NA CANCANTA!

Part 13

by @halimatukhalil


13


Sallamar Abid ta katsemin tunanin da nake yi sai da na amsa masa ya shigo daga cik gefena ya zauna ya miqomin wayar dake hannunsa


"Yaya Sumayyah ki amsa waya Yaya ya bani qawarki na kiranki"

Ban tsammanin kiran kowa ba bayan Halima Kuma itace dai qawar tawa da Yaya Samir ke da number 'dinta hakanan kuma naji gabana yana fa'duwa haka dai na daure na anshi wayar,wayar Yaya Samir babu password hakan yasa na kar'ba na danno number 'din Halima na bi kiranta 

Sallama nayi mata bayan ta 'daga jin bata amsamin ba yasa na cire wayar a kunnena na duba wayar ba wai an katse ba ne haka nayi tunanin ko ba service haka dai na sake maida wayar kunnena na sakeyin wata sallamar kukan Halima naji da shashshekarta tuni na ru'de gabana ya cigaba da fa'duwa na daure na fara tanbayar Haliman

"Halima lafiya maike damunki,ba zakimin magana ba sai kuka mai yafaru dan Allah ki sanarmin kar nima ki sani kuka"

Da wannan lallashin da nake yiwa Halima yasa ta yin shiru tana ajiyar zuciya zuwa can ta soma magana

"Sumayyah qaddara ta riga fata duk qoqarinmu ba xamu guje mata ba,kuma kowanne bawa da irin yadda qaddararsa ke zuwar masa,haka dole kowa yayi haquri da irinta sa,saboda cikar imaninka"

Shiru nayi Ina sauraren Haliman Kuma bugun zuciyata na tsananta qaruwa na dai daure na ce

"Halima dogon jawabin nan ya isheni duk nasan da hakan,ki sanar dani abinda ke faruwa dan Allah,hankalina ya kasa kwanciya"

Halima ta 'danyi shiru kafin ta ce

"Exam din mu ta qualyfying ta fito sai dai Sumayyah ajinmu mutum goma suka samu ciki..."

Gaba na ya qara fa'duwa na dakarta da Halima idona yana zubar da hawaye masu zafi

"Babu ni a cikin wa'danda suka ci ko?"

Nayi mata tanbayar saboda Ina da yaqinin haka ne jikina kawai ya bani

Shiru tayi na sake jefa mata tanbaya

"Ban ci ba ko?"

Cikin qinqina ta ce

"Eh..ey"

Bata kuma sake cewa komai ba 

Nice ma na sake qoqarin yin magana amma naji tayi shiru alamun ta katse wayar hakan yasa na cire wayar a kunne na na miqawa Abid da hawaye suka cikamin idanuwa na


Abid ya soma magana

"Yaya Sumayyah mai yafaru ne kike kuka"

Hawaye na na goge na ce

"Bakomai Abid"

Kallona yayi ya ce 

"A'a da komai fa Yaya Sumayyah ki fa'damin Dan Allah"

Na sake ce masa

"Bakomai Abid,kaje ka kaima Yaya wayarsa"

Ya ce

"To shikenan zan kai masa amma dai zan fa'damasa kuka kike bayan kin gama wayar"

Haka Abid ya tashi ina kallansa sau tari idan na gansa muna wata firar Ina tunawa da Ahmad da yake kusan kamarsa,haka a halayyarsa nakan tuna Ahmad saboda yadda shima Abid ke da kyawun hali sam ba ruwansa da sabgar 'yan gidansu,shi da Yaya Samir halayyarsu ta banbanta da 'yan uwansu su akwaisu da tausayi da son zumunci sa'banin sauran kowa halin iyayensa ya biyo,batun qualyfying 'dinmu ta fa'domin a raina na rasa mai zanyi kuka zanyi ko me da zan ji sauqi a zuciyata kaina na kife a qasan carpet 'din da nake kai zaune ina wani irin kuka Mai ciwo shikenan karatun da na saka rai zanqarasa bazai samu ba,karo na farko na fa'di jarabawa,shin ta ina iyayena zasu nemo ku'din da za'a biyamin na kammala karatuna na sani babu mu 'din da neman na yau da kullum muke ta yaya zamu nemo ku'din biyan jarrabawa,dukda Ina da yaqinin a cikin dangin mahaifina akwai wa'danda mutum dubu zasu biyawa jarabawa ba tare da arziqinsu ya girgiza ba amma inada yaqinin banda ni hakan yasa ma ban saka rai ba,yasa kuma na shiga damuwa mai tsananin gaske


