SUN KASHE TA

CHAPTER 8 KANWA UWAR GAMI

by @hassanahunkuyi

BABI NA TAKWAS

GIDAN HAJIYA BARA'ATU

Babban falo ne mai ɗauke da mahaukatun kujeru, a tsakiyar falon, kayayyaki ne bajabaja birjik ko ina. Ba wasu kaya ba ne sai haja ta sayarwa dangin kayan mata, kayan kwalliya na mata, turaruka masu tsada, ga takalma, atamfofi; lesuka, shadda da sauransu. Kai har da su kayan maye.

A zaune bisa kujera wata hamshaƙiyar mace ce kyaukyawa mai matsakaicin tsawo, tana da ƙiba mai suna Hajiya Bara'atu. Za ta kai kusan shekaru hamsin a doron duniya. Hajiya Bara'atu ta yi suna a kan wannan sana'a tata na siye da siyarwa musamman kayan ɗa'a a faɗin ƙasar nan. To amma kusan tsuntsu biyu ko uku take jifa da wannan sana'ar.

A shekarun baya, tafi mayar da hankali wajen safarar mata zuwa ƙashashen waje inda a ke koya masu karuwanci. Yadda ta ke yi har take samun matan da take safarar da su a lokacin shi ne, ƙyauyaku ta ke bi, ta samu masu rangwamen gata da marayu ta kwaɗaitar da su da abin duniya har ta rinjaye su su biyota birni daga nan sai ta wasge da su.

Haƙiƙa, ita tsohuwar mai laifi ce kasancewar ta sanadinta wata yarinya ta ɓace har yau ba a San inda take ba. Wannan dalilin ya sa iyayen yarinyar suka haɗa ta da hukuma. Ban da haka kuma akwai da dama matan da suka rasa rayukansu a sanadin fita da su ƙasashen da ke maƙwafta da Najeriya, masu sa'ar cikinsu kan dawo da mugayen cututtukan da suka ɗauko sakamakon yin karuwanci. Yanzu haka nemanta ake yi ruwa a jallo. Dalilin haka ta bar kowa da komai da duk tsabar dukiyarta ta yo hijira zuwa Kaduna.

A Kadunan ta shahara a fannin huɗɗa da manyan mata, mata masu sukuni masu ƙumbar susa. Haƙiƙa ta yi ƙaurin suna a wajensu ta hanyar siyar da kayan ɗa'a. Yayin da ta yi suna sosai wajen mata masu shaye-shaye. Hajiya Bara'atu ba a nan kawai ta yi ƙaurin suna ba, ta shahara wajen tara matan banza a sheƙe aya. Ba ta jin tsoron Allah balle kunyar zubar da girmanta wajen shashanci da ƙananun mata.

A da, ita kaɗai ke sana'ar siyar da kayan ɗa'a, inda take kaiwa gida gida, da ta fara samun kuɗi sosai, sai ta ke haɗawa da kayan maye, da shaiɗan ya buɗe mata hanya sai ta fara haɗawa da kawalci. Tafi tafi sai ta fara zuwa Dubai tana shigo da kayan kwalliyar mata. A yanzu haka tana da manyan shaguna a manyan garuruwan Najeriya wanda ta wakilta wasu matan suna yi mata hidima.

A tsakkiyar Falon, kusa da Hajiya Bara'atu, wata matashiya ce, kyakkyawa baƙa mai suna Zeenah. Zeenah za ta kai shekara talatin da wani abu. 'yar asalin ƙaramar hukumar Ikara ce da ke jahar Kaduna. Sun daɗe tare da Hajiya Bara'atu, ita kuma nata ƙaddarar shi ne, auren dole za a yi mata, ta falle ta shigo uwa duniya, sun haɗu da Hajiya Bara'atu ne a bakin titi inda ta ga Zeenah da ƙullin kaya a ɗan kwali tana gudu.

A nan Hajiyar ta ci burki da motarta, har ta ɗan gogi Zeenah, daga ƙarshe dai Hajiya Bara'atu ta kai ta asibiti. Bayan an sallami Zeenah sai Hajiya Bara'atu ta taho da ita gidanta, wannan shi ne sanadin haɗuwarsu da har yanzu ba ta taɓa zuwa Ikara ba, balle iyayenta su san inda take, da halin da take ciki.

