CHAPTER 7 IDAN BAKA IYA KAMA ƁARAWO BA....
🗡️🩸SUN KASHE TA 🩸🗡️
©️ HASSANA ABDULLAHI HUNKUYI
JAN HANKALI
Sunayen mutane dana garuruwan da na yi amfani da su a cikin wannan labarin, ba na yi amfani da su don cin zarafi ko kuma don cin mutuncin wani ko wata bane.
BABI NA BAKWAI
GIDAN RAMLA
Tunda Ramla ta samu sa'ar gayyato Izzatu gidanta, ta tura ƙanninta hutun dole, shi kuwa malamin da yake koya masu karatu, ta gama wassafa abinda za ta yi masa wanda ba zai ƙara marmarin zuwa koyar dasu ba. Bayan sallar la'asar, mai gadi ya yi sallama da Ramla yana mata albishir ɗin zuwan malam Muttaƙa. Ta ce, "Ka je ka faɗa masa yaran sun tafi hutu, kuma ni bana jin daɗi ya je sai na neme shi."
Bayan minti ɗaya, mai gadin ya sake dawowa ya ce, "Malam Muttaƙa, ya ce ki leƙo saƙo zai baki." Ranta ya ɓaci, a fusace ta ce, "Ka je ka ce ya baka saƙon ka kawo mini, ko kuma jeka kawai, bari inje in amsa." Mai gadi yana bada baya, Ramla ta saka wasu shegun kaya, fanɗarinka tsirara, sai ta ɗora ƙaton hijabi a sama ta doshi farfajiyar da suke ɗaukan karatu. A zaune bisa kujera ta iske Malam Muttaƙa, hannunsa riƙe da wata doguwar takarda, kansa a duƙe. Sai da Ramla ta ƙare masa kallo kana ta yamutsa fuska ta ce.
"Ga ni Malam, an ce zaka bani saƙo? Ina saƙon yake?" Bai dago kai ya dubeta ba, ya miƙa mata takardan dake hannunsa ya ce, "Ga wannan ki karanta a tsanake, amma kada ki bar Alhaji ya gani…” A gadarance ta ce, "Ai ba sai na karanta ba, zaka iya karantawa, babu Kowa daga ni sai kai, don haka ina jinka." Ta sami wuri ta zauna tana hura hanci karenta ya kama zaki.
Malam Muttaƙa ya ce, "Nasiha ne da ma na taho in baki a rubuce don zaifi zama a ranki fiye da in karanta maki, amma tunda haka kika zaɓa shi ke nan." Ya warware takardan ya fara karantawa. "Hajiya Ramla, Allah yana sonki da rahma tunda ya rufa maki asiri, ina jin ni kaɗai ne a gidan nan na fahinci halin da kike ciki, na halaka, ki tuba ki koma ga Allah tun kafin asirinki ya tonu a wajen mai gidanki, tun kafin fushin Allah ya sauka a kanki. Domin, MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE, "MAFI GIRMAN ABUNDA NA KE JIN TSORON A KAN AL'UMMATA SHI NE, AIKIN MUTANEN ANNABI LUD."
Mene ne aikin mutanen Annabi LUD? Shi ne luwaɗi da maɗigo. Allah ya tsaremu, Hajiya Ramla, a wani hadisin, so uku a jere manzon Allah yana tsine wa wanda ya ke aikata irin aikin mutanen Annabi LUD. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "ALLAH YA TSINE WA WANDA YA KE AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD, ALLAH YA TSINE WA WANDA YA KE AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD, ALLAH YA TSINE WA WANDA YA KE AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD."
Malam Muttaƙa ya tsagaita haɗi da kallonta, sai yaga tana harararsa, alamun nasihar ba ta samu matsuguni a zuciyarta ba, hakan bai dakusar masa da ƙuduri da kyakykyawar niyyarsa ba. Ya ci gaba da faɗin, "Bari ki ji kaɗan daga cikin illar yin maɗigo. Maɗigo yana ɗaya daga cikin manyan laifukan da Ubangiji ya kyamata, shi yasa duk mai yi zai haɗu da fushin Allah haɗi da waɗan nan illolin.
