TAKAICIN UBA

8

by @nazeefahnashe

TAKAICIN UBA…….



Na



Nazeefah Sabo Nashe.


***.






8….



Driving yake yana sauraron Karatun Alkur’ani daga k’ira’ar sudais. Shi ka’dai ne abinda yake saurare ya rage masa zugi da ra’da’din rashin Hibbarsa. Ko da ya yi parking a makeken wajen shak’atawar kasa shiga ya yi ya shiga cusa hannayensa cikin tarin sumar gashin kansa da ya gadota daga gurin Ummeeynsa. Ya dinga cukuikuye gashin yana jin kansa na sara masa kafin ya mayar da seat ‘din kujerar ta sa ya koma ya kwanta tunanin rayuwarsu da Hibba na sake bujiro masa….


K’arar da wayarsa ta yi ne ya farkar da shi daga wancan tunanin, ba sai ya kalli screen ‘din wayar ba ring tone ‘din ya sanar da shi wacece ‘Ummeey’ ya fa’da yana sakin murmushin gefen kumatu kafin ya jawo wayar ya kanga a kunnensa. Cikin muryar shagwab’a kamar yarda ya saba mata magana ya ce “Hayateey!” Ummeey daga ‘daya gefen ta saki murmushi tana jin da’din sunan da yake kiranta da shi. “Amin ya gida hope dai kana lafiya, muma kwanan mu uku a Nigeria.” Ya ‘dan yi dum da waya a kunne kafin ya ce “Nigeria kuma how comes? Ya aka yi Abeey ya barku kuka je?” Dariya ta yi sosai kafin ta ce “Da kansa ya sauko ya ce mu je. Yauwa ba wannan yasa na kira ka ba, Amin bu’de kunne da kyau ka ji lokaci ya yi da ya kamata ka yi aure.” Wani irin dum ya ji k’irjinsa ya buga, Ummeey zata sake janyo masa wani jidalin kenan shi tun yaushe ya cire maganar aure a rayuwarsa, ya Riga ya gama da wannan babin an gama samun mata na gari tun bayan da Hibba ta rasu. “Ba ka ji ni ba ne?” Ummeey ‘din ta fa’da with a serious tone. Sakin ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce “Na ji Ummeey, amma ina neman alfarma, not now please, wallahi ban shirya aure ba, ko kuma na ce na gama buk’atarsa a rayuwata tunda dai Hibba ta haifa min mai yi min addu’a.” Cikin b’acin rai Ummeey ta ce “Ko da nice nake so?” Muryarsa a cunkushe ya ce “Don Allah Ummeey a bar maganar, please!” 


“Ka yi k’arya kuwa in bar maganar aure, haka kawai da ranka da lafiyarka in dai ba mu’amala kake da matan banza ba ai ya kamata ace zuwa yanzu ka ajiye iyali, don haka magana ‘Daya da zan maka na samar maka mata y’ar aminiyata ta yarinta da nake yawan baku labarinta wato TALATU, don haka umarni na baka ba shawara ba..” kafin ya ce komai ta katse wayar don ta san idan ba haka ta yi masa ba,

Ba zai ‘d’au zancen serious ba.


Gaba ‘daya ji ya yi zuciyarsa ta karye, ya tabbatar tunda ta fa’da ‘din sai ta cika alk’awarinta. Ya runtse idonsa yana tunanin menene mafita? Wannan karan kam ya zama dole ya bijirewa umarninta, shi kam da zata bar shi haka ma tsaf zai iya rayuwarsa har ya koma ga lillahi babu aure. Wajen shak’atarwa da bai shiga ba kenan, ya da’de a zaune a motar kafin ya ja motar da sauri ya fice daga garden ‘din.





____________


Tun Asuba da ta mik’e bata farka ba, ta shiga gyaran gidan da abincin da ta san Amma ta fiso, gurasar larabawa da alkubus sai kunu da k’osai. May be idan Amman ta ga wannan hidimar da ta mata ta sassautawa zuciyarta daga fushin da ta tsiri yi da ita tun jiya da bak’uwarta da ta kira bak’ar bak’uwa ta zo gidan. 


Sai da ta jera kayan akan dinning table da taimakon mai aiki. Sannan ta kunna sunnah t.v tashar da ta san Amman ta fi muradin kallo a koda yaushe. 



Tsaf ta fito cikin shigar alfarma. Ta dinga bin falon gidan da kallo ganin yarda aka canja masa tsari. Ga dadda’dan k’amshi da aka baje falon da shi, na abinci da na k’amsashshen turaren wuta mai sanyaya ruhi na mutanen chad. Murmushi ne ya so sub’uce mata sanin cewa Ayra ce duk ta shirya hakan sarai ta san neman sulhu take tun jiyan tana lura da ita fushin da take da ita yana damun zuciyarta, sai dai ba zata bari ta fuskanta ba.


