Duk kyan Namiji

Chapter 33 (The end)

by @azizat

*💮DUK KYAN NAMIJI💮*

............. ....👳.... ..............


0️⃣3️⃣3️⃣

Wasa-wasa sai da Alhaji yai sati biyu a asibiti kafin aka sallameshi. Har lokacin bai daina jin ɗacin abinda Nafy ta aikata ba.

Mama ta gama zuba ma sa abinci ta shiga ɗaki dan ta ɗauko maganin sa sai dai har ta dawo bai fara cin abincin ba. Yai tagumi yana tunani.

"Haba Alhaji, ka dai ji mi likita ya ce akan ba ƙaramin rabo ka yi ba, da ba ka samu paralyse ba, dan Allah ka dena tunanin nan"

"Fatima, ka haifi ɗiya ka aurar da ita ga wanda ta ke so amma ba ka tsira ba, ki duba abinda yarinyar nan ta yi, ba ta tsaya anan ba har tana neman kashe auren 'yar uwarta"

"Alhaji zamani ne, ka haifi yaro ba ka haifi halinsa ba. Sai dai kawai mu ci gaba da yi mu su addu'a. Ka ci abinci sai ka sha magani"...

......................

Sai da Alhaji ya warware sosai sannan ya kira Nafy akan ta fito da miji cikin wanda su ke zuwa nemanta dan ba za ta zauna tana ma sa ashshararanci a gida ba.

"Alhaji banda wani tsayayye" ta faɗi a ɗan tsorace

"Na ba ki sati biyu ki kawo wanda ya miki, idan ba haka ba zan aurar da ke a wanda na ga dama"

"Alhaji dan Allah ka bari na koma makaranta wallahi saura sati biyu mu fara jarrabawar gama Makaranta"

"Ja'ira akwai abinda karatun ya tsinana mi ki ne banda dama da ya buɗe miki na ki dinga abinda ki ka ga dama. Idan kin yi wani auren kya cigaba da karatu idan mijinki ya barki amma anan gidan kam kin gama karatu "

Har sati biyun dai Nafy ba ta kawo kowa ba, to wa za ta kawo duk cikin ma su zuwa ba wanda ya mata, 'yan dama-daman ma da ta musu maganar su fito ma guduwa su ka yi.

Abbas kam wata guda kenan da asirin sa ya tonu aka jefa shi prison, ya je sun haɗu da wata Hajia a Kaduna ashe mijin matar na bibiyarsu. Har hotel ɗin ya zo ya sa aka kama Abbas. Ya sha bugu a wajen bodyguards ɗin mutumin kafin daga bisani aka miƙashi ga 'yan sanda abinka da masu kuɗi tuni akayi cuku-cuku aka haɗa ƙarya da gaskiya sai ga shi an turashi zaman yari na shekara biyar...

Aure ne aka yi daga fatiha sai kai amarya ba wani hidima ko taro, Alhaji ya hana, da ke Hajia ma ta saduda yanzu itama ba ta yi wani yunkurin yin wani hidima ba . Wani distant cousin ɗin su ne a can Ningi Alhaji ya aura ma ta. Munnir Ilyasu malamin makarantan sakandare ne yana da mata ɗaya da yara biyu.

Zaman gidan dai da daɗi ba daɗi tana zaune, babbar matsalar ta shine Nusaiba, Nusaiba tanada baƙin kishi kusan koyaushe su na cikin musanyawa junan su baƙaƙen maganganu. Ba laifi Munnir yana ƙoƙari, sai dai shima ɗin ba irin mijin da ta ke buri bane, yanada ƙoƙari kam ba kaman Suhail ba sai dai he's not romantic. to ina iya romance a wajen Malamin Maths? Lol...

Tana kwance hayaniyar su Bahijja ya tasheta. Dukkansu sun tare a gidanta saboda Hudu ya biyawa Baba da Umma kujeran Hajji. Kwana uku kenan da tafiyar su.

Ta fito daga ɗakinta ta nufi falo inda hayaniyar ke tashi.

"Ku dai ba za ku bar mutum yai bacci lafiya ba. Yanzu miye na ihu"

"Anty Lubna wai Ɗahir ne ya ce Hibba ta kira sunan sa. Harda rantsewa" Bahijja ta amsa ma ta

Lubna tai murmushi ta ce " Ina sauran?"

"Su na kitchen"

Leƙa kitchen ɗin ta yi taga girki su ke yi " Sannu da aiki fah"

" munga baccin na ki yai daɗi shiyasa ba mu tashe ki ba"

"Kun kyauta ai"

Sai da ta koma ɗaki ta ga wayarta na ringing ta yi saurin ɗauka saboda sunan da ta gani.

Khairy ce ta kira akan ta haihu da safe ta samu ɗa namiji. Lubna ta sa ihu tana tsalle...

"Ba za ku zo bikin Yaya Abdallah ba kenan?"

