Chapter 5&6
MANUFA
NA
AMINA ABUBAKAR YANDOMA
(Meenat A Yandoma)
ArewaBooks:- Meenat_A_Yandoma
Wattpad:- Meenat_A_Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFIN MANUFA LITTAFIN KUƊI NE AKAN NAIRA 500 KACAL! ZA KI TURO KUDIN TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 2294023532 AMINA ABUBAKAR U.B.A BANK. KO KATIN MTN NA 500 TA WANNAN NUMBER *** SAI KI TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER ****
*PAGE 5️⃣&6️⃣*
... Haka Motar ta rika mirginawa cikin ramin. Wani dutse ta buga ya Tarbeta amma duk da haka mutanen cikinta basu san inda kansu yake ba. Asubar farko mutanen dake giftawa ta wurin ne suka lura da motar dake gaf da faɗawa cikin ramin sai dai dutsen ne ya hana ta faɗawa. Ba tare da bata lokaci ba Suka kira ma'aikata aka fito da motar ba ƙarami mamaki suka yi ba ganin mutane biyu mace da namiji sunyi jina-jina Kai tsaye asibiti suka wuce dasu.
Wayoyinsu duk sun farfashe sai dai aka cire Sim card din Yazid aka mayar a wata waya, lambar da yayi sebin da HAJIYA ita aka kira. Bugu ɗaya taɗauka. Jin abinda jami'an tsaron ke faɗa mata a zabure ta Mike tsaye tare da sakin wayar.
"Lafiyarki kuwa"?.
"Alhaji Yazid sunyi hatsari yanzu haka suna asibiti."
"Subhanallahi! Gaggauta shiryawa muje."
Ko da suka isa asibiti a can suka tarar da mahaifan Zinatu.
Mahaifiyar Zinatu kuka take ta kar ranta zai Fita ganin halin da ɗiyarta ke ciki.
Da ƙyar ma aikata Suka samu suka rabosu da wurin saboda ba a so a riƙa hayaniya.
Kwance suke saman gadajen su dake gaf da juna! Zinatu ce ta fara farkawa saurin me da idanunta tayi ta rufe tare da ɗago hannun ta dake sanye da kalula ta dafe goshinta. Ta ɗauki kimanin mintuna biyar kafin ta sake buɗe idanunta. Da mamaki take kallon inda suke domin dai ta lura ba a gida suke ba. Gefen ta ta kalla nan tayi tozali da Yazid dake kwance gefe. Ras! Gabata ya yanke ya faɗi a gigice ta miƙe zaune...
...Jarumtarta ta tattara wuri ɗaya tare da tunkarar mutumin da bata dan waye ba.
Tamkar wadda kwai ya fashe mawa a ciki haka take tafiya. Hannun ta ta miƙa da nufin juwuyo dashi sai dai mi? Kafin hannun ta ya sauka jikin shi bat! Ya bace. kafaɗarta taji an dafa, kyarma jikin ta ya ɗauka hannun ta kama tare da juwuyowa. Daskarewa tayi tare da buɗe baki zata saki ihu. Rufe wa bakin yayi ta kasa ihun face kallo shi da take.
Tsaye yake zaman iska jikin shi farare kaya ne Tamkar fatalwa idanunshi sun kumbura su yi jajur ga wani gashi daya zubo a gefen fuskar shi.
Kyalkyacewa yayi da dariya tare da nuna ta da yatsa. Fizgota aka yi sai gata a gaban shi. "Latifaaa! Guduna zaki yi? Tun da ki ke kin taba jin inda mata ke gudun mijin ta? In kin guje nI zaki guji abinda muka haifa ne? Latifa kinyi kuskuren aikata abinda kika aikata, ba a yi mani haka domin ni ba kanwar lasa bane. Kina nufin bayan kudin sadakin da kika ci yanzu ma wani aure ki ka yi"?.
Ya ƙarasa maganar tare a fusace.
"waye kai? A ina na san ka"?.
Ta fizgo maganar da ƙyar.
Babbakewa yayi da mahaukaci yar dariyar da ta hadda sama gidan girgiza.
"Ba shakka bil adama baki da amana! In kin kasa tunawa dani juya baya ki ki gani."
Da ƙarfin tsiya aka juyarda ita.
Ƙatuwar mage ta gani tsaye a gaba ta tana rarraba ido.
"Abinda ki ka haifa ma kina nufin kin manta dashi"?.
Saurin rufe idanunta tayi Allah ya bata sa a ta kwala ihun da yayi sanadin farkawa Latif ya fito a guje.
Tsaye yaga ta Tamkar an dasa ta.
"Latifa Lafiyarki kuwa? Mi ya fiddoki cikin daren nan?"?.
"Aljanu Latif, ka raba i da gidan nan in ba haka ba zasu zautani."
"Aljanu kuma ya aka yi ni ban gansu ba. Kawai firgita ce kika yi zo mu koma ciki."
Ƙiri-ƙiri haka ta Latif ya nuna mata gigin barci ne tayi alhakln ita tasan idonta biyu a zahiri ta gani. Kasa komawa barci tayi har gari ya waye tana zaune.
Da kyar ta hada masu kalaci da abu yayi motsi zata firgita ta kwala a Latif kira.
Tun abun na bashi haushi har ta koma bashi dariya. Ganin a tsorace take ya saka shi zama gidan bai fita ba har azahar.
Kiran da aka yi mashi na gaggawa ne ya saka shi fita ba dan Latifa taso ba.
Zaune take cikin gidan taji murya yara.
Miƙewa tayi domin tasan gidan a kulle yake. Bata ga kowa ba dan Haka ɗakin ta sake komawa tare da jin faɗuwar gaba.
