CHAPTER 10 KUDA WAJEN KWAƊAYI AKA MUTU
BABI NA GOMA
GIDAN HAJIYA BARAATU
Hajiya Bara'atu ta yi shiru tana sauraron bayanin da ke fitowa daga bakin Sajida, ba ta katse ta ba har sai da ta dasa aya haɗi da miƙa mata ambulan ɗin. Ta amsa ta na murmushi, “Haka nake sonki tawan, aikinki yana kyau don haka tunda na samu tudun dafawa, daga nan ka da ki koma gidan 'yan makaranta, kin gama aikinki da kika samo mini madafa, duk ma wacce Surayya ta ba wayata sai na zaƙulota."
"Hajiya, komawa ta ya zama tilas, ban ɗauko akwatina ba... "
"In don akwati ne, ki bar masu za ki samu mafiyinsu daga wurina"
"Ai kuwa dole ne in koma don na ba mai gadi gyaran babbar wayata... "
"What! Kin yi hauka ne? Ta ya ya za ki ba shi gyaran waya? Ke ba ki san inda ake gyarawa ba ne? Wasu mutanen ba su da amana sai sun gama yi ma mutum tonon silili kafin su maido maka da wayar."
Sajida ta yi murmushi, "Ka da ki ji komai Hajiya, ai na siye mai gadi ba zai yi mun rashin arziki ba... "
"Ji mini yarinya don Allah, ke ni fa yanzu an sha ni, da ɗan gari a kan ci gari, ai ba zan taɓa manta amanata da Surayya ta ci akan waya ba, ki je ke kika sani. Amma dai zamanki ya ƙare a gidan 'yan makaranta, akwai wani aikin da zan kuma sanya ki, ki je gobe ki zo ki sameni da ƙarfe goman safe."
Bayan tafiyar Sajida, Hajiya Bara'atu ta ɗauko shisha ta fara ja, a dai-dai lokacin da ta ke ƙoƙarin yin magana a waya. "Hello Janet, idan Zeenah tana kusa ku zo tare yanzu."
Ta aje wayar sannan ta buɗe wasiƙar da Sajida ta kawo ma ta, rubutu ne bai wuce layi ɗaya da rabi ba, ba kuma wani muhimmun abu aka rubuta ba face, “Ki zo Kaduna State University. Faculty of Education, sai ki tambayi Izzatu Bunkure, ko ki ce Izzatu 'yar ƙwalisa.”
Hajiya Bara'atu ta yi tsaki a ranta, tana mai ci gaba da nazarin yadda za ta ɓullo wa wannan sabon lamari, haƙiƙa ba ta raba ɗaya biyu, Izzatu 'yar hannun ce kuma ƙila akwai wata ƙwaƙƙwaran dangantakar da ke tsakanin su da Surayya, idan kuwa haka ne, to tabbas Izzatu na da masaniyar inda wayarta ta shiga, ƙila wayar tana wurinta, ƙila ma ta banko asirinmu...'
Sallamar Janet da Zeenah ya katse Hajiya Bara'atu daga tunanin da ta lula, ta bi su da kallon takaici ta watsar, su duka su ka zauna a kujerar kusa da ita su na kallonta.
"Amma wallahi kuna ba ni mamaki, wato har kuna samun damar yin barci alhali ga ƙalubalen da ke gabanku, kun san Allah? Sanin kanku ne saboda ku nake son asirinmu ya rufu. Kun san ina da kuɗin da idan wata guguwar tonon silili ya ta shi zan iya murƙusheta da ruwan kuɗi, A'a kuna can kun mutu lami lafiya, ni nan kun bar ni da yi maku ciwo."
"A yi haƙuri Hajiyarmu." suka haɗa baki gaba ɗaya. Hajiya Bara'atu ta bi su da harara tana faɗin, "Sajida ta zo mini da bayanin Izzatu, wacce asirinmu yake tafin hannunta." A nan ta zayyane masu komai, ta ci gaba da faɗin.
"Mece ce shawararku? Ta ya ya za a tunkari Izzatu? Na ce Sajida ta dawo gobe don aiwatar da abin da kuka tsara." Janet ta yi dariya, "Hajiya ai wannan abu mai sauƙi ne, cire wando ta kai, kawai.... Kin gane ai?" A nan su ka ƙuƙƙulla abin da za su yi game da Izzatu 'yar kwalisa.
