17-18
๐๐
๐
17
Bayan Usman ya shiga Argungu,the following day ya hadu da Nasir. Ya fada ma Nasir zuwan shi Zamfara da duk abubuwan da suka faru.
Nasir kawai zba mishi ido ya yi,yana mamakin wannan soyayyar da Usman ya ke yi wa Hauwa. Tun da ya ke a duniya,ko a cikin tatsuniya bai taba jin labarin SOYAYYA irin ta Usman ba... Shi wallahi bai ma yadda da Hauwa, amma ba yadda zai tun da Abokin sa na sonta.
Juyowar da Usman zai yi,sai ya ga Nasir ya zuba mishi idanuwa,kallon shi kawai,yake yi,ba bu ko kyaftawa.
"Nasir lafiya ka ke kallo na haka,kamar ka ga wata halitta? Ni fa shawara na zo nema wurin ka." Cewar Usman.
Ajiyar zuciya Nasir ya yi ya ce " Ni dai ba shawara ka zo nema wuri na ba, Usman. Tun da ba ka nemi shawara ta ba a zuwanka Zamfara,to meyasa za ka nema yanzu?"
Haba Nasir ya za ka yi min haka,Kai kasan zuwan nan ban zauna nayi planning din shi ba ,abu ne kawai ya ta so. San nan nasan ko kowa bai fahimce ni ba ,Kai za ka fahimce ni, kasan cewar ka Aminina,kuma dan uwana ,wallahi Nasir idan ba ka fahimce ni ba,to babu Wanda zai iya fahimtata. Usman ya na maganar cikin kunci!
Ganin yanayin da Usman ya ke ciki ya ba wa Nasir tausayi,kasan cewar damuwar da Usman ya ke ciki. Shi kanshi Nasir ,abun da farko haushi yake ba shi,ganin yadda friend din shi mai son wasa da dariya amma lokaci kadan SOYAYYA duk ta birkita shi,kamar ba shi ba.
Amma daga baya yayi understanding abokinsa sai ya dawo jin tausayin shi.
Shirun da Nasir ya yi yana tunani,shi ya sarewa Usman kwarin guiwa.
Ajiyar zuciya yayi, har ya tashi zai tafi,a sanyaye...
Motsin da Nasir ya ji shi ya ankarar da shi cewar Usman wuce wa zai yi...
Sai ya yi saurin rike...
๐๐๐๐
๐๐
๐
18
Ya yi saurin rike hannun Usman,ya sa ke mayar da shi wurin zaman sa. "Haba dan uwa, mai ya yi za fi shi ba wuta ba" ? Cewar Nasir. Ai bamu gama magana ba,amma shi ne za ka tafi.?"
Ahankali ya sauke ajiyar zuciya..."Da gaske za ka taimake ni?"
"Me zai hana in taimake ka,ai babu abun da za ka nema ban yi maka ba,matukar ba sabon Allah ba ne." A cewar Nasir
Usman bai san lokacin da yay yi hugging Nasir ba,ya na murmushi.
"Toh yanzu was the plan da zamu yi kafin muje wurin Mama?"
Murmushi Nasir ya yi...Kai dai akwai ka da zanzana wallahi.
Dundu Usman ya kai mishi``` ...
```Da sauri Nasir ya jaye ya na dariya.
"Ni da ya kamata ace ka na lallabawa,amma don cin zali,za kazo ka yi min dundu...sai in fasa zuwa wurin Mama"
Hararar shi Usman ya yi,"ba sai ka fasa zuwan ba mugani"
Shima Nasir, hararar sa ya yi "sai ka ce zai iya zuwa shi kadai" yana danne dariyar da ke taso ma sa"...
Da sallama su ka shigo falon mama. Sun iske ta zaune tana kallon TV...
Su ka duka har kasa,su ka gaishe ta. Tun da su ka gaishe ta, Usman ya koma gefe,kansa a duke kamar sabon maraya...
Mama tasan akwai abun da su ke so,kuma ko wane irin abu ne toh yana da mahimmanci.
Ta san halin su tun ba yau ba,idan su na son wani abu,toh za ka gan su sumisumi kuma kan su a soke kasa...
Ta yi murmushin manya...ta ce "Nasiru ba ri in kawo maka abinci,tun da Abokin na ka miskilancin ya tashi,balle ya zubo muku abinci"
Da sauri Nasir ya ce "wallahi mama a koshe nake."
"Toh shikenan...ta koma wurin zamanta."
Tana kallon su ta gefen ido su na kuskus,ba ta dai ce musu komai ba.
Nasir ne ya katse shirun da cewa "mama dama akwai maganar da ke tafe damu...ko daga jin maganar sa kasan a tsorace yake,gudun kar asamu akasi...
"To Nasiru Ina jin ka, Allah ya sa lafiya,tun da naga Babana ya sawo ka a gaba nasan "ba za a rasa nono a rugga ba"
"Lafiya lau mama,dama kan maganar yarinyar da Usman ke so ce."
" Alhamdulillah! Masha Allah, lallai wannan babbar magana ce,ta na maganar ta na gyara zaman ta."
Ka gani ko Nasiru, Allah maji rokon Bawa ya karbi adduar mu,ya cire mishi son yarinyar can...ya ma sunanta...?
Ba Usman ba,har Nasir sai da ya dago kan sa da mugun speed jin abun da mama ke cewa...
"Ah Ina yarinyar ta ke?" Mama ta jeho mu su wannan tambayar.
Cikin karfin hali Nasir ya ce " ba anan garin ta ke ba."
"Allah sarki,a wane gari take?"
Ahankali Nasir ya kwashe komai ya fada wa mama...
"Tashin hankali wanda ba a sa masa rana!"
Yar mutan Argungu โค๏ธ