Tsakanin mu 6
by @mumirfaan
Runtse idanuwa tayi ta buɗe a hankali tamkar wacca taga mugun abu, ganin hankalinsa baya kanta yasa ta fara tafiya a hankali, tana zuwa saitin ƙofar gidansu Jameel ta sadda kanta ƙasa tace "Ya Jameel ina kwana?" Bata jira amsarsa ba ta cigaba da tafiya.
"Ruƙayya!" Taji ya kira sunanta tsayawa tayi ta ɗan waigo tana kallansa, inka ganshi bazaka taɓa cewa shi ya kirata ba, don hankalinsa nakan wayar dake hannunsa, rausayar da kanta tayi tare da juya idanunta sama, ganin still be kalli inda take ba yasata taɓe baki kamar wacca zatai kuka tace "Ya Jameel ka kirani kuma kai banza dani"
"Ki jirani bari na kaiki" yana gama faɗan haka ya buɗe ƙofar gidan ya shiga, bayansa tabi da harara tace "Se kace nace ya kaini, se wani shan ƙamshi yake ma mutum...."
Bata ƙara sa faɗar maganarta ba taga Get Man ya wage masa Get ɗin gidan, parking yayi a gaban ta baice mata komi ba, kama Handle ɗin motar tayi ta buɗe ta shiga, "Ya Jameel ina kwana" ta ƙara gaishesa a karo na biyu.
"Lafiya kalau, yau ya na ganki ke kaɗai ina Baban?"
Ya jefo mata tambaya.
Shiru tayi tana tunani tayaya yasan shi yake kaita alhalin basa ganin shi a anguwar lokacin da ze kaita School.
"Ruƙayyatu!"
"Na'am" ta faɗa tana Confusing ɗin sunan.
"Baba ya tafi ne?"
"A'a, yana nan" ta faɗa tana ɗan satar kallansa.
Be ƙara ce mata komai ba, a haka har suka ƙara sa makarantar.
Ƙoƙarin fitowa ta fara ya katse ta da cewa "Ƙarfe nawa zaku tashi?, Ko Baba zezo ya ɗauke ki?"
"Girgiza kai tayi tace "Ya tafi ƙauye maybe da yamma ze dawo".
"Okay ƙarfe nawa zaku tashi?"
Ƙara kallanshi tayi tanaso ta ga full face ɗin sa amma yaƙi barin su haɗa idanu.
"Ƙarfe 9 zamu shiga Exams kuma yau Paper ɗaya zamuyi da zarar na fito kawai zan dawo gida" ji tayi ba daɗi, ganin yadda yake mata magana kamar wanda akaiwa dole ya kawota.
"Okay 11:00AM zanzo na maidaki gida"
Gyaɗa kanta tayi jiki a sanyaye tace masa "To shikenan, Nagode"
Satar kallanta yayi kaɗan ya kauda kansa gefe.
Tana sauka yaja motar ya fita daga harabar makarantar.
Ganin da sauran lokaci yasata ƙara sawa Senior Section don ta samu tayi karatu a tsanake, samu tayi ta zauna gabda wani Class da ba'a komai dashi don ya ɗan samu matsala hakan yasa ba'a karatu a cikin.
Haka kawai ta tsinci kanta da annashuwa cike da farin ciki ta ciro book ɗin ta ta fara karantawa, bini-bini ta saki murmushi.
Shiru tayi jin motsi a bayan Class ɗin, jin kamar iska ce yasata ƙara maida hankali wajan karatun.
"Tsaya mana!"
Taji Muryar Uncle Sufyan ta bayan, murmushi tayi jin Muryar sa don tana da tabbacin gunta ya zo.
"Kaga an fara taruwa" jin Muryar mace ta ƙarajin a inda taji sautin muryar Uncle Sufyan, gabanta ne yayi mummunan faɗuwa, ta aje Notebook ɗin a hankali ta fara bin inda take jiyo sound ɗin wannan budurwar.
