Part 21
Cikin abinda bai wuce awa 'daya ba muka qaraso Gwarzo kayana aka saukemin ganin jiran samun napep zata zamarmin aiki machine na hau badan na saba ba,nafi sabawa da napep tafi sirri jakata na gaban machine ina baya duk sai naji daban sa'ata guda ma hijabi nasa,unguwar da zaikaini na fa'da masa sabuwar unguwa kenan har kofar gida aka saukeni na sauka na bashi ku'di ya saukemin jakata ya wuce gidan su Abbah nake kallo babu laifi gidane mai kyau da qaton gate 'dinshi tunanin rayuwar da muka bari kuma muka dawo nakeyi a lokacin da nake kallon gidan,muryar Rumaisa da naji ta dawo dani daga tunanin da nakeyi
"Yaya Sumayyah oyoyo"
Kallon Rumaisan nayi da murmushi fuskata
"Rumaisa daga Ina kike haka"
Kai ta 'dan sosa"naje gidan Aunty Jamila ne"
Na kalleta" kya sosa qeya da kyau ai da safe kin Kama hanya gidan mutane,bansan tun lokacin da kika tafi ba,Ni kamamin jakarnan mu je ciki"
Kamamin tayi muka fara tafiya,Rumaisa ta ce"A'a fa Yaya ban da'de da zuwa ba Mama ta aikeni ma"
Na jinjina Kai muka qarasa kofar gidan tura kofar gate 'din mukayi muka shiga da sallamarmu Hajiya da take zaune brander din dake gefen 'dakunansu,kallonmu ma bata yi ba bare amsawa dauriya nayi na ce"Hajiya sannu da gida,ina yini"
Tsaki tayi min"na yi tunanin ai ansamu guri baza'a dawo ba,anje ana cin gajiyar Wanda yayi aiki tuquru ya tara ba malalacin ubanku ba,ai danasan Hashim zai dauke ki gidanshi da ban amince ba gwara a barku ko zaku mutu cikin talauci,laifin duk na ubanku ne malalaci mai sakaran zuciya shi lallai so ya qi rabuwa da uwarku ya samu ko ya samu madafa ma"
Kallon Hajiya kawai muke harta gama maganarta sai kace mu tsarartane,wannan zancen nata kan kawai taqi jininmu saboda kaf cikin 'ya'yan ta Abbanmu ne bashida wadata shine kawai abinda ya janyo hakan,ko dake bama ita ba har Baba Abbansu Abbah haka yake yin maganganunshi shi acewarshi ya gama dawainiyar karatu da Abbah ya zauna sakarci dan aikin ma ko koyarwa baisamu ba
Muryar Rumaisa najiyo cikin zafin zuciya da bansan tana dashi"ai Hajiya arziqi ba nufinmu bane mu kanmu ba haka muka so ba rayuwar tamu"
Ina qoqarin tsawatar mata naji Hajiya na ce wa"to mara kunya,ai Allah yace bawa na tashi na taimakeka kuyi zuciyar neman nakai kuyi ku'di ba zuciyar maida magana ba ma rasa kunya masu gadonta Kun gada wajen uwarku fitsararriya mai mugun hali"
Saurin jan Rumaisa nayi da Jakarta tawa,zuwa 'bangarenmu, nima nasan jan magana tane matar da sallamarmu bata amsa da zata samu lada ina ga amsa gaisuwa ta,bayan nasan halin Hajiyar ma sai addu'a ita indai ba ka da shi to ba abokin yinta bane,
"Yaya aida kin barni da ita ya zata riqa fa'dama na magana mune muka halicci kanmu,Kuma duk maganarta tafi ga Mama,ai gwara Abbah 'dan tane shafuwarsu ce"cewar Rumaisa,ni bansan haka ma Rumaisa ta iya tsara zance ba kamar wata babba ko ni na tsara wannan zancen abin mamaki ne,wajen wasu,duba da qanqantar shekaru na,saidai Rumaisa ta zuciyane da alama dan ita din magana ma bata dameta ba,shiru kusan shine amsarta sai kallo,abunda zai harzuqata babbane ko ni bata min bare Hajiya kuma wadda ta haifi Abbah,muna shiga 'bangaren mu da sallamarmu,jin sallamata duka sukayo waje daga 'daki sunamin oyoyo falon muka rankaya muka shiga mamah ce zaune da fara'arta ta kalleni
