NAMIJIN DUNIYA...

MABUDI

by @realmarubuci

NAMIJIN DUNIYA...



© Alhassan auwal Dambatta

Real Marubuci✍️

***



01...


Asabar, 12:30pm.

Jaji military Cantonment,Kaduna State.


Tun da duku dukun safiya aka rarraba jami'an tsaro da kananan sojoji masu jar hula adukkan sassan ciki da wajen barikin don tabbatar da tsaro.

Ko ina ka duba an share tsaftsaf kuma an killace komai a wajen da ya dace saboda manyan bak'in da ake da tabbaci da yakinin zasu halarci gagarumin bikin da za a'a gudanar a yau cikin barikin tsakanin yar gidan shugaban hafsan sojojin sama na k'asa wato Air Marshall Habu Mutuwa da d'an gidan kakakin shugaban 'yan majalisar dattijan shugaban kasa na yanzu sanata Ahmad Bukar Gole.

Tun a yammacin jiya aka hana shige da fice a wad'ansu sassa da dama ba a iya cikin garin Jaji kadai ba har cikin kaduna, musamman daga bakin tashar kawo zuwa garin Birnin yero.

Sannan aka kunna dukkan kyamarorin da suke daukar hoton bidiyo na masu kaiwa da komowa a kowane lungu da saqo don a yanda ake jin labari har shugaban kasa zai halarci bikin a matsayin babban bako kuma uba ga yaran da za a daurawa auren.


Takanas aka debo masu shirya waje daga kasar amurka, aka ware wani fili na musamman a cikin babban filin Sports Complex na barikin, aka zuba wasu fararen Canopy's masu masifar kyau da shimfidu da kujeru na alfarma.

Hakanan a bangaren girki an debo kwararrun chiefs daga sassa daban daban na duniya don baje kolin fasaharsu, aka wadata su da duk kayan da suke bukata aka zuba su a cikin wani makeken kitchen a bangaren Officers mess.

Kamshin girki ne kala kala ke tashi a wajen wanda duk wayewar mutum idan ya kalla sai ya zama dan kauye. A kalla kalolin girkin da aka yi sun haura kala hamsin. Ga lemuka da launin abubuwan sha samfur samfur har da irin kalar da mutum bai taba gani ba.


A can gidan AM Habu Mutuwa kuwa abun ba'a magana don shagalin da ake shiryawa bada labarin sa zai iya zama kauyanci ko bata lokaci.

Kamshin turaruka kala kala ne kawai ke tashi.

Ga manyan mata masu aji da isa sunci ado da gwala gwalai da tufafi na kece raini kowacce tana ji da kanta kamar ita ce tafi kowa kyau, sun rarrabu kabilu barkatai, Musulmai da Kiristoci.

Can gefe guda kuma aka killace wata rumfa ta musamman wacce babu kowa a cikinta face kawayen amarya kadai su goma sha biyu har da Twin sister dinta Ilham cikon ta goma sha uku.

Gaba daya yammatan sunyi shiga iri daya cikin wani kalar sari mai shara shara launin sararin samaniya da feshin d'igo d'igon bak'i, kowacce ta saka siririyar sark'a irin wacce indiyawa ke sakawa a gaban goshi. Wani k'arin abun sha'awa dukkansu farare ne sol babu bak'a ko d'aya a ciki, kowacce kuma an yi mata zanen jan k'unshi a ciki da wajen yatsun hannayenta hagu da dama.


Duk cikin gidan babu rumfar da ta kai rumfar da suke ciki kyawu da daukar hankali don idan ka hangesu daga nesa zaka iya rantsewa ba hausawa ba ne face ka matso kusa.

Duk wannan abu da yake faruwa ko a jikin amarya Lailah bata damu ba duk kuwa da tana iya hangen kowa da komai daga can cikin windon d'akinta a saman bene.


Tun dazu Ilham ke zuwa tana yi mata magiyar tayi wanka ta fito don jama'ar da suka taru saboda ita su ganta amma ta k'ekasa k'asa tace sam ba zata fita ba, bisa dole ta janye jikinta ta koma kan sabgoginta don sarai tafi kowa sanin halin da 'yar uwar tata take ciki wanda ita a ganinta ba komai ne ya haddasa mata hakan ba face, wawanci, kauyanci, da gidadanci da son zuciya da zubar da ajin da Allah ya yi mata wanda ba kowacce mace ce ke gamon katarin samun irinsa ba.

