan su tare na ga ba ƙaramin dacewa su ka yi ba"
Nafy dai murmushi kawai ta ke yi dan ba ta da abin faɗi. Irin rayuwar auren da ta hangowa kan ta da Suhail kenan. Irin rayuwar da za su zama abin kwatance cikin mutane, sai dai tun ba aje ko ina ba ta ga saɓanin haka.
Harira ta cire gyalen ta ta ce " ni gidan na ki na rowa ne ko ruwa ba za a kawo mana ba"
Nafy ta yi saurin tashi ta shige kitchen gaban ta na faɗuwa. Ba ta ɗauka su uku za su zo ba, shiyasa ta siyo coke biyu ga shi kuma Suhail ya shanye ɗaya saura ɗaya. Ta sake leƙa fridge ɗin ta a karo na ba adadi tana tunanin ko miraculously za ta ga coke uku a ciki. Sai dai ɗayan nan ce a ciki har yanzu, ta ɗauko jug ɗin ta mai kyau ta ajiye a saman fridge sannan ta fito da goran ruwa wanda ruwan fanfo ta ɗura a ciki ta sa a fridge yai sanyi ta tsiyaya ruwan a cikin jug ɗin. Kwana uku kenan rabonta da satchet water saboda ba kuɗi, ruwan famfo ta ke sha.
Sai da ta gama jera mu su abinci ta ce Bismillah.
"Wallahi Nafy falon ki warin wiwi ya ke yi" Zuby ta faɗi tana toshe hancinta.
Gaban Nafy ya faɗi musamman da Harira ta ce itama tunda su ka shigo ta ke jin wani ƙauri-ƙauri wari-wari.
Nafy ta ja tsaki ta ce " wasu ƙannen Suhail ne su ka zo ɗazu da abokansu. To cikin su akwai masu shan wiwi. Da ya ke na fita maƙota sai su ka kunna suna sha, anan falon fa, dan raini. Dana dawo na fara faɗa saiga heartbeat ma ya shigo. Kunga dukan da ya mu su kuwa, wallahi da ƙyar su ka gudu a gidan nan" ta ƙarasa maganar tana 'yar dariya.
Zuby da Harira su ka kalli juna, dan sun san Nafy kamar yunwan cikin su. Idan tana shirgo ƙarya su na ganewa, kuma tabbas bayaninta yai mu su kama da zuƙe ta malle.
Zuby ta ce Allah ya kyauta yayinda Amira ta fara ba ta shawara akan kar ta bari ƙannen miji su raina ta.
Sai da su ka yi sallar Azahar sannan su ka buɗe abincin da ta kawo wanda su na buɗewa Nafy na wiki-wiki da ido.
"Wallahi ko a gidan ku ba a kawo mana abinci haka. Ba nama ba komai" Harira ta faɗi tana ƙara cakwkwala miyar ko za ta ga wasu naman bayan yanka biyu da ta tsamo daga ciki.
"Wallahi ƙannen Suhail su ka cinye, ni ban sani bama sai yanzu da ke tuntuni na gama haɗa girkin na zuba a cikin...." ba ta ƙarasa ba Zuby ta ce "Allah Nafy Lubna ta fiki karrama baƙi. Gulma fa mu ka je gidan ta, munje ma ta bagtatan ba tareda ta san da zuwan mu ba amma ta karramamu"
Harira ta ce " ai jinta kawai na ke yi. Tun friday mu ka ce za mu zo fa, amma mu zo ki fara mana maganar ƙannen Suhail. A'a dangin Suhail ba ƙannen sa ba"
Haka su ka ɗan tsakuri abincin kowa ya tashi yana gunaguni. Da za su tafi Nafy ta ɗan haɗo mu su chinchin a leda wanda shima ba wani yawa gareshi ba. Amira ce ta ƙarɓa amma Harira da Zuby kauda kai su ka yi dan wanda su ka ci a gidan Lubna ma yafi wanda ya ke cikin ledan da ta basu yawa.
Sai da ta rako su waje ta ke basu haƙuri tareda mu su alƙawarin idan za su kuma zuwa gidan ta za su ga karramawa mai kyau. Su dai jinta su ke amma sun san akwai matsala a gidan Nafy, auren da bai fi sati uku ba amma ace su zo gidan ta ruwa kawai ta iya basu ba kayan zaƙi-zaƙi ba nama a miya.
Sai da ta shiga ɗaki sannan ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara jin haushin Suhail...
Sai da ta gama shiryawa sannan ta fito ta sameshi a cikin mota bayan ta rufe gidan. Ƙofar gate ɗin gidan su ya tsaya ya ce ta gaida su Alhaji shi zai wuce kallon ƙwallo.
Ta kalle shi da mamaki "me ka ke nufi? Ba za ka shiga ku gaisa da Alhajin mu ba?"
"Nafisa an daɗe da fara wasan fa, so ki ke sai an je hutun halftime kafin na isa wajen ne. Ki je kawai zan zo mu gaisa wani lokacin"
"Ba zan fita ba, dole sai dai mu shiga gidan mu tare" ta faɗa tana haɗa rai.
"Shikenan to bari mu je gidan kallon ƙwallon tare" ganin da gaske ya ke har ya tada mota ya sa ta yi saurin cewa ya tsaya za ta fita...
Tana shiga gidan su zuciyarta na tafarfasa, wai mijin ta ne kallon ball ya fi gaishe da iyayenta muhimmanci. Ta riga ta kimtsa ƙaryar da za ta yiwa Hajiya da Alhaji idan su ka tambayeta ina Suhail.
Kamar yadda ta tsammani tambayar farko da Hajiya ta mata shine ina Suhail? Ta amsa ma ta da cewa shi ya kawota amma ya wuce gaida abokin sa da yai accident da yamma. Zai shigo idan ya zo ɗaukar ta.
A bakin Ladidi da Rahma ta ji labarin zuwan Lubna gidan. Wanda hakan ya sa kishin Lubna ya ƙara ɗarsuwa a zuciyarta, labarin da su Harira su ka bata da kuma wanda ta ji yanzu sun haɗu sun sa zuciyarta tai wani duhu.
Da ta gaida Alhaji a falonsa ta ma sa zancen komawarta makaranta da kuma sanar da shi za ta fara registration a goben.
Shi ma Alhajin dama bai sa a ransa Suhail ne zai cigaba da biya ma ta kuɗin makaranta ba dan haka ya ce "nawa ne kuɗin?"
"Akwai school fees, departmental da zan biya da kuɗin su litattafai...."
"Ki lissafta komai ki turomin nawa duka kuɗin zai kama, idan kin je gida. Zan tura mi ki gobe da safe Insha Allah"
"Na gode Alhaji" ta faɗa tana jin haushi a ranta, ace bayan aurenta ma sai ta dawo gida neman kuɗin makaranta.
Har tara da rabi na dare ba Suhail ba dalilinsa, numbar sa kuma a kashe. Ƙarshe dai ganin dare ya yi ya sa Hajiya ta ce ta je driver ya kai ta gida, ta tashi jikin ta a sanyaye.
©AzizatHamza2020