Part 24
24...
Haka muka gama kwashe kayanmu da ba yawa garesu b dama muka qarasa lodasu a akori kura dukkanmu ba wanda yanayinsa yake cikin dad'i muka bar gidan kafin su fito ma su sake 'bata mana rai a qasa muka tafi ha'de da Abbah Musa da shine yasan gidan,ba laifi tafiya ce mai 'dan nisa ba ma 'da ba mai nisa ce ma ba sababbin unguwanni bane ba,gidane ginin qasa Abbah Musa ya nuna mana shi da muke qoqarin qarasowa,ba shida ko filasta ma amma Alhamdulillah yafi mana gidansu Abbah da suka cire soyayyar iyaye da 'dansu suka wulaqanta shi kanshi Abbah ma bare mu da mama a qofar gidan muka toge muka jira Abbah Musa ya bude kofar da a zauren muka isar da kayanmu harma an kawo su gidan sun juye da Abbah Musa ya basu 'daya daga cikin key din gidan gaba ɗaya muka shiga cikin gidan da cikin azama muka fara kinkimar kayan zuwa cikin gidan mai da'kuna uku da banɗaki sai kitchen na langa langa da alama muguwar zuba yake yi kitchen 'din amma gaba ɗaya muna farin ciki da samun canjin da Abbah ya kasa ɓoyewa ya dubi Abbah Musa"Musa bansan da wanne ido ko kalmomin da zan dubeka ko na furta ma ba nagode sosai ka taimakeni lokacin da nake jin a yadda matsalar ta tasomin nafi kowa buqatar taimakon"
Abbah Musa ya girgiza kai"Haba Abdullahi ai yiwa kaine duk wanda zai taimaki wani to yasa a ranshi kanshi ya yiwa ba wani ba,kamar wanda yaƙi taimakon kanshi ya yiwa,ladan bai isheni ba ai da zan gaza yi ma taimako dan ko da ƙarfin jikina zanyi ma ,muma a harkar karatu ka taimakemu ai kayi karatu amma ka bari muyi exam tare da saboda mu karatun baima dame mu ba ,sai gashi mun rigaka cin moriyarshi,Abbah Musa ya fa'da murya raunane da alamun rayuwar tamu ta dameshi da muke ciki" ni da nayi tsaye kusa da su hawaye naji suna zubomin cikin rashin shiri
Abbah ya dafa shi"Haba Musa karka damu dan Allah samunku ai nawane ba gashi ba ka fahimceni ka dubemu abin da a cikin gidan mu hatta da iyayena sun kasa wannan fahimtar,ni haka rayuwar ta namun da'di ina fahimtar abubuwan da a cikin yalwar arziƙi ne yayi ka'dan na fahimta"
"Allah ya mana suttura Abdullahi wucewa zanyi akwai rijiya a makwabta nan gida jikin nan 'din kusa su samo muku ba matsala batun ruwa sai dai ko su yaran suqi zuwa danni sai na siya sanda muka zauna yarane masu qyuya Allah ya bani"cewar Abbah Musa yana koƙarin ficewa
Abbah ya ce"sunga kana samunka ne niko karsu ɗebo ma su ga ni"
Abbah Musa ya tsaya da fara tafiya "na shafa'a ba muyi sallama da Hauwa'u ba,nasan sai tama ciwan baki kasan mata"
Abbah yayi dariya kawai ya kira Mama ta fito t sake ma Abbah Musa godiya sukayi sallama ya qarasa fita Abbah n biye da shi zuwa rakiya waje
Sai sannan na shiga ɗakunan ina leƙawa da babu isassun siminti a ƙasa duk ya cire tabarmi muka shishshifiɗa da ba manya bane dandanan muka shiga ayyukan gidan da share share muka yi muka gama su Rumaisa suka shiga ɗebo ruwa nima har dani ba laifi daga shigarmu gidan matan gidan suna da kirki gidan kuma mai kyau ne babu laifi ba kamar wanda muke ciki ba akwai yarinya kusan sa'ata a gidan Malika da shiga ta muka fara fira ta nada kirki kamar iyayenta dana ga alamar hakan haka muka dinga kinkimo ruwan saina zauna ma nice nake jawowa suna kaiwa gidan Malika dake wanke wanke a gefen rijiyar tana ɗan san muyi fira na dai ɗan sake da ita muna firar makarantah,ita ma mate 'daya muke bata samun qualyfying ba amma shirin biya mata akeyi ma kuma tana tunanin ɗora karatu ma ,naji ina ma nice ita haka na taya ta murna tana tanbayata wanne course ya kamata idan tazo jamb tasa ka nayi dariya na aje gugar dana gama jan ruwan
"Wallahi bansani ba duka fa tare za muyi candy ai sai dai ki tanbayi yayunki da suka ta'ba jamb ɗin,suka samu wucewa University ai"
Tayi dariya"ok na tuna fa hakane,zan tanbaya zumuɗi ne fa kawai kinsan ba'a tashi farawar ba ma"
Na jinjina kai "Nace hakane kuma,Allah ya taimakemu,bari na tafi,mungode"
Malika ta ce"Amin tom sai na shigo ko anjima ne,na qarasa aiki,kina kitso ne?"
