CHAPTER 4 SAURA ƘIRIS
🗡️🩸SUN KASHE TA🩸🗡️
©️HASSANA ABDULLAHI HUNKUYI
JAN HANKALI
Sunayen mutane dana garuruwan da na yi amfani da su a cikin wannan labarin, ba na yi don cin zarafi ko kuma don cin mutuncin wani ko wata ba ne.
BABI NA HUƊU
GARIN BOMO
Misalin ƙarfe bakwai dai-dai motar su Mai Jama'a ta yi fakin a wata makarantar firamare dake garin Bomo. Anan suka tambayi wasu yara 'yan makaranta, gidan su Imamau mai ɗan kunni. Sun taki babbar sa'a, domin yaron da suka fara tambaya ɗan kusa da gidan ne, don haka shi ne ya yi masu jagora.
A hanya suka tsaya yin shawara, sun yanke Hadiza ce zata isa gidansu Imamu. Mai Jama'a da Ado Adamu zasu tsaya nesa da gidan, sunyi haka ne saboda wasu dalilai nasu. Don haka yaron yana nuna wa Hadiza gidan, sai ta ciro ƙaton sunƙin biskit ta ba shi haɗi da sallamarsa.
A ƙofar gidan akwai wata dattijuwa tana tuyan ƙosai, waje guda kuma robar koko ne da kunun siyarwa. Hadiza ta yi sallama mai ƙosai ta amsa. Bayan gaisuwa ya ƙare, Hadiza ta zarce da faɗin. "Iya, don Allah nan ne gidan su Imamu mai ɗan kunni?"
"Eh, nan ne yarinya. Ince dai lafiya?"
"Lafiya lau. Da ma zuwa nayi in ba shi aikin yin ɗan kunni da sarƙa na biki." Iya ta washe baki. "Hmm Imamu mai haja, mai yan mata, ai na zaci ko kece kishiyar ta wa da ake koɗawa."
"A'a, bani bace, kwatancensa aka yi mana, shi ne muka yo takanas daga kaduna don ba shi aiki."
"Ah! Da sassafen nan haka? Shiga cikin gida kisha koko da ƙosai kafin ya fito wanka."
"A'a bari dai in tsaya anan, ai ba daɗewa zanyi ba." Ta saka hannu ta ɗauki ƙosai ɗaya tana ci. Hakan ya burge mai koko da ƙosai don haka ta miƙe tana faɗin.
"Bari inje in wartakosa haka nan, Domin indai Imamu ne sai ya kai awanni a bayi yana tirzan jiki kamar macen da ke son canza fatar jikinta, na ga dai ba wani kyau ya fini ba."
Hadiza ta yi dariya, ta dai gano Iya mai ƙosai kakar Imamu ce, shi ya sa ta waiga, ta hango abokan aikinta suna ɗan ta ba hira da mutanen wani dandalin siyar da abin Karin kumallo, ta tura ma su tes ɗin akwai nasara, Imamun yana nan bai fita ba. Cikin haka, Iya ta fito tana sababi, "Ki yi haƙuri ‘yannan, ni ban taɓa ganin namiji da son ƙyaleƙyale kamar mace ba, sai Imamu..."
Fitowar Imamu ne ya sa Iya ta yi shiru, sai hakan ya ba shi damar faɗin. "Ka da a cinye ni ɗanye, gani na fito Umma..." Ya maida kallonsa ga Hadiza ya ce, "Barka da zuwa, Ina kwana, ke ce kika kawo aikin biki?"
"Lafiya lau, kai ne Imamu mai ýan kunni?"
Eh, ni ne."
"To bismillah."Suka ɗan keɓe nesa da mai ƙosai.
Bayan sun sabunta gaisuwa, Hadiza ta ce tana kallon Umma, "Hala Umma, kakarka ce?”
"Kakata ce ta wajen uwa, nan ina dangin uwa ne, dangin babana suna Huntuwa."
"Masha Allah, ya kasuwa?"
"Alhamdulillah."
