Duk kyan Namiji

Chapter 23

by @azizat

*💮DUK KYAN NAMIJI💮*

............. ....👳.... ..............


0️⃣2️⃣3️⃣

Yau da sassafe Hood ya fita, dan haka tana gama shiryawa cikin kayan NYSC ɗin ta, ta kira Ado mai Napep wanda Hood ya samar ma ta don ya dinga kaita office da take primary assignment na ta. Sai da ta rufe ko'ina sannan ta fito bayan da ta ji horn ɗin Ado a ƙofar gidan.

Ta leƙa ɗakin Umma ta ce

"Umma nnnna fita" Umma da ke gyaran gado ta ce "a dawo Lafiya Lubna"

Sai da ta zauna cikin keken sannan su ka gaisa da Ado wanda ke binta da kallon mamaki ta jikin mirror. A zuciyarsa yana faɗin 'ko budurwa ai ta ji kunyar fita haka balle kuma matar aure' ya girgiza kai dan ba huruminsa bane ya maida hankalin sa kan tuƙin da ya ke yi.

Ƙarfe biyu ta gota kaɗan ta shigo gidan, gaba ɗaya a gajiye ta ke. Ta leƙa kitchen ta gaida Umma da ke rabon abinci. Umma ta bi bayanta da kallon mamaki 'ba dai haka Lubna ta fita ba?' Shine tambayar da ta ke yiwa kan ta.

Dama tunda ta ga machine ɗin sa a ƙofar gida ta san ya dawo dan haka buɗe ƙofa kawai ta yi ta shiga falon da sallama.

Yana zaune ya sa laptop a centre table yana faman aiki a kai ta shigo. Bai ɗago ya kalleta ba ya amsa sallamar tareda cewa "sannu da zuwa Hayaty"

Ƙarasowa ta yi ta manna ma sa peck a goshi ta ce " sannu da aiki"

Sai a lokacin ya ƙare ma ta kallo lokaci guda kuma annurin fiskar sa ta ɗauke.

"Ba dai haka ki ka fita ba?" Ya faɗa yana ƙoƙarin tattaro nitsuwar sa.

"Yeah, yau Alhamis ka manta CDS zamuje"

"Innalillahi, you mean a haka ki ka fita daga gidan nan, ba jacket ba hijab ba gyale ba komai, like this" ya faɗa yana nunata da yatsa.

"But Hood zafi a ke fa. And...."

"To hell with zafin da ake yi" ya daka ma ta tsawa " haba Lubna! Ai ko a gida bai dace ki fita haka ba balle kuma yanzu da ki ke mata ta" ya da

"What's wrong wwwwith how i dress? Kkkkkayan NYSC na sa which is mandatory for me. Yes ban sa jacket ɗin sa ba saboda ana zafi, but i covered my head. Sai da na ɗaura ɗankwali kafin na sa hular....."

"Ya isa" ya faɗi ransa a ɓace, idan ya ce zai bayyana ɓacin ran sa zai iya rufeta da duka saboda tsabar kishi da ke cinsa.

"Daga yau, ban yarda ki sake fita haka ba. Idan ba za ki saka complete kayan bautar ƙasar ki ba, sannan ki haɗa da madaidaicin hijab then forget about going anywhere"

"You cant dictate how i should live mmmmmmy life, i have right to wear anything that makes me comfortable....."

"To ba a gidan Hudu ba, gidan Hudu dole ki yi shiga ta mutunci yadda...."

"Thank God muma muna da gida and i'm going back home" ta katse shi tareda shigewa cikin ɗaki da sauri.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tareda dafa kan sa yana huci.

Akwati ta jawo ta fara haɗa kayanta tana masifa "inada 'yancin sssssaka kayan da naga dama, and you cant take it away from me" sai da ta gama haɗa kayan, ta cire kayan jikinta ta sa doguwar riga baƙa ta yafa gyale ta ɗau handbag ta jawo akwati ta fito.

Laptop ɗin sa kawai ta gani a falon. Ta yi tsaki ta fito, ƙannen sa na cin abinci a ƙofar ɗakin Umma ta zo wucewa.

"Anty Lubna tafiya zakiyi?" Amina ta tambaya. Ba ta amsa ma ta ba ta fice daga gidan. Ta yi saurin shiga ɗakin Umma tana faɗin " Umma ga Anty Lubna ta fita da babbar akwati"

Umma ta yi salati ta ce "maza bita ki ce ta zo" ta ɗau waya ta fara kiran Hudu.

A ƙofar gida Amina da Bahijja su ka samu Lubna ta tsare wani mai keke, tana tsaye yana shigar da akwatin ta cikin keken.

"Anty Lubna wai ki dawo inji Umma"

"Ki ce ma ta tayi haƙuri but i'm going home"

Bahijja ta ce "Anty yaji za ki yi? Me yaya ya mi ki?"