Cak ta tsaya ganin Uncle Sufyan yana ƙoƙarin Kissing ɗin wannan ɗalibar, gashi ko kaɗan basa jituwa da *Alanta* sunan da Class Mate ɗin ta suka saka mata, yarinya ce mara kamun kai, duk wani malami da aka ga yana tarayya da ita to wannan malamin daga ranar ya tashi daga mutumin kirki ya koma na banza, bata yadda Uncle Sufyan bane, ta kasa yadda cewar shine yazo bayan Class yake ƙoƙarin Lalata da Students ɗin sa, yaushe ya zama haka, ko dama halin sa ne haka bata sani ba, wani saliva ta haɗiye me zafin gaske daga maƙogwaronta, a hankali ta dafa bangon dake kusa da ita tanaji kamar zata faɗi, tana kallan ikon Allah, ta runtse ido ba adadi tana so ta tabbatar wa da kanta mafarki take, runtse idanu tayi batasan lokacin data saki wata ƙaramar ƙara ba ganin yadda suke ƙoƙarin haɗe bakinsu waje guda, a ɗan firgice Uncle Sufyan ya tura Alanta gabansa na faɗuwa, buɗe idanuwanta tayi yayinda siraran hawaye suka biyo baya ta ɗaga kai tana kallanshi, dafe kanshi yayi yana faɗin "Please Ruƙayya ki fahimce ni......" Hannu ta ɗaga mai alamun ya dakata tai sauri tabar wajan, tafiya take amma ita kanta bata ganin hanyar da zata bi kasancewar idanunta sun ciko da ruwan Hawaye, can cikin makarantar ta kutsa in da bakajin motsin komai se kukan tsintsiye, ƙasan Bishiya ta samu ta zauna ta dafe kanta jin yadda yake sara mata, kifa kanta tayi a tsakiyan cinyoyin ta, wani irin kuka ne ya ƙwace mata, ba abinda kakeji face sautin kukanta.
Akai-akai yake duba agogon dake ɗaure jikin hannunsa yana duba lokaci, hankalinsa gabaki ɗaya yana kanta don yana da tabbacin sun gama Exams, fitowa yayi daga Office ɗin sa yana ƙoƙarin fita, ganin Secretariat ɗin sa ta shigo ya dakata da fitar da zayyi, cike da girmamawa tace "Sir kayi baƙi"
Furzar da iskar dake bakinsa yayi yace "Kije kice na fita"
Ya faɗa yana ƙoƙarin bin wata ƙofar ta daban, ganin bakin nasu suna da mahimmanci yasa ta ɗan ɗaga murya ganin ze fita tace "But Sir....." Shiru tayi ganin ya ɗaga mata hannun ya fice.
Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ta ina zata fara da baƙin, domin tabbas ta tabbatar musu da yana cikin Office,
Jiki ba ƙwari ta fita taje ta samesu tayi musu bayani akan ya fita amma ba ze dade ba ze dawo.
Sosai Alanta take dariya tana bawa ƙawayan shashancinta Labarin abinda ya faru yau ita da Uncle Sufyan.
Haɓa Fiddy ta riƙe tana faɗin "Wallahi bansan Uncle Sufyan munafiki bane se yau, haka dama yake" cike da ɓacin rai tace "Kinga Alanta wallahi bana iya kula wa ƴannan mazan saboda na tsani naga mutum na Allah sannan naga ashe a bayan idon al'umma tantiri ne, yanzu in zaki dafa Qur'ani kika cewa mutane ga halinsa wallahil Azim se an ƙaryata ki saboda an mishi kyakkyawar sheda"
Alanta cize baki tayi tace "Naga Alama wallahi don da wata ƴar J.S tayi ta ganmu baki ga yadda ya wani razana ba, kinji maganganu a bakinsa bazaki taɓa cewa Ustaz bane" (Sunan da ƴan S.S 3 suke kiransa dashi)
Ɗayar kuwa tsaki tayi tace "Allah ya kyauta banason mutum munafiki, kuga dai irin wa'azin da yayi ta yiwa Faruq akan wata takai ƙararsa ya taɓa mata hannun"
Haka suka cigaba da hirar su akan Uncle Sufyan tare da mamakinsu.