Hajiya Bara'atu ta gyara zamanta haɗi da kafa bututun shisha a bakinta ta ce da Zeenah. "Haba, Zeenah. Kin faye nawa da rashin kazar-kazar, ki yi sauri ki haɗa masu kayan mana kin san fa Hajiya Tani ba ta son jira, Abuja za ta wuce yanzu."

"Hajiya, na haɗa komai da komai, kayan matan ne kawai ya rage don ban san na dubu nawa za a haɗa mata ba." Hajiya Bara'atu ta ɗauko wayarta ta zaƙulo hirarta da Hajiya Tani ta shiga faɗawa Zeenah abubuwan da za ta harhaɗa.

Bayan Zeenah ta haɗa komai sai ta ɗauka ta fita zuwa waje inda direban Hajiya Tani ke jira. Ita kuma Hajiya Bara'atu ta ci gaba da zuƙar shishanta. A haka Zeenah ta dawo ta risketa. Ko kafin ta zauna Hajiyar ta ce. "Kunyi waya ne da Janet?"

"Eh, mun yi waya ɗazu, ta ce sun ɗan sami matsala a hanyar shiga ƙasar Niger, jami'an NDLEA Sun yi awon gaba da wasu daga cikin magungunan, amma ta wuce da mafi yawan daga cikinsu. Ta ce ba ta samu Mallam Bara'u ba. Amma an ba ta tabbacin kila gobe ya dawo. Ta ce kuma na faɗa maki ta nemi wayarki ba ta shiga ba amma ta turo maki saƙo."

Hajiya Bara'atu ta ture shishan waje ɗaya ta ce, "Zeenah je ki boyis kwatas ki ce Rayyanu ya je ya kira mini Sajida yanzun nan." Har Zeenah ta kai ƙofar falo, ta ji Hajiya Bara'atu na faɗin, "Ko kuma dawo kawai ka da ki kira shi, sai anjima zan kirata a waya."

Zeenah ta dawo ta haɗa gaba ɗaya kayayyakin da aka barbaza a tsakar falo, ta zuba na zubawa a jaka wasu a kwali, wasu a Ghana most go ta ɗauka ta kai sama. A lokacin da ta dawo ne Hajiya Bara'atu ke faɗin. "Wai kuwa ko kun ji ana cigiyar Surayya ko a (social media) kafar sa da zumunta?"

"Hmmm, Wallahi Hajiya har yanzu ban ji ko sau ɗaya ana cigiyar danginta ko wani nata ba, kai ina kyautata zaton tuni fa an yi jana'idarta an rufe babinta."

Hajiya Bara'atu ta yi ɗan shiru kafin ta ce, "Ai sai dai iyayenta su haifi wata ba Surayya ba, ni Hajiya Bara'atu, ni ce za ta yiwa tonon silili? Ni ce za ta turo wa wata ƙazamiyar Malama don ta yi mini wa'azi? Wallahi ba a yi matar da za ta shiga hurumina na ƙyaleta ba. Abu ɗaya nafi buƙata yanzu, son sanin wacce ta ba wayata, ba ma wayar ce abin damuwa ba irin memorin cikin wayar, shin ko za ki iya tuna sunan wacce taba ajiyar wayar?"

Zeenah ta yi saurin girgiza kai, "Ai har ta mutu ba ta ambaci sunan kowa ba, ni dama shawarar da zan ba ki Hajiya ita ce, mai zai hana a je can gidan da ta zauna haya wato gidan 'yan makaranta a bincika kayanta, don na san ba za a rasa wani shaidar da za mu samu kafar kama duk ma wanda ta ba wayarki ba, Hajiya idan asirinmu ya tonu sai na fi kowa muzanta…”

Hajiya Bara'atu ta katseta, "Sannu 'yar albarka, kin san Allah? Abin da yake raina ke nan, shi ya sa nake son ganin Sajida, ita ce zan sa aikin leƙen asiri gidan 'yan makaranta. Ko dubu nawa zan kashe sai mun sami ɗakin haya a gidan. Koma ki kira mun Rayyanu ku zo tare."