"A'a Sumayya ba tsammani,haka ayam"
Murmushi nayi mata na zauna nima gefenta a saman tabarmar da take kai duka suma zama sukayi kusa dani
"Mama ashe kun da'de da dawowa nan ko a waya baku fa'da min ba"
Murmushi mama tayi"To ya za'ayi Sumayya mu 'daga miki hankali,Mai gidan ya ce indai bamu bar gidan ba a washe gari ya dawo waje zai fiddo mana da kayan ya gaji da zaman namu ba ku'din haya,shine dai Abbanku shima ya fusata ya kwaso kayanmu muka dawo gida,anan 'din Baba da Hajiya dakyar suka barmu muka zauna"
Shiru nayi Kamar bazanyi magana ba saboda takaici nace "yanzu ma mun tadda fa'dan Hajiyar,Rumaisa saida ta tankamata"
Mama ta kalli Rumaisa"Kin kyauta Rumaisa kina gani tunda muka dawo zama baya mana da'di shine Kika biye mata, saboda ki sani a wata matsalar,dama shirin naki na munafinci ne rashin kunya ce cike da bakinki ko?,ina sakwan nawa"
Rumaisa da kamar tasa kuka tace"kiya haquri Mama,abunne munata jin ciwanshi Hajiya bata kyautawa,Aunty Jamilar tace zata aiko Shureim bata qarasa murzawa ba"
Mama na kalla da murmushi"Yau Mama taliya 'yar murjj za'a ma na kenan,naji da'di jallop ce ko da miya?"
Mama ta kalleni da hararata "to da Maggi za'a ci ba ku'din siyo barkono ma,sai dai qila Jamilar ta ha'do mana dashi"
Nayi saurin girgiza Kai"A'a Mama ga ku'din da Abbansu Halima da na Batul suka bani,na hau mota to sai yaya Baffa ya bayar ma"
Mama tayi murmushi"Masha Allah,Allah ya bar zumunci, amma da baki anso ba dai,wannan lokaci kowa na ta kanshi"
Sadik da yake ta kallona nasan da magana bakinshi na ko ji ya fara"Yaya Sumayya ina tsarabarmu take "
Na ce masa"yanzu za'a siyo badai biscuit da alewa ba na manta a mota ban siyo ba"
Na juya ga Mama "Yawwa Mama ina Ahmad yazo ya siyo,naga banji motsinshi gidan ba"
Mama ta ce"Lallai Sumayya kin manta Ahmad da kwallo kenan tunda yau weekend ina zaki ganshi kuwa ai ya shige unguwa,sai yunwa ta ciyoshi kyaga ya dawo Kamar yaci babu,ga Rumaisa ko Khadijah sai ta siyo,ko Sadiq,Khalil ma yasan wajen ina rubuta masa shikenan"
Na ce "Haka ne Mama amma dai Ahmad nashan zagi wajen Hajiya da Baba nasan"
Mama ta yi 'yar dariya"kema kinsan zasu fasa ne,haka suke ce masa mai zuciyar ubanshi sai iya ball ya iya yawan tafiya,ni kuma dama 'yar matsiyata bansan da'din arziqi ba bare nasa Ahmad ya tashi ya nema"
Dariya nima nayi na ce"Haba ainasan za'a rina,ina Aisha take ne mama"
"Tana 'daki tana barci,kinsan Asma'u ta zo tana Katsina qila yau zata dawo ta wuce gidan nata,wannan karan a motarta tazo ma,ta fara driving tana baro cikin gari da motar"
Murmushi nayi kawai jin zancen Mama"kuna cikin wani rigimar kenan Aunty Asma'u ai 'yar hau ce Mama wallahi,nifa banasan ma ace muna da wani relationship"