Idan ta tuno yanayin fuskar gayen da zubin kirarsa abun yana d'aga mata hankali da jefa ta cikin mamaki, da haushi da bak'in ciki.

Wanne kalar asiri ya yiwa Lailah da ta haukace a kansa haka?, Anya ba matsafi ba ne?.

Idan ba haka ba mene ne ya ja ra'ayinta a kansa har take neman rasa hankalinta da rayuwarta a kansa?.


Ta ciji yatsa tare da ajiyar zuciya mai nauyin gaske.

Lokaci guda kuma ta mike zumbur daga wajen da take zaune domin tunanin da ya fado mata yanzunnan a cikin ranta ta yi imanin shine kadai mafitar da zata kawo karshen komai.


A yau dinnan zata yi maganinsa, ba zata sa a kashe shi farat d'aya ba saboda bata taba aikata kisan kai ba kuma bata jin za ta iya.

Makudan kudade zata biya wanda za a yi masa wani gagarumin sharri har takai ga ya fada hannun jami'an tsaro zuwa gaban alkali a kotu, yanda za a yanke masa hukuncin zaman gidan yari har karshen rayuwa, watakila a dalilin haka za ta hakura da shi ta yi biyayya ga wanda mahaifinsu ya bata a matsayin abokin rayuwa.

Tana gama ayyana haka ta bude securityn wayarta ta lalubo lambar wani tantirin dan iskan soja mai mukamin Sergeant, wanda sau tari take bashi kwangilar ayyuka masu kamanceceniya da irin wannan.

"Yau zan kawo karshenka Abulheekmah..."

Ta fadi wannan magana da murya mai kaushi kamar tana tsaye a gabansa kafin ta kara wayar a kunne ta fara magana cikin gadara da isa bayan ta tabbatar Sergeant ya d'aga kiran.

*


Har zuwa kusan karfe d'aya da yan mintoci wanda ya rage baifi saura minti hamsin a daura aure ba Lailah bata yi yunkurin komai na shiryawa a matsayinta na amarya ba.

Sau biyu Ilham tana tura mata mai kwalliya tana koro ta, karshe ma ta datse duka kofofin sashen da take da mukulli kuma ta rufe layukan wayoyinta.

Ta zauna k'asa dirshan tana kallon agogon bango cikin jiran mintuna arba'in masu zuwa wanda take da tabbacin da zarar sun cika mala'ikan daukar rai zai ziyarceta, duk da bata da yakinin wajen da zai ajjiye gajiyayyen ruhinta tsakanin barzahu ko wata duniyar daban da take mafarki.

Wannan shine kawai damuwarta.

Ta so ace ta samu ganin Abulheekmah ko kuma zantawa da shi ta wayar salula domin ta fada masa irin mutuwar da zata yi amma damar samun hakan ta yi mata nisa. Babu waya a hannunsa, ta bangarenta Kuma an kulle mata dukkan kofofin da zata iya sulalewa don ta je su gana.


Zuciyarta na k'una, hawaye masu zafi na fita daga idanunta.

Tasan duk inda yake a yanzu yana cikin kwatankwacin halin da take ciki koma fiye da nata.

Ko kad'an bata da na sani akan wannan k'unar bak'in wake da ta yanke hukuncin yi duk da yanda take jin zuciyarta na bugawa fat fat kamar zata tsaga kirjinta ta fito waje.


Lokaci na kara matsowa tana k'ara jiyo sautin motoci da jiniya barkatai ba adadi.

Ko ina ya cika ya batse a ciki da wajen gidan anata shagulgula kala kala, wasu na faman ciye ciye, wasu na tikar rawa, hakanan masu daukar hotuna, kowa dai da kiwon da ya karbeshi.

Adadin giftawar sakwanni da mintuna adadin canjin yanayin da Lailah take ji a jikinta. Tun tana ganin komai garau har idanunta ya fara nuna mata dishi dishi alamar ajalinta na k'ara kusantarta kamar yanda take tsammani.

Dakyar ta iya mikewa jiri na kwasarta ta lalubo takarda da abun rubutu ta rubuta wata gajeriyar wasika da harshen Spanish ta ninke ta jefa karkashin gadonta.

Ta tabbata matukar Indo bata manta da wasiyyar da ta yi mata ba zata zo har nan ta lalubi takardar bayan mai afkuwa ta afku.