Janet, ‘yar jahar Ogun ce, a can wani ƙauye, tana da ɗan ilmin boko wanda za a kira hana gori, ita ma dai kamar sauran ‘yan tawagar Hajiya Bara’atu ne, wato tsohuwar mai laifi ce. A lokacin da ta gama karatun koyon aikin jiyya, sai aka tura ta sanin makamar aiki a wani asibiti, son zuciya da son tara ƙyaleƙyalen duniya, ya sa aka haɗa baki da ita aka sace wata jaririya aka siyar, sai suka ce jaririyar ta mutu, jin wannan mummunar labarin ya kusan zautar da iyayen jaririyar, kasancewar sai da suka shekara ashirin kafin su samu haihuwar. Daga baya da liƙi ya ɓalle Janet ta fahimci ana nemanta, ta falle ta shiga duniya har Allah ya kawo ta Kaduna. Inda ta yi arangama da Hajiya Bara’atu a super market, a nan suka yi abota, a da Janet, ta kan kira iyayenta su gaisa amma da liyafa ta ci gaba, sai ma ta canza lambar waya ta yadda ko sun kirata ba ma za ta shiga ba.
*********
KASU, KADUNA
Tun ƙarfe biyar na yamma, Sajida ke zaune a kafteriya tana jiran fitowar Izzatu daga lacca, Sajida ba ta zauna zaman jiran Izzatu ba har sai da ta gama binciken komai game da ita, ya zuwa yanzu ta haƙƙaƙe lallai Izzatu irin tasu ce, don haka shawo kanta ba zai yi wuya ba.
Ƙarfe shida da 'yan mintuna, Izzatu ta dira a wajen cin abinci, ta zauna a kujera haɗi da ɗauko madubi ta gyara fuskanta da maiƙo ya fara ɓatawa, kana ta yi odar lemon kwalba da snacks. Ta ɗaga kwalbar ke nan idonsu ya haɗu da Sajida, sai ta sakar ma ta murmushi haɗi da isa kujerarta.
"Manya 'yan ƙwalisa, ya karatu ya jin daɗinki?”
"A ina kika san ana ce mini 'yar ƙwalisa? Ni ban taɓa ganinki ba sai yau, in ce dai lafiya? "
"Lafiyar ta kawo haka, amma gama shan lemun sai mu zanta sosai."
Izzatu ta aje kwalbar ta ce, "Ina jinki, faɗa mini a ina kika sanni?"
"Haba, ke kuwa kin faye ƙosawa da ujula to duk saurin anguwar zoma ta jira a haihu... "
Hakan sai yaba Izzatu dariya, shi ya sa ta ci gaba da shan lemunta a yangace, a kaikaice Sajida tana ma ta kallon ƙurulla. Izzatu ba ta ƙara magana ba har ta gama.
"Na gama, ja mu je?”
"Zuwa ina?"
"Ah, ina kuwa, ke nake jiran jin ta bakinki, sauri na ke yi yanzu Hajiyata za ta zo ɗauka ta.”
"To, ni sunana Sajida Ningi. Hajiyarmu ta aikoni wajenki, ita ce wacce muke taka rawa da bazarta, hamshaƙiyar mai kuɗi ce a nan garin, hamshaƙiyar 'yar kwangila ce, kuma 'yar kasuwa, sannan tana taɓa safara. Ta ce ta sha ganinki a makarantar nan, amma ta rasa yadda za a yi ta tuntubeki."
Sajida ta buɗe jakarta ta fiddo da wata 'yar ambulan ta miƙawa Izzatu. "Ga shi ta ce ki sha sweet." Izzatu ta amshi ambulan a banzance, ta jujjuya shi a wulaƙance don ta san babu wani abin ku zo ku gani a ciki.
"Ki buɗe mana ki gani, so nake ki tabbatar da Hajiyarmu ba ƙaramar ƙwaro ba ce balle ki yi tunanin ko abin hannunki ta ke nema, A'a ita bangon gishiri ce duk wanda ya dafa ta sai ya lasa. To ba ma ita ba sha ƙundun, ni ɗin nan da nake taka rawa da bazarta ba ki da abin da za ki ba ni na yaba maki." Hakan sai yaba Izzatu dariya, tana dariya tana buɗe ambulan haɗi da faɗin, "Ɗan magori wasa kanka da kanka, to ban da cika baki dai..."
