Chapter 26
by @azizat
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣2️⃣6️⃣
Samun Amal ya warwarewa Nafy damuwarta. Tun tana ɗari-ɗari da abun yanzu ta zo ta saki jikinta. Da Suhail da ba Suhail duk sammakal. Shi ɗin ma Suhail ya ga chanji tattare da ita dan yadda ta ke binsa bini-bini a da, yanzu ta dena. Shi yanzu babbar matsalar sa bai wuce yadda zai samu Abba ya barshi ya auri Basma ba. Kuma ya sani ko karan hauka ya cizeshi Abba ba zai taɓa yarda ba. Auren shi da Nafy dududu wata takwas ne fa. Sai dai idan har yanason ya samu abinda ya ke so ajikin Basma sai dai ya aureta duk da yanzu ma yana samu ɗin to amma ya san idan har ya aureta zai samu ninki ba ninki domin yanzu kaman chicken change ta ke bashi.
Basma Bukar ɗiya ce ga Senator Alhaji Bukar Mele wani hamshaƙin mai kuɗi kuma ɗan siyasa ne. Asalin sa ɗan Maiduguri ne amma yana zaune da iyalin sa a Abuja. Basma ita kaɗai ce 'ya mace a wajen Alhaji Bukar kuma yanaji da ita sosai. Dawowarta daga ƙasar Spain kenan inda ta haɗa degree ɗin ta na biyu shekararta ashirin da uku. A wajen biki ta haɗu da Suhail kuma kyaunsa da yauƙinsa ya gigitata. Duk girman kan ta saida ta sauke ta nemi magana da shi. Tun da kuwa su ka exchanging contacts ya zamana kullum suna manne a waya. Saboda Basma kusan duk weekend Suhail yana Abuja. Yadda Basma ke sake ma sa kuɗi ya sa ya ƙarara gigicewa a kanta.
Kuɗi su ne muradin Suhail, bai da niyyar neman su ta wahala sai ta daɗi. Tun yana secondary school daya gane yadda 'yan mata ke haukan son shi ya sa a ran sa auren jari zai yi. Auren Nafy ma ya zo ma sa ne a lokacin da baida yadda zai yi...
Zuwan Suhail Abuja duk weekend bai taɓa damin Nafy ba, asalima ƙofa ce ta buɗe ma ta domin ta ji daɗin ta ba tareda ɗar-ɗar ba.
Aurenta da Suhail da kuma haɗuwarta da LK ya banbanta ma ta namiji da muna namiji. Ta gane abin ba daga kyau bane. Domin duk kyaun namiji idan ba zai iya tsayawa ya sauke nauyin sa yadda ya kamata ba to a wajen mace fa tamkar fanko ya ke.
Mace 'yar gata ce, ka nuna ma ta so ka nuna mata kulawa, ka ciyar da ita, da daddare ka sauke hakkin ka yadda ya kamata. Malam ko yaji ba za ta yi ba, kuna nan manne da juna, sai dai ayi faɗa a shirya kawai.
Duk kyaun mutum duk kuɗin ka idan ka gaza ta ɓangaren kula da mace musamman wajen raya sunna da kuma nuna ma ta so da ƙauna to fa kamar hoto haka za ta dinga kallon ka.
(Zamani ya ƙawata mana zina ta zamto tamkar Ado ko kuma abin yayi. Ba ga 'yan mata da samari ba harda mazajen aure da matan aure. Ada maza ma su aure aka sani da neme-nemen mata amma yanzu kam har matan aure su na yi. Sai dai Allah ya sa mu fi ƙarfin zuciyoyin mu. Kuma abin ba yare ba addini, kowacce irin mace na iya yi. Mafiya yawan matan aure da su ke wannan abun sun fi kama hujja da rashin gamsar da su da mazan su ke yi, yayinda wasu kuma rashin godiyar Allah ne kawai domin suna yi ne don kuɗi ko ƙyale-ƙyale ko kuma dan samun wani abin duniya wanda sun manta duniyar kwata-kwata mai ƙarewa ce.
Iyayen mu na da da daɗi ba daɗi, da gamsarwa ba gamsarwa za su zauna da mijin su tsakani da Allah har mutuwa ta raba ko kuma idan mutuwar aure ta zo. Amma mu matan zamanin yanzu bamuda wannan haƙurin, but still idan har kin kasa samun nitsuwa da mijinki kin yi magana kin yi dabaru abu ya ƙi yiwuwa is better ku rabu akan ki je ki faɗa zina, domin babban kaba'iri ne.
Sannan mu 'yan matan yanzu, mu kan sa buri akan mazajen da zamu aura. Idan ba mu bi kuɗi ba zamu bi kyau to duk wannan ba su ke riƙe aure ba. Wata ma dan kawai ta haɗu da saurayi wanda ke aiki a Abuja sai ta kori tsohon saurayin ta da su ka yi shekara da shekaru suna tare, wata kawai dan saurayinta ya yi karatu a ƙasar waje shine abin burga har zai sa ta aureshi not minding halin sa ko ɗabi'un sa.
