SUN KASHE TA

CHAPTER 9 KIFI NA GANINKA MAI JAR KOMA

by @hassanahunkuyi


🗡️🩸SUN KASHE TA🩸🗡️


©️ Hassana Abdullahi Hunkuyi


         JAN HANKALI

Sunayen mutane dana garuruwan da na yi amfani da su a cikin wannan labarin ba na yi amfani da su don cin zarafi ko kuma don cin mutuncin wani ko wata bane.


BABI NA TARA

GIDAN ‘YAN MAKARANTA

Ranar Talata misalin ƙarfe biyar na yamma, Hadiza ta faka motarta a bakin ƙofar gidan 'yan makaranta. Ta kashe motar, ta fito ta ƙwanƙwasa babbar ƙofar, amma babu wanda ya zo ya buɗe, don haka ta tura ta shiga. Kai tsaye ta nufi ƙofar wani babban falo, wato ɓangaren Hajiya Ma'u, to amma kafin ta isa, ta yi kiciɓis da Baba mai gadi shi da Sajida sun sakko daga saman bene. 

Hadiza ta ja ta tsaya har suka ƙarasa isowa gareta, "Baba barka da yamma." Ta ce da Mai gadi. Cikin girmamawa kamar yadda ta gaiahe da shi, haka ya amsa mata, don ya ga tasha bambam da sauran matan da kan zo gates-gatse su na gaishe shi. 

Hadiza sanye take da kayan mutunci, doguwar baƙar riga ce a jikinta, ta ɗan rufe kanta da siririn mayafi. Hannunta riƙe da waya. Saɓanin Sajida da ke sanye da ɗamanmun kaya, riga da siket kai babu ɗan kwali. Mai gadi ya ce, "Barkan ki dai Hajiya, wa kike nema?"

"Na zo wajen mai nan gidan ne."

"To, ai kuwa ta ɗan je anguwa, amma ina ganin ƙila ba za ta daɗe ba, sai ki jira ta."

"Ɗakin haya kike nema? Da sai ki zo kawai mu zauna tare babu kwabonki." Sajida ta faɗi ta na kallon Hadiza a kaikaice. Hadiza ta yi murmushi, "Na gode da karramawa, to amma ba haya na zo nema ba. Na zo wajen wata ƙawata ce."

Mai gadi ya yi dariya, "Ai ba Sai kin ga Hajiya ba, kawai faɗa mini wace ce ƙawar taki, yanzu sai in binciko maki ita. Koma ba ni ba, duk wanda kika aika zai kira maki koma wace ce idan har ba ki so ki shiga."

"Wajen Surayya Mustafa na zo." In ji Hadiza.

"Surayya Mustafa?" Sajida ta maimata sunan, fuska a ɗan ɗaure. "Eh, Surayya Mustafa nake nema, Allah ya sa tana kusa. "Inji Hadiza ta faɗi tana naƙaltar fuskar mai gadi.

Mai gadi ya yi gyaran murya, "A gaskiya Surayya Mustafa ba ta dawo ba." Ya juya ɓarayin Sajida ya nunata da hannu ya ce, "kin ga wannan matar? To ita ma Surayyan take jira ta dawo, kin ga kun yi biyu ke nan..."

Cikin sauri Sajida ta katse shi, "A'a, ni ba ita nake jira ba, kawai da ma na taɓa faɗa ma ta duk lokacin da na zo Kaduna harkokina a nan zan sauka don ta sha ba ni labarin gidan 'yan makaranta, shi ya sa na ji ina sha'awar zama ko na 'yan watanni ne."

Hakan da ta faɗa sai Hadiza ta ji tana son zama a gidan don ta hango buƙatarsu ta kusa biya, kuma dama ai abin nema suke biɗa, tunda kuwa marubuciya ta haifi biro da takarda sai a yi ta rubutu. 

Hadiza ta ce tana kallon Sajida, "Ashe kema ƙawarki ce? Allah sarki Surayya Mustafa, ƙawallinmu ke nan, akwai ta da kawaici, yanzu dai da ke zan kama ƙafar ganinta, don Allah yaushe za ta dawo? Zan sami ganinta a yau kuwa?" Baba mai gadi ne ya ba ta amsa, "A gaskiya ba ta kusa, ta yi tafiya yau kusan sati biyu har yanzu ba ta dawo ba."