**********

"Assalamu alaikum." Sajida ta katse Hajiya Bara'atu. "Yawwa Sajida, har kin iso? Zauna mana kamar wata baƙuwa." Sajida ta zauna tana murmushi. "Hajiya barka da war haka. Rayyanu ya ce ki na nemana ruwa a jallo, Allah ya sa ba laifi na yi ba."

"Haba, wanne laifin za ki yi mini Sajida? Ai ke bakya laifi, yanzu ma wani aiki zan sanyaki, wato farauta za ki fita zuwa shahararren gidan hayan nan mai suna gidan 'yan makaranta, ai kina da labarin shaharar gidan wajen aje gogaggun ma'aikatan Gwamnati da 'yan makaranta ko?"

Sajida ta gyaɗa kai tana murmushi, ta san farautar da za ta yo wa Hajiyar. Hajiya Bara'atu ta ce, "Yanzu wa kika bari a shagon? Don na san Kubra ba ta dawo ba."

"Ban bar kowa ba."

"OK, to ba ni mabuɗin shagon, domin za a yi kwana biyu ba a buɗe ba, yanzu za ku je da Rayyanu direba, zuwa gidan 'yan makaranta, za ki kama haya a gidan, duk runtsi ki ce kina son ɗakin da Surayya Mustafa ta ke zaune ne, idan kin samu sa'ar shiga ɗakin, za ki ga kayanta, to ki duba komai a nutse ko za ki ga waya, idan babu, to ki lacce kayan a hankali za ki ga memori, shi kawai nake buƙata a cikin kayan nata. Idan ma baki gani ba to ki tambayi mutanen gidan ko ta ba su ajiya, ta dai ce wai ta ba ƙawarta ajiya ne."

"Surayya Mustafa?" Sajida ta maimata cike da ɗaure kai, ita ta zaci aikin kawo matan da ta saba ne za ta yi, sai ta ji saɓanin haka, to wace ce Surayya Mustafa? Wanne matsayi ta taka a wajen Hajiya Bara'atu har da za ta ɗauke mata waya?'

"Sajida, ka da ma ki matsama kanki wajen son sani wace ce Surayya. Amsar kawai ba ki santa ba, ki je ki yi abin da na ummurce ki, ba na son a sami akasi, duk wani baƙon abu da kika gani a gidan ki yi mini waya. Yanzu tukuna ina mabuɗin motarki?" Sajida ta miƙa mata, "Yawwa to ba na son ki nuna ke wata ce, Rayyanu zai kai ki yanzu a mota.”

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, Rayyanu ya sauke Sajida a ƙofar gidan 'yan makaranta. Suka ƙwankwasa, baba mai gadi ya leƙo bayan sun gaisa sun faɗa masa ƙudurinsu na son ganin Hajiya Ma'u, ya je ya yi masu iso suka shiga katafaren falonta. Zaman minti biyar suka yi sannan Hajiya Ma'u ta fito tare da wata budurwa.

Bayan gaisuwa suka faɗa ma ta buƙatarsu. Hajiya Ma'u ta ce, "Nan gidan haya ne na mata, ba ma ba da haya ga namiji ko mata da miji... "

"Mun san da haka" Rayyanu ya katseta. Da ma ga wacce ke son ɗakin haya nan." ya nuna Sajida. Sajida ta yi saurin faɗin, "Eh, ni ce nake so Hajiya, fatan ba zan taka miya ba, ba na son zama ko ina idan ba a gidan nan ba saboda tsaronsa da tsaftarsa da ake ban labari. Fatan zan dace."

Hajiya Ma'u ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Gaskiya kin taki sa'a kuwa, don akwai wani ɗaki a yanzu haka babu kowa a ciki, to amma kusan an kama sai idan za ki biya kuɗin hayan shekara don wacce take son ɗakin ba ta da kuɗin da za ta iya biya a shekara. Sanaya ɗauko littafi ki shigar da bayananta." ta ce da 'yar budurwar ɗiyarta.

Sanaya, ta ɗauko wata ƙatuwar littafi ta buɗe haɗi da ɗora biro, "Ya sunanki?" Ta tambayi Sajida.

"Sajida Ningi."

"Shekaru fa?”

"Arba'in da... Arba'in dai-dai"

"A ina kike Aiki?”

"Hmm."

"A'a, ita ba ma'aikaciya bace, 'yar Kasuwa ce, zuwa za ta yi ta dunga komawa can inda take kasuwancinta." inji Rayyanu.