Ba ta amsa ba ta shige cikin keken. Amina ta riƙe hannunta. "Anty Lubna dan Allah kar ki tafi"

"I'm sorry" ta faɗi tareda cewa mai keken ya wuce su tafi.....

Sosai Umma ta ke ma sa faɗa kamar za ta dake shi.

Kan sa a ƙasa yace "Umma kin ga fa shigar da tayi ta fita daga gidan nan, shiga ne da bai dace ba kwata-kwata"

"Na sani Abba, amma kuma ba haka ake gyara ba. Sai ka bari ta zauna ta nitsu ta huta tukunna, kafin ka fara nutsar da ita kan abinda ta yi. Amma ta shigo gida zafin rana, gajiya, yunwa duk ta shigo da shi amma ka hauta da faɗa ai dole ran ta ya ɓaci...."

Yai shiru yana sauraronta, shi kan sa bai ɗauka abin da ya faɗa zai sa Lubna ta bar gida ba. Saboda ma ya samu sanyi a ransa ya sa ya fice a gidan sai gashi ko nisa bai yi ba Umma ta kira shi wai Lubna ta tafi gidan su.

Sai da ta gama mishi nasiha sannan ta ce da yamma ya je ya dawo da matar sa.

......................

Tana miƙawa mai keke kuɗin sa motar Mama ta iso gidan. Ganin Lubna da akwati ya sa Mama ta yi saurin fitowa daga cikin mota lokacin maigadi yana ƙoƙarin buɗe gate ɗin gidan. Ba ta ce ma ta komai ba ta jawo akwatin ta zo ta sa shi cikin boot ɗin motar ta. Har lokacin Lubna na tsaye tana kallon yadda fiskar Mama ta ke a murtuke tana ma gaisheta ɗazu amma ba ta kulata ba.

"Ki shigo" ta faɗi tareda buɗe ƙofar motan ta shiga. Jiki a sanyaye ta shiga motar itama.

Suna shiga ɗaki ko hijab Mama ba ta cire ba ta ce "mi ya faru na ganki da akwati?"

"Mama i'm not going bbbback to that house"

Lubna ta faɗi

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil. A kan me?"

"Mama wwwwai a gidan sa bazan sa kayan da na ke so ba. Shi a gidan shi sai-sai-sai na sa hijabi idan zan je CDS duk zafin da ake yi. Imagine Mama he's trying to control my life...."

Mama ta buɗe baki tana kallon yadda Lubna ke ta ƙorafin shirme.

"Shi ke nan?" Mama ta tambaya.

"Yes" ta amsa

"Kin ci abinci?" Mama ta tambaya tana ƙoƙarin cire hijabin ta.

"No"

"Je kitchen ki nemi abinda za ki ci. Ban yarda kuma ki gayawa kowa dalilin zuwan ki ba"

Sai da Lubna ta fita daga ɗakin sannan Mama ta yi ajiyar zuciya dan hankalinta ya tashi da farko. Ta san idan ta ma ta magana yanzu ba fahimtarta za ta yi ba, gara ta bari sai ta nitsu tukunna.

Tana cikin chanja kaya Lubna ta shigo ɗakin da gudu ta faɗa banɗaki. Kafin Mama ta yi wani magana ta ji ƙaran aman da Lubna ke kwararawa. Ta jima a banɗakin kafin ta fito bayan ta wanke fiskar ta. Zama ta yi a bakin gado tana fitar da numfashi a hankali.

"Dama bakida lafiya ne?" Mama ta tambaya tana taɓa goshinta.

"Kitchen ɗin na ƙarnin kwai ne"

Mamaki ya kama Mama, yaushe Lubna ta dena son soyayyen ƙwai, abinda ta fison shi ma akan dafaffe.

"I thought you like fried egg"

"Yes, but i dont what's wrong with me this days. Jiya ma sai da na yi amai har sau biyu"

Mama ta zauna gefenta ta ce " did you see your period this month?"

Lubna ta zaro ido, satin da ya wuce ya kamata ta ga jininta kuma ba ta gani ba. Ita tama manta ba ta yi ba.

Ta girgiza kan ta idonta cike da hawaye.

" I'm i sick?" Ta tambaya a hankali.

"Ina tsammanin alkhairi ne, amma dai yanzu mi za ki ci?" Mama ta faɗi fiskanta wasai.

"Potato porridge da zobo"

"An gama 'yar Mama yanzu zan haɗa mi ki"....

Sai bayan sallar la'asar sannan Mama ta kira Lubna, lokacin ta ci abinci ta warware. A hankali ta fara yiwa Lubna nasiha tana nutsar da ita gameda haƙuri a gidan miji.

