SUN KASHE TA

CHAPTER 2 A SIYAR DA RAI A NEMO SUNA

by @hassanahunkuyi

🗡️🩸SUN KASHE TA🩸🗡️

©️HASSANA ABDULLAHI HUNKUYI

JAN HANKALIS

unayen mutane dana garuruwan da na yi amfani da su a wannan labari, ba na yi don wani ko wata bane ko kuma don cin zarafi da mutunci ba.

BABI NA BIYU

CID OFIS

ASP Janfalan zaune a ofis bisa kujera mai juyawa, a gabansa takardu ne birjik. Ya saka hannu ya dauki takardan da Dr. Aminu ya bashi na binciken da aka yi akan gawar matar, (wato doctor report). Ya yi shiru yana tuno bayanin Dr. Aminu a safiyar jiya bayan daya duba jikin gawar. ASP Janfalan ya faɗa a hankali, "Wane irin rashin imani ne haka? Waye ya yi ajalin wannan matar? Me ta yi da zafi aka yi mata kisan gilla irin haka?" Ya maida kallonsa bisa tarin tarkacen abubuwan da aka gani a jikinta, wato zobuna da ýankunne haɗi da sarƙan ƙafa da ýar hannci duk na zinare.

Ga kuma wani sarƙa da kwaɗo mai tawirar zuciya, duk cikin kayan ƙawar da aka samu a jikin gawar, sarƙar ce mai mugun arha. Haka kuma a cikin tarin zobuna akwai wani guda ɗaya mai arha wato azurfa ce, akwai ɗigon dutse mai ƙyalƙali a tsakiya. Sannan, a cikin ledar da suka tsinta a kusa da gawar, akwai zanin atampa a ciki wanda ya sha jini ya ƙoshi, da alama jinin mamaciyar ne aka goge da shi. Banda wadan nan tarkace babu abinda aka gani a tare da ita wanda zai bada kafar da za a gano makashin nata.

Ya saki ajiyar zuciya, yayinda tausayin matar ya kamashi, ya faɗa a ransa, 'Idan abinda likitan can ya faɗa mun gaskiya ne, to lallai wannan matar ta ɗanɗana kuɗarta kafin zuwan mala'ikan mutuwa gareta...' Ƙarar wayarsa ce ta katse masa wancan tunani. To amma kafin ya danna maɓallin amsa kira, wayar ta katse, duk da haka bai koma ga tunanin tsananin uƙubar da mamaciyar ta sha kafin mutuwarta ba, Sai ya miƙa hannu ya ɗauki ɗaya wayar ya danna wata numba haɗi da karawa a kunninsa, aka amsa daga can ɓangaren. "Hallo.” ASP Jafalan ya ce, "Waye ya ɗauki wayar?” Jin hakan ya sa wanda ya ɗauki wayar ya gano mai maganar, shi ya sa cikin ladabi ya ce, "Ado Adamu Gombe ne sir.”

ASP Janfalan yana da son barkwanci a lokacin da babu aiki, a mafi yawon lokuta kuma ya kan rikiɗe ya zama dodo a lokacin aikin ke nan. Kusan shekarunsa biyar yana jagorantar wannan (section) sashi. "Ina Mai Jama'a?" inji ASP Janfalan.

"Yana nan yallaɓai" Ado Adamu ya sake amsawa cike da girmamawa.

"Hadiza fa?”

"Ta je ta yi karin kumallo, yanzun zaka ga ta dawo."

"Yawwa, to ina son ganinku ku ukun, sannan ku taho da bayanin binciken da kuka yi akan fyaɗen da akai wa 'yar gidan mai gadi."

"Insha Allahu yallaɓai, zamu kasance a wurinka yanzun." Ado ya maida wayar ya aje a lokacin da Mai Jama'a ya shigo. "Hala ASP ne?” Inji Mai Jama'a.

"Eh, shine, ya ce yana son ganin mu a ofis yanzu." Ado ya amsa.

"Ƙila game da binciken makashin matar da aka tsinta shekaran jiya ne ko?” Mai Jama'a ya faɗi yana ƙoƙarin zama a kujerarsa, ya ci gaba da kallon Hadiza yana faɗin.