Nayi murmushi"A'a banayi Mamarmu dai tanayi,inkinaso zan mata magana saikizo ta miki"na lura dai Malika surutu gareta har ya wuce nawa da da ma banwai cika surutu ba
"Kai da kin kyauta min yafi sati a tsefe na baki labari inata kame kamen mai kitso inda nake zuwa yayi nisa yanzu na rage san yawan kuma"cewar Malika na bita da "uhmm hakane sai anjiman to da haka na fice ina mamakin surutun ta haka daga ha'duwa abun har mamaki ya bani ma
Ina shiga gida sallama Mama ta amsa min da tayi shinfiɗa a waje,tana murmushi "Ai su Khadijah sunce min kinyi sabuwar ƙawa a gidan ɗebo ruwan" na zauna gefen Mama ina ce wa"Mama ke dai bari kawai kamata ta ke tare zamuyi candy amma surutu tsiya gareta daga haɗu wata da ita har naso na gaji"
Mama ta harareni"ke kin manta naki surutun cakwaikwaiwa kenan,kin sake haɗuwa da kalar ƙawayen naki kenan ai",jin Mama ta ƙi yarda da zancen surutun Malika na ƙyaleta ai zata zo gidan zata tabbatar nata surutun ba irin namu ba ne ba,na canza zancen da "Mama Abbah har yanzu bai dawo ba wallahi na fara jin yunwa"
"Eh nasan dai yana hanya insha Allah"Mama bata gama rufe bakin taba mu kaji sallamarshi ya shigo hannunshi ɗauke da icce da nasan bazai wuce na ɗari biyu ba sai leda kuma ita ma a hannun, miƙewa nayi na ansa iccen nayi hanyar kitchen Rumaisa ta ƙaraso ansar leda ita kuma naji Abbah yana "ƙyaleta Rumaisa fulawa ce a qasa saman wayar Sumayyah ce,samo roba a zuba fulawar a ciki ayi ko ɗan wake ne"
Inda muke zaune na dawo na zauna Rumaisa ta wuce samo roba na ɗan ɓata fuska Abbah dake gefen mu ya kalleni ya kalli Mama"Hauwa'u mai kika ma Sumayyahn taki ne"
Dariya Mama tayi"me zan mata kuwa kasan ba tasan ɗan wake shine taji za'a yi take ɓata rai"
Abbah ya kalleni"Au wai shine abin ɓata rai bari toh ayi wainar fulawa amma in baku ƙoshi ba ruwana" na amsa da toh,Mama ta taɓe baki"ka dinga biyowa yaran nan musamman Sumayyah ma"
Dariya Abbah yayi"toh naqi biye ma ta,ita da ba yayye gareta da zasu biye mata ba,indai inada hali kam hukuncin Sumayyah da ta yanke shi za'a riqa zartarwa a gidannan bama na iya abinci ba,kema kika yi wasa saita qarasa har kwashe fadar yarda da shawararki a wajena,nifa kinsan ba ruwana babba mace ne ko namiji yana nan dai matsayin shi"
Mama tayi dariya "naji dai ai ni na haifi a bata bazan ji haushi ba,amma kar a waremin Ahmadi na,duk hankalin Sumayyah shi namiji ne ya fita tunani"
Abbah ya ce"oh my God,ai ni ma namiji ne nafi Ahmad tunani in na tanbayi shawara naji baiyi ba wadda Sumayyah ta bayar to zan shawarina da kaina,ya bari ta ci fadarta shi ko yaushe muna tare"