Sallamar da Abid ya sakeyi ta dawo dani daga tunanina ta Kuma tsayarmin da kukan da nake amsa masa sallamar nayi ya Kuma shigo ya maida kallensa gare ni

"Yaya Sumayyah kuka kike ko,ina jiyowa tun daga kofar 'daki ki barwa Allah komai"

Na _daga masa kai

Da ga nan ya ce 

",Yaya yana waje yace kije yana compound"daga nan ya fice nima ba nida za'bi illah na saka hijabi nabi bayansa


A tsaye na hangosa fuskarsa babu wata walwala sallama na masa ya amsamin na gaishesa ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar tawa,wanda bansan dalilin hakan ba yana nunamin kujerun robar da ke kusa dani yana qoqarin jan 'daya daga ciki ya ce

"Ki zauna ma na"hakan yasa na ja nima na zauna da Bismillah baki na


Kallon da Yaya Samir yake min da na kasa jurewa nayi qasa da kaina


Shirun da ya ratsa tsakaninmu can Yaya Samir naji gyaran muryarsa ya fara magana

"Sumayyah dan Allah kiyi haquri da duk yadda rayuwar zata zo miki na sani hakan babu da'di,naji kamar ina ma nine ke,rayuwarki tana bani tausayi dukda na sani jarabtace daga Allah,nasan komai Sumayyah,ni Haliman ta fara yiwa maganar bansan ta Ina zan tunkareki da zancen ba hakan yasa na ce ta sanarda ke da kanta,ko damuwar zatazo da sauqi a gareni, Sumayyah ba ni da sauran nutsuwa duk da nasan kin cancanta na miki komai sai dai yadda zan riqa kyautata miki ba tare da na 'batawa su Abba rai ba,bansan ta ina zan misalta bo'dadden halayyar Abba da Ummi ba dan Allah kiya haquri Sumayyah ki 'dauki komai na rayuwarki bisa kaddara kuma komai zai wuce"

Kai kawai na 'dagawa Yaya Samir don bansan irin amsar da zan basa ba don zan iya fashewa da kuka ina fara magana,magana shima ya cigaba dayi

"Yanzu ki kwantar da hankalinki,zanyi magana da Abba zan biya miki ku'di ki zana a private idan lokaci ya tashi"

Ban wani gasgata lamarin ba dan nasan abin Kamar da Kamar wuya shiga islamiyya ma sun hanani bare Kuma biyan ku'din zana exam,hawaye suka cikamin idanuwa na don ina da tabbacin kawai lallashi ne kawai,na dai daure na ce

"Yaya Samir ko ban zana na ba na kar'bi kaddarata,amma Yaya Samir Halima da Batul nake so naji sun samu,hankalina yafi tashi idan na tuna su bansan tasu makomarba"


Yaya Samir ya kalleni

"Ki share hawayenki Dan Allah,sai na fa'damiki komai"

Ba nida zabi illah na goge hawayen na fara saurarenshi

"Batul da Halima duk sun samu,Sumayyah kece kawai Allah ya qaddaramiki hakan ba wai dan baki da qoqari ba illah kawai jarrabata ce daga Allah hakan Allah yaso,idan Allah yaso zai jarrabci bawa saiya jarabceshi da abubuwa kala kala bawai dan bai sanshi ba,sai dan yana nufin mutum da wani alkhairi"


Bana sauraran zancen Yaya Samir sosai na kife kaina jikin gwiwa ta ina kuka da bana jin akwai mutumin da nake buqata a yanzu bare jin muryar wani,a kusa da ni,qaddara ce na sani amma bansan kalar ta wa ba a lokaci qanqani komai ya sauya min,ni ka 'dai nasan ciwan da na ke ji da ra'da'din da nake ji da babu mai fahimtata.