"To, baba ka na ganin yaushe ne kuke sanya ran dawowar nata?" Hadiza ta faɗi. "Gaskiya ba mu sani ba. Kawai dai muna jiran gawon shanu ne." Sajida ta faɗi tana mai nace kallon Hadiza. 

Hadiza ta ce tana kallon baba mai gadi, "Mene ne lambar ɗakinta?”

"Ki na nufin Surayya Mustafa? lamba 22 na sama. Amma a yanzu ni ce a ɗakin." inji Sajida. "OK, to ni zan tafi, amma idan na dawo zan same ki?”

"Eh, to ko don ke na ƙara adadin kwanakin da zan yi, a da na ce idan na yi wata guda zan yi balaguro, amma tunda na yi sabuwar ƙawa zan... "

"Ya sunanki to?" Hadiza ta katseta. 

"Ni sunana Sajida Ningi. Duk lokacin da kika zo za ki sameni, idan ma ba ki sameni ba ki yi ma baba mai gadi magana." Suka yi musanyan murmushi yayin da mai gadi ya bi su da na shi murmushin yana faɗin. "Mata ho! Sarakan zumunci, yanzu fa shi ke nan zumunci ya ƙullu."

Hadiza ta tafi, tabar baba mai gadi da Sajida a ƙofar gida su na ɗaga mata hannu. A nan suka tsaya su na tattauna halin wasu 'yan hayan, da idan za su yi tafiya ba sa faɗawa mai gidansu balle abokan zamansu. 

Baba mai gadi, ya ce yana duban Sajida, "Ina mamakin inda wannnan ƙawa taku ta je tsawon sati biyu babu ko waiwaiyen kayanta, da alamu Surayya ba ta faɗa ma Izzatu inda za ta je ba, Hajiya Ma'u kuwa ta ce tunda Surayya ba ta faɗawa kowa, babu mai barin kayanta a gidan. Mafari ke nan da Izzatu ta tafi da su."

"Haba, shi ya sa banga ko tsinke a ɗakin da Surayya ta zauna ba, ashe abokiyar zaman ta ce ta tafi da komai nata?"

"Ai kuwa babu abin da aka bari na Surayya a gidan nan, duk Izzatu ta tafi da su, amma tabar mini wasiƙa cewa idan ta dawo na ba ta za ta ga adireshin inda ta koma."

"Iko sai Allah, to tunda ni ƙawarta ce, gani kuma zaune a ɗakin da ta zauna, ka ba ni wasiƙar na ajiye mana, ƙila lokacin da za ta dawo ba ka nan."

"Eh, kin kuwa kawo shawara mai kyau, ka da ma na je na yar. Tsaya ina zuwa." Ya shiga ɗan dakinsa ya fito da ambulan, tsoho mai riƙon amana, yadda aka ba shi haka ya miƙa mata yana faɗin, "Ga shi." Ta amsa tana jujjuya ambulan ɗin haɗi da latsa shi wai ko za ta ji memori a ciki, ta yi ƙaramin tsaki, ta faɗa a ranta. 'Adireshi ne kawai ashe...'

"Me ki ka ce?" Baba Mai gadi ya katseta. 

"Cewa na yi, ya batun gyaran waya? An kammala kuwa? Allah zama babu babbar waya babu daɗi, zan shiga ciki ina son zuwa wata 'yar anguwa, kafin na dawo ina son ka amso mini wayata."

Ta kawo dubu biyu ta ba shi, "Ka yi kuɗin mota." Ba ta tsaya sauraron godiyar da yake antayo ma ta ba, ta hau sama. Ko da da ta zauna a bakin gado sai tunani da son ganin Surayya Mustafa ya ɗarsu a ranta. Ta juya wasiƙar da aka ba ta, ji ta yi kamar ta buɗe ta ga me ke ciki sai kuma ta tuno da Hajiyarsu, idan ta buɗe ta ci amanarta, alhalin babu cin amanar juna a dangartakansu. Gama tuno hakan da ta yi sai ta miƙe cikin sauri ta canza shiga, ta bar gidan.