"Kinga Sumayya ba ruwanki da Asma'u duniya makaranta ce,karta kamaki ta lallasa,dan tunda ta ganmu gidan kamar jiranmu take ko gaisawa da Hajiya naje yi su Khalil kuwa ba damar suyi wasa da Haidar,da farouk,sai fa'da tayo kaina Kamar nice Khalil 'din shi dama nata Khalil din ta hanashi wasa dasu ya hanu shi kuma,ai Asma'u tana taqama da arziqin nan,Kamar ita ta farayinshi"
Qagara nayi Mama ta kammala zancen Mai cike da 'bacin rai
"Wai mama ina Abbah na matsu naganshi ne"
"Bazai jima ba zai dawo kije ki huta haka"
Na miqe jin kalaman Mama ina dafa cikina"Wallahi kuwa Mama yunwa ma nake ji,Sadiq ya siyo mana biscuit din Rumaisa ta siyo kayan miya mama Dan Allah ta manja za'ayi mana,miyar jajjage,Rumaisa sai ta jajjaga ai greater dinmu na nan ko"
Rumaisa ta kalleni"Kai Yaya Sumayyah banason greating kema kinsani hannuna ya dinga yaji"
Mama ta kalli Rumaisa tayi tsaki"waye to zai miki shi,Ahmad 'din bayanan da Kika raina na saki aiki kice shi zaiyi yace zaiyi"
Dariya nayi na ce"Mama ai kinsan tsakanin Ahmad da Rumaisa da amana ai"
Daganan na fice na shiga dakin gadon Mama saman katifarmu da take jingine na tayar na kwanta, barcin gajiya dana zafin duka ya daukeni mai wahala dan har lokacin bai gama zafi ba dukan da nasha bana wasa bane,kai kace sata nayi, biscuit ma ban tsaya jira ba sai barci 2:30pm na tashi,shima kukan Aisha ya tasheni na dauketa na fita da ita na miqewa Mama nayo alwala na tayar da sallah ina idarwa Abbah na shigowa kallonshi nayi kawai dan da ganinshi a galabaice yake da yunwa Allah sarki Abbah,ni dai nasan idan bai ci ba bamai bashi kuwa ko Hajiya Kai kace ba ita ta haifeshi ba duk tunaninsu auren Mama ya qara tsiyatar da shi kuma dama shi tun asali ba shi da shi,ko da bai auren ba bazai yi ba 'yan uwanshi masu san zuciya ne,sunfisan kansu akan 'yan uwansu kamar ball suke bugashi yana musu dawainiyar da basa gani ba wanda yake niyyar masa cuku cukun samun aiki,saboda san zuciyarsu,ganin karatun nashi ya fara nisa ba'a bun yi yaga gwara yayi auren ya tara iyalai shima,suko su Hajiya basu damu yayi ba,kuma bata gaji da qinshi ba saboda ba shida komai fafutukar karatu ya gama na masters yana gamawa ya tattagi aure ya rufawa kanshi asiri kafin Allah ya kawo abinyi girman gidan su yasa part din Baba ya zama nashi yasa Mamanmu ciki mamar tamu ba wai arziqin shi ta kallah ba dan kam bashida shi itama nata iyayen haka mamarmu ce hope dinsu akan sanadinta zasu rage wani kukan,saboda yadda samari masu ku'di bama ku'din iyayensu ba ke zuwa wajenta,amma ta tsaida Abbah,da kanta ta tunkari matsalar ba wani ya tunkarar mata ba,halaccin da Mama ta yiwa Abbah shiyasa ya kasa rabuwa da ita dukda hakan 'yan uwanshi suke so, duk da yasan rabuwar canjin alkhairi zata zamarwa Mama amma shi tashi rayuwar da makomarmu ka'dai yake kallo da tausayawa,zuwa yanzu da al'amuran suka sake rinca'bewa, maganar Abba ta katsemun tunani na
"Mutanan katsina,yau kike tafe ashe"