"Lubna babu auren da babu matsala a cikinsa. Zaman aure zaman haƙuri ne. Kina cewa Hudu ba shi da 'yancin hanaki sa kayan da ki ka ga dama, Lubna he has every right, mijin ke nefa. Ke matar sa ce kuma dole ya nuna kishi a kan ki matuƙar yana son ki...."

Mama ta cigaba da yi ma ta nasiha, Lubna ta yi lamo tana jin ta. Ƙarshe da Mama ta fara labarin wuta da Aljannah sai ga Lubna tana kuka.

"Ke waya gaya mi ki idan anyi faɗa da miji gida ake dawowa?. Ai tsayawa za ki yi ki shirya tsakaninku, ga dabaru nan kala-kala sai wanda ki ka yi amfani da shi. Look barin ba ki sirrin shiryawa da miji and i know indai kina amfani da shi ba za ki sake zuwa gida irin haka ba..."

Sai da ta gama gaya ma ta dabarun sannan ta ce ta kira Hudu ta ce ya zo ya ɗauketa bayan sallar Isha.

Yadda Mama ta tsareta da ido hakan ya sa dole ta kira shi ɗin.

Ƙoƙarin tada machine ɗin sa ya ke zai je gidan su sai ga kiranta ya shigo.

Sallama ta yi a hankali sannan ta ce " wwwwai inji Mama ka zo ka ɗaukeni bayan sallar Isha"

"Angama ranki shi daɗe" ya faɗi cikin farin ciki...

........................

Da ya zo falon Alhaji ta buɗe ma sa, dama Alhajin baya nan. Mama ta haɗa su ta musu nasiha, ta ƙare da cewa " Malam Hudu sai dai fa ka cigaba da haƙuri dan Auta sai a hankali, kasan 'yar boko ce"

Kan sa a ƙasa ya ce "Insha Allah Mama"

Sai da za su fita ta ce wa Lubna gobe za ta kawo ma ta akwatin ta idan za ta wuce Makaranta.

Cikin su ba wanda yaiwa ɗan uwansa magana har su ka kai wajen da ya ajiye machine ɗin sa. Yana tada machine ɗin ta hau bayan sa su ka bar gidan. Suna cikin tafiya su ka wuce wani mai tsire ta ce "Hood wait"

"Minene?"

"Zan ci tsire" ta faɗi a hankali.

Komawa wajen mai tsiren su ka yi ya tsaya zai karɓa mu su sai yaga ta biyo shi. Tana zuwa ta ce mai tsire ya miƙo ma ta tsinke ɗaya. "An gama Hajiya" ya faɗi yana shirin cire naman a jikin tsinken, ta yi saurin cewa ya barshi haka.

Hudu ya zuba ido kawai yana kallon ta. Ta je ta zauna a kan benci tana cin tsiren tana lumshe ido. Ya ƙaraso wajen ta ya ce "ba za ki bari mu kai gida ba. A bakin hanya mu ke fa"

"Dont spoil the fun please, ka zauna mu ci anan" ta faɗi tana cigaba da cin abinta. Inda Allah ya taƙaita ma sa, ba mutane a wajen. Mutum ɗaya ne a ɗaya bench ɗin yana cin tsire shi ma. Ya ɗan tsaya a gabanta saboda ya tareta daga masu wucewa. Sai da ta gama cin tsiren ta ce ya ƙarɓo ma ta wani. Na ɗari biyar ɗin da aka haɗa ma sa a leda ya kawo sai ta ce ba ta son wanda aka sa a leda na jikin tsinken ta ke so. Ba mu su ya je ya ƙarɓo tsinke biyu ya kawo. Ɗaya ta kuma ci ta ce ya isheta.

"Mu tafi ko?"

"Ruwa" ta faɗa a sakalce.

Baya son barin ta a wajen saboda mutumin ɗazu ya sa mu su ido ya riga ya gama cin tsiren sa amma ya ƙi tashi.

"Hayaty ki bari mu je gida mana"

"No" ta faɗi da sauri. Dai dai kunnen ta ya raɗa ma ta cewa " ko mu tafi ko kuma na kissing ɗin ki a nan. And you know my kisses ends with...."

Ta yi saurin miƙewa tsaye, yai murmushi ya miƙa mata handkerchief ɗin sa ta goge hannunta sannan su ka bar wajen.

Ɗakin Umma ya shiga ya miƙa mu su ledar tsire sannan ya shige sashen su. Lubna kam kunyar Umma ya sa ta wuce sashen su direct ba ta bi shi ɗakin Umma ba.

Tana shiga ta cire kayan jikin ta ta faɗa banɗaki ta juye ruwan zafin da ke cikin flask ta sirka ta fara wanka. Da ya shigo ɗakin jin tana banɗaki ya ce " ruwan zai ishemu na shigo mu yi wankan tare?"

"Nooo" ta faɗi da ɗan ƙarfi. Murmushi yai ya fita dan ya locking ƙofar su.