"Eh, ni 'yar kasuwa ce, na zo Kaduna yin wani cinikayya ne, da ma ina jin labarin gidan nan a bakin ƙawata Surayya Mustafa, na yi ma ta alƙawarin duk ranar da na zo Kaduna a nan gidan zan kama haya."

Sanaya ta kalli Hajiya Ma'u, sai Hajiyar ta kalli Sajida ta ce, "To ai ɗakin da za ki zauna a nan Surayya ta zauna tare da wata ƙawarta Izzatu. Ita ma Izzatun ta tashi shekaran jiya." Sajida ta yi saurin faɗin, "Eh, Surayya ta faɗa mini dama ko na zo ba zan same ta ba, ta yi wata yar tafiya ne."

Bayan an gama duk abin da ya dace, sun biya kuɗin hayar, sai Rayyanu ya koma ita kuma aka kai ta sama, ɗaki mai lamba 22. Sajida ta zauna shiru tana son tuno ko ta taɓa arangama da Surayya Mustafa a gidan Hajiya Bara'atu. Take ta ji wani abu mai kama da ƙunci ne ko kuma nadama ne oho? Amma dai sam ba ta ji daɗin zuwa wannan waje ba, ba ta san wane irin hatsari aikin da Hajiya ta sakata yake da shi ba.

Sajida, shekarunta arba'in, baƙa ce amma ta zama fara da taimakon shafeshafe, ba wata kyakkyawa ba ce sosai, tana ɗaya daga cikin ma'aikatan da Hajiya Bara'atu ta ɗauka masu lura ma ta da shagunanta. Sajida, ta hannun damar Hajiya ce sosai, domin tana yi mata kawalcin mata kuma tana samun ciniki Sosai ta shagonta.

Sajida, ta taso a gidansu marainiya ce, ba uwa ba uba sai kakanni. Ta taso a wajen kakarta ta wajen uwa, kakar ke mata komai na buƙatun rayuwa. Hatta makarantar boko, kakarta ce ta sanyata. Da ta gama firamare ta kai ta makarantar Kwana, anan tarbiyyar Sajida ta fara lalacewa.

Tana ajin ƙarshe a sakandare, a wani hutu da aka yi masu sai ta yiwa kakarta ƙaryar ance, su ba za su je hutun gida ba, za su ci gaba da karatu ne saboda zuwan jarabawa. Ai kuwa kakarta ta yarda da wannan batu sakamakon ta je gidan ne da saurayinta a cewar yana ɗaya daga cikin malamansu. Suka taru suka yi wa kakarta daɗin baki har ta amince ba tare da wani shakka ba.

A wannan hutun, Sajida a gidan saurayinta ta ƙarar da shi. Ta koma makaranta da guzurin ɗan saƙo wato ciki, labarin samun cikin Sajida ya haifar ma da kakarta ciwon hawan jini. Daga ƙarshe ta kwanta dama. Ko da Sajida ta dawo gida, gaba ɗaya dangin uwa da na uba suka juya mata baya. ƙarshe suka koreta ta shiga uwa duniya. Shi ma saurayin korar kare ya yi ma ta da ya fahinci za ta ɗora masa nauyi da jidalin zama uba, alhali bai shirya amsa sunan baba ba.

Wahala da damuwa suka taimaka cikin ya zube. Maimakon ta koma gida ta natsu. A'a sai ta sami aiki a wani gidan dafa abinci tana masu wanke wanke, tafi tafi ta samu ƙarin girma sakamakon kyau da gogewar da ta yi, sai aka mayar do da ita mai miƙa abinci idan an buƙata.

A nan suka haɗu da Hajiya Bara'atu, ta je cin abinci, bayan ta gama ta biya kuɗi, Sajidan ta miƙa hannu za ta amsa sai Hajiyar ta riƙe hannunta haɗi da ƙura ma ta ido. Tun daga wannan rana suka ƙulla zumuncin shaiɗan. Mafari kenan da Sajida ta bar aikin a gidan dafa abinci ta dawo ƙarƙashin iko da mulkin Hajiya Bara'atu... Sajida, ta datse tunanin da ta ke yi ta fara

dube-duben cikin ɗakin da Surayya ta taɓa zama.