Yana cikin Staff yayi shiru, ya rasa abinda ke masa daɗi a rayuwa, saboda irin kallan da Ruƙayya ta jefeshi dashi kallo ne na ƙiyayya, shi mamaki ma ya ke meya kawota wajan saboda ko kaɗan Students ba zuwa gun suke ba, ya sauke ajiyar zuciya ba adadi, yana tsoron yaje inda take karta tona mai asiri hakan yasa ya yanke shawarar inta koma gida zeje ya sameta.
A hankali ta ɗago da fuskarta tana runtse idanuwa saboda ranar datake haske mata fuska, fuskarta ta kumbura saboda kukan data sha, ga idanunta sunyi jajir, ba abinda kakeji sai ajiyar zuciya data ke saukewa akai-akai, zumbur ta tashi daga wajan batasan tayi bacci a gun ba, sauri -sauri take kar a shiga Exams, tsayawa tayi wani irin hawaye me ɗumi ya sauka a kuncinta, Students ta gani suna ta fitowa daga Class hakan na nufin har an gama Exams kenan, ta rasa me zatai, cikin sanyin jiki ta doshi Class ɗin su, babu kowa a ciki, dafata taji anyi "Ruƙayya me yisa kika zauna a gida har wannan lokacin gashi angama Exams ɗin ma"
Kukan data ke ɓoyewa ne ya fito fili tama rasa me zatace mata, hankalin Fadeela ne ya tashi ganin yadda jikin Ruƙayya ke rawa, "Wayyo Allah Ruƙayya meke damunki?, Me yasa me ki haka?, Me akai Miki?" Ta faɗa itama cikin tashin hankali tun da taga fuskar Ruƙayya, ga wani irin rawa da jikinta ke yi, kamo hannunta tayi suka shiga Class ta zaunar da ita kan Kujera "Bari na kira Uncle Sufyan ince ya nema maki alfarma gun Uncle Tajuddeen ya bari ki zana paper ɗin yau" ta miƙe kenan ta ruƙe hannunta Muryar ta a dashe tace "Karki kiramin kowa please Fadeelah...."
Bata bata bari ta ƙara sa ba ta hango Jameel yayi Parking motarsa, "Ga Ya Jameel nan yazo" ta faɗa tare da koma wa ta zauna kusa da Ruƙayya, gyaɗa kai kawai Ruƙayya tayi bata ce mata komi ba se faman sauke numfashi take daƙyar.
Fadeelah kallanta tayi tace "Ruƙayya ki faɗamin meya sameki haka, Kinga yadda kika koma ne?, Wai duk akan baki samu Paper ɗin yau bane"
Murmushi Ruƙayya tayi tana kallanta da jajayen idanunta gyaɗa mata kai kawai tayi kamar wata ƴar maye ta koma ta kwanta.
Shiru ne ya biyo baya, Fadeelah miƙewa tayi zata fita.
"Fadeelah!"
Ruƙayya ta kirata, tsayawa tayi tana kallanta tace "Don Allah kar kije gun Sufyan, Karki damu zan zana Paper ɗina kamar yadda kowa ya zana"
Fadeelah ganin Jameel yana ɗan waige-waige ta gane Ruƙayya yake nema, "Ba can zani ba, naga Ya Jameel tun ɗazu yake tsaye babu mamaki ke yake jira, zance masa baki da lafiya ne"
"A'a zan iya tafiya bari nazo mu tafi, Fadeelah don Allah ban ragowar Pure water ɗin can"
Ba musu ta miƙa mata window taje ta wanke fuskarta, ta dawo ta ɗan goge ta, dafa kafaɗarta tayi tace "Muje"
kanta a ƙasa suka fara tafiya har suka ƙara sa inda yake, Jameel ganin sun taho yasashi shiga mota yana jiran ta shiga, tana shiga motar Fadeelah tace "Se gobe, kizo da wuri Karki ƙara missing Paper, zan wa P.C magana muji ko Allah zai sa ya bari ki zana Paper ɗin yau"
Tun da ta fara maganar take harararta haɗe da yi mata signal akan tai shiru bata lura da hakan ba.