Ta kasa ƙarasa abin da ta yi niyar faɗin don mamakin abin da ta gani sun zubo ƙasa daga ambulan ɗin. Daloli ta yi arangama da su ɗai-ɗai har dala ɗari biyar, ($500 US dollars). Da yake kwanyarta tana ja, nan take ta juya waɗannan daloli zuwa kuɗin Nigeria, ta ga naira dubu ɗari da tamanin da tara da dari bakwai da arba’n da takwas, (#189,748). Izzatu ta yi ɗan shiru kafin ta ce, "Ya ma kika ce Sunan Hajiyar taku?"
"Batun sanin sunanta da inda take ba su taso ba, don ta horeni da ka da na faɗa maki komai game da ita har sai kin aminta kin amsheta hannu bibiyu, to daga nan... "
"Hmmm, lallai na yarda da Hajiyar nan taku, ashe ba banza ba kike ta koɗata. Shi ke nan na gode da hidima, Fatan kin iya Hausa Sosai, don Bahaushe ya ce, yaba kyauta tukuici, ga shi ki kai ma ta ki ce na gode."
Izzatu ta taɓa ƙirjinta dai-dai wajen zuciyarta ta dunƙulo hannu ta miƙa wa Sajida ta ce, "Ki kai wa Hajiyarku." Sajida ta miƙa jakarta ta saka ma ta, sannan suka kwashe da dariya.
Sau biyu Sajida na zuwa a mabambamta lokuta, kuma ko wane lokaci da irin nau'in abin hasafin da za a kawo wa Izzatu daga Hajiya Bara'atu. A zuwan da Sajida ta yi na uku ne, ta zo ma Izzatu da wata 'yar jaka shaƙare da kayan kwalliya da su turaruka har da lesuka ɗinkakku.
Bayan Sajida ta miƙa saƙo ta ce, "Hajiyarmu ta ɗokanta da son ganinki amma sai idan ki na da lokaci, za ta aiko da mota a ɗaukeki ku gaisa." Ai kuwa itama Izzatu ta ɗokanta da son sani wace ce wannan hamshaƙiyar.
To amma wacce ƙarya za ta yi wa Ramla har ta je ta dawo ba tare da ta gane wani abu ba? Yawwa ƙaryar mutuwa za ta yi ta ce an kirata daga gida ce wa ana nemanta. "Ki ce na gode da hidima, sannan ki ce a shirye nake da mu gaisa gobe da yamma kamar yanzu." Suka yi sallama. Tun a lokacin Izzatu ta fara saƙe saƙen abin da za ta faɗa wa Ramla.
Washegari, bayan Ramla ta dire Izzatu a makaranta sai ta shirya wasiƙar ƙarya ta ba mai sayar da abinci cewa idan Ramla ta zo, ta ba ta, ta kuma faɗa ma ta, ta nemi wayarta ba ta shiga ba.
Da yamman wannan ranar, Rayyanu ya faka mota a jikin wata bishiyar da ɗalibai ke zama, Sajida ta je ta kira Izzatu suka shiga motar gaba ɗaya, da ma sun saba, saboda haka ba su yi zaman kurame ba, ko da yake, yawancin hirar, Sajida ce ke maganar, sai wani lokaci Rayyanu ya sako baki. Da haka suka isa katafaren gidan Hajiya Bara'atu.
Sun je sun iske su Janet a falo suna kallo, Yayin da Zeenah ke zuƙar shisha. Sajidan ta zauna yaraf tana faɗin, "Zauna mana 'yar ƙwalisa, ina Hajiyarmu?" Janet, ta ce cikin karne ido, su Hajiyarmu ana tsalo wanka." Ta mayar da ganinta ga Izzatu ta ce, "Lallai kin ci sunanki 'yar ƙwalisa, ko ba ita ba ce Izzatu?"
"Eh, ni ce, sannu ya gida?"
"Ki zauna mana sosai." inji Sajida, ta ci gaba, “Ba fa baƙuwa kike ba, me kike da buƙatar sha?"
"Ba na buƙatarki komai, amma dai kina iya kawo mini ruwan sanyi."
Sajida ta yi ma ta raɗa a kunni, "Ya na ga kina ɗari-ɗari? Ki ɗauki nan gidan a matsayin naki." Izzatu, ta yi murmushi, amma haka kawai a cikin zuciyarta ta ji babu daɗi, sai ta ji dama ba ta zo ba, idan kuma Ramla ta fahimci ga inda ta je fa? Me za ta ɗauketa alhali ta yi ma ta komai?