"Yawwa, don Allah haɗin kai da neman taimako na zo nema a gareka, Imamu."
Imamu ya yi shiru yana sauraronta, ita kuma tana kallonsa ta saka hannu cikin jaka ta ɗauko sarƙar da aka gani a jikin mamaciyar nan ta ɗaga sama dai-dai fuskarsa ta ce. "Zaka iya tuna wacce ka ba wannan sarƙar?" Hadiza ta faɗi tana naƙaltan fuskansa. fuskan Imamu ta nuna kadaran kadaham. Har da ɗan guntun murmushi ya ke faɗin. "Sarƙa ta ce ai, wacce na ba Surayya."
"Haka ne, to amma yaushe ne ka ba ta? Zai kai kamar tsawon wane lokaci?" Imamu ya ɗaga kai sama alamar tunanin ranar da ya ba Surayya kyautar sarƙan, zuwa can ya ce. "Yau zai kai kamar sati biyu, na dai manta takamaiman ranar, amma tabbas zai kai sati biyu. Surayya ce ma ta fara bani sarƙanta, ni ma sai na ba ta nawa har na rubuta numban wayata a baya, a ciki kuma sunana na rubuta."
"To, amma me yasa ka rubuta sunanka da numban wayarka?”
"Na yi haka ne don kawai taƙi karba, don ta matsa mini sai na bata wani abu wanda zaisa ta dunga tunawa dani saboda za ta yi tafiya."
"Surayyan, budurwarka ce?"
"kusan haka."
"Kamar ya ya, kusan haka?”
"Ita ce ke sona."
"Kai baka sonta?"
"Gaskiya tafi ƙarfina. Wai ma Hajiya me ya kawo waɗan nan tambayoyin ne irin na ya ya aka haifeni? Fatan dai lafiya?"
"Lafiya sumul, amma yaushe ne ganinka da Surayya na ƙarshe?"
"A ranar da muka yi canjin sarƙoki, ta ce mun suna da wani sha'ani, bata son zuwa amma antinta Hajiya Tani ta matsa saita je, don zata bata zinarensu ta kai a siyar daga nan saita canzo masu wasu, amma ita ta fi son zuwa inda za ta yi leƙen asiri don ta hango akwai nasara."
Hadiza ta ɗan yi Shiru kafin ta ce. "To don Allah ina son ka faɗa mun komai na abinda ka sani game da Surayya." Fuskan Imamu a ɗaure yake faɗin, "Ban san wani abu mai tsawo game da Surayya Mustafa ba. Amma zan iya cewa, Tare muka yi NCE da ita a FCE zariya. Za kiyi mamaki idan na faɗa maki a wancan lokacin Surayya Mustafa ba ta da ƙawaye sai maza, hakan ya sa a duk lokacin da muka haɗu take matuƙar bani haushi, tun a lokacin ta faɗa mun baki da baki tana so na, nace bana son mace mai huɗɗa da maza, hakan ya sa muka yi faɗa sosai. Har muka gama karatunmu ba ma magana.
To, amma bayan shekara uku, sai muka sake gamuwa a ABU Samaru zaria, taje wajen ƙawarta haɗi da ba ƙawar saƙo, ni kuma naje da hajata ta siyarwa. Wato ýan kunni fashion da su Sarƙoƙi.
Muka ɗanyi hira sama-sama, inda take faɗa min wata Hajiya ce daga kaduna ta aiko ta da kayan ɗa'a, ta kawo ma wasu matan. Har a lokacin ta ke faɗa mini zata yi fito na fito da Hajiyar..."
"Me ye sunan Hajiyar?" Hadiza ta katse shi. "Imamu ya ce, "Gaskiya a lokacin ban tambayeta ba, amma bayan mun ɗan shaƙu da juna, tana kira na a waya muyi hira. ran nan na tambaye ta sunan Hajiyar da ta ke son ta yi fito na fito da ita.
