SUN KASHE TA

CHAPTER 3 BAKIN RAI BAKIN FAMA

by @hassanahunkuyi

🗡️🩸 SUN KASHE TA🩸🗡️

©️ HASSANA ABDULLAHI HUNKUYI

JAN HANKALI

SUNAYEN MUTANE DA NA GARURUWAN DA NA YI AMFANI DASU A CIKIN WANNAN LITTAFIN, BA NA YI DON WANI KO WATA DON CIN ZARAFI DA CIN MUTUMCI BA NE.

BABI NA UKU

FAGEN BINCIKE

Su Hadiza, kusan kwana suka yi suna kiran numban wayar da suka gani jikin kwaɗon sarƙar gawar nan. Amma ko sau ɗaya bai shiga ba, a saboda haka sai suka yanke shawarar zuwa kamfanin sadarwar dake da alhakin samar da numban.

Da misalin ƙarfe goma na safe, motar su Hadiza ta yi fakin a katafaran kamfanin sadarwan nan na ƙasa dake garin kaduna. Bayan sun nuna katinansu dake alamta su ‘yansandan ciki ne wato CID. Sai suka gabatar da kawunan su haɗi da bayyana muradinsu.

Hannu bibiyu babban manaja ya karɓe su, sannan shi da kansa haɗi da mataimakinsa suka fara binciken babbar kumfutarsu. Sun ɗauki kusan awa biyu kana suka hattama. A inda babban manaja Sani Musa ya fara yi masu bayani.

"Eh lallai sunan mai wannan layi ke nan Imamu Dauda, yana zaune a Samarun zariya. Amma anan bincikenmu ya nuna mana layin ba shi a kan waya kuma sannan wurin da yake babu sabis don yau kusan kwana uku ke nan ba a yi amfani da layin ba."

Su Hadiza suka kalli juna, suka haɗa baki wajen faɗin, "Yawwa mun gode manaja. Zamu wuce Samaru yanzu, amma don Allah da zarar kun gano wani manaƙisa da ake aikatawa da wannan numba ku faɗa mana, haka kuma da zarar an kunna wayar a sanar mana, muma za muci gaba da gwada sa'armu."

A cikin mota, Mai Jama'a ya ce, “Yakamata idan Munje zariya, mu raba kanmu kasuwa, kasuwa, don ina kyautata zaton ƙila Imamu yana kai ýankunnaye kasuwanni ne."

Ado Gombe, ya ce. “Ni kuwa gani nake kamar mu ɗunguma zuwa ainahin kasuwar sabon garin zariya gaba ɗayanmu, sai mu yada zango a layin masu siyar da gwalagwalai. Haba ku tuna tsabar gwalagwalan da ke jikin gawar mana, babu mamaki Imamu, gwal yake siyarwa, ƙila a wajensa ta siya gwalagwalan da aka gani a jikinta, babu mamaki wannan sarƙar ya ba ta ne saboda cinikin da tayi masa."

Hadiza ta girgiza kai, "Na ji a jikina duk ma wanda ya bata sarƙan to sonta yake yi, kun manta rubutun da aka yi cikin hoton zuciya? an tsara ne cikin gwanancewa. Haka ita kanta kwaɗon sarƙan mai hoton zuciya ce."

Duk suka yi shiru, baka jin motsin komai saina ƙarar injin mota, zuwa can Mai Jama'a ya ce, "Idan muka je zariya zamu rabu kashi uku, ke Hadiza, kece zaki je babbar kasuwar sabon garin zariya. Ado kuma zai wuce kasuwar cikin zariya, ni kuma zan nufi Samaru kai tsaye. Saboda haka zamu haɗu a zariya motel mu ci abinci mu huta sai mu baje kolin binciken da kowa ya yi, mugani ko akwai nasara." Duk suka yi amanna da wannan tsari.

Washegari suka fatsama fagen fama, kowa ya kama gabansa. Misalin ƙarfe uku da kwata suka hallara a jikin wata bishiya na zariya motel. Bayan sun ci abin ke nan. Ado Gombe ne ya fara magana. "Har na gama bilayina babu wani wanda ya san Imamu mai ýankunne, da naga wankin hula zai kaini dare, sai na dunga bin layi layin da ake siyar da kayan ƙyale ƙyale na mata amma Allah baisa na dace ba."