Ta zauna tana sake addu’ar fatan alheri ga Ayran kamar yarda ta kwana tana yi a cikin sujuda, ji take kamar warwarar matsalar Ayran ce ta zo. Ita kanta ta ji tana son Ayran ta yi wannan auren ko da sonta ko ba son ranta. 


Tana jin takun tafiyar Ayran, ta kawar da waccan fuskar tata mai yalwar fara’a ta saka wacce ta aro tun yammacin jiya, mai wuyar kallo a wajen Ayran mai fa’dar mata da gaba da sakata ‘dimuwa. Zuciyar Ayra ta buga sosai ganin har a lokacin waccan caku’da’ddiyar fuskar tana nan tare da ita. Ta yi k’asa da kanta tana jin yarda zuciyarta take bugu a hankali take furta ‘Wannan bak’uwa ta cuceni na shiga uku, ban tab’a ganin fuskar mahaifiyata a haka ba kamar yau.’ 


Jiki a sanyaye ta isa gefen Amman kamar yarda ta saba ta rab’a jikinta da nata a hankali ta bata sumbata a kumatu “Ammaty Ina kwana?” “Lafiya” ta fa’da tana sake ‘d’aure fuskarta sosai, Ayran gabanta ya fa’di sosai ganin ba sassauci da da ne sai ta janyota itama ta ha’da goshinta da nata kafin ta ce “Lafiya lau Auta ta, kin tashi lafiya.” Ta dinga wasa da hannunta kafin murya a raunane ta ce “Amma I cooked your favourite dish.” Ta ‘dau tsawon lokaci kafin ta yi jarumta ta kawar da tausayin Ayran daga ranta ta ce “Ana sa’im.” Ayran ta dinga kallonta wani iri kafin ta ce “Sa’im kuma Amma? Yau fa laraba idan ban manta ba.” 

Zuciya a dake ta ce “Na sani. Kuma ki k’yaleni haka bana son magana.” Tuni idanun Ayra ya fara tsiyayar da hawaye ta dinga bin ta da kallo kafin ta fashe da kuka ta fa’da kanta. Amman bata hanata ba amma fa bata saka hannu ta rarrasheta kamar yarda ta saba ba. Duk da zuciyarta tana bugu haka ta mayar da idanunta kan T.V a zahirance kallon take amma a ba’dinance kukan Ayra ne yake tsaya mata a zuciya. Ta da’de tana kukan kafin Amman ta saki ajiyar zuciya ta ‘dago kanta. Idanunta cikin nata ta ce “Saurareni Ayra, idan kina son ganin walwalata ya zama dole wannan karan ki yi ya’ki da zuciyarka ki amincewa auren nan, idan ba haka ba kin bar ganin walwala ta. A kullu yau min ina gaya miki ba duka maza ba ne halinsu ‘daya akwai wa’danda halinsu ya Sha banban da na mahaifinki yanzu yayyenki ba duk sun yi auren ba, duk da ta ki k’addarar ta fi ta su girma, kada ki manta ni kaina idan na tuna lamarinki abin yana min ciwo wani lokacin kwana nake ban yi barci ba saboda tsananin b’acin rai kuma ma ba wannan ba, ki tuna wani abu ‘daya mana yau ace na mutu na barki ina za ki kama? D’an uwana ‘daya tak da nake da shi kina ganin dai shekaru ashirin ba mu ji labarinsa ba, aurenki fa shine abinda ya fi cancanta..” Hawaye take idanunta ba k’akkautawa ita Kanta Amman danne zuciyarta take bata bayyana nata kukan ba, amma wanda take yi a zuciyarta ya fi na Ayran yawa ya fi shi kuma ciwo. Ayran da sauri ta mik’e ta shige wani k’aramin falo da yake k’asa. Kuka take sosai tana tunanin ina ma zata iya da ta amincewa aurennan tunda yanzu ta lura burin Amma gaba ‘daya ya tattara ga son aurar da ita, sai dai ina har a lokaci zuciyarta bata karkata da neman rushewar wancan adawar da takewa aure ba, ba zata iya ba ba zata iya ha’da makwanci da namiji ba…. Ba zata iya bawa namiji lokacinta ba balle ta masa girki ko ta nuna masa wata kulawa Menene Mafita? Shine kawai abinda take tunani ta runtse idanunta kawai tana hango wata mafita da take tunanin ita ce zata tserar da ita daga wannan auren ba tare da kowa ya zargeta ko ya k’alubalanceta ba…. Ta dinga sakin ajiyar zuciya tana jin cunkoson b’acin ran da zuciyarta ta yi tana warwarewa hankalinta ya kwanta ta mik’e tana ka’de jikinta….





