CHAPTER 6 MANYAN MATA, YAN ƘWALISA
🗡️🩸SUN KASHE TA🩸🗡️
©️HASSANA ABDULLAHI HUNKUYI
JAN HANKALI
Sunayen mutane dana garuruwan da na yi amfani da su a cikin wannan labarin, ba na yi amfani da su don cin zarafi ko cin mutuncin wani ko wata bane.
BABI NA SHIDA
KASU, KADUNA
Izzatu, ta fito daga ɗakin ɗaukan lacca a kasalance, amma dukda ɗinbin gajiya da yunwar data kawo ma ta hari, bai hana keɓe kanta a wani saƙo don ta gyara fuskanta da mai ya tsatstsafo ba.
Ta buɗe jakarta ta fiddo da jan baki ruwan hoda ta shafa a laɓɓanta, sannan tabi fuskanta da tsadaddiyar hoda haɗi dasu hodar ido wato eyeshadow. Da ta hattama ta manna abin hanci, ta ɗaura sarƙan ƙafa haɗi da maƙala zoben ƙafa, sannan tabi jikinta da kallo. Hakan bai gamsar da ita ba sai da ta ƙura wa fuskanta ido a ɗan ƙaramin madubin kayan kwalliyar, ta ga ta yi zan-zan. Ko wacce ta fito wanka yanzu ba zata gwada mata ƙyallin fuska ba. tana murmushi tana fesa turare, duk wanda ya wuce sai ya waigo ya sake shaƙar ƙamshin turaren.
Sannan ta tako a hankali zuwa kafteriya, inda zataci snacks da ɗan juice, amma koda ta iso sai tayi turus saboda rashin ganin motar ƙawarta Ramla, haka nan ta zauna a gajiye tana yan tunane-tunane har zuwa lokacin da ta tambayi kanta.
'Wai don me nake yin karatun nan? Don me mutane ke karatun boko? Don suyi aiki? Ko kuwa don kawai a kira su yan boko? Kai ni fa na gaji da karatun nan, bacin bana son zaman gidan aure ba, dana cika burin baba nayi aurena kamar yadda yake muradi... "
Wata 'yar ajinsu, Tally ce ta yanke mata taɗin zuccin da takeyi da faɗin. "A'a, kaga 'yan matan gaya, masu kyau da tsada, meye sirrin ne? Dube ki kamar ba daga ɗaukan lacca kika fito ba? Sai kace yanzu kika tsalo wanka? Wa kike jira ne haka?"
Kamar Izzatu ta shareta, don wani lokaci Tally ta faye shiga shirgin da ba nata ba, da son jin yadda aka haifi mutum, ba da ita za ka kasa abu ba, amma kafin ka farga ta kwashe.
Izzatu ta kauda kai wani wajen dabam ta ce. "Barzahu zani, shi ya sa kika ga na ci ado haka," Tally ta tuntsure da dariya maimakon ta ji haushi ta ce, "Aje lafiya, ni kam ban shirya zuwa barzahu yanzu ba, ko kema nasan da walaki goro cikin miya, kibi a sannu 'yan mata."
Ta wuce tana mata wani irin mugun dariya. Izzatu ta maida hankalinta wajen wayarta dake ƙara, data duba sai taga sunan Ramla, kafin ta amsa ta ji tsayawar mota a kusa da ita. Babu bata lokaci ta miƙe fuska a ɗaure ta isa ga Ramla dake zaune a mazaunin direba.
Babu bata lokaci Ramla ta cillar motar bisa titi cikin gwanancewa sannan ta kalli Izzatu dake shan mur ta ce. "Waya taɓo mini ƙawallina?"
"Wallahi karatun nan yana bani kashi, wai shin Ramla, don me ake karatun boko ne? Ina nufin bayan mutum ya gama piramare da sakandare? Me yasa ake son ci gaba da karutun? Allah karatun nan ya isheni na dole nake yinsa, domin da shi na fake ina sha’anina."