Mai Jama'a ya yi gyaran murya, "Ni kuwa da farko harna fara murna karena ya kama kura. Don ina shiga kasuwar na tambayi wani yaro ko yasan wani mutum wanda ake kira Imamu mai ýankunni samaru? Yaron ya ce ya sanshi bari ma ya rakani, na bishi tinkis tinkis sai wajen wani tsoho mai kayan koli, babu abinda baya siyarwa na kayan kwalliyar mutanen karkara, sannan waje guda ga citta, kanunfari; masoro; kinba; kirfa; citta mai ƙoƙo; kanwa; jar kanwa; da dai sauransu. Muna zuwa sai yaron ya ce ga liman ɗin, nayi sansarakwai, da ya ce ga liman ɗin, ni da na ce Imamu shi ne zai kawo ni wajen ɗan tsoho liman?"

Duk suka tuntsure da dariya. Hadiza ta ce, "To ina marabar danbe da faɗa? Imamu da liman duk ɗaya ne. To ya kuka ƙare da liman? Fatan ka siyo mana tsarabar gautan ɗaci da sabulun salo na sha don banji ka ambace su ba." ta ƙarishe tana dariya. Sa'annan ta ci gaba da faɗin.

"A nawa bangaren binciken akwai ɓurɓushin nasara da ga tsakiyan bincikena, amma kamar kowa ne na sha wuya don saida na karaɗe kasuwar sabon gari da wajen masu siyar da gwalagwalai banga wanda ya ce ya taɓa jin mai suna Imamu ba.

Awajen wani mai akwakun siyar da ribon da fashon ɗin ýankunni haƙarmu ya kusa cimma ruwa, yadda muka yi kuwa shi ne, a kusa da shagon ma gwal, wani mai akwakun ya ce, "Sai na ji kamar kina tambayar Imamu mai ýankunni ko?" to sai naga ya ƙura mun ido yana mun kamar kallon sani, da naga haka na iso gaban akwakun na taɓa wani tuntun ɗin abu da mata ke sakawa akansu wato acuci maza, na ce nawa?"

Bai bani amsa ba ya zarce da faɗin,"Idan Imamu kike nema to yana ƙarshe layi kusa da babban titi.” Na yi saurin faɗin, "Idan babu damuwa ka zo ka rakani sai in baka wani abu."

Da muka je sai aka faɗa mana yau kwanan Imamu biyar rabonsa da fitowa kasuwa, jin hakan sai wani a wurin ya ce, “Ina zaton Imamu yana zuwa kasuwannin ƙauye kai kaya ne, don yafi yin ciniki acan saboda fashon ɗin ýankunni da sarƙa da yake yi.”

Anan naga wata yarinya ta zo ta amshi sallahun sarƙa da ýan kunnin daya haɗa mata. Dana amsa na duba sai naga ýan kunni da sarƙan duk da hotunan yarinyan a ciki, hatta ɗan abin hannun saida aka maƙala mata hotonta.

Hakan da na gani ya bani tabbacin lallai Imamun da muke nema ne. Na dubi abokan sana'ar nasa na ce, "Ko akwai mai lambarsa?" Wani a wurin ya ce, "Duk lambobinsa basa shiga, yana kyautata zaton yaje kauyen da babu sabis ne.” Na ce, "To abani numban in gwada." Dana kira yaƙi shiga saina ɓata rai kamar zan fashe da kuka.

Wanda ya rakoni da naji suna kira lauwali ya ce, "Ince ko lafiya Hajiya?"

“Ai kuwa babu lafiya, gobe bikin ƙanwata ga kayanmu da muka bashi aiki a wurinsa, ko akwai wanda ya san garinsu?"

Korau ne ya ce ya sani, shi ne kuma ya kwatanta mini kauyen su Imamu.... Saboda haka, yanzu sai mu ɗauki hanya domin da zafi-zafi akan bugi ƙarfe don na hango ɗayan biyun..." Ado Gombe, ya nisa. "Sannu da aiki mace mai kamar maza." Ta ƙarishe da faɗin, "Amma fa babu kwari, don ban iya riƙewa ba."

"Kunga bahaushe ya ce da safe ake kama fara, mu bari sai gobe mu daka sammako kafin ya fita, daga nan zuwa bomo baifi tafiyan yan mintina ba, Don haka sai kowa yaje ya kwanta ya huta ayi bitar abinda zamuyi a goben." inji Mai Jama'a.