" Auta ma zo mu ga amarya ƙarshen shekara idan mun shigo ƙasar"

"Oh im happy ffffor you sis"

"Sai anjima, barin kira Mama" daga haka ta kashe wayar.

Da yamma lis ta je gidan su dama Hudu ba ya gari.

Shirye-shiryen biki ake gadan-gadan har sabon fenti aka yiwa gidan na su.

Su na zaune da Mama su na duba wasu zannuwa Mama ta kalli Lubna da kyau ta ce " dama dalilin yaye Hibbatullah kenan?"

Lubna ta sunkuyar da kai. Mama ta yi murmushi ta ce "Allah ya raba lafiya" Lubna ta amsa da amin.

Suna cikin hira Nafy ta kira Mama sai da ta amsa wayar su ka gaisa, sannnan Nafy ta fara roƙon Mama akan ta roƙa ma ta Alhaji ya amince ta zo bikin Ya Abdallah.

"Zan yi iyaka ƙoƙari na, kin san indai maganar ki ne Alhaji ba son ji ya ke ba"

Sai da su ka gama wayar Lubna ta ce " i pity her Mama"

"Ni ma ina tausayinta, son zuciya da ƙwaɗayi shi ya kaita ga halin da ta ke ciki yanzu. Allah ya sa dai ta nitsu" Lubna ta amsa da amin...

Duk yadda Mama ta yi akan Alhaji ya bari Nafy ta zo bikin Abdallah amma Alhaji bai amince ba. Dama tunda aka ɗaura aurenta ya ja ma ta kunne akan bai yarda ta zo gidansa ba sai dai idan shi ya nemi ta zo, haka aka sha biki babu ita. Abdallah yatare da amaryarsa Hafsah, 'yar Bajoga ce da ke Jahar Gombe sai dai a Bauchi su ka haɗu a bikin wani abokin sa...

Suhail da amaryar sa Basma su na zaune lafiya a Abuja. Watan su biyu kenan da aure. Yanzu kam ya dena shaye-shaye hakanan yana ƙoƙarin kula da Basma sosai musamman saboda bayaso abinda ya faru da Nafy ya faru da Basma, dan harda sakacinsa a dalilin cin amanarsa da Nafy ta yi. Shaye-shaye da ya dena kuwa ya taimaka ma sa wajen samun kuzari sosai.

Ƙazantarsa ta ɗan ragu atleast yanzu yana flushing immediately yai bayangida (Lol 😂) ko dan bayaso ya upsetting amarya...

.........................

Rayuwa ta cigaba da tafiya, ayi faɗa ayi daɗi Lubna na nan da mijinta su na renon cikinta wanda haihuwa ko yau ko gobe.

Shirye-shiryen bikin Rahma da Ja'afar ake yi, zumuncin da ba a haɗa ba lokacin Lubna da Abdallah shi yanzu za'a haɗa, sai dai wannan karan dukkan su biyu suna son junan su.

Aabid na gama service Alhaji ya ce sai aure dan tsoron yaran yanzu ya ke dan haka duk da Aabid bai samu aiki ba tukunna Alhaji ya buɗe ma sa shago a Kano sannan ya biya mu su hayan wani gida na Shekara uku.

Wannan karan Alhaji ya bari Nafy ta zo bikin Rahma. Ya rage fishi da ita ne wata ɗaya da ya wuce lokacin da ta haifi bakwaini yaron ya koma dan ta wahala a haihuwar sai da aka ƙara ma ta jini leda uku.

Sosai Nafy ta nutsu to Idan ba ta nitsu ba ya za ta yi tunda mutuwar Amal ya ma ta ishara.

Amal ta mutu watanni uku da su ka wuce, ta bi wani kwartonta guest house ɗin shi a can Lagos lokacin mijinta ya tafi saro kaya a Dubai. Ɓarayi su ka shigo gidan abu ya zo da ƙarar kwana aka bindige Amal shi ma Chief AbdulLateef Agbaje an harbe shi sai dai shi bai mutu ba.

Hajia kam lamari na duniya ya nutsar da ita. Ta ajiye makaman yaƙi ta dena gaba da Mama. Lokacin bikin Abdallah ma tare su ka haɗa kai aka yi biki lafiya. Wannan bikin ma komi aka tambayeta sai ta ce a tambayi Hajia Fatima ita ce uwar ango da amarya.

Anyi biki lafiya aka kai amarya gidanta achan Kano. Duk yadda Lubna ta so ta yi rakiyar amarya Hudu bai barta ba, Mama kam faɗa ta mata saboda wautar Lubnan.

Kwana uku da kai amarya Lubna ta haihu. Ta samu identical twins duka maza, wahalan da ta sha wajen haihuwa ya sa ta ce da Hudu daga wannan ta dena. Hudu dariya yai ya ce  "Hayaty ki yi addu'a kawai Allah ya kawo ma na ma su albarka"

Ranan suna an sha shagali sosai, dan Alhaji ma ba ƙaramin kuɗi ya kashe ba saboda yaran Lubna ne jikoki na farko da su ke 'yanbiyu a familyn su.