Ramla ta ni sa, “Akwai dalilai masu yawa da kansa mutum faɗaɗa ilminsa, kinga kamar ni zan iya cewa na faɗaɗa karatu nane ba don inyi aiki ko neman kuɗi ba, sai don ace ni mai ilmi ce, in kuma fita daga sahun jahilai, kin San kuwa wani mawaƙin hausa ya ce, "Duk wanda ba shi da ilmi, da shi da jaki basu da maraba." To amma ke me yasa kika damu kanki da son sanin dalilin da ya sa mutane ke faɗaɗa ilminsu na boko?" Izzatu ta nisa, "Haka kawai tambayar ta addabi zuciyata." Ramla ta yi tsaki, ta kauda wannan batun ta sako wani, "Wai ya batun Surayya ne? Ta dawo kuwa?"
"Wallahi har yanzu, ga shi yau kusan sati biyu ke nan, ni kaina abin ya dame ni, fatan ba wani babban matsalar ce ta auku da ita ba"
"To kin tambayi Hajiyar gidan ko tasan inda taje?"
"Hajiya, ba ta san komai na Surayya ba."
"Mai gadi fa, kin tambayeshi ko ta faɗa masa inda taje?"
"Ke matar nan fa zurfin ciki gareta, kinga dai ɗakinmu ɗaya da ita amma wallahi ba zan ƙarar da komai nata ba, ke ko waya takeyi ƙaryarki kiji me take cewa balle kisan da wa take magana, babban abin ɗaure kai, ban taɓa ganin wani ko wata sunzo wajenta ba."
Ramla ta gyaɗa kai, "Allah ɗaya gari bambam, to yanzu ke da zaki bini ya ya zaki yi da kayanta da ke ɗakinku? Kada ki bar mata kayan daga baya a sace mata wani abu azo ana kuka dake."
Izzatu, ta ce a lokacin da motar ta yi fakin a katafaren wani babbar ƙofa, “Da ma abinda na tsayar shi ne, idan kin amince zan tafi da kayanta zuwa gidanki sai inbar numbata ko adireshin inda zata sameni ta amshi kayan idan ta dawo, tunda komai nata mai tsada ne, gaba ɗaya suturunta babu mai arha."
Ta ke Ramla ta ba ta goyon bayan tahowa da kayan Surayya, don so take taga ita ko wannan Surayyar wace irin mace ce mai girman kai haka? Ita wace ce da bata huɗɗa ko magana da kowa? Ita wace ce da ba a san alƙiblarta ba?
Cikin ƙanƙanin lokaci Izzatu ta haɗa kayanta dana Surayya suka sakko ƙasa wajen mai gadi. Mai gadi yana ganinta ya miƙe yana faɗin, "Da ma Hajiya ta faɗa mini yau ne zaki tashi, fatan dai ba wani matsala kuka samu da ɗaya daga cikin mutanen gidan ba? Ko ita Hajiyar?"
"A'a, babu wata matsala, sai dai Hajiyar ce taƙi yarda in bar kayan Saurayya a ɗakin, wai saidai in tafi dashi tunda ɗakinmu ɗaya, ita bata san komai nata ba, yanzu ga takarda nan, na rubuta adireshi na a ciki, duk ranar da Surayya ta dawo ka bata zata ga inda zata sameni.”
Baba mai gadi ya amshi wasiƙa yana faɗin, "Ni ma fa wallahi ko kasheni za a yi bazan iya fasalta kamannin Surayya ba, ban taɓa ganin mace irin haka ba, Sai fa ta shigo gidan nan amma ta tafasa a sauke ba zata ce mini ba, koda yake sai nake ganin kamar a buge take shigowa..."
Hon ɗin motar Ramla ne, ya sa Izzatu ta katse Baba mai gadi, ta kawo kyautar kuɗi ta bashi kana ta fita da sauri shi kuma yana ɗauke mata da wasu kayan yana godiya har wajen mota.
ZAN CI GABA IN SHAA ALLAHU
***