Bayan wasu kwanaki da na 'dauki komai a bisa qaddarata na Kuma amshi hakan,walwalata ta soma dawowa saboda yadda kullum nayi waya da Umma a wayar Yaya Samir takan kwantarmin da hankalina


Yau da shirin zuwa aiken Ummi na ta shi,dutsen safe zamu ni da Abid gidan qanwar Ummi Aunty Ramla kasancewar weekend be qarfe goma muka fito bakin titi ni da Abid da nake sanye da doguwar rigar material sai mayafina kalar brown kwalliyar fulawar jikin material 'din muna tafe muna fira cikin wasa da dariya munyi matuqar sabo da Abid matuqa kamar mun shekara da shekaru tare haka muka tsaida napep muka shige muna fa'damasa unguwar da zai kaimu dutsen safe low-cost,babu laifi munyi 'yar tafiya,kafin mu isa unguwar har qofar gida aka qarasa damu,muka miqamasa ku'di muka fito ni da ma ban ta'ba zuwa gidan ba Abid ne yake jagorantar tafiyar sai da muka qwanqwasa gate 'din gidan da mintina kafin zuwa can muka ji alamun tafiya,hakan yasa muka tsaida buga gidan Aunty Ramla din ce ta bu'de kofar da fuskarta ba yabo ba fallasa tayi mana izinin mu shigo ciki bayanta muka bi har zuwa ciki a babban falo muka zauna saman kujera muna gaishe da Aunty Ramla din haka dai ta amsa tana 'dan shan qamshi har mamakin hakan nayi ganin da Abid na taho ya kamata ace ta 'dan saki fuska ko danshi dukda bansan halin Aunty Ramla din ba qila hakan take bamu jima sosai gidan ba muka fito Dan yaran Aunty Ramla biyu duk basa nan,suna gidan kakanninsu,bamu samu napep ba anan qofar gidan ganin zamu da'de yasa muka fara tafiya a qasa dukda saqon da muka amso masu nauyi ne amma ba muda za'bi banda muyi kama kama muka riqe hannun ledar nida Abid muka fara tafiya zuwa bakin titin hankalinmu kwance muna fira da Abid yana bani labarin Aunty Ramla Wanda a labarin na fahimci halayyarta ce shariyar data mana,amma dukda hakan har dama wulaqanci na fa'da a raina labaran Aunty Ramlan ya dinga bani na tun kafin tayi aure har zuwa yanzu wani abun har dariya take bani a raina Kuma "ina lallai su Abid tona asiri ne"

"Sumayyah!, Sumayyah!!, Sumayyah!!!"

Kin kiran ba 'daya ba ba biyu ba yasa ni waigowa tare kuma da san tuno Mai muryar tsammanin da nayi ko hakan ne 

Malam Hamid ne idan ba idona ne suke min gizo ba,domin a sanina lokaci baiyi tsawon da zan manta da shi ba,kallon mamaki nake masa,nima shi yake min a hakan har ya qaraso inda muka tsaya,gaishesa nayi ya amsa da murmushi fuskarsa haka Abid ma ya gaishesa Malam Hamid ya miqawa Abid hannu suka gaisa yana tanbayarsa sunansa Abid yayi murmushi ya fa'da masa da alamu Malam Hamid ya birgesa guri na ya juyo ya maida dubensa gareni

"Wato da ba zaki juyo ba ko?,harna fara tunanin qila bake bace,dan muryarki kawai na ji harna cigaba da tafiya nayi tunanin ke ce"

Nayi murmushi nace

"Eh nice nima da farko banyi tsammanin kai bane,saboda banyi tunanin sake ganin ka ba"

Murmushi yayi 

"To saboda me,bayan kinsan nan garinmu ne"

Shiru nayi dan bani da tacewa danni ganin mai ku'di nakewa Malam Hamid Ina zansa wa raina tunanin ganinsa,karo na biyu