Dab da wannan lokaci karamin jirgin Helicopter fari tas mai dauke da tambarin gidan gwamnatin tarayya ya ratso sararin samaniyar barikin dauke da shugaban k'asa President Aliyu Mohammed tare da DG d'insa da wasu zababbun Dss guda uku.

Ya sauka a can gefe guda a farfajiyar wannan katafaren fili da aka tanada.

Ganin haka yasa aka kara tsaurara tsaro fiye da kowanne lokaci ainun, ya zama ba shiga ba fita Koda nan da can.


A gaggauce zababben gwamnan jahar Kaduna Engineer Dr. Mubarak Idrees tare da mai martaba sarkin Zariya His Royal Highness Muhammad Farouq da ayarin wasu yan majalissu da sanatoci kusan guda goma suka yi ayari wajen taryar shugaban k'asar karkashin jagorancin Senate president Ahmad Bukar Gole.


Duk mahalukin da ya halarci wajen sai da ya mike tsaye don girmamawa har sai da President ya zauna bayan an kammala caje ko ina kafin kowa ya zauna.

 Nan da nan waliyyan ango da amarya suka gabata gaban babban limamin gari aka fara shirin daurin aure.


Duk wannan abu da ke faruwa ashe tun daren jiya Abulheekmah ya samu damar shigowa cikin barikin a sirrance da taimakon wani abokinsa kurtun Military police d'aya daga cikin masu gadin First gate.

A dakinsa ya kwana kasancewar gwauro ne ba shi da aure kuma tun da gari ya waye ya fice a barshi shi kadai a dakin bayan sun gama karya kumallo.

Kaiwa da komowa kawai yake yana faman cizon yatsa cikin wasi wasi, takaici da rashin sanin abun yi. Zuciyarsa na bugawa kwatankwacin gudun saurayin aljani.

Ya sani sarai dazarar ya fita an yi ido hudu da shi sojoji zasu cafkeshi don yana da tabbacin babu inda AM Habu Mutuwa bai raba hotunan fuskarsa ba tare da bada umarnin idan an ganshi a cafkeshi ta kowanne hali.


Lokacin da agogon hannunsa ya nuna masa karfe d'aya da minti arba'in da uku ne hankalinsa ya tashi matuka, musamman da ya ji karuwar hayaniyar mutane da kuma sautin giftawar jirgin shugaban k'asa.

Tabbas a wannan lokaci ana dab da daura auren masoyiyarsa Lailah da wanda bata so. Ana dab da yi musu mummunan yankan da ba zasu taba warkewa daga zafin ciwon sa ba har zuwa lokacin fitar numfashi daga cikin gangar jiki.

Lokaci guda ya zabura ya bud'e kofa ya fito cikin sassarfa da hanzari bayan gama yankewa kansa shawarar cewa tilas sai ya halicci wajen daurin auren saidai duk abunda zai faru ya faru.

*

A can gidan AM kuwa labari ne ya canza daga kyakkyawa zuwa mummuna ainun, daga dariya zuwa koke koke da tashin hankalin da ba a yi tsammani ba.

Cikin fitar hayyaci da gushewar hankali Ilham ta dauki mota ta fice zuwa filin Sports Complex.

Babu wanda ya yi gangancin tsayar da ita a cikin jami'an da ke gadin tituna saboda kowa ya san motar gidan AM ce kuma duk wanda ya gani yasan ba lafiya ba.


Irin gudun mutuwar da take fafarawa zamu iya cewa Allah ne kadai ya kaita wajen lafiya.

Tana isa ta ja wani wawan burki har saida kura ta tashi.

Sojoji kusan ashirin suka yo kanta da bindigu don tunanin ko wani ne ya kawo hari.

Tana fitowa kuma kowa ya yi turus, aka bata hanya ta ruga da gudu zuwa wajen da ta hango mahaifinta zaune ta na kuka wiwi.

Tun kan ta k'arasa ya tashi a sukwane ya taryeta cikin rawar jiki da bugun zuciya mai tsanani.


"What is happening my daughter? What makes you crying like this?... Tell me please..."


Ya tambayeta cikin murya mai rawa.

"She's no more Dad, Lailah ta had'iyi zuciya ta mutu.."

Ya zabura cikin wani irin k'araji kamar a filin yaqi yace

"Whattt....? Are you out of your mind Ilham...?"


Ya soma jijjiga kai, hajijiya na kokarin dibarsa.

"Stop saying that please... This is Unbelievable..."


*

Kar ku karanta ku wuce ba ku ce komai ba.

***