Ahmad dai baisan wainar da ake toyawa ba yana ɗaki ana sana'ar barci kamar kasa haka yake nasan da tuni mun kacame da gaddama,Rumaisa ta dawo da roba da saida ta nemo ta ajewa tayi aka fara ciromin wayata a kwalinta yadda aka bada ta Abbah ya miqamin a bata yana "Ai Abbah Musa na faɗamin kyan wayar nan,da inada kuɗi ai na siya miki n siyawa mamanku da ni kaina kuma"nayi dariya daga cikin kwalin ya cirota ya miqamin yana"kona kunnata a bani aro ma"nidai dariya nakeyi muna ƙoƙarin ha'da ƙullun waina ɗin hankalin mu kwance ba muda zullumin komai sai yau da kullum amma ba bu tunanin cin mutumcin kowa duk da dai ba kayan wani muke ci bashi ba amma a wannan rayuwar na dauki cin mutunci basai haka ta faru ba,kawai akan abinda babu mai yiwa kansa ma sai a ci maka mutunci dukdan ko bahagon tunanin gazawarka ce,haka muka fara soya wainarmu Ni Kam a na cireta daga kasko nake cinta danma fulawar da yawa a ƙalla kofi biyu da na tabbatar ni zan kusa cinyeta ma,da yamma yaran sun fice da Abbah ya samu islamiyya zai kai su ni kam nace ba yau ba sai an huta gaskiya zan fara zuwa haka dai Abbah da bai cika San takuramin ba ya amince Mama ko sai faɗa take tana aiko ta yarda na yau amma bata yarda gobe ba kuma ni zan wanke wanken gidan rashin dai zuwan baisa na huta ba shi ko Abbah makaranta ya samu iya kuɗin Laraba ake kaiwa kuma yaji ana da karatu yaga gwara yayi ta maza dan zaman gidan ma bari ta ishesu ma,yaga kuma ga sauqi ya zo
Sallamar da na ji nayi saurin leqowa daga ɗaki da nake kwance sallamar Malika naji amsa mata sallamar nayi ta ƙarasa shigowa ta dubeni
"Yayi Sumayyah barci ma kike yi ko,kitso nazo fah"
Na ce "ya fara ɗauka ta dai, shi go na ma mamarmu magana",Cikin ɗakin ta shigo ta zauna ni kuma na fito na je na fa'da wa Mama Malika tazo kitso,a waje mamarmu tasa nayi shinfiɗa na dawo ɗakin ina faɗa mata ta fito
"Ban ga ƙannan ki ba,suna ina"cewar Malika
Na ɗan yi murmushi na ce"Sunje Islamiyya Abbah ya kai su ance bayan gidan nan ce,ba kuɗin term ake biya ba bansan sunan makarantar ba"
Malika ta kalleni"lah nima makarantar nakeyi ai,kwarai ta kyauta ce sisi ba'a bayarwa sai goma ashirin kuɗin Laraba,to mu makarantu anan kusan duk na kyauta ne ma,to kuɗin babu yawa"
Na ce"Allah sarki mu a unguwar da muka zauna a cikin Kano ba laifi da tsada gaskiya"
Malika ta ce"Hakane nima dan da karatu yasa ba'a canzamin makaranta ba yaka mata kema ki shigo gaskiya"
Nan nake shaida mata nima gobe zanje da haka muka fito,Mama da tuni ta fito haka Malika suka gaisa da Mama ta zauna ta miƙa ma kibiya aka fara kitso Malika nada gashi sosai har mamakinshi nayi na kalleta "Dole kiƙi yin kitso da wuri gaskiya"
Tayi dariya kawai na ɗaura da Allah "Masha Allah kina da gashi "
Mama ta ce"oh Sumayyah anga gashi an ruɗe"
Malika ta ce"wallahi kuwa Mama kamar ita ɗin bata da shi"
Kukan A'isha yasa ni miƙewa naje na ɗaukota Mama ta ce"haɗo da zani ki goyata, yanzu tayi barcin goyata nayi ina jijjigata,har ta koma barcin,labarin Islamiyyar da Abbah yakai su Rumaisa na ke bawa Mama da cewa nan Malika ma takeyi,Mama da farin ciki take cewa "shikenan kin huta kin samu ƙawa ƙila ma a barki a jinsu"
Nace"Wallahi Mama nima naji daɗi sosai da naji haka"