Maganar Malam Hamid ta katsemin tunanina

"Kinyi shiru kullum na kira Halima saina tanbayeta ya kike takan cemin lafiya lau,Kuma har lambarki na buqata tace baki da waya yanzu haka da ta yayanki na nan kuke gaisawa,ni kuma banwai amsa ba saboda bansan mai zance masa ba idan na kira"

Na jinjina kai alamun na gamsu da maganarsa

Ya cigaba da cewa"na samu labari jarrabawar ku batayi kyau ba Allah yasa hakan yayi sanadiyyar samun nasararku a nan gaba,abun sam baimin da'di ba Sumayyah saina ji kamar ni abun ya faru dani"

Dukda banason a tuno min abunda ya faru amma hakanan na daure 

"Nace Amin nagode"

Bai qyale maganar haka ba,ya ce 

"Yanzu kinga rana ta farayi kimin kwatancen gidanku na nan sai na samu lokaci nazo,mu qarasa maganar da bamu qarasa ba a baya"

Shiru nayi Ina tunanin maganar da nasan ta soyayya ce take nufi ba dan ina da buqatar sa a rayuwata ba na masa kwatancen gidan tare da jagorancin Abid a kwatancen kawai dai saboda kirkinsa nayi masa kwatancen amma gaba 'daya a Raina kulllum bani yake Malam Hamid ba sa'ana bane a soyayya bare kuma aure dukda bansan koshi waye ba

Haka muka yi sallama yana Mai min alqawarin zaiso a satinnan insha Allah,daganan muka cigaba da tafiyarmu Abid yana tanbayata waye shi wannan,na masa bayaninsa,a matsayinsa na malaminmu ya dubeni

"Gaskiya Yaya Sumayyah yana da kirki sosai"

Nayi dariya na ce

"Kai Abid daga ganin mutum haka ai ba'a shaidar mutum Karan farko"

Ya jinjina kai ya ce

"Hakane",daganan muka sauya firar da wata" har muka qaraso bakin titi

Abun abun mamaki nan 'dinma babu motoci ga zafin rana haka naji Kamar nasa hannu ka na fashe da kuka dan tsabar takaici da bakin ciki ga fangon kaya a hannu tsugunnawa mukayi muna roqon Allah ya kawo mana mafita,babu jimawa mota mai kyau sosai ta tsaya kusa da mu da ni ba ma'abociyar sanin mota ba bare nasan sunanta ko ku'dinta horn aka yi mana ganin bamu san mai ita ba mukayi shiru jin qarar bu'de motar yasa muka 'dago kanmu,Abid naga ya qarasa gurin mutumin da yafito daga motar da alamu Abid yasan mutumin nima kallansu nayi 

"Kawu"naji Abid ya fa'da

Saurayin da Saida ya kirasa kawun na kallesa tabbas yana yanayi da Umminsu Abid 

Tambayar Abid yayi

"Yana ganku anan Abid"

Abid ya sosa kai 

"Mota muka rasa"

"Ku shigo na kaiku gida yi ma waccen da kuke tare magana" kawun ya fa'da da ba musu ya qaraso guna Abid 'din niko tun kafin ya qaraso na miqe dan gajiye nake dama,kayan muka kinkima mu ka qarasa wajen motar,Abid ya bu'de min gidan baya na shiga a lokacin har kawun ya shiga mota abid 'din ya shiga gidan gaba kusa da Kawun nasa sai a lokacin na gaida Kawunsu Abid 'din ya juyo ya amsa kafin ya juya ina jinsa yana cewa

"Abid wannan wace ban gane ta ba"

Abid naji ya ce

"Yaya Sumayyah ce,'yar qanin Abbanmu ce Abba Abdullahi"

Naji yana ce wa

"Au ita ce rannan naje gidan na ku,Ummin ku ke bani labarin zuwan nata"

Waigowa Kawun yayi ya sake kallo na naji ya ce

"Yasu Asma'u ai sai yanzu naga Kamar ki da Asma'un"