Sai da ta shirya za ta kwanta ta ce "i'm sorry" yai kamar bai jita ba, ya cigaba da danna wayar sa. Ta matso ta ɗaura kan ta akan cikin sa ta ce " ka yi haƙuri dan Allah"

Ya ajiye wayar ya jawota jikinsa sosai ya ce "I'm sorry too wifey, promised me duk abinda ya faru ba za ki yi yaji ba. We'll solve all our problems together, ba sai an jimu ba" ta gyaɗa ma sa kai.

Sosai su ka gamsar da junan su cikin wannan dare. Sai da dukkan su su ka samu nitsuwa ya ce "ashe dai ana son miji amma ake kaiwa kasuwa" ta rufe idon ta tana dariya....

............................

Ya yi kyau sosai cikin shigar shadda ruwan ƙasa da yai. Tana kallo a falo ya fito bayan ya gama buɗe jikin sa da turaruka. Ƙanshin da ta ji yasa ta ɗago kai ta kalle shi.

"Zan ɗan jima ki kulle ƙofa idan na fita, idan na dawo zan yi amfani da key ɗin wajena na buɗe gidan"

"Sai ina kuma?" ta tambaya tana ƙarewa kyakykyawan mijin na ta kallo

"Dinner, yau ake dinan ƙannen Yasir"

Ta ɗan ja ƙaramar tsaki ta ce " dama aka ce mutum tara ya ke bai cika goma ba. Ga kyau har kyau amma duk na banza"

Da sauri ya juyo ya ce "mi ki ka ce?"

"Abu ga shi ɗan tsurut. Duk miƙewar sa baya wuce tsayin yatsata ta tsakiya. Ga rashin kuzari, minti uku, huɗu, biyar ta kwanta, ita da tashi sai wani lokacin"

"Nafy ba dai dani ki ke ba ko?"

"Da wanda ya tsargu na ke, har in ana kiran maza su o'e za su fito ne?, ai sai dai su koma gefe su nemi skirt ko zani su ɗaura"

Babu wanda za a zagi manhood na shi yai shiru.

Cikin ɓacin rai Suhail ya ce "wani irin cin mutunci ne wannan. Dan Uban ki mi ki ke nufi da su o'e sai dai su sa skirt? Da ni ki ke kenan"

"Yo ƙarya na yi ne?, kai kan ka ka san abunka ɗan ƙarami ne. Ba wannan bane ma babbar matsalar. Maimakon ka yi wasa dani ka sarrafa ni, yadda zan yi kukan daɗi na gamsu kamar yadda kowani gwarzon namiji ya kamata ya gamsar da matar sa. Amma ba abinda ka iya, idan ka shiga ciki ma minti nawa ka ke yi?...." saukar mari ya hanata ƙarasa maganar...

...........................

Zaune ta ke a cikin ajin abin duniya ya isheta. Ɗazu da ta ga shigowar Walidah sai da jikinta yai sanyi, Walidah ta yi haske har da 'yar ƙiba. Ita kuma gata nan yadda ta ke da haka ta ke yanzu. 'Yar hasken da amaren nan ma ke yi ita ba ta yi ba. Ba haka ta hangowa kan ta ba lokacin da ta ke soyayya da Suhail.

Harira ta ɗan taƙaleta da biro ta juyo. Miƙa ma ta wayar hannunta ta yi. Nafy ta ƙarɓa wayan tana kallo. Wata writer ce tayi amfani da hoton su na wajen dinner a matsayin book cover ɗin ta. Ƙaramar tsaki Nafy ta ja sannan ta maidawa Harira wayar. Saboda akwai lecturer a ajin Harira ta ɗan yi ƙasa da kan ta, murya ƙasa-ƙasa ta ce " Amaryar Suhail kin yi suna fa. Kinga yadda ake cewa kun haɗu" Nafy ta kauda kai kawai tana tunanin inda za ta samu mafita wa kan ta...

Yau ma dai sai da ta yi amai a office ɗin su, Helen wanda su ke office tare ta shigo da awara office ɗin. Tana jin kanshin awaran ta ji amai ya zo mata.

Tsokalarta Helen ta fara amma bata gane inda zancen Helen ɗin ya dosa ba.

Da ta dawo gida ta samu yaran na cin ɗan wake. Ba ta taɓa cin sa ba, anayi a gidan su kuma tana ganin yadda su Nafy ke son cin abin sosai, amma ba ta taɓa ci ba. Amma yau gani ɗaya ta ma sa taji sha'awar cin sa.

"Baheej idan akwai ssssaura, ni ma ki zubo min abinda ku ke ci"

"Anty Lubna yaushe ki ka fara cin ɗanwake?" Bahijja ta tambaya. Amina da ke danna waya ta ce "Anty Lubna kodai-kodai"