Sallamar da muke ji kamar daga sama yasa jiki na daukar rawa kamar mazari Muryarsu Aunty Asma'u nake ji,da ko jiran amsa wa basu yi ba suka faɗo cikin gidan mama suka shiga nunawa su uku ne Aunty Asma'u,Aunty Mubaraka ,Aunty Maimuna, Mama da take kitso kanta na ƙasa dan bata ɗago ba ko da taji sallama nan suka shiga nunata suna cewa"Hajiya ce ta turo mu ta jaddada miki ta yafe miki ɗanta da haka kike so kika kuma shirya,shegiya 'yar gidan talakawa da duk wanda ya auri irinku cikin tsiya yake ƙarewa, kuma ku raba shi da 'yan uwanshi da iyayenshi kuma Yaya Hashim ya ce na shaida muku yana nan gobe zuwa garin,zai shigar da qarar tuhumar mijin naki hukuma ya fito masa da ɗansa kuma wani abu yasa mi Samir sai Sunje ko kotun ƙoli ce akan hakan,dan mun riga yanzu mun yafewa Abdullahi ke bare kuma yaranki suyi tunanin raɓarmu anyi gadon makirci da mugun abu masu ƙashin tsiya" Haka suka cigaba da ciwa Mama mutunci kamar su rufeta da duka kai jin shirun nata ma yayi yawa sai su kayo kanta Aunty Asma'u tayi kukan kura sai Mama taji saukar duka nan Mama ta zuciya ita ma suka fara faɗa ko kawa ganin haka suka rufarwa Mama mu kam baya mukayi ina kuka sai Malika ce ta fice waje ta kira maza aka fitar dasu daga gidan da kyar ranar kam naga bala'i na rasa mai muka tsarewa mutanan nan haka muna takanmu da abinda zamu ci sunce abar musu gida an bari amma har nan ma saida sukayi bincike aka musu kwatance,ba wadda nafi mamaki sai Aunty Asma'u kinada yadda zakiyi kina rigima da waɗanda kin fisu da ƙulla musu sharri basu ji ba basu gani ba,bamu tsare musu komai ba Malika mamaki ta shiga yi sosai na abunda ya faru da jin alaqar mu da su,nan aka cewa Mama za'a kaisu wajen hukuma ta ce "a qyale su kawai" dan mu kam ta mu ta ishe mu banji banda wainar fulawar nan zamu sake samun wani abu mu ci ina muka ga qarfi ko bakin rigima harda dambe ni saboda baqin ciki ban ko tanka ba,dan banida bakin magana ga goyon A'isha bayana kawai na barsu da ubangiji ya gaggauta saka mana banida bakin tsiya dan rigimar tasu duk sanka da faɗa to abun nasu yasha kan kowa,Malika harta tafi da mamaki da al'ajabi take kallan abun,duk da ba wai tasan wani labarin akanmu ba,iya abinda ta gani na yau kawai ta sani,koda Abbah ya dawo haƙuri ya shiga bawa Mama dan shima ya rasa yadda zai yi da abubuwan,yadda na hasaso ɗin ba abinci yau ma kwaki gari ,muka samu mukaci shima ba dan ƙoshi ba ba wai rigimar ce ba zamu iya ba dasu ƙarfin tane ba mu da shi mu ba wani abu garemu ba bare muce muna ci rigima kuwa ai sai ana da yadda za'ayi shiyasa ganin haka ma suke takamu abinda Abbah ya guje mana yasa ta kwashe mu kusa da shi to ga yadda Ubangiji ya tsara komai nan da tsammanin zuwan dame gobe zatazo garemu shin Abbah Hashim zaizo da gaske tuhumar Abbah ɗin ko a'a nakasa wani tunani ma bare ko na tuna wata mafita da zan samar mana na har zuwa wayewar gari.