Yara su ka ci sunan Alhaji da Daddyn Lubna wato *Hassan da Hussain* amma ana mu su inkiya da *Aahil da Aadil*

Watanni biyu da haihuwan Lubna, Hafsah matar Abdallah ta haifi 'yanbiyu mata, su ka ci sunan Hajia da Mama wato *Zainab da Fatima*...

***

Usman ya shigo gida ɗauke da Muhammad, tare su ka je aka musu aski.

Waya su ka samu Walidah na yi, ya sauke Yaron sannan ya miƙa ma sa ledar ice cream da su ka siyo.

"Kar ka ɓata kayanka fa Abbana, ka sha a hankali"

"Sweet ina nawa ice cream ɗin" Walidah ta faɗi a shagwabance

"Ki ka ce chocolate ki ke so kuma an siyo miki"

"To ai baka ce za ku biya ku sayi ice cream ba"

"O'o wannan junior ɗin da shegen kwaɗayi ya ke"

Ta rolling idon ta sannan ta buɗe chocolate ta fara ci.

"Oh na manta in gaya ma ka, da Ya Suhail mu ke magana lokacin da ka shigo. Kirana yai wai Basma na da ciki, ka ga yadda ya ke ta zumuɗi"

Usman ya ce "Allah ya raba lafiya" ta amsa da amin...

............

Gidan su Hudu ta je gaisuwa, Baba ne ba lafiya a gidan ta bar 'yan biyunta, dama ta gaji da rigimar su. Hibba kam na wajen Mama kwananta biyu ma a can.

Tana shiga falo ta kunna wuta sai ta ga an decorating falon da flowers da balloons. Wani kati ta gani akan center table an rubuta *go to your room* ta yi murmushi ta wuce ɗakinta anan ma ta ga wani card ɗin akan gado tareda wani paperbag ta karanta card ɗin *wear this dress* ta buɗe jakar ta fiddo da wata sexy gown kalar strawberry ta yi murmushi ta wuce banɗaki a gurguje ta yi wanka ta fito ta sa kayan ta ɗan shafa powder ta sa kwalli sannan ta shafa janbaki kaɗan sannan ta fesa turaruka. A kan dressing mirror ɗinta ta ga last card ɗin da aka rubuta * looking sexy?, now to my room*

Flat shoe ta saka kalar golden sannan ta saka ɗan kunnenta na gold wanda Alhaji ya siya ma ta lokacin aurenta. Kai tsaye ta wuce ɗakin sa, ya sha decoration sosai sannan gefe guda kuma cake ne akan ɗan ƙaramin table an rubuta *happy birthday to the angel of my life*

Yana tsaye ya sha farin suit.

"You look handsome" ta faɗi tana murmushi.

"And you look ravishing my queen"

Kissing hannunta yai sannan ya ja ta ta yanka cake ɗin.

"I have a gift for you Hayaty"

Ya miƙo ma ta wata ƙaramar gift box. Ta amsa ta buɗe " ya Allah! A car. My star you ddddont have to...."

"Kin cancanci fiye da haka matata, uwar 'ya'yana. Kin soni ba tareda kin yi la'akari da sana'ata ba ko inda na fito, kin soni tsakani da Allah. Yanzu da Allah ya buɗa mini dole na kula da ke"

Ya sake miƙa ma ta wani babban envelop ta amsa ta buɗe.

"Bbbbut the twins are young"

"Na sani, haka za su haƙura har mu je mu dawo. Ai naga ba su wani damu da nono ba"

Rungume Hudu ta yi tana kuka. Kyautar mota da Kujeran Hajji lokaci guda.

"I cant thank you enough Habibi" ta faɗi tana ƙara shigewa jikin sa

"You know how to thank me ai" ya faɗa yana murmushi.

" ni kan ka kaini na ga motata"

"The car can wait baby" ya faɗi tareda ɗaukar masoyiyar sa bai sauketa ko ina ba sai kan gado....


*The end*

*Alhamdulillah*

Ina godiya ga duk wanda ya karanta labarin nan daga farko har ƙarshe. Thank you.

Allah ya bamu Ikon amfani da faɗakarwan da ke cikin sa, ya kuma gafarta mini kurakuren da na yi a ciki.

*To all lovely single girls out there, its not always about the looks... rufin asiri, kwanciyar hankali da soyayyar gaskiya ta fi DUK wani KYAN NAMIJI*

Godiya ga waɗannan bayin Allah wanda comments ɗinsu ke sa ni nishaɗi a koda yaushe:

Anty Hauwa Jiddah

Sis Fatimah Kano

Anty Murja Na'ikke

Sis Surayya

Sis Jamila

Mommy na Aisha Maina

My two sisi Karimat and Rafi'at.

Da duk waɗanda suka so littafin a lokacin dana rubuta shi dama yanzu da na sake dawo da shi.

Jazakumullahu bil jannah, amin.