1. A kan iya daukar cutukan zamani ta hanyar madigo.
2. Yin madigo yana raunata imanin mace.
3. Yana gusar da kunya gaba ɗaya.
4. Fushin Allah yana sauka ga masu wannan aikin.
5. Gushewar mutunci a idon mutanen kirki.
6. Masu yin wannan aiki sukan samu kansu a cikin kuncin rayuwa.
7. Rashin yin kyakkyawan karshe ga masu aikata maɗigo.
8. Rashin sha'awar Aure.
9. Za a kai lokacin mace ba ta sha'awar...”
Tsakin da Ramla ta yi ne ya sa ya dakata da karatun, ya cika da mamaki, sai kawai ya nannaɗe takardun ya mayar cikin aljihu sannan ya ɗan kalleta haɗi da ci gaba da magana, “Hajiya Ramla, kefa uwa ce, ba zaki ji daɗi a dunga aikata baɗala da ýaýanki ko kanninki, ko kuma dai wani naki ba, to balle ace da kanki ne kike aikata alfasha irin haka, kufa mata, ku ne iyayen al’uma, ku ne katangar al’uma, tsakani da Allah idan mijinki ne kika kama yana neman jinsi irin nashi ya za ki ji? Wane irin nasiha za ki yi masa? To don Allah kiyi wa kanki faɗa kada ki sake balle ki kuskure har Alhaji ya gano halin da kike ciki.”
Ya dauko wayarsa daga cikin aljihu, ƙirar Tecno pop 2 plus ya nuna mata ya ce, “Kinga wannan abar, to shaiɗaniya ce ta ƙarshe, kiyi takatsantsan da ita, ba saboda komai yasa na ce haka ba, sai lura da nayi ta shagaltar dake da yawa, ina lura a duk lokacin da muke yin karatu, bakya maida hankali ga karatun sai daddana waya, na taba yi maki magana kika ce karatun da nake yi ne kike naɗa.”
Ya numfasa haɗi da daga murya kamar mai yi mata faɗa ya ce, “A yau, an wayi gari duniyar kimiya da fasaha musamman duniyar yanar gizo (internet), na ɗaya daga cikin hanyoyin da ke koyar da alfasha da baɗala, da duk wasu munanan dabiun da kika sani da ma wanda baki sani ba, musamman a social media. Na taba kama wata dalibata tana zuwa islamiyya da katuwar waya, dana duba wayar sai da na zuba hawaye…”
"ƙurungus! Ka gama yi mini fadan ubana? Ko da yake zaka iya sati kana magama baka gaji ba, to ni na gaji, haƙurina ya ƙare, a dunkule idan na fahince ka Malam Muttaƙa, kana so ka ce ni shaiɗaniya ce? Kallon mare kunya kake mun? So kake ka ce ni 'yar maɗigo ce? Murna kake yi da shiga ta fushin Allah, so kake Allah ya tsine mun? Don Allah idan ka isa, kasa Mijina Aƙilu Maude ya sake ni yau, kai, albishirinka, ka san ƙawayen huɗɗan nawa? Daga matarka sai uwarka, kai mece ce a hannunka in ba babbar waya ba? Me kake yi da ita…”
"Inna lillahi wa Inna ilaihi rajuun." Malam Muttaƙa ya faɗi haɗi da miƙewa a kiɗime, ya kamo hanyar fita amma sai Ramla ta sha gabasa, ta cire hijabinta ta cukuikuiye Malam da shi kana ta fasa kuka haɗi da kiran mai gadi.
Mai gadi, ya shigo a sukwane, ya riski lokacin da Ramla ke faɗin, "A she kai ba malamin kirki bane Malam Muttaƙa? Ashe da wata mummunar manufa a tare da kai...” mai gadi ya kawo mata agaji, da ƙyar ya warware cukuikuiyewar da ta yi wa Malam Muttaƙa, Mai gadi baiyi wata wata ba ya zafga masa Mari. Kafin Malam Muttaƙa ya yi yunkurin yin wani abu, tuni Mai gadi ya fitar dashi waje, ya dawo ya iske Ramla tana ta kuka, tana ganinsa ta ce.