"Akwai jan aiki a gabanmu, kes ɗin matar nan murɗenɗen kes ne, za mu ci kwakwa kafin mu gano makashinta." Girgiza kai Hadiza ta yi haɗi da zama a kujerarta. Ado Adamu ya ce yana dubanta, "Ka da ki yi wahalar zama balle kiji daɗi ki kasa tashi, wannan uwar abinci da kika naɗa. In so samu ne ki kwanta ki nannagi barcinki."

Duk suka miƙe suna murmushi, yayinda Hadiza ta buɗe dirowa ta kwaso wasu takardu ta ce, "Ado, kamar ka shiga zuciyata, Wallahi banƙi inbi lafiyar gado ba, to yana iya? Talaka baiga ta zama ba balle kwanciya. Muje na kwashi abinda nake buƙata." Su ukun suka hau sama zuwa kiran ASP Kabiru Janfalan.

Duk kan su ukun police inspectors. Kuma matasa ne, ma su jini a jika, ƙwaranru ne, haziƙai masu aikin tuƙuru, aiki irin na asiyar da rai a nemo suna, aiki irin na bakin rai bakin fama. Ba zasu haura shekaru talatin ba kowanne su, Hadiza ce ƙaramar su, shekaruta ashirin da shida. Aduk lokacin da aka sami kisan gilla irin na matar da aka tsinta shekaran jiya, sune akan saka a gaba don zaƙulo mai laifin.

Sunje sun iske ASP Janfalan zaune bisa kujera yana bitar rahoton likita na binciken gawar matar da aka yi wa kisan gilla. Gaba ɗaya suka haɗa baki wajen gaida shi. "Yallaɓai barka da war haka."

"Barkanmu dai, ku zauna mana." Babu jinkiri suka yi yadda ya buƙace su, Ado Gombe da Mai Jama'a a kujera guda, yayinda Hadiza ta zauna a daura da su, amma duk suna fuskantar ASP Janfalan ne.

Bayan shiru na ɗan sakan, ASP Janfalan ya ce, "Kuna sane da kes ɗin matar da aka kawo shekaran jiya ko? To wannan karon sai kunyi da gasken-gaske kafin ku iya gano makashinta." Duk suka amsa haɗi da ƙura ma shi ido a yayinda ya ɗauko rahoton likita game da gawar, fuskarsa cike da tausayi ya ce, "Hmmm, haƙiƙa an azabtar da matar nan kafin a kasheta, a bayanin da likita ya yi mun sai na ji matar ta yi matuƙar bani tausayi. Bari in ɗan karanto maku rahoton kuji, wata ƙila sai kun zubar mata da hawaye." ASP Janfalan ya buɗe (Doctor report) bayanin likita, a kasalance ya soma karantawa.

"Wannan matar anyi mata horo mai tsananin, anyi mata mugun azaba ta hanyoyi da dama. Na farko an kulleta a ɗaki tsawon wani lokacin, bayan da aka yi mata wata gurɓatacciyar allura da sirinjin doki. Don an caccaka mata allura a kwiɓinta da tsakanin cinyoyinta. Ita wannnan allura da aka yi ma ta, tana cire duk wata gajiya ko raɗaɗin ciwo wanda daga ƙarshe kan saka mutum sumewa, daga nan jijiyoyi su saki sai mutuwa."

ASP Janfalan, ya kallesu yaga sun maida hankulansu kacokan gare shi, hakan ya sa ya ci gaba. "Sannan, a cikin jinin mamaciyar da aka gwada an gano guba ta dalilin (overdose) anfani da magani fiye da ƙima, wanda akayi mata da kayan maye, irin su koken. Sannan akwai alamar shaƙa a wuya wanda da wuya farar ɗaya a gani sai an lura sosai a wuyan mamaciyar.