Surayya, ta yi dariya ta ce "Abin sirri ne, amma na yi maka alƙawari zan faɗa maka idan na hattama bincikena." To, amma abinda ya ɗaure mun kai da Surayya Mustafa shi ne, yadda naga tana facaka da kuɗi, ta ce mun Hajiyar ce ke mata ɓarin kuɗi, tun daga nan, na fara baya-baya da ita musamman da na tambayi ainahin garinsu da tarihinta ta ce, "Abin sirri ne."
Yanzu na yanke hukuncin duk ranar da ta dawo daga tafiyar da ta ce zata yi, to zance mu rabu, idan ba zata faɗa mun ko ita wace ce ba. Don a ranar da za tayi tafiyar, ta ce inyi mata addu’a ko bayan sun gama biki, zata yi tafiyar da, kota dawo ko ba ta dawo ba don bakin rai bakin fama ne..."
"Yanzu kana nufin har kuka rabu ba ka san alƙiblan Surayya Mustafa ba? Ba ta faɗa maka garinsu da inda take zaune ba?"
"Ba ta faɗa mun komai daya danganceta ba, amma dai a kaduna ta ce mun tana zaune, a wani gidan haya da ake kira gidan 'yan makaranta."
"To, Imamu, saidai kayi haƙuri kaci gaba da yiwa Surayya Mustafa addu'a domin ta amsa kiran mahaliccinta."
"Inna lillahi wa Inna ilaihi rajuun, mai kika ce? Hatsari ta yi a tafiyar? Ya salam, Wayyyo Allah." Ya ɗora hannu akai yana girgizawa. Hadiza ta fiddo da hotunan gawar Surayya ta nuna masa, yana kallo ya kauda kai yana fidda hawaye."Waya kasheta? Kun kama makashin nata?”
"Shi muke nema yanzu, Saboda haka zan baka lokaci ka je ka zurfafa tunani ko kila a cikin hirarrakin da ku ka taɓa yi ta taɓa ambato sunan wani ko wata da suke takun saƙa. Ka tuno ko ta taɓa suɓul da baka ta faɗa maka danginta ko garinsu. Ga numbata, idan ka tuno wani baƙon al'amari saika doka mun waya, haka kuma idan muna son wani ƙarin bayani zan tuntuɓe ka." Hawaye yana bin kwarmin idonsa ya ke faɗin, "Insha Allahu, zan sanar daku." Hadiza ta yi sallama da su ta kama gabanta cike da al'ajabin wannan lamari.
A mota ta zayyane wa su Mai Jama'a duk yadda ya wakana."Yanzu me kuka hango game da wannan murɗenɗen lamari?" Ado Gombe ya numfasa, "Ni na hango nasara, tunda muka sami damar sanin sunar mamaciyar, wanda ada kuwa bamu isa mu kirata da kowane suna ba sai mamaciya ko gawa. Narasa ta biyu kuma da muka samu shi ne, sanin sunan gidan da ta zauna. Ina ji a jikina haƙarmu zata cimma ruwa idan munje."
Mai Jama'a, ya ce. "To Amma dole ne mu saka ido sosai akan duk wani motsi na Imamu, don ya zama abin zargi, bamu sa ni ba labarin gaskiya ya bamu ko ya ɓoye wani muhimmun batu." Hadiza ta numfasa haɗi da kallon rubutun da ta yi ta ce, "Wai wace ce wannan Surayya Mustafa? Ina ji a jikina kamar... Allah dai ya jiƙanta. Yanzu dole zamu rabu gida biyu, wani zaije FCE Zariya ya binciko mana ainahin wace ce Surayya Mustafa da irin dangantakarta da jama'a, sannan a cikin jerin sunayen ɗaliban da aka ɗauka a shekarar 2013. Ba za a rasa ganin ƙila ko adireshinta ba. Ni zanje gidan 'yan makaranta inyi binciken a can, saboda haka waye zaije FCE? Waye zai saka ido akan Imamu?” TA ƊIGA ALAMAR TAMBAYA A GIDAN YAN MAKARANTA.❓❓❓