Bugun ƙofar gidan ake Tamkar za a karya ta.
Jiki ba kwari ta nufi ƙofar tare da buɗewa.
Yaro ne ɗan kimanin shekaru uku tsaye da robar bara.
"Iya ta ki taimaka mani da sadakar ruwa."
"shigo daga ciki ɗan malam."
Bayan ta ɗebo ruwan umurtar yaron tayi ya matso ya amsa, daga inda yake tsaye a bakin Get sai gani tayi ya miƙo hannu luuu ya nufi inda take. Watsar da ruwan tayi ta shige ɗaki tare da maido ƙofa tana haki.
Wayar ta taji ta fara ruri alamun kira na shigowa.
Hannu ta kai ta ɗauki wayar. Baƙuwar Number ta gani daukar kiran tayi amma yaki daukuwa, tayi ya kai sau uku sannan ya dauki.
Wata irin hayaniya me razanarwa taji ana yi mata a kunne. Da sauri ta ajiye wayar gabatan ta na dukkan uku-uku.
"Shine kika barar da ruwan bayan bani zani sha ba ɗan ki nazo in amsar mawa."
Almajirin dake gefen ta tsaye ya faɗa.
Idanu ta fiddo waje tare da dafe kirji!
Ta fara yin baya-baya har sai da ta dangane da bango. Rarrabuwa Almajirin ya riƙayi har sai da ya cika ɗakin. Dariya suka kece da ita tare da nuna ta da hannu.
Hannun jinjiri taji ya saƙalo mata wuya tare da kira.
"Mamaaa...
...Fitilar dake saman Bedside ta kai hannu da nufin ɗauka ji tayi an fizgeta tare da daka mata tsawar da ta tilasta mata toshe kunne.
"Yaro bai san wuta ba sai ya taka. Yarinya kina ƙoƙarin shiga gonar da ba taki ba, tabbas kin ciri tura da ban gama dake ba har nazo yi maki gargaɗi. Domin ire-irenki na kashe su fi a ƙirga. Na lura kina so ki rasa rayuwar ki ta hanyar shisshigema Mahir da ki ke yi. Kada ki bari mu sake haɗuwa ta biyu domin bani da kyau bani da imani in da ya bi ma ba bi ba. Ki rabu da Mahir ko kiyi ta rayuwar ki. Babzo domin in cutar dake ba zuwa nayi domin in yi maki gargaɗi na ƙarshe Mahir nawa ne ni ɗaya, in kunne ya ji jiki ya tsira. "
A na kaiwa nan taji tsit! Doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da laluba Fitilar da aka fizge daga hannu ta.
Can gefe ta jiyota. Babu alamun tsoro ta kunna Fitilar tare da haskawa amma wayam babu komi.
Murmushin da bata san dalili shi ba ya kubce mata.
" Mutum ko aljan bai isa ya rabani da soyayya Mahir ba, duk wata ba razana bani jinta. idanuna sun rufe a ƙaunar Mahir."
Tana kaiwa nan addu'a tayi ta mayar da kanta ta kwanta.
Ko da gari ya waye Junaid ta umurtar daya kira me aiki a maida mata kwayeyen ɗakinta.
" Ke kuma mi ya kashe maki su lokaci ɗaya ko Nepa ce tayi maki ɓarna"?.
"Momi ni dai na farka ne kawai na ga sun mutu."
Da kanshi ya mayar mata da kwayeyen tare da Zama a gefen gado.
"Aminatu!"
Dago kanta tayi domin tasan magana me muhimmanci ce zasu yi.
"Minah mi yasa komi zanyi bani burgeki baki ganin duk wata soyayya da nike nuna maki. Ki sani ni ɗan uwanki ne duk wanda zai nuna maki so sai dai ya biyo baya na."
"Banda Mahir."
"Waye Mahir kuma?
Tsuru-tsuru tayi domin bata yi tsammani maganar ta fito fili ba.
" Dake Nike magana waye Mahir"?.
Ya ƙarasa maganar tare da daka mata tsawa.
"Bafa aure na ka ke ba da zaka saka mani ido akan al'amura na."
"Minah ni ki ke Fadama haka"?.
"Junaid bani son tashin hankali ka fitar mani a ɗaki."
"Zan fita Minah amma ki sani ban taba tunani zan iya kisa ba sai a kanki. Duk saurayi da na gani tare dake zan iya aika shi inda ba a dawowa."
A fusace ya fice ya bar ɗakin.
A gurguje ta shirya tare da saukowa falon.
"Uwata ina zuwa naga kin shirya"?.
"Momi gidansu Sady zanje in duba ta bata jin dadi."
"OK amma ki sani tare da Driver zaku tafi kuma kada ki daɗe."
"to Momi."
Kamar jira yake suna tafiya a guje ya ja motar shi ya bisu.
Ganin Driven yayi hanya su Sady ya sakaya ta sanar dashi unguwar da zata je.
Kai tsaye gidansu Mahir suka nufa ba tare da sanin Junaid Yana bin su a baya ba.
Bakin hanya ya ajeta ta shige cikin lungu su Mahir. Da sauri Junaid yabi baya ta.
Zaune ta iskeshi saman wani dutse. Farin ciki taji ya ɗarsu a zuciyar ta.
"Mahir!"
Ta Kira sunanshi cikin sanyin murya.
Ɗagowa yayi ya kalle ta tare da mayar da kanshi ƙasa ba tare da ya tanka ba.
"Ow! Kice saboda wannan miskinin ne ki ke wulakanta soyayya ta? Yau zan tabbatar maki da cewa zan iya yin komi dan ganin na mallake ki."
Yana rufe bakin shi shaƙar Mahir yayi tare da haɗashi da bango ya maƙure...
Meenat
***