Haka kuma binciken likita ya nuna, anyi amfani da mamaciyar fiye da kima, bama hakan ne abin tashin hankalinba, sai na yadda aka yi amfani da wani abu mai kama da ƙarfe ko wani abu mai ƙarfi a ka cusa mata a gabanta. Abin zai kai kusan inci biyu, mafari ke nan da jini ya ɓalle domin saida hanjinta ya tsunke...” Kukan da Hadiza ta saki ne ya sa ASP Janfalan ya dakata, su kansu mazan da aka sansu da dauriya saida suka share ƙwalla.

Bayan sun ɗan natsa, ASP Janfalan ya ci gaba. "Wannan matar za a iya cewa azaba biyu zuwa uku suka kaita kushewa. Allurar gubar jini da aka yi ma ta, sai tura ma ta ƙarfe a gaba da kuma shaƙetan da aka yi. Ko waye ya aikata wannnan ta'asar, da izinin Allah sai yaga ta kansa tun a duniya."

Ya fidda iskar da ta cika huhunsa, sannan ya tura masu tarkacen abubuwan da aka gani a jikinta. Hadiza ta saki nannauyar ajiyar zuciya, kafin ta yi magana Ado Gombe ya rigata. "Yallaɓai, banda waɗan nan tarkace babu wani abu da zai haska mana hanya?”

"Babu komai, sai dai zan iya ce maku, duk yadda aka yi mamaciyar ta fito daga gidan masu hannu da maiƙo ne, duba da gwalagwalan da aka samu a jikinta, sarƙan wuyarta da wani zoben azurfa ne kaɗai masu arha.” Hadiza, ta miƙa hannu ta ɗauki sarƙan tana kallon kwaɗon sarƙan, tana buɗewa ta miƙe da sauri tana faɗin, "Akwai ƙananun rubutu a cikin kwaɗon sarƙan nan. Imamu mai ɗankunni, Samaru, aka rubuta."

Ta miƙa wa ASP Janfalan, ya amsa haɗi da saka gilashinsa na ƙara ƙarfin gani, Ya maimaita sunan, "Imamu mai ýankunni, Zamaru." Da ya gama gani sai ya miƙa wa sauran mazan biyu kowa ya kashe ƙwarƙwatar ido. Mai Jama'a, ya ce, "Alhamdu lillah, kunga a ƙalla mun fara samun tudun dafawa, wannan kwaɗon sarƙan shi ne zai zame mana mabuɗin buɗe ƙofar binciken mu."

"Anya wannan ɗan sarƙa ya isa ya zame mana abin tinƙaho a binciken da zamuyi? To waima idan mun tashi zuwa binciken, wane samaru zamu nufa? Kunsan fa Allah ɗaya ne gari bambam.” inji Ado Gombe.

"Ni kuma sai na ji a jikina, Imamu ba shi ne ya yi ajalin matar nan ba, ina ganin da shi ne, ba zaiyi gigin barinta da shaidar da zaisa a yi saurin kamashi ba.” ASP Janfalan ya faɗi yana binsu da kallo. "Yallaɓai, da ma ba zamu dogara da ɗan wannan sarƙa ba, to amma dai ko babu komai ina kyautata zaton ta dalilin sarƙan zamu gano makashinta da ainahin dangi da sunan mamaciyar, ku tuna har yanzu fa ba musan wace ce gawar da muke fafatukan nemon wanda ya kasheta ba." Hadiza ta faɗi tana sake nazartar sarƙan.

Da ta sake juya bayan kwaɗon sarƙar, sai ta yi arangama da numban waya, cikin sauri ta janyo hankulansu gareta. "Ina zaton fa, kayanmu ya tsinke a jikin kaba, mu ɗauka mai laifin nan yana hannunmu kawai. Kun gani wawan harda saka numban wayarsa."

Duk suka natsu har ta gama karanto numban wayar, Kowa ya dauka sai ta ci gaba da faɗin, "Hasashena ya nuna mini zamu dace da yin arangama da mai laifin, abinda yakamata muyi shi ne. Kowanne daga cikin mu ya duƙufa kiran numban nan za a dace.”

ASP Janfalan ya nisa, "kuma fa kina da gaskiya Hadiza. Hasashenki akwai ƙamshin gaskiya, Allah ya baku sa'a da nasara." Duk suka miƙe suna addu’ar neman sa'a a wurin Allah.