Na ce masa

"Suna gida lafiya lau"

Da haka yaja motar cikin mintina qalilan muka qarasa gida parking yayi muka fito harda Kawun su Abid 'din shine ya 'dauki ledar saqon yana janmu da hira har muka qarasa cikin falon da ba kowa a falon sai Yaya Samir 'din,yn danna wayar shi d Tv kunne Amma babu volume,sallamarmu ya amsa yana murmushi fuskarsa kusa da shi kawun ya zauna ya bashi hannu

"A'a Malam Samir ana gida kenan"

Yace 

"Eh wllh Kawu Mahmud,yanzu da naji shiru basu dawo ba nake tunanin Kiran lambar Aunty Ramlah"

"Ayya wllh a hanya na ha'du dasu suna jiran abin hawa"

Ba muqarasa jin zancen ba muka wuce ciki, kitchen Ni na nufa,na kawo musu lemo zan tashi Yaya Samir yace

"Zauna mana firarki mu keyi da kawu Mahmud,yace waya ya kamata na siya maki,aikin isa riqewa"

Na kalli kawu Mahmud yayi murmushi

"Eh mana Sumayyah gudun wannan matsalar,Kuma aikin isa riqewa na yaba da natsuwarki"

Ni dai Kai na mayar qasa naji an fara yabona,ni Kam banaso

Kawu Mahmud naji yana cewa

"Ya na ga ta duqar dakai,haka,nidai Samir na ya ba da yarinyar natsuwarta kam,ni bansan ma 'diyar waye ba,da farko,ashe 'diyar Asma'u ce,"

Yaya Samir yace

"Eh ka manta ta ne Sumayyahn Samir tana yarinya"

Naji kawu yace

"Dan Allah muje yanzu a siyo mata wayar,nifa banasan 'bata lokaci kasani ina cewa tom nafiso ayi"

Inajinsu Ina kallonsu kuma sun birgeni Kamar abokai a haka

Kawu Mahmud bayan sun miqe ya dubeni

"Taso muje ki za'ba da kanki"

Na miqe nace "Bari na Kira Abid"

Yaya Samir yace

"A'a Malama Sumayyah,qyaleshi kawai"

"Tom"na iya fa'da

Nabi bayansu,a motar Kawu Mahmud muka fita,wani shopping store na wayoyi muka tsaya, mukayi parking

Muka fito Yaya Samir ne driver din tare muka shiga nidai ban iya za'ban waya ba haka suka za'barmin Iphone,d qarama maxfone,wai acewarsu saboda iPhone bata riqe caji,anan har layuka aka siyamin akamin register,nayi murna sosai nayi musu godiya

Nakasa Kuma fahimtar dalilin hidimar Kawu Mahmud wajena,daga ganina haka dai muka shiga mota ina tunani,bansan alaqarmu ba amma inaji a raina,kawai qila,shima yana cikin samarin Aunty Asma'u dai, shi yasa"


Murna Bayan dawowarmu ban jira na caza qaramar ba,Na kira layin, Halima,duk abinda zanyi bana manta Halima,itace take fara fa'domin a raina,inasan Halima,fiye da tunani,inajin wayarnan dama tana nan tare za'a siyamana,Batul kam ba tada wata matsala,ita dai biye mana take yi,aurenta ma,tana gama makaranta za'ayi nafi tunanin,kirana biyu bata 'daga ba,na aje wayoyin na saka caji ko Mai yasa oho,tunaninta nakeyi kawai,Halima rayuwarta ta yimin,komai nata,ina sanshi,Bata da San hayaniya kamar ni haka Halima take,


Ina kwance ina tunanina naji qarar wayar tawa,Halima ce ,na katse kiran nabi da sallamata

"Qara ta yimin kunne, Sumayyah,ba dai kinyi waya ba,"

"Nayi murmushi HalimanSumayyah, kenan,kafin nace

"Oh Halima haka kike yi Kuma yanzu"

Tace

"Kiji 'yar rainin wayau dan Ina murna shine kike min wulaqanci,ya miki kyau"...