Sana'a ba abin gudu bane kinada saurayi ko miji Carpenter,Tailor, Mechanic, ɗan achaɓa, mai Napep, bricklayer, ɗan kasuwa ne yana saida kifi ne ko kayan gwari ya ke saidawa, Etc. Ki rungume shi ki bishi da addu'a kawai ya zame mi ki alkhairi. I know wassu iyayen su suke tunzura 'ya'yan su da cewa sai mai degree ko masters, a'a sai mai aikin banki ko likita ko manager a wani kamfani. All this doesnt matter idan har 'yar ki ba ta samu farin ciki da kwanciyar hankalin aure ba.
Mu ji tsoron Allah a duk inda mu ke, kin samu wanda yai boko sosai fani'ima, idan ma mai sana'a ki ka samu fani'ima as long as halal ya ke samu thats all that matters ki bi shi da addu'a kawai. Allah ya sa mu gane amin)
..........................
Waya su ke da LK, Lawal Karamba saurayin da Amal ta haɗasu wata biyu da su ka wuce kenan. Sallamar su Harira ya sa ta yi saurin katse kiran bayan ta ce ma sa ta yi baƙi.
"Oyoyo, Zuby yau ku ne a gidana" ta faɗi tana dariya.
"Ai wallahi kin bamu mamaki Nafy, wato ma saboda mu bamuda aure sai sa ki ka gujemu ki ka koma wajen matan aure sa'annin ki ko?" Zuby ta faɗi tana hararanta.
"Haba dan Allah, wanni irin magana ne wannan"
Harira ta ce " mun san komai ai, inace saboda Amal Idris ki ka dena kulamu. Matar da na san tarihinta, tantiriyar 'yar bariki ce da ta yi ƙaurin suna. Ni bana tantama idan aka ce ba ta dena halinta na da ba duk da kuwa da aure a kanta."
"Kayya Harira, ke kowanni gulma kin sani. A ina ki ka ji wannan kuma"
"Chan ta matse mi ki. Mun zo mu sanar da ke za a kawo kayan auren Zuby ranar asabat, idan kinga za ki iya ki zo ki gani" Harira ta faɗi tana ƙarewa Nafy kallo.
Nafy ta yi 'yar dariya ta kalli Zuby ta ce " ƙawas ki ce abin ya zo"....
Ba su bar gidan Nafy ba sai da su ka ma ta tatas akan sharesu da ta ke yi musamman tunda aka yi hutu a makaranta ko sau ɗaya ba ta neme su ba har gashi hutun na shirin ƙarewa.
.............................
Sosai Lubna ke samun kulawa daga ɓangaren iyayen mijin ta zuwa wajen na ta iyayen. Cikinta ɗan wata bakwai ya ƙarɓi jikin ta. Ta ɗan yi laulayi watanni ukun farko amma yanzu tana jin jikin ta normal. Cikin iyayen Hudu ba wanda ya sanar ma sa Lubna na ɗauke da ciki, yo da kunya ai. Su Amina kuma tunda Lubna ta mu su kashedi akan kar su gaya ma sa sai su ka ja bakin su su ka yi shiru.
Wata shida ya kamata Hudu yai amma ya kira wai wasu hidimomi sun riƙe shi aƙalla zai ƙara wata ɗaya kumadu. Ranan Lubna sai da ta ji kaman ta gaya ma sa tanada ciki saboda takaicin rashin dawowar sa.
"Ke da kin dena sona, idan na ce ki ɗan min dabaru ma sai ki ƙi" ya faɗi a lokacin da su ke video call. Tun da cikin ta ya fara tasowa ta dena ma sa 'yan dabarun da ta saba ma sa domin ya samu nitsuwa idan suna video call.
"Ba abinda zzzzan yi tunda har wata ɗaya za ka ƙara dan ka ji daɗin zama acan"
"Haba Hayaty, ke kan ki kin san i miss you like crazy. Ba yadda zan yi ne kawai."
"I miss you more" ta faɗi kaman za ta yi kuka...
.............................
A bakin gate su ka haɗu da Suhail wanda fitowar sa kenan daga gidan, sai da su ka gaisa da Usman sannan ya wuce. Walidah kam daga sannu ba abinda ta kuma ce mi shi. Ganin Suhail ya sa ta ƙara godewa Ubangiji da ya sa ta yiwa iyayenta biyayya, tunda gashi Usman ya zame ma ta komai. Suhail duk ya koɗe da ka ganshi ka ga wanda bashida nitsuwa, to ina zai samu nitsuwa shi daya sa shaye-shaye a gaba.