________________



Magriba sakaliya ya shiga gidan nasa. Alh.Sulaiman turaki ya yi parking a bakin harabar gidansa. Kana ganinsa ka ga usulin fulani kuma ingarman namiji mai tsayi da fa’di fari tas da shi, farin nasa har wani ratsawa yake yellow. Ba walwala a fuskarsa ko ka’dan don bai kasance daga cikin mutane masu walwala ba. Ya dinga amsawa masu gadinsa sannu da zuwan da suke masa fuska a ha’de. 

Ta k’ofar baya ya shiga gidan nasa, k’ofar da direct zata sada shi da stair case ‘din da zai hau zuwa part ‘dinsa.


Ta ga shigowar tasa ta ji kuma takunsa don haka ta mik’e tsam ta sake bulbulawa kanta turare sannan ta bi bayansa, ta cikin sashen da take da zai sadata itama da stair case ‘din nasa. Ta yi kyau sosai cikin shadda light brown da ta sha ‘dinkin y’an senegal, jelar gashinta sai reto take a gadon bayanta. Farin ciki fal fuskarta da zata yi arba da shi a yau bayan shafewar wasu watanni tunda ya dawo wajen amaryarsa bai sake waiwayarsu ba don haka ta shirya taran sa tana son kuma ta nuna masa tana nan a Hameedarta mai tsananin kishi wanda dama dalilin hakan ya sa ya barta a can k’asarsu ya kuma hanata zuwa Nigeria. Sai yanzu da ya tabbatar girma yazo mata hankali ya samu ya san da wuya ta zo ta aiwatar da haukan kishi zata ji kunyar hakan. Tsawon shekaru sha biyar da aurensa da amaryarsa tun a lokacin ta so dawowa mahaifarta cikin dangin babanta amma S.Turaki ya kafe sam bai amince da hakan ba kuma ko hutu bai amince ta zo ta yi ba. Yanzun ma an kai ruwa rana kafin ya amince da zuwan nata, kuma zuciyarsa tana d’ar-d’ar sai dai ko a waya bai nuna mata ba, dalilin yayan Babanta ne ya sanar da shi ya kamata ta zo ta ga dangi yaranta kuma su san dangin kakansu tunda Amin da y’ar uwarsa ne kawai suka tab’a zuwa. A can ya ha’du da ita wajen business ‘d’insa soyayya mai k’arfin gaske ta shiga tsakaninsu, duk da ra’ayinsu ya sha banban shi mai kafaffiyar zuciya ne yayin da ita kuma ta kasance mai sassauk’an hali. Ko a wajen tarbiyyar yara sai da suka sha artabu don sosai ya nuna mata ya fi son yaransa su tashi da harshen hausa a bakinsu ba harshen su na labanawa ba, don dole ta amince take musu magana da duka harsunan biyu shi yasa suka iya hausa kamar me? Tunda itama bahaushiyar ce mahaifinta haifaffen cikin garin kano ne kuma asalin bahaushe, mahaifiyarta ce kawai ta kasance daga jinsin larabawan labanon. Tun lokaci da ta rigime da son zuwa Nigeria shi kuma ya tattara ya mata yaji tsawon wata bakwai sai da ya ga abin nata ba na k’are bane sannan ya ce su tattara su taho ya gama musu gini.



A hankali ta tura k’ofar idanunsu suka gamayya da juna. Fuskarsa ta ‘dan saki ka’dan yayin da tata ta washe da fara’a gaba ‘daya ta dinga jifansa da k’awataccen murmushi.

Hannu kawai ya mik’a ya janyota kusa da shi ba tare da ya yi magana ba. Ta shige jikinsa sosai tana k’ok’arin kawar da kishin da yake k’asan ranta. Sosai ta shiga nuna masa yarda ta yi kewarsa tana gaya masa yayinda shi kuma ya shiga sarrafata ba bakin magana a tunaninsa hakan ne kawai Zai nuna mata ya yi kewarta ba ‘dan ka’dan ba…..




Zazzafan coffee ‘din ta shiga jujjuya masa tana k’ok’arin mik’a masa murya a sauk’ak’e ta ce “Na samarwa Turaki mata…” gaba ‘daya cup ‘din ya sub’uce a hannunsa yana dubanta ya ce “Ba dani ba, na gama yiwa Turaki aure yana zubar min da mutunci ta hanyar sakin yaran mutane..”