Kallon Abbah nayi da ko a yanayin maganar a galabaice yayi
"Eh Abbah sannu da zuwa"
Mama najin muryar Abbah tayi saurin leqowa
"Abbahn Sumayya kazo ga abinci,tun fa safe bakaci komai ba,sai kuyi maganar zuwa anjima"
Cikin falon ya shige nima bin bayani à Abbahn nayi muka zauna zaman cin abincin lokacin har Ahmad da banji shigowar shi ba,sai lokacin na ganshi,kallonshi nayi
"Lallai Ahmad ayawo kenan,koma ka zo mu gaisa kasan ina cikin da'ki"
Kai ya gya'da "Barni Yaya yunwa nake ji wallahi,yanzu Mama ke fa'da min kindawo qila kin tada sallah,naji yunwa,muci abinci ke dai kawai"
Dariya nayi kawai "Ana ta shan ball har 2 bance ma kayi sallah ba"
"Kai Yaya da wannan ranar wata inuwa muka samu muka kwanta ne,saida mukayi sallah, tukunnah,na taso na dawo gida"
Da haka na zuba abincin nafara ci kamar kar ta kare Saida na qara wata inason taliya ta murza d miyar jajjage ta manja sosai musamman ta sha Maggie star Ina tayiwa Mama Santi har muka gama,Abbah kuwa wani plat mama ta taqe masa saida ya cinyeshi tas,hannu duka muka je muka wanko aka bu'de faifan fira,Abbah Mama ya kallah
"Hauwah taya aka samu ku'din cefane?, harda wannan miyar haka mai da'di gaskiya da da ku'din gobe ma ita zamu yi"
Mama dariya tayi"Kasan dama wajen Asiya na samo fulawar to 'diyarka Sumayyah na zuwa ta bada ku'din na motane da Abbah Ahmad,da Abbansu Halima suka bata sai shi Baffah ya biya ku'din motar"
Abbah yayi murmushi "Allah sarki naji da'di Sumayyah ,Allah yayi miki albarka,zanko kira su na musu godiya,ya Kika taho haka"
Hawayen da ke qoqarin fitomin na maidasu ina girgiza kai,abunda ya faru duka na zayyana wa Abbah da Mama saidai ko zancen wata soyayya tsakanina da Yaya Samir duk ban basu ba iya dukan da nasha wajen Abbah,na fadamusu,ina tunanin Zan sake dagula lissafin su Abbah da wannan zantukan,ina tunanin Zan samu daidai dani ne,ba wai Hamid ko Yaya Samir ba,sai yanzu nakejin Ina ma na kar'bi Yaya Hakim amatsayin halaccin da zanwa Halimah,amma dakaina naqi amincewa saboda wasu tunanuka nawa da ban tabbatar da har lokacin Firdausin na tare da Yaya Hakim ba amma dai na barshi da za'bin shi na asali da addu'ar Allah ya daidaita su.
"Yaya Kika zauna Abbah Hashim ya doke ki haba dan Allah,akan qaramar matsala,shi to wanda kikace yazo wajenki har haka tafaru me yasa yakasawa Abbah Hashim bayani dalla dalla cewa saqo aka bashi ya baki to ina ruwanki da alaqarsu da Fatimah kince bama ki jima ba,kawai mu dai ba'a qaunarmu ne kawai,mun zama bare ne,saboda ba muda shi,amma Allah bai manta mu ba,yana sane damu da halin da muke ciki ubangiji ke azurtawa samu da rashi na shi ne,bama tunanin akwai mutumin da zai tsiyatamu ko azurtamu face da izinin ubangiji"
Kukan da yake cin zuciyata na fashe dashi,da jin maganganun Ahmad yana magana Kamar wani matured saboda yadda rayuwar tazo mana muka samu experience na rayuwar da muke ciki,qaryar da nayi kenan,na barwa Fatima Hamid zancensu ma banaso naji na sake tsanar tun karar rayuwar su Abbah Hashim ko da a cikin mafarki bare ido bu'de,na sake tunawar yanzu da idona da kunnena duk na fahimci tsanar tsantsa da akemana a dangin Abbah da sune ginshiqinmu wani kukan na sake fashewa dashi