Abba ne ba lafiya su ka zo gaishe shi duk da kuwa itama ba isashshiyar lafiyar gareta ba haihuwa ko yau ko gobe.
Sai da su ka gaida Abban ya fara mu su faɗan miyasa za su zo bayan Walidan ma ba lafiya gareta ba.
"Abba kuma shikenan ba zan zo na gaisheka ba" ta faɗi a shagwaɓance.
"To to angode da gaisuwa ya jikin na ki"
Ta amsa da sauƙi....
Kwanan su uku da zuwa gaisuwa Walidah ta haihu. Ta samu ɗanta namiji. Murna wajen Usman ba a magana. Gidan su Walidan ma murnan ake kamar a kanta aka fara samun jika, duk da kuwa na ta ne jika na biyar a gidan....
Ranan suna anyi shagali sosai inda yaro ya ci suna Muhammad Ɗahir.
Daga gidan sunan ma Nafy ta wuce gidan su, dan ta kwana biyu ba ta je ba. Da ta san abinda za ta tarar kenan da ba ta je bama. Hajiya ce ta sata a gaba akan ko sun je asibiti itada Suhail. Ga Walidah da aka yi auren su kusan tare ta haihu ga Lubna na ma ta kusa haihuwa ita kuma shiru.
"Hajiya kina magana kaman wanda na shekara biyar ban haihu ba. Kowa fa da lokacin sa, ni nafiso ma na haihu bayan na gama makaranta"
"Uban ki Nafisa" Hajiya ta faɗi tana ma ta daƙuwa.
"Ki je asibiti a duba ki idan bakida matsala shima sai ya je"
Jin Hajiyar kawai ta yi amma haihuwa yanzu haram. Yaushe ma ta fara moran jikinta, ai haihuwa sai nan da shekara uku.
Sai da za ta tafi Hajiya ta ce " Nafy ko kin fara planning ne?"
"A'a Hajiya"
"To wallahi ki je asibiti a duba ki"
.........................
'Yar ƙaramar liyafa su ka shirya saboda tarban Hudu. Duk da dai iya yasu-yasu ne amma an shirya ko'ina, kayan ciye-ciye da lashe-lashe kam ba'a magana.
Tun jiya Lubna ta je aka mata ƙitso da jan lalle irin wanda Hudu ke so...
Ƙarfe tara na safe jirgin su ya sauka daga Abuja, inda daganan ɗin kai tsaye park ya wuce ya nemi mota, bai samu motar Bauchi direct ba kawai ya shiga ta Jos. Lokacin da ya iso gida ƙarfe biyar na yamma.
Shigar baƙar jeans da bakin shirt sai baƙar Balenciaga sneakers da ya sa a ƙafarsa. Kasancewa da ya shigo Nigeria akwai zafi ya sa tun a Abuja ya cire baƙar blazer da ya sa akan shirt ɗin. Yai haske yai ƙiba, jikinsa sai sheƙi yakeyi.
Tun daga ƙofar gida yara keta ihun Hudu ya dawo Hudu ya dawo. Da zugar yara ya shigo gidan wanda su ka taya shi ɗaukan kaya sai da ya sallamesu sannan su ka tafi. Ɗakin Umma ya shiga suka gaisa ya tambayi Baba ta ce yana kasuwa.
Baza ido ya ke ko zai ga shigowar Lubna amma ba ta shigo ba. Sun jima suna hira da Umma kafin Umman ta ce ka shiga ka gaida iyalinka. Ya sosa kai ya fita dan dama tun ɗazu a matse ya ke.
Da hanzarin sa ya shiga falon yana kiran Hayaty. Kayan daya gani an jera a tsakiyar falon ya tabbatar ma sa nayi ma sa tanadi na musamman. Ɗaki ya shiga da sauri amma bai gan ta ba, ya leƙa banɗaki still batanan. Da ƙarfi ya fara kwallawa yaran kira.
"Amina, Bahijja.....ina Antyn ku ta ke"
Amina sai dariya ta ke yi. Yayinda Bahijja ta ce" Yaya tana ciki fa ba ka ganta bane" ita ɗin ma dariyar ta ke.
Sake duba ɗakin yai harda leƙa ƙasan gado da ƙasan kujerun falo. Da sauri ya fito daga falon a harzuƙe sai dai turus ya tsaya lokacin da ya tozali da matar sa tsaye ita ɗin ma da alama falon za ta shigo. Kallonta ya ke yi sama da ƙasa, lokaci guda kuma ya calla ƙara. Da sauri Lubna ta sa hannu ta rufe bakin sa tana cewa " Umma"
Hannu na rawa ya fara shafa cikin na ta yana cewa " Hayaty yaushe, why, when...."
"Abba ka san dai a gaban ƙannen ka ka ke ko" muryan Umma ta ƙatse shi. Da sauri ya ja hannun matar sa su ka shige sashin su sannan ya sa key a ƙofar...
©AzizatHamza2020