"Ka kira Aƙilu ka faɗa masa abinda Malam Muttaƙa ya so aikata mun don yaga yara basa nan." mai gadi ya yi shiru yana nazarin abinda zai faɗi idan ya Kira numban Alhaji Aƙilu, ganin ya yi shiru ya sa Ramla ta ba shi kuɗin da ta shirya don irin wannan lalurar ta ce, "ungo ka saka kati ka kira Aƙilu, ni ba zan iya tarar tsabar idon mijina in faɗa masa Malam Muttaƙa ya so keta min haddi ba."
Kamar dole Mai gadi ya aikata abinda aka ummurce shi, ko da yake, abinda ya gani, shi ne ya faɗa wa Aƙilu, wato ya ga Ramla da Malam Muttaƙa cukuikuiye a hijabi suna faɗa, shi bai ma lura da yanayin shigar da Ramla ta yi ba.
Washegari, Aƙilu Maude ya dira a kaduna, koda ya shigo gidan, abinda mai gadi ya faɗa masa da farko, yanzun ma abinda ya sake maimaitawa ke nan. Amma da yake Ramla shaiɗaniya ce, hatsabibiya ce, Aƙilu yana shiga ya cidda ita tana kuka, ganinsa yasa ta zo ta rumface shi tana faɗin, "Malam Muttaƙa, ba Malami bane, shiga rigar malamai kawai yake yi yana ci da addini, babban abinda yafi baƙanta mini rai shi ne, kamani ya yi zai yi... "
Munafukar, wai ita nauyi da kunya ya hanata ƙarasawa, ran Aƙilu ya yi mugun ɓaci. A wannan rana Malam Muttaƙa a caji ofis ya kwana, ya sha wuya kafin a sake shi, wannan shi ne ƙarshen zuwansa gidan Alhaji Aƙilu koyar da iyalansa, da ma haka Ramla ke so, yanzu za ta more rayuwata da Izzatu idan ta zo.
Ranar da Aƙilu ya koma da daddare misalin ƙarfi goma na dare Ramla ta dawo daga gidan ƙawarta kusan a buge, ta dauki jakarta da waya ta kulle ko ina na motar, sannan ta isa bakin kofar ɗakinta bata ma kula da sannu da zuwan da mai gadi ke mata ba. Ta na bude kofa, NEPA ta yi halinta, a da idai lokacin ne ta ji ƙamshin turare ya daki hancinta, ta shiga ɗaki da sauri ta rufe kofa garam!
Ta Fara lalube a cikin duhu har Allah ya ba ta damar kunna tocilar wayarta, duk da haka hasken bai wadatar da falon ba balle ya gamsar da ita. ƙirjinta ya buga da ta ga mutum zaune a kujera, fuskarsa sanye da baƙin kyalle, hannunsa rike da sharbebiyar wuƙa.
Ta yi jarumtar faɗin, “Waye?” Idonta kir! A kansa, nan take tsoro ya kamata ta zubar da duk abinda ke hannunta, ta kwarma ihu. A lokacin ne mai gadi ya zo ya na kwankwasa mata kofa, wanda ya yi dai dai da lokacin da shu'umin ya zaro wuƙa ya dora a maƙoshinta ya ce, "Me Malam Muttaqa ya yi maki kika sa mijinki ya kulle shi? Malam Muttaƙa mutumin kirki ne yana ɗaya daga cikin mutanen da suka saka ni a turba na gari, amma saboda makirci irin naki kika ƙulla masa Sharri zaiyi baɗala dake? Na baki zuwa gobe kije caji ofis ki wanke shi, idan ba haka ba, billahil lazi, sai wannan wuƙar ta sha Jininki, kuma in tona maki asiri a wajen mijinki."
Da shu'umin ya gama razana Ramla, Sai ya haura ta taga, ita kuma ta yi sauri ta rufe tagan, ta fara hada kayanta. Ta fito janye da jaka ta kulle kofa ta nufi wajen motarta. Mai gadi ya rufa mata baya yana tambayar inda za ta je, sai da ta shiga cikin mota ta zauna Sannan ta ce a ranta, ‘Ina ganin ɗaliban Malam Muttaƙa ne ke son ganin bayana, tun lokacin da aka rufe shi, sakamakon ƙaryar keta mini haddi da nayi masa, ake yi mini barazanar daukan rai.