Abbah da kwallah ta taru idan shi
"Haba mana Sumayyah ki bar kukan haka zaki sake tayarmin da hankali kina tasomin da abunda yayi shekaru yanacin zuciya ta Ina kokarin rayuwa kamar kowa da aza farin ciki a rayuwata,nasani tun asali 'yan uwana basa qaunata hatta da iyayena da matsalolin rayuwa ta janyomin haka,dana San haka zata faru da ban turaki gidan Hashim ba,duk yadda na nisanta kaina dasu Samir ya janyo hakan da wata 'baraka a tsakaninki da Samir ta faru da bazan iya yafewa Samir ba,na rasa ina zanyi na samu rayuwar yadda nake mafarkin samunta,da ba mamarku ban san ya duniyata zata kasance ba amma ubangiji ya sa ta zama mata ta ta bawa yarana tarbiyya a halin da muke basu ta'ba daukemin magana da zata tadamin hankali na,nasan Allah na tare damu da duk mutanan ke cikin mawuyacin hali irin Wanda muke ciki"
Ahmad da shine ka'dai bai tashi ba dan duk su Rumaisa na waje ,suna Shirin wanka,muka fara zancen Ahmad ya kalli Abbah
"Dan Allah Abbah kada kayi kukan kaike sake kwantar mana da hankali idan baka ciki namu bazai kwanta ba,ku muke kallo muji hankalinmu na qara kwanciya kuma a halin samu da rashi muji zamu iya rayuwa ko munci ko da bamu ci ba 'din"
Mama takallemu Ni da Abbah"Haba dan Allah kun tasamu kunata hawaye da kuka kuna tuna abubuwan da basu da anfani kuna nema ku jefawa kanku wani ciwan daban,idan kunyi waye zai taimakeku bayan ubangiji,yanzu rayuwa ta canza kowa kanshi ya sani sanda kake da buqatar taimako ba'a yima shi,idan kuna tunani haka ciwo zaku sawa kanku,waye cikinmu abun baya damunshi, amma mun tuna ubangiji is there for us"
Sainake jin zancen Mama kamar ba'a hayyacinta take ba Kamar bada jin da'di itama take ba,kasa cewa komai nayi ,sai Abbah
"Nagode Hauwah,insha Allah na daina,dama da'dewar da kikaga nayi ban dawo ba gidan haya na fita nema,Baba yace yana buqatar bangaren shi Asma'u zata zubamasa kayan furnitures ne,toh shine dalilin jimawar tawa,na bada cigiya,wajen Musa abokina, ku'din hayar a hankali na biyasu,ke kuma saiku Kama sana'a da yaran nan ko awara duk gatanan yara nayi bakin titi wa'danda sunfimu rufin asirin ma zama ba wata sana'a ba da'di yara qara girma sukeyi,ga karatun Sumayyah ma sai ko Neco kafin Fara biya a samu hanyar Allah nada yawa sai a biya mata ta zana takardun nada anfani ai,an fara a kammala da'di"
Mama na gani tana share hawayenta ta maida kallanta ga Abbah"Yanzu shima Baba hardashi a irin wannan maganar idan baka bansan yadda rayuwarmu zata kasance ba,naji nadamar dawowa ta,har gwara a fiddo mana kayan waje ba zamu rasa na Allah da zasu taimakemu su bamu matsugunni,wallahi zumunci da iyaye a rayuwar ka da ta 'ya'yan ka ta kasa tasiri,Kaya haquri ko ubana yayi hakan zan fa'da da zafin zuciya,yaushe yama maganar baka fa'da min ba?"