Rufe motar tayi tace "Ina Wuni"
"Lafiya kalau" bata ƙara ce masa komi ba haka zalika shima haka, sede maganar Fadeela se yawo take mishi a ƙwaƙwalwa, kamar yaya bata samu Paper ɗin yau ba, alhalin lokacin datazo ba'a fara taruwa da yawa ba.
"Ina kikaje?" Ya jefo mata tambaya.
Ruƙayyah ta lula duniyar tunani hakan yasa bataji me yace mata ba.
Ɗan satar kallanta yayi yaga tun da yaga sun taho kanta a ƙasa har yanzu taƙi bari yaga fuskarta.
"Ruƙayyah!" Ya kira sunanta yana kallanta, a ɗan firgice ta amsa ta ɗago tana waige-waige, caraf suka haɗa idanu, wani irin burki ya taka wanda baisan yayi haka ba, hakan yasa ta ɗan buge kaɗan.
Kallanta yayi da mamaki "Ke!" Ya kira sunanta, "Na'am" ta faɗa kanta a ƙasa.
"Ina kikaje baki samu Paper ɗin yau ba?" Ya faɗa ya kafeta da fitanannun idanunsa.
"Ina naje kuma?" Ta faɗa tana mamakin kalamansa.
Wani irin kallo ya jefeta dashi, "Wallahi Yaya ba inda naje ina School"
"Kina school kuma kikai missing Paper ɗin yau?"
Kukan datake ɓoyewa ne suka zubo tace "Wallahi Yaya ina Makaranta bansan an shiga aji ba" kuka ta fara sosai ga murayarta ya dashe, shiru yayi yana nazari.
Cikin sanyin murya yace "Ki natsu ki faɗamin mai ya faru?"
Girgiza kanta tayi alamun bazata iya faɗa mai ba, ƙanƙame jikinta tayi tana wani irin kuka, ita yanzu tsoron maza ma takeyi babu mamaki duk haka halinsu yake, don ta gani tun daga Ya Jameel har zuwa Uncle Sufyan.
Jameel ganin kamar a tsorace take yasa ya ɗan sassauta murya yace "Faɗamin kinji ƴar Ummi, mai ya hanaki zana jarabawar ki?"
Jin sound ɗin muryarsa kusa da ita yasa ta ɗan samu natsuwa kaɗan, "Uncle Sufyan ne"
Cike da son jin abinda ya faru yace "Me yayi Miki?"
"Ba ganinshi nayi da wata ba ya......"
Dogon tsakin dataji yayi ne takasa ƙara sa abunda zata faɗa mai, a hankali ya fara tafiya dan maganar tata ma ba ƙaramin haushi ta bashi ba, don ta ganshi da mace shine take ƙoƙarin hallaka kanta akansa, hankalinsa nakan Titi yace "Ki tsaya soyayya ki hallaka kanki, kamar ki ace bazaki maida hankali akan karatun ki ba, kin ɗauki soyayya kin sawa ranki, saboda tsabagin iskanci da sangarta paper din yau ƙin yi kikai saboda kin ganshi da mace" magana yake cike da ɓacin rai, ganin yadda lokaci guda ta canza kamar ba ita ba dan ta ganshi da budurwa, shi babban baƙin cikinsa rannan data ganshi da mace nunawa tayi ko a jikinta....
Tunaninsa ne ya tsaya jin tace "Kiss fa yazo ze mata se gani"
Shiru yayi yana kallanta yace "Ya taɓa Miki hakanne?"
Girgiza kai tayi tace "Ko hannuna be taɓa taɓawa ba amma ga mamaki na naga..." Shiru tayi hawaye na zuba daga idonta.
"Ki rabu da shi ba mijin aure bane..."
Katse shi tayi da cewar "Saboda me?"
"Saboda ɗan iska ne, tayaya yasan ga wacca yake so yaje yana soyayya da wata, na faɗa Miki ba sonki yake ba, wata dama yake so game dake da zarar kin bashi ze rabu dake, anyi haka yafi dubu"
"Amma Yaya Jameel Inhar Uncle Sufyan ɗan iska ne kai......."
Maganar tsayawa tayi daga maƙogwaronta ganin kallan daya wurgeta dashi.