Abbah ya ce"da safe ne zan fita mukayi karo da shi shima zai fita gaisuwar ma tawa bai ansa ba sai qudirinshi da yake cin shi"
"Bakomai gasu ga Asma'u nan da sauran insha Allah watarana zamu samu canjin rayuwa ko ma Ya ne,ubangiji na tare damu,ba zamu ta'be ba madogarar duk lamura Allah ,waman yatawakkal Alallahi fa huwa hasbuh"fa'din Mama
Mama tana da ilimin addini matuka,Kai kace tayi haddar Alqur'an zallar biyece da tasa harta kusa haddar saboda tilawar Alqur'an,shiyasa rayuwar mu ta zama kafin mu kalli kowa a lamuranmu tom ubangiji muke fara kallo,shine mahaliccinmu maji'bancin lamuranmu,saina ce Abbah yayi dacen mata matuka,Kai duk ma 'yan uwan mama haka rayuwarsu take sunasan taimako musamman garemu basu kyashin su yima Mama komai suke da shi,dama saina ce zamanmu anan 'din yafi mana da'di akan kanon matsalar su Hajiya yasa Abbah kwashemu,anan ma ina cikin qawayena sa'annina da suke familyn mama ne,Dan ni bama kowa nasani a familynsu Abbah dan duk tafiyar tasu kalar ta guda ce su dai basu qaunar talaka,babu laifi suna da rufin asiri,ne shiyasa,miqewa nayi Kamar an tsikareni bedroom na shiga na lalubo jaka ta na ciro wayar da kawun yaya Samir ya bani da ku'din da Yaya Samir ya bani na dawo na ajewa Abbah su a gabanshi kallona yayi da firgici
"Sumayyah ina kika samo wayar nan iPhone 11promax naga an rubuta a kwalin sai wannan ku'din zasuyi 20k"
Murmushi nayi nayiwa Abbah bayani tare da fa'dar abunda naga ya cancanta ayi dasu
Murmushi yayi Abban da Ahmad ya dauki wayar dake cikin kwali yana dubawa
Abba yace"Kai Ahmad ajiyeta haka,kasan babba ce,yanzu shi Mahmud ya miki wannan kyautar haka, lallai Mahmud yayi ku'di sosai Asma'u taqi shi,gashi sanadinta ya miki wannan kyautar,dama Mahmud banji zai jure halin Asma'u,dan sai addu'a, Asma'u arziqi na mata hayaqi akan nan nata,Allah yasa kada labari ya sameta Mahmud ya siya miki wayarnan sai tace zatayi wata maganar"
Ahmad yace"Kuma Abbah sai ka barta tayi ,irin wannan wayar muka Saida ai mun warke insha Allah,ina ganinta a wayar abokina hotonta,Abbah shegen tsada gareta na baka labari wannan wani Mai amanar zakasa ya Saida mana"
Mama ta ce"Ai koni kan wayarnan idan Asma'u tace zatayi wani haukan ban kyaleta,yawwa sai Abbah Musa ka bashi ya siyar tunda ya fika sanin garin yanzu"
"Hakane Hauwa'u shi zan kaiwa, Sumayyah ki cire layi idan akwai a ciki"
Da toh na amsa na kar'bi wayar na cire,saida na cire na kunnah nagoge message dana turawa Hamid call logs ma ban kalleshi ba banji inada matsala dashi "
Mama Kam da Abbah ubangiji suka riqa yiwa godiya da 'daga hannunsu ubangiji mai taimakon mutum bada saninshi ba,ji muke kamar talaucinmu ya yanke a dalilin hakan,lallai naga ribar taimako ba kasan mai zai haifar ba ko ya kayi shi a dalilin kyautar da mutumin yayi a zuwan ba komai ba ce,mu tana shirin zamar mana komai 'din,Ni kaina a mafarki banta'ba tunanin zan ta'ba danna babbar iPhone haka na dauketa sai dai naji ta a novels budurwa mai aji da nasaba da kyau da ku'di ta riqe wadda ita a wajenta bakomai ba ce amma a wajena ta zama komai,nikam waya tazama jarina,ko da zamu fa'di amma zata toshe mana wasu kafofin da damuwoyin da suka tunkaromu,da hatta iyayen Abbah sun kasa magance mana koqarin tura mu suke ma................
Sumayyah Abdallah Khalil the Actress
Doughter of
Hauwa'u Ibrahim Alhassan